《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ Page 2

Advertisement

*ƘADDARAR RAYUWA*

Writer^Zaynab bawa

Follow on Wattapd^zeyybawa

Haske writers association💡

page 2

Takaitaccen tahirinsu

Shi dai mahaifin hafsa sunansa shine hamisu

Hamisu mahaifansa ba wasu masu karfi bane, sai dai rufin asiri irinna ubangiji, hakan suke godiya da samunsu domin idan sun fita nema zasu nemo su kawo ad'aura sannan asamu asaka abaki, hakan baya daga musu hankali domin sunada wadatar zuci Allah yabasu tawakalli kokad'an basu dauki kansu sunkai wani matsayiba,

Kuma basu kasance masu mutuwar zuciyaba, basa zama kuma basa raina sana'a komai qanqantarsa har indai zasu samu su biya buqatun kansu dana iyalansu toh Alhmdllh zasuyi buga-buga su tashi su nemo,

Hamisu su goma ne ciff wajen mahaifinsu maza bakwai mata uku, mahaifinsu sunansa malam sa'adu mahaifiyarsu hafsatu amma anfi kiranta da laraba kasancewar ranar laraba aka haifeta, hamisu shine na biyar acikinsu, babban yayansu shine zakari matansa uku da yara goma sha biyar duk cikinsu yadan fisu wadata domin har shago yake dashi akasuwa yana aunarda amfanin gona dake manomine yakanyi noma sannan idan rani yayi ya ebi amfanin yakai kasuwa, saina biyu amadu, matansa biyu dakuma y'ay'a goma, na uku jamilu yaransa tara, na hudu sabiru, na biyar hamisu, sai ta shida halima wacce yarinyar hamisu taci sunanta sai, ta bakwai hindatu itama hamisu yayi mata takwara, takwas da tara duka mazane ali da habubakar, autansu kuma ikilima,

Kowanne acikinsu yanada sana'a harda matan cikinsu ba'a rasasu da y'an qulle-qulle haka na kayan miya, haka rayuwa take tafiya musu dai kowannensu yana dan taga zawa wajan taimakon dan uwansa dayake sun kasance masu zumunci,

Koda bikine kowani abun sune suke taruwa su rufawa junansu asiri."

Mahaifiyarsu hafsa kuwa su ukune wajan mahaifansu matan babansu biyu, sunan mahaifinsu shine musa matarsa ta farko itace baba rabi'a tunda ya aurota shekara da shekaru ko 6atan wata bata ta6a yiba, sai bayan shekaru masu yawa yaqara aure ya auro sa'adatu wacce tana zuwa cikin qanqanin lokaci Allah ya azurtata da haihuwa tasamu mace suka sanya mata suna ummikursum wacce ake kiranta da ummi, sai ummusalama wacce ake kiranta da salma sai qaninsu habibu, daganan itama Allah ya tsayar matada haihuwar, malam musa shikam Alhmdllh ahakan ya godewa ubangiji,

Advertisement

Suma dai bamasu hali bane amma dake babansu mahaucine koyaya yadan samu kudi yakansai dabba yayanka ashiga kasuwa,

To zaman gidansun dai gashi ga yanda yake baza'ace komaiba domin wata rana ayi dad'i wata rana akasim haka, saboda dama shi dan adam arayuwa bazai kasance kullum cikin jin dadiba, A'a wata rana dole sai Allah ya jarabceshi, wani lokacin kuma idan zaman lpyrsu ya zagayo abun gwanin sha'awa,

Aihini matsalar dama akan sameta daga wajansu duka biyun domin daga mahaifiyarsu ummi har baba rabi babu mai hakuri cikinsu dole idan d'aya yaywa d'aya bazasu iya hakuriba sai sun tanka to daganan ake samun sa6ani, amma sukan dan dauki kwanaki ba'asamu sa6aninba kuma, haka har yaran suka girma, kowacce cikinsu tana qoqarin bawa yaran tarbiya babu kyashi aciki domin baba rabi'a tace da nakowame arziki da dukiya ba'a muguntarsu, idan har suka sami matsala to tsakaninsune amma nai ta6a yara."

Lokacinda hamisu yafara neman auran ummi batafi shekara sha huduba,

Haka har suka dai-dai aka bashi izinin turo mahaifansa,

Koda yaje gida ya sanar mahaifinsa yace yadakata zaiyi bincike, kusan kwanaki mahaifinsa bai bashi wani bayaniba baiyi qasa aguiwaba wajan qara zuwa ya tunkareshi, nisawa mahaifinsa yayi sannan yace" hamisu bawai naki taka bane amma kasan mahaifanta mahautane sannan kuma sanin kankane jinin fulani baya haduwa da mahauta,

Sunkui dakansa yayi cikin tarradadin maganarda take shirin fitowa a bakinsa tayaya mahaifinsa zai kar6i zancen,

Cikin ladabi yace" baba wannan al'adane ba addiniba baba addini bai hanamu aurensuva al'adace tahana dan Allah baba aduba wannan lamarin,

Gyada kai mahaifinsa yayi sannan yace" shikenan kaje Allah ya za6arda mafi alkhairi, sunkuida kansa yayi ya amsada amin sannan yayiwa mahaifinsa godiya yafice,

Koda babansu yayi shawara da yan uwansa wasu sun amince wasu kuwa basu aminceba, shaida musu yayi tunda shine yagani ahaka yanaso dan haka su barshi kawai ya auri kayarsa suyi masa addu'ar sanya alkhairi,

Advertisement

Haka badan wasunsu sunsoba suka amince."

Itakuwa wajan ummi bata wani samu matsala da mahaifantaba dankoda akazo neman auranta sun amince, aka sanya lokaci,

Ba'adauki lokaci mai tswoba akayi auren,

Zama lafiya sukeyi shida ita cikin aminci da kyautatawa juna,

Dafarko danginsa basu sotaba amma daga baya kyawawan halayanta yasa take zauneda kowa lpy,

Shekara biyu da auransu ta haifo diyarta mace aka sanya mata sunan mahaifiyarsa wato kakar yarinyar hafsa, ma sha Allah yayi qoqari yanemo abunda aka samu dai-dai gwargwado anyi suna, aka gama lpy alhmdllh, babanta yakan cemata hafsan wani lokaci yayinda ita kuma mahaifiyarta take 6oye sunan tana kiranta da sawwma, yarinya tataso da wayonta sam batada kuka bazama kasan da qaramar yarinya cikin gidanba har kazo kafita, idandai bawani jimawa zakai ba, saboda Allah ya zuba mata hakuri, bayn shekara biyu kuma taqara haifo yarinya aka sanya mata sunan qanwar mahaifinta sadiya suna kiranta da halima, tazarar shekara daya da rabi ta bata atsakani ta haifo wata yarinyar tata kaawai tofa! Daga nanne kuma tafara dan fuskantar matsala wajan dangin mijin wai tana haifo y'ay'a mata, aikuwa dai kunsani dama cece kuce bata qarewa wajan dangin miji, wannan yafadi nasa wancan yafadi nasa,

Cikinsu hindatuce kawai mai kareta dayake ita tanada sanyin hali, kuma itama ce masu takeyi menene aibun a haihuwar yara mata?

Ita kuma ummii Maganganunsu baya daga mata hankali saboda tasan cewa cikinda ya haifi mace shine zai haifo namiji balle itakanma ai bataga bolar y'ay'a mataba domin da akwai su kansu masu cece kucen bazata gansuba domin suma aii matane,

Itafa abunma yana bata mamaki wai ace y'a macece mai kushe d'iya mace, Allah dai yakyauta kawai amma dai tsarinfa baiyiba, ranar suna yarinya taci sunan qanwar mahaifiyarta wato ummusalma, ana kiranta da salma kamar dai qanwar mahaifiyartata."

Tadan dauki Wani lokaci kafin taqara samun wani cikin wannan cikin tun kafin ta haifeshi aka fara fadin to kardai suji, aikuwa Allah da ikonsa taqara haifo diya mace, sun tashi akai zasuyi magana hindatu tace ita ina laifinta ai ba ita yakamta kuga laifi ba,

Ai ita abunda aka bata shi take saukewa kamar ajiyane aii za'a baka ajiyar bakine kabada fari? Duka sun fahimci abunda take nufi dan haka duk takashe bakinsu babu wanda yaqara cewa komai."

Tadan dauki lokaci sosai kafinnan taqara samun ciki, shikan hamisu murna yakeyi abunaa domin ta wajansa kokadan babu matsala yanason yaransa kuma yana murna da kyautarda ubangiji yabashi, kullum addu'arsa shine Allah yasanya musu albarka,

Kuma haka ya tashi wajan neman nakansan domin cida iyalansa,

Haka rayuwa take musu yana dan sana'arsa idan lokacin rakene toh rake zai koma sara ko kuma mangoro kokuma wani abundai haka yakeyi,

Girmanda sawwma tadanyi gakuma wayo yasanya suka fara daura mata talla domin karuwar hanyar samunsu,

Suna sakaci sosai da kula da dawowarta domin idan babu ciniki sosai takan iya yin dare sosai kuma basa damuwa, da wannan sakacin har abunda yafaru yazo yafaru, duk da kasancewar babu mai kaucewa qaddararsa."

Wannan kenan

Mukowa cikin labari muga yanda rayuwarsu taci gabada tafiya."

Follow

✔️ote

Comment

Share

To be continued

Zaynab bawa

💞💕

    people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click