《ƘADDARAR RAYUWA》Page 3
Advertisement
*QADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Zaynab bawa
Follow on
Page 3
Haka rayuwa taci gabada tafiya har hafsa tagama junior secoundry school dinta, amma daga nan sai karatun ya qaqare yatsaya saboda dama can yau ajene gobe ba'ajeba,
Tana gama junior kuwa sai abun ya gagara daga nan sai aka ajiye karatun agefe, saboda rashin kudinda za'a dauki d'awainiyar karatun,
Dake yarinyace mai fahimta ta fahimci halinda suke ciki hakan yasa bata wani d'aga hankalintaba, dama da dad'e da sanyawa cikin ranta cewa wata rana dole zata bar karatunnan kodan qannenta suma su samu suyi nasu karatun."
Haka aka ajiye rayuwar karatunta agefe aka cigaba da fuskantar yanda rayuwa take zuwa."
Kamar kullum haka baba hamisu yake fita arana yayi tallah yayi buga-buga yasamo musu abunda zasu rufawa kansu asiri aranar,
Ayau kam abun yaci tura baba hamisu ya zagaya amma babu wani ciniki gashi rana tadukeshi har wani jiri-jiri yake gani badon yasoba yasamu waje haka yazauna domin hutawa yahuta tsawon minti talatin sannan yatashi yunwa yakeji sosai amma gani yakeyi bazai iya cire kudi yasiya abu yaciba saboda yasan halinda yabar iyalinsa aciki da ikon Allah cikin wasu awanni aka samu ciniki agwalumarda yake turawa abaro duka yaqare godiya yayga ubangiji yazauna yadan huta daga nan saiya dauki hanyar kasuwa yasiya musu abun buqata daganan saiya wuce gida,
Yana zama wata y'ar gindin bishiya yazauna bai dade da zama ba baccin gajiya yadaukeshi, yashari kusan 40minute yana bacci wanda ba hakan yasoba, yaso yahuta na kaman 20minute ne yakama hanyar gida saboda yabar yara da yunwa, salati yayi yamiqe ganin lokaci yadanja agurguje yayi alwala yashiga masallaci ya gabatarda sallan la'asar, ya iddar yafito yakama hanyar kasuwa, domin aunan abinci, sanda yaje shago yagama lissafi abubuwanda za'a kawo masa sannan ya sanya hannu zai dauki kud'i amma wayam kudin yace d'aukeni ahankali babu komai cikin aljihunsa, wani irin baqin ciki da tuquqin takaicine yakamashi ga dukkan alamu yana bacci aka lalume aljihunsa,
Advertisement
Hakuri yabawa mai shagon sannan yajuya yaja baronsa wani tuquqi yakeji cikin ransa lallai ya tabbata wannan duniya cike takeda rashin imani, amma idanba rashin imaniba ko kallonsa a ido kayi zaka fahimci irin talauci da wahala dayake ciki, yanayin kayan jikinsama kawai zai nuna maka irin talauci dayake ciki amma rashin imani har yakaiga anyi masa sata,
Yana tafiya yana tunani sam hankalinsa baya kan hanya sai jinsa yayi yafada cikin kwalbati dake bakin titi,
Subhanallhi kawai kakeji mutanen wajan suka dau salati, gabaki daya suka yiyo kansa taimaka masa sukayi yafito aciki yad'an kururje sanna kuma ya bugu,
Haka suka taimaka masa ya'isa zuwa famfo ya wanke jikinsa, godiya yayi musu sannan yakama hanyar gida amma rad'ad'in zuciyarsa dayakeji yafi masa na jikinsa,
Koda ya'isa qofar gida yadauki lokaci kafin ya'iya takawa ya qarasa cikin gidan da sallama,
Zama yayi can gefe mama wacce take kitchen jin shigowarsa yasanya tataso tafito ganinsa cikin wani yanayin yasa hankalinta yatashi, qarasowa tayi tana fadin baban hafsa lpy kuwa??
Kallonta yayi cikin damuwa amma yakasa furta komai, durqusawa tayi agabansa cikin nuna kulawa tafara fadin dan Allah baban hafsa kafadamin mai yake faruwa zan shiga wani halin idan kayi shiru haka,
Fitowar hindatu yasanyashi juyawa yana dubanta alokacin yaji wani hawaye ya zubo a fuskarsa, runtse ido yayi ya fidda huci sannan yadubi mama yace" ummi ban samo komaiba" ban dawo manada komaiba ummii" bansan yaya zanyi da way'annan yaranba bansan mai zan basu suciba,
Zaunawa tayi gefensa cikin yanayin kwantarda hankali tace kada ka tada hankalinka, Allah bazai hanamu abunda zamuciba,
Kada ka d'aga hankalinka kana iya qoqarinka wajan ganin ka biya mana buqatarmu, wuni zubur kakeyi cikin rana dan ganin ka nemo mana abunda zamu sanya abakinmu, iya tsawon rayuwarka jin dadinka da komai da sadaukar akanmune,
Na rana daya dan baga samuba bazamuji zafin kaba, Allah yaga zuciyarka ya aiko manada abunda zamu rufawa kanmu asiri
Advertisement
Yanzu hakama babu yunwa ajikinmu, fitarka keda wuya yaya zakari ya aiko manada shinkafa takai tiya goma, cikin amfamin gonarsa harda gero tiya uku,
Sanyi yaji sosai aransa jin cewa iyalansa sun samu abunda suka sanya acikinsu, hamdala ya dingayi yana godewa Allah sannan kuma yana godewa yaya zakari,
Miqewa tayi tadauko masa ruwa cikin kofi tamiqa masa sannan tawuce zuwa kitchen ta dauko kwanan abincinsa ta ajiye agabansa,
Sai alokacin ta lurada kayan jikinsa yanda ya kurkurje amma dayake yafara cin abinci yasanya bata tambayeshiba sanda yagama,
Tambayarshi tayi maiya faru nan yake shaida mata akan kudin cinikinsa aka kwashe yana tafiya yana tunani kuma sai yafada cikn kwalbati,
Sosai ta tausawa masa, sannan taci gabada yimasa magana akan yadaina sanya damuwa cikin ransa shi kadai dayake kallon kansa shine kawai yarage musu madogara idan kuma wani abun yasameshi wani hali yake tunanin zasu shiga?
Yanzuma haka yana raye kenan balle bbu ransa,
Tashi tayi tahada masa ruwan wanka mai zafin gaske yashiga ya duma jikinsa,
Kafin yafito tadauki kayanda yacire ta zuba cikin ruwa tafara gogawa amma kuma bbu omo dan haka tadauki kanwa tazuba cikin ruwan ta wankesu iya yanda zata iya fiddasu tashanya,
Duk wannan abunda yake faruwa sawwma tana tsaye bakin labule tana jinsu, hawaye ke zuba a idanuwanta wani irin tausayin kansune yake tsurga mata, suna cikin wani irin hali wanda yakamata dole atausaya musu,
Suna cikin halin qangin rayuwa, QADDARAR RAYUWA ta afka musu, a iya saninta tasan mahaifinta iya qoqarinsa yanayi wajan ganin ya biya buqatarsu amma abun yafi qarfinsa,
Zama tayi tana tunane-tunane tana tausayawa rayuwarsu, batasan sanda kuka ya kwace mataba hafsa tanada qarancin shekaru amma kuma tanada tunani mai zurfi, tanada hankalin gaske batada hayaniya, Allah ya sanya mata son mahaifanta da tausayinsu sosai cikin ranta,
Tana zaune ahaka har jikinta yayi sanyi bata samu tafita ko sannuda zuwa tayiwa mahaifintaba.
Shikuwa baba yana fitowa awanka ya canja kaya yafito dubansa mama tayi tana fadin ina kuma zakaje?
Zanje yiwa yaya zakari godiya!
Miqewa tayi tace kadan bari mana kahuta akira sallar magriba idan kayi zuwa isha'i saika tafi,
Baiqi tataba saboda yasan tafadi hakanne dan tanason yahuta,
Komawa yayi yanemi waje yazauna yajira har aka kira magrib aikuwa yadan samu hutu dan shima yadanji dadin jikinsa,
Alola yayi sannan yafice masallaci,
Sai alokacin sawwama tafito ad'aki, dake duhu yadan shiga yasanya mahaifiyarta bata fahimci yanda tayi kuka jikin tayi sanyi sosaiba.
Cikin gida suka zauna, suka jira dawowar mahaifinsu,
Sanda yadawo suka dan ta6a hira sannan yaran suk shiga suka kwanta itama mama suga shiga,
Kafinsu kwanta take tambayarsa cewa gobe tanason zuwa gida tagaida mahaifanta,
Amsa mata yayi da fadin Allah yakaimu goben da rai da lpy,
Zuwa yamma ko magriba saina biyo miki mudawo saboda nima na kwana biyu banje na gaidasuba,
Allah yakaimu suka fadi sannan sukayi addu'a suka kwanta bacci."
Itakuwa sawwama tadad'e batayi bacciba tana saqe-saqe cikin ranta ta yanda zata 6ullowa lamarin,
Abu dayane yakeyi mata kaikawo cikinta ranta wanda hakan kawai take ganin shine mata mafita, domin wanann lamarinsu idanba sun tashi sun nemi mafitaba rayuwarsu tana cikin hadari sosai,
Hakan tasanyawa ranta shiyasa take ganin daren yayi mata tsawo, Allah-Allah takeyi gari yawaye tagama ayyukanta tatafi aiwatarda abunda yake cikin ranta,
Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita."
To be continued
Zaynab Alabura
✔️ote
Comment
share
Follow
💞
Advertisement
- In Serial34 Chapters
Drakon the Necrolord v2
Rewrite of my novel Drakon the Necrolord. 100 thousand years ago the system apocalypse began and all of the known worlds with sentient life in the universe got merged together forming a super planet. Orcs elves humans dwarves and hundreds of other species now living on one planet. These are the memoirs of one of them. Written with the help of the AI in his head and a little help from his friends. As a note: I have tons of worldbuilding done (probably way more than needed, as that was why the rewrites took so long. Depending on the reception here I might do more stories in the same universe and/or build a wiki with all my worldbuilding stuff.
8 169 - In Serial6 Chapters
Duplicity
Follow the charming yet devious Lyman Leepsky as he and four magical creatures attempt to survive in a small town in an alternate dimension Earth, fighting off demons, debt collectors, and deep ones as they sort out their differences in this adorable slice of life magical adventure strung across two worlds! Yaaaay, friendship!Except... friendship isn't going to heal the uncurable trauma they have. No, that's way too unreasonable.-------------------------------------------------------This stories first couple chapters are pre-written over the course of three months of notes, worldbuilding, well-thought-out planning, and of course, writing. This is the second biggest writing project I've ever undertaken, and I strive to make it my best. I hope you think so too!
8 158 - In Serial9 Chapters
Beyond Evolution
Bam! Truck-kun, wtf?! I didn’t do anything wrong! Wait, are you god? I get to reincarnate in a fantasy world? I will even have super powers? With this will I finally be able to do all I want?! I will become cool, right? The whole universe will be within my grasp! Thank you, Truck-kun! I will never forget you. Wait, what?… Truck-kun… Screw you! ***** Disclaimer: All materials used in the cover are royalty-freeThis novel is not written with the intent to earn money and therefore a strict release schedule does not apply. I will try to upload the first 7 chapters with the regularity of one chapter every three days, after that the schedule is likely to change to one chapter per week. This would also entail that I will not be putting too much effort into writing this though I will attempt to maintain a decent quality. There will likely be no editing on my part, frankly, I don’t have too much time for this, but we’ll see how it goes.
8 325 - In Serial11 Chapters
The Chameleon's Gift
“Heaven is high, and our people are far away.” War is looming in the world of man. Long have the Senlin tried to avoid it, but every day their numbers fall, and their way of life is increasingly threatened. Caw and Rock are members of the Pachon, one of the few remaining tribes of the Senlin. They are an ancient and sacred bloodline, their magical abilities enhanced by powerful heirlooms, cultivated over generations. When Caw loses both her and Rocks heirlooms to a Shen hunting party, she has no choice but to try and get them back.
8 202 - In Serial29 Chapters
Bleeding Out
The Confederate Battle Flag is alive- But it isn't what you might think. Dixie (as he goes by nowadays) has been stuck inside America's head all these years. First a voice of opposition, then blunt annoyance. Then council. He has changed. And America needs him more than ever.*may be offensive. Dixie is a good guy in this. Do not read if this offends you or if you are triggered by violence*
8 116 - In Serial15 Chapters
HIM ↬ timothée chalamet
in which an actress searching for a comeback finds love instead[SOCIAL MEDIA x REAL LIFE]#1 in beautiful boy :P
8 165

