《HASEENAH》PAGE 73&74
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*73~74*
Ganin ta kusa shigewa ciki hakan ya sanya shi ƙara sauri, yazo dab zai shiga d'akin kenan Ammi ta fito daga bedroom d'inta, wata birki ya ja ya tsaya ya fara sosa k'eya.
Kallon shi tayi cike da tuhuma tace "lafiya?"
Cikin kunya ya fara kame kame da k'yar ya tattaro nutsuwar shi ya haɗa maganar yace" dama wajanki zanje ko kina da paracetamol"
Mamaki ne ya kama ta, mutumin da a wajen shi ake kar6a yau kuma wai yazo kar6a, ganin irin kallon da take mishi ya sanya shi saurin cewa" Ammi nawa ya ƙare ne wallahi shiyasa"
Dukda haka bata yarda da abinda yace ba, a tak'aice tace dashi" banida shi"
Juyawa yayi cike da jin haushi zai tafi.
Muryar Ammi ya jiyo tana cewa" ka shiga hankalin ka, naga rawan kan naka ya fara yawa"
Bai juyo ba haka bai tafi ba, bi ta gefen shi tayi ta wuce nan ta barshi tsaye.
Haseenah ko tana shiga ta rufe k'ofar ta zauna tsakiyar gadon ta janyo ledar da Mahmud ya fara bata tayi, ta kai kusan 3mins tana kallon ledar amma ta kasa bud'ewa, can ta daure a hankali ta fara zazzago abinda ke ciki.
Dogayen riga ne guda biyar sai turare biyu designers, sure da su lipstick, sai wata ƙaramar zoben gold tana ta faman walwali, ga receipt d'inta a ciki, warware receipt din tayi, ganin kudin da ya siya zoben 150k, zaro ido tayi waje cike da tsoro da kuma mamaki, da sauri ta nad'e ta mayar ciki, wata 'yar ƙaramar card ce ta fad'o daga jikin wata riga, ɗauka tayi Dan card ɗin ta dauke mata hankali ganin zanen jiki mai kyau ne.
Advertisement
A hankali ta 6alle shi ta fara warware wa, ganin abinda ke jiki ba ƙaramin razana ta yayi ba, da sauri ta sake card d'in ta dafe k'irjinta da ke faman bugawa.
'''*I love U*'''
Abinda ta gani knan an rubuta shi with pink bold italics nd fonts.
Dukda sanyin AC dake busowa amma gumi take yi, dafe fuskanta tayi da duka hannu biyu, na shiga uku, abinda take furta wa kenan.
Da k'yar ta samu ta saisaita natsuwar ta sannan ta sake janyo ledar Sameer.
Shikuma wannan karon necklaces ne da zobe da chain with Bangles na gold, shima ta buɗe receipt d'in Dan ganin menene, 850k ta gani rubuce a jiki, hanunta ne ya fara rawa, damuwa da tsoro ƙarara ya bayyana a fuskar ta, tsoro take yanzu in Ammi ta ga wanann uban kudin da aka kashe mata me zata dauke ta? Wata handbag d'an madaidaici Black colour, ɗan gefen shi da wata ƙaramar teddy bear, jakar ta Mata kyau sossai, shima akwai card cikin ledar, ɗauka tayi ta warware, wannan karon abun yafi firgitata, maimaita wa ta fara yi cikin zuciyar ta.
'''*Will u marry me?*'''
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, abinda zuciyar ta da bakin ta ya fara ambata wa kenan.
Ƙaramar envelope ta gani nan ta buɗe, 50k ne a ciki na yan 500, wayyo Allah na.
Dafe kanta tayi haɗe da shafa kanta, nan mayafin kanta ya zame gashin kanta ya sauka, girgiza kanta ta fara yi kamar mahaukaciya, lokacin barin gidan nan yayi, koda kuwa bata ji sauk'i ba ya zama mata dole ta bar gidan.
Dan haka tashi tayi ta maida kayan cikin ledar duka, mik'ewa tayi ta nufa hanyar fita da nufin nuna ma Ammi kayan, turus tayi ta ja ta tsaya kaman me tunani, dawowa tayi da baya ta zauna, buɗe ledodin tayi ta cire kuɗin da set na English gold ɗin da Sameer ya bata da kuma card ɗin, ta buɗe dayan ledar ma ta cire zoben da card ɗin da Mahmud ya bata, side drawer ta bud'e ta zuba su sanann ta rufe ta kwashi zallan kayan ta nufa d'akin Ammi.
Advertisement
A hankali ta shiga nan ta sami Ammi zaune tana shan lipton, zama tayi a gefenta sannan ta ajiye ledodin a gaban Ammi ta sunkuyar da kai.
Janyo ledodin Ammi tayi duka ta duba.
Cikin rashin fahimta ta kalleta alamar tuhuma, ganin irin kallon da Ammi take mata duk ta daburce, sunkuyar da kai tayi ta kasa haɗa ido da Ammi k'irjinta na bugawa.
Ammi tana buƙatar bayani amma to tayaya zata mata?.
Wata dabara ce ta fad'o mata, mik'ewa Ammi tayi ta buɗe wata jaka ta ciro memo da biro, rubutu tayi sannan ta mik'a wa Haseenah, a sanyaye ta kar6a dan ganin menene a jiki.
Gani tayi Ammi ta rubuta *Explain*
A sanyaye ta Fara rubutu.
Kar6a Ammi tayi dan ganin menene a jiki.
Abinda ta gani ya daure mata kai, ganin sunan Mahmud da Sameer a jiki.
Girgiza kai ta fara yi cike da damuwa, "akwai damuwa" abinda Ammi ta furta kenan.
Buɗe ledodin ta fara yi, kaya ta gani a ciki, ba tare da tace komai ba ta mik'a wa Haseenah ledar sannan ta mata alama ta tafi.
Kwashewa tayi ta kama hanya jiki ba k'wari ta fice.
Binta Haseenah tayi da kallo, a zuciyar ta fad'i take," too much of everything is dangerous"
Wato kyan Haseenah yayi yawa, dole ta haddasa masifa.
Tsoro ne ya cika ta, kar sanadiyar wanann yarinya a fara samun matsala karo na farko cikin yaranta.
*I have to do something*
Mik'ewa tayi ta Fara zirga-zirga a d'akin, ji tayi gaba ɗaya kanta yayi zafi.
Ta rasa samun mafita, abinda ta yanke shine ya zama dole ta dage da nema wa Haseenah magani dan tayi bayani inda danginta suke ta mayar da ita, dan bazata iya wannan abun ba.
Haseenah kuwa ganin yanayin tar6ar da Ammi ta mata ba ƙaramin d'aga mata hankali yayi ba, to yanzu da ta nuna mata wa'yannan gold's d'in ya kenan? Uhmmm wata ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta kwanta.
Kasa bacci duka sukayi, Ammi na neman mafita sameer na zargin Mahmud, Mahmud na jin haushin Sameer sannan Haseenah na neman mafita.
Ya kenan?
Bacci 6arawo ne kawai ranan ya sace su ba dan sun sani ba.
Dan haka da safe wajan yin breakfast ba Wanda ya kula kowa, Ammi tana musu kallon tuhuma sameer da Mahmud na hararar juna, Haseenah ko kamar mara gaskiya ta kasa d'agowa.
Haka sukayi zaman kurame, duk irin kallon da sukeyi wa juna Ammi na kallon su, hakan ya dad'a tayar mata da hankali.
Suna gamawa Haseenah ta koma d'aki.
Tunani take sossai kan abubuwan da suke shirin faruwa, dan yau ta ga sam Ammi tak'i sake mata, its better for her to leave tun kafin wani abu ya faru, bai kamata ta zama silar wargaza musu farin cikin su ba, tunda taimakon ta sukayi suka ceto rayuwar ta.
Dan haka nan da wasu kwanaki zata tafi.
To da k'afa zan tafi?
Abinda ta tambaya kanta kenan, nan kuɗin da Sameer ya bata suka fad'o mata, lokaci ɗaya ta saki murmushi ta koma ta kwanta.
Da haka wani bacci ya sake awon gaba da ita.
For comments 08144932303
Advertisement
-
In Serial70 Chapters
The Court of Souls?
What do we talk about tonight?~“How about a story?”~Fine by me. Which story? Hopefully a good one.~“There was once a lonely child in a world filled with myths, gods and demons. Only power counted there and the weak were worse than cattle. A world where survival of the fittest ruled.”~Was it strong then?~“No, but the child had a power. One that made him stand between light and darkness. Nothing could escape him, so he was shunned by his people.”~ What did he do? Did he fight his fate? Did he hide his power? What was it?~“Oh, he fought. He fought a lot. And no thing could escape his power. It was something that everyone had to live with.”~So he became a hero and changed the world?~»…”~Tell me.~“Nooo, that’s not how the story goes. This isn’t a story of a noble man, doing good amidst a sea of monsters. This is a story of a demon who was… kinder than the rest.”~A kind demon? How boring.~“I think it would be better if I tell the story, so you can judge for yourself.”~So tell the story!
8 545 -
In Serial877 Chapters
My Doomsday Territory
On doomsday, Tang Yu unexpectedly got the Lord of the End System, he remained very calm. Lack of experts? I will construct a pub so I can make ten draws in a row; Lack of food? I can’t be too cheap with the large pack full of food supplies sent from the market; Lack of safety? Arrow Tower, Mage Tower Artillery and all kinds of automatic defence buildings. Having many isn’t too many; Lack of equipment? Workshop production must produce high-quality items. Sir, would you like one? We are having a 20% discount special at nine! ………… In short, this is a story of Great Lord Tang building up his territory, attacking some monsters, and ripping off…… Cough, making some money at the same time.
8 1539 -
In Serial329 Chapters
Wolf Bloodline
King Einar, the astonishing king of the great and only continent, one day decided to choose a new heir to his kingdom, among his five and most precious sons. By giving each of them different duties, King Einar, did something unchangeable and unimaginable that day. With giving them an order, and not only a task or a quest to accomplish, but he also wanted his sons to accomplish their duty with maturity, with honor, with pride. But nothing, he wanted to do went in order, just because of his son. The eldest and most powerful brother "Yores", opposed this situation. He decided that it would be better, if the King gave them a seconds chance. But everything was chosen, and he found himself another solution to conquer his biggest rival. Lost, against anything that he wanted to win. So he made a deal with the most powerful lineage, "The Apocalypse Lineage", to take the throne. And by obtaining power, he started a rebellion. After Yores took the throne, he ruled people in such a manner for years. Damaged many relations and made himself the evilest person to ever be seen. But even his reign, came to an end. A wolf descendant, one of the strongest lineage's person challenged Yores. Jiro, the strongest person among bloodlines. He was so brave, so strong and so dauntless, he was someone who changed many things. The Battle of Jiro and Yores continued for three days exactly, and their battle, being heard all over the continent, changed the entire world. But the real story to be told, was only beginning....
8 320 -
In Serial37 Chapters
Red Junction
The hottest place to be murdered by zombies during the Colorado Gold Rush is RED JUNCTION. They have everything: Sex, guns, and gold. Vendettas. A dog named Dude. Dirty secrets and dirtier mouths. Whiskey by the bottle. And also, zombies are going to eat everyone. My Literary Zombie Western Masterpiece.
8 288 -
In Serial17 Chapters
Heathers On Instagram ✔️
Last book (maybe) to be in the "...On Instagram" series. Users and ships in first chap! ????<>-That non-binary kidDISCLAIMER! I DON'T OWN HEATHERS! ALL RIGHTS GO TO THE OWNERS!Started: 27/7/18Ended: 30/8/18
8 185 -
In Serial9 Chapters
Eddsworld Oneshots
I Am A Fucking Hypocrite. Enjoy These I Suppose.
8 92
