《HASEENAH》PAGE 71&72
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*71~72*
Tashi Mahmud zaune yayi, dan kwanciyar ma gagarar shi tayi, tagumi ya buga haɗe da riƙe kanshi, ji yayi komai ya kwance mishi, tunanin Haseenah ya dame shi, wannan lokacin babu abunda yakeson gani sai ita.
Gashi dare yayi ba halin fita, to inya je Kuma ta ganshi me ze ce Mata?
Tsuka ya ja ya koma ya fad'a Kan gadon, kallon ceiling ya cigaba da yi, ya rasa Gane Kan shi kwana biyu, ko yaushe tunanin ta ke damun shi.
To ko sonta yakeyi ne? Da sauri ya ba kanshi amsar no, that's impossible, yarinyar da inya ganta ranshi 6aci yakeyi.
Da wannan tunanin ya lumshe Ido bacci Mai nauyi ya d'auke shi.
Da asuba da k'yar ya iya tashi ya nufa masallaci, Yana dawowa ya koma ya kwanta.
Abu kaman wasa ya fara Zama gaske, Dan Mahmud tsanin damuwa ya bayyana a fuskan shi, wannan karon in bai ga Haseenah ba baya jin dad'i, gashi ganin yanda Sameer yake shige Mata Yana k'ona mishi Rai, Dan ma ya ga Bata cika kulashi ba, Amma abun ya fara kaishi bango, Dan tun Yana jurewa har ya kasa hak'uri.
Sameer ko chance yake so ya samu ya bayyana wa Haseenah cewa Yana sonta, ganin duk hanyar da zaibi Dan ta Gane cewa Yana sonta Amma Bata ma San yanayi ba, hasalima basar dashi take.
Ammi Kam shuru tayi ta zuba ma sarautar Allah Ido, Dan Bata je garin d'aga hankalinta ba ma balle tayi magana, Dan duk ta d'auke su Kan wahalar da kansu suke, Dan bazata ta6a Bari D'aya daga cikinsu ya aure ta ba, Dan jira take Haseenah ta samu sauki su tattauna ta Mai da ta gidan su.
Advertisement
Shiyasa Bata ce komai ba ta k'yale su.
Yau ta Kama weekend, wajan ya tashi da yanayin sanyi, Dan Haka dukan su basu tashi da wuri ba, kowa na cikin blanket.
Sai wajan k'arfe 11 sanann Ammi ta taso su.
Katuwar rigar sanyi iya gwiwa ne jikin Haseenah, ta ciki ta Sanya farar k'aramar Riga da bak'ar pencil skirt, kanta sanye da mayafi ta d'aura.
Karasowa tayi ta xauna gefen su, daga Mahmud har Sameer zuba Mata Ido sukayi, kowa da abunda yake ayyanawa cikin zuciyar shi.
Ita kuwa ko kallon inda suke Batayi ba, Dan Haka abinci ta zuba ta Fara ci.
Suma jiki a sanyaye suka Fara cin nasu.
Dukan su tunani iri d'aya ne cikin zuciyar su, wato zasu furta wa Haseenah abinda ke cikin ransu.
Kowa tunanin hanyar da zaibi ya fad'a Mata yake, to gashi Bata ji, ya zasuyi?.
Duka dabara ce ta fad'o musu, Dan Haka kaman had'in Baki duka suka sake murmushi.
Cike da nishad'i suka kammala cin abincin su, Dan Haka suna gama wa kowa ya koma d'akin shi.
Mahmud Yana shiga ya Danna numbar Junaid, Yana picking ya fara fad'in" bro da Allah shirya ganinan zuwa zaka rakani wani waje"
Yana gama fad'in Haka ya kashe wayar.
Toilet ya fad'a ya shiga wanka, bayan ya gama ne ya shirya cikin kananan Kaya ya d'au makullin mota ya fara saukowa.
Ido biyu sukayi da Sameer shima ya fito daga d'akin shi sanye cikin yadin gezna milk colour, ba k'aramin kyau ya mishi ba.
Ba tareda sunyi magana wa juna ba kowa ya kau da Kai suka fice.
Mahmud sai washe Baki yake, yau Haka kawai yake jin shi cikin nishad'i, Dan Haka Kai tsaye gidan su Junaid ya wuce.
Bai shiga ba kiran shi yayi a waya sanann ya fito.
Yana shiga ya kalli Mahmud yace" abokina ya akayi ne? Ko dai yau za'a d'aura auran naka da gimbiya Haseenah ne?"
Advertisement
Wannan magana ba k'aramin dad'i ya mishi ba, hakan ya sashi washe Baki yace" don't be faster than ur slippers, very soon in shaa Allah, Haseenah ta Zama tawa"
Dariya Junaid ya saka sannan yace" yanzu Ina muka nufa?"
"Shopping zaka rakani abokina"
Atare suka saki dariya sanann ya tada motar suka Kama hanya.
Bayan Mahmud ya dawo ne Kai tsaye d'akin shi ya nufa d'auke da k'atuwar leda, xube kayan yayi Kan gadon shi ya fara kalla, duk Wanda ya d'aga ganin Haseenah yake sanye da kayan ya Mata kyau.
Hakan ya sanya shi murmushi kaman mahaukaci.
Jin an Kira sallah ya sashi mik'ewa ya fice.
Da daddare bayan sun gama having dinner, dukan su zaune suke kowa Yana fargabar abunda xai biyo baya.
Haseenah na gefen Ammi xaune suna kallo, Mahmud da Sameer kuwa sai tsilli tsilli suke da Ido.
Ammi ce ta mik'e ta shige d'aki, ganin Haka ya sanya Sameer da Mahmud mik'ewa da sauri kamar Wanda aka soka musu k'aya, mamaki ne ya Kama su duka suka dubi juna ba tare da sunce komai ba.
Haka kowa ya nufa Kan stairs da sauri sauri.
Suna shiga d'akin su kowa ya d'auko ledar ya fito.
Da sassarfa Mahmud ya sauko, har lokacin Haseenah na zaune yanda ya barta.
Ganin ita kad'ai ce ya sanya shi k'arasawa da sauri wajan ta, Zama yayi a gefenta, da sauri ta d'ago a tsorace ta dube shi, gabanta ne ya tsananta bugu, murmushi ya sake Mata, maimakon ta mayar mishi sai ta sake Baki cike da mamaki, ledar hanun shi ya mik'a Mata, kasa kar6a tayi Dan Bata yarda shid'in bane.
Gyad'a Mata Kai yayi alamar ta kar6a, a hankali ta mik'a hannu ta kar6a sannan ta ajiye a gefen ta.
Jin k'arar bud'e k'ofar ne ya sanya Mahmud kallon wajan, Sameer ya gani Yana saukowa.
Mik'ewa yayi ya bar wajan, hakan yayi wa Sameer dad'i, Zama yayi gefen ta sannan shima ya mik'a Mata ledar hanun shi, kar6a tayi shima had'e da yin murmushi, sunkuyar da Kai tayi ta kasa d'agowa.
Tunani take yau Kuma me yake Shirin faruwa da ita ne?
Ganin ze matsa Mata ya sanya ta mik'ewa ta kwashi ledodin ta nufa hanyar d'aki.
Mamaki ne ya cika shi ganin ta da Leda biyu, to ai shi d'aya ya Bata, aina ta samu d'ayan?
Mahmud ya tuna sanda ya sauko ya ganshi suna zaune, gaban shi ne ya fad'i, me hakan yake nufi?
Mik'ewa yayi da sauri yabi bayan ta Dan ganin menene aciki?
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial10 Chapters
Two Gods Battled, I Dealt the Finishing Blow, Profit?
The battle between good and evil has ended long ago, now the God of Creation and God of Destruction are fighting, trying to be better than the other, destroying the earth in the process.On the final clash of the two Gods, they dealt a fatal blow on each other, weakening them beyond their expectations and when the two lost strength to move, the ground below them opened. A man who appeared from the hole dealt the finishing blow.Losing its god, the earth started to crumble and a week after the death of the two gods, the man who ate them was summoned to another world.With the power of the two gods at his disposal, what can the ultimate hikkikomori, who stayed true to his path even when the world was ending, do in the new world?
8 208 - In Serial17 Chapters
Spirit Shaman
When Fifteen-year-old Kai is not chosen to receive a Spirit Pet he decides that he'll go into the woods and find one. What he finds instead is a sinister creature called a Wendigo, and an old bear guardian spirit named Panchu whom binds with him in order to save his life. Now together they must find a way to bond, fit into Kai's village, and kill the Wendigo before it binds with another child ... the Chiefs daughter.
8 178 - In Serial9 Chapters
MOAS ; Coming Home
We're the line between the world and the much weirder world. We protect people from news they aren't ready to hear. So when they need us, we fight the battles they can't. And when we can't do that, we keep them safe. That is S.H.I.E.L.D.... We are S.H.I.E.L.D.Book 4(No Intended Love Interest)(Marvel's Agents Of S.H.I.E.L.D. Season 3)
8 117 - In Serial42 Chapters
MUHAMMAD
I decided to bring it back after it being taken down 3 times.THIS BOOK IS NOT ABOUT MUSLIMS!!!!! Take that mess some where else besides my comments or just don't read it.
8 111 - In Serial17 Chapters
The Untended Endearment
The biggest war of the era is fought to avenge a woman's honor . She got her justice and fair share of respect and recognition but she wasn't the alone woman present in the epic. There are many others who were left alone in dark. They got nothing neither their sacrifices got recognition nor their emotion were considered. Join me on the journey to embark the whirlwind of their emotions and try to cast a glance on their lost identity and a light on their unsung sacrifices.
8 88 - In Serial33 Chapters
Gentleman ♡
A story of heart break, betrayal, and so much more..
8 86

