《ƘADDARAR RAYUWA》K page 103
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 103
Already sun san address nasu Sadam kafin su isa sun rigada sunyi booking motarsa zatazo ta daukesu ta yanar gizo sun rigada sun tura address din batareda bata lokaci ba suna sauka suka motar ta daukesu tafiyar minti hamsin ce tsakanin filin jirgin da gidansu Sadam Har kofar gidan motar ta ajiyesu suka karasa suka danna bell,
Shiru na wani lokaci suka sake dannawa, bude kofar akayi Hameeda ce Sawwama tatsaya kallonta kawai yarinyar ta girma sosai ga tsayi yanzu tana 7years kenan amma girmanta kamar wacce takai 10yrs, Hameeda ta ihu tace "Ammie da mugun mamaki Sawwama ta juya tana kallon Yareema bata taba tunanin Hameeda zata ganeta ba, Tabudi baki zatayi magana Hameeda ta daka tsalle ta dale ta da murna itama Sawwaman ta kankameta,
Hamdan ne yabiyo bayanta yana dubawa yaga mahaifiyarshi da murna ya karaso yana fadin Ammie, Sawwama cikeda fara'a tace "na'am hamdan amminka ce, cikin nutsuwa ya taho ya rumgumeta Hafsa wacce take tsaya bayansu dan tun kwala ihun Hameeda suka fito tace "kubar Ammintaku tasamu karasowa ciki, hamdanne ya saketa ya riko hannunta Hameeda kam kamar za'a kwace mahaifiyartata taki sakinta,
Yareema kallonsu yakeyi cikeda sha'awa uwar da yaran sai duka suka bashi tausayi,
Suka shige ciki gabaki dayansu suka zauna kan kujera daya daga Itada Yareema Hameeda ta dale cinyarta shikam dama muhammad na makale da Yareema,
Hamdan ne yace Hameeda bazaki sauka ma Ammie a cinya ba kina bata wahala ya kalli Sawwama yace "Ammie ki tureta Sawwama tayi murmushi ta riko fuskarsa tace zo kaima ka zauna kaji bazakuyimin nauyi ba,
Kamar wanda yake jira yazo ya shige jikinta,
Saida Hafsa tayi magana kafin tadago ta dubeta ita harta ma manta da zamanta a wajan, cikeda fara'a Sawwwama ta gaisheta ta amsa itama fuska a sake,
Sai can Sadam ya fito dake shi bacci ma yakeyi tunda bai fita aiki ba baiyi expecting zuwannasu da wuri haka ba,
Saida gabansu su duka yafadi, da suka hada ido karfin guiwa tasamu ta sakar masa murmushi saida yayi ajiyar zuciya sannan shima ya sakar mata murmushi,
Sawwama ta girma ta zama cikekkiyar mace Sawwamat daya sani ya aura a shekara GOMA SHA SHIDA itace tazama haka idanba ace matsayinda take dashi wajansa ya sanya bazai iya mantataba toda tabbas bazai iya gane Sawwama ba,
Daga ganinta zaka tabbatar tana rayuwa cikin jin dadi mai cikeda kulawa da tarayraya, yanzu Sawwama matar manya ce tabbas domin idan wanda baisan Sawwama ba yanda ta juyo ta rikide baza'a taba cewa tunda can ba cikin dukiya aka haifeta ba,
Ya karaso ya zauna gefen kujerar Yareema yabashi Hannu sukayi musabaha,
Bayan sun gaisa ta kalleshi tasakawa zuciyarta dakiya tace "Yaya sadam ina wuni?
Lafiya Alhamdulillahi yafadi alokacin yake kamo hannun muhammad wanda hankalinsa yake kan yan uwansa da suke jikin Amminsa,
Muhammad yaje jikinsa yanata yimasa wasa,
Advertisement
Jin hayaniyarda tayi yawa ya sanya Abida fitowa dan ganin wanda sukaso dafarko bata gane Sawwama ba saida ta isa wajan gabanta yafadi ganin Sawwama tsabar idanuwanta ya rufe bata lurada wanda yake gefen Sawwama ba ta yatsine fuska tafara zantuka, tace "toh wajanwa kikazo kuma? Bayan naji labarin kinyi aure? Aurenne ya mutu kokuma mijinne yasake mutuwa?
Sawwama tayi murmushi mai cikeda takaici tace wajan Wajan Yarana nazo,
Tabe baki tayi tace "koh wajan uban yaranba,
Siririn tsaki Sawwama taja tace "ko wajan ubansu nazo ai ban fadi ba,
Ranta yafara baci tadubi Sadam tace "Yaya sadam har yanzu wannan bata daina halinta ba?
Yaya kake iya zama da ita?
Zata sanya maka ciwon zuciya,
Sadam ya sunkuyarda kai kawai yarasa mai zaice shikma baisan wace irin mace bace Abida,
Gidan ubanwa zai kaini da kike gaya masa wannan maganganun?
Afusace Sawwama ta sauke Hameeda dake gefentata cafko hannun Abida tayi hanyar waje,
Babu wanda yayi kokarin yin magana bare asamu mai dakatarda ita,
Ita kanta Hafsa kallon ikon Allah kawai takeyi ashe karamin kishi Abida keyi da abida, bata taba kallon tasantsan kishi a fuskarta ba irinna yau dataga Sawwama,
Suna kaiwa waje Sawwama ta banko kofa ta rufe babu mai iya jiyosu ko ganin abunda sukeyi,
Sawwama tasaki hannun Abida data biyota kamar rakuma, cikeda bacin rai tafara magana tace "Ashe har yanzu kina wannan halin dabbancin naki?
Wai sai yaushe zakiyi hankali? So kike kisa sakawa Yaya sadam ciwon zuciya?
Abida zata kuntuma mata Ashar tayi saurin dakatarda ita tace "A'a yanzu ba daa bane ki iya harshenki, koda wasa, yakamata ace yanzu kiyi hankali kisan cewa na girme miki a tsara,
Ba wannan ba abunda na jawoki na fada miki kashesi jan kunne dakuma shawara yakamata ace yanzu kinyi hankali kinbar wannan kauyancin,
Da mamaki Abida take kallon Sawwama, Sawwaamarda abaya ko yatsa aka sanya mata bazata ciza ba yau itace take kashedi,
Kuma niba wajan mijinki nazo dukda banace banzo danna ganshi ba saboda inada aurena inada iyalina acan gefe kuma inajin dadin rayuwata, toh Amma babu yanda na iya har indai bazaki canja hali ba bazan iya kallon Yaya sadam cikin matsala ba zan iya kashe auren nazo na aureshi, tunda dama bawai nadaina sonsa bane yananan acikin zuciyata ko kadan bai raguba sai dai kawai soyayyar ta rikide daga da aure zuwa ta yan uwantaka,
Yanzu mijina nake matukar so ammahar indai bazaki canja hali ba banda wani zabin daya wuce na dawo cikinku mu zauna, ke shaidace akan irin sonda nake yiwa Yaya Sadam tunda har zai iya rikidewa yakoma kan wani daban, yanayi zai iya dawo dashi muhallinsa na baya, indawo na rungumi yarana, su girma gaban uwarsu da ubansu amma faruwar hakan ya danganta daga sauyawarki,
(Sawwama tafadi wannan kalamanne kawai saboda tanaso ta samarwa sadam zaman lafiya a gidansa Bawai zan zata iya rabuwa da Yareema ba, eh tabbas dagaske ne soyayyar Sadam bata ragu azuciyarta ba saina tausayinsa daya karu kan soyayyar amma ahalin yanzu ba soyayyar aure takeyi masa ba, Sadam shine jigon duk wani abunda tazama a rayuwarta shine wanda ya daura rayuwarta akan hanya, hakkine akanta itam tayi iyawarta dannema masa zaman lafiya acikin gidansa)
Advertisement
Jikin Abida har bari yakeyi jin kalaman Sawwama gani takeyi kamarma yanzu tazo kashe aurenne ta dawowa Sadam,
Calm down Hajiya Abida bawai kashe auren nawa zanyiba idan kika zauna zaman lafiya dashi nima zan zauna lafiya agidana har Abada in sha Allahu,
Ga mamakin Sawwama sai taji Abida tace "kinyi alkawari? Koda yake ba abun mamaki bane idan akayi la'akari da yanda ta tsorata,
Uhm eh nayi alkawari cewar Sawwama amma zan ringa waya da yarana danjin halinda ake ciki, shikenan nima nayi alkawarin bazan sake tada masahankalinba, kin kyautawa kanki Sawwama tace hadeda shigewa gaba tafara tafiya kai tsaye tabude kofar takoma dake ba'ayi locking dinta ba,
Abida tabiyo bayanta suum-summ zata wuce daki sai tajiyo muryar Sawwama tana fadin kizo kugaisa da mijina dasauri Abida ta juyo suka gaisa tawuce daki,
Kowa yanaso yaji Abunda yasa Abida sanyi haka amma babu wanda ya iya tambaya."
Kudi sosai Yareema ya kashewa twins ya saya musu abubuwan tsaraba kala-kala,
Kwana biyu sukayi agidan amma Abida bata shiga harkarsuba sam abun har mamaki yake bawa Sadam da Hafsa sanin rashin mutumci irinna Abida,
Zamanda sukayi Sadam Ya fahimci cewa Yareema na matukar son Sawwama da abunda ta haifa gabaki daya, yanayin yanda yake tarayrayarta sai yakeji inama da awajansa tasamu irin wannan kulawa haka amma yanzuma bai baci ba zai bawa matansa dai-dai gwargwado danya dauki darasin yanda ake lailaya mace kamar kwai."
Ya lura Sawwama tacire duk wani abu aranta ta dauki Kaddararta ta rumgmi gagarumin sauyin da ubangiji yayi mata,
Suna Hira da Yareema,
Sadam yake ce masa lallai Sawwama tayi sa'ar miji Allah yayi mata sauyi yadubizyciyarta,
Murmushi Yareema yayi sannan yace "nikuma gani nakeyi kamar nine mai sa'ar ba itaba domin ban taba cin karo da mace mai kyawawan dabi'u kamarta ba, murmushi mai ciwo Sadam yayi yace "kuma bana tunanin har Abada zakaji wannan karon,
Sawwama nada kyakkyawar zuciya Cewar Yareema kuma bata manta halaccida bakinta tacemin bazata taba mantawa dakaiba domin kai shigone arayuwarta, a hankali a zamana da ita saida nafahimci wanenen kai,
Nasan cewa KADDARAR RAYUWA ce tazo mukj ahaka amma soyayyar da kuke yiwa junanku banaji akwai abunda zai rabata, tacemin har Abada bazata daina sonka da ganin girmankaba sai dai soyayyar da take maka yanzu tasha bambam data baya,
Eh ai dole zata sha sun bambamta cewar Sadam soyayayrda takemin abaya yanzu tadawo kanka domin ka kwaceta,
Dariya dukansu suka saka,
Haka idan suka zaune sukeyi sun ringa hirarraki kenan,
Kwanansu 5 suka shirya tafiya, Hameeda tayi kuka ba kadanba saida su dukansu sukaji babu dadi babanta yayiwa Yareema Alkawarin ana hutu zai kawosu sannan da zarar Hameeda tagama primary zai basu ita gabaki daya danya lura tana matukar son mahaifiyarta,
Godiya sosai sukayi masa har ita kanta uwar taji dadin hakan sosai,
Haka suka tafi cikeda kewar juna har suka tafi Abida bata sake tada musu rikici ba."
—————-
Tun daga wannan lokacin duk hutu sai Sadam ya kawowa Sawwama twins sunyi hutu a wajanta daga karshe ma yabata Hameeda gabaki daya."
Sun shiga na shekara biyar da aure amma Sawwama shiru,
Ranar ta shirya tsaff tasamu Yareema adakinsa sai dai tana taraddadin yanda zai dauki zancenda taje masa dashi,
Zama tayi gefensa saida yagama karanta shafin da yake sannan ya rufe alqur'anin yajiyo ya dubeta, murmushi ta sakar masa shima ya maida mata, matsonan ki fadamin meke tafe dake dannaga bakinann kamar akwai magana,
Wani murmushin tasake saki sannan tamatso ta kwanta jikinsa tayi kasa da murya tace "ina waccar shekarar da mukaje saudi yace "ehem inaji mai yafaru acan?
Mun hadu da wata sunanta nabila mun gaisa ta ganmu tare dakai shine take cemin itace tsohuwar matarka bayan mundawo sai nake tambayar ruma tabani labarinta tanada kirki sosai ta kula dakai,
Se akayi yaya? Ya tambaya da mamakin abunda Zai biyo baya,
Uhmm dama nace ko zaka aureta idan andace sai kaga Allah yabamu yara ta wajanta, tunda kaga auranda tayi bayan naka bata zaunaba,
Da mamaki yake kallonta yace "Anya! Anya kina sona kuww? Kowace mace na gudun kishiya ke kinaso?
Ni nace miki nadamu da yarane? Wanda nake dasu sun isheni, balle me menene na kara aure? Tunda naga aike kin haihu idanma da matsala ko wajena ne, kinga bbu wani amfani kara auren har indai akan hakanne,
Turo baki Sawwama tayi tace "ina sonka mana kaima kasani wannan sai dai kafada kuma kishiya nifa duk aurenda nayi na zauna da ita,
Shafa gashin girarta yayi yace "toh ni agidana karki zauna da ita sai gidana yafita daban kamar yanda nima nafita daban,
Uhmm kawai tace zata mike ya dawo daita yace ai baki idaba dawo nan, indawo inyi mene bayan kaki jin shawarata,
Bari kiga mai zakiyi yafada yana rumgumota,
Kokarin kwacewa takeyi yace "tsaya mana toh kiga nima na gwada sa'ata shammatarsa tayi ta fauce kasancewar tasan yaran basa gida yau zasusha soyayyarsu yanda ransu yake so,
Tana sauka daga gadon tafara tafiya a hankali shima yabi bayanta yana fadinta tsaya ya gwada sa'asarsa ganin yana shirin cimmata ya sanya ta kara sauri taku uku ya kara ya cafkota rumgumeta yayi da karfi saida tasaki nishi, yace ""ni kike kaiwa kasuwa koh? Waina kara aure toh naki sayuwa kici gaba da zamada abunki haka babu maiso,
Tana kokarin kwacewa tace "kabari kagani idan nayi tallah daka wawa za'ayi dan kowa naso,
Tsayawa yayi yana mamaki wai dagaske Sawwama aure takeso yakara?
Shidai baitaba kallon matarda takeso dan karan kanta ayi mata kishiya ba sai ita, shikuma dai ara'ayinsa baida niyyar auren mata samada daya kuma har yanzu hakan yakeji aransa,
Tana kokarin kwacewa ya dauketa cakk bai ajiyeta ko'inba sai cikin dakin nishi ya tsaya yanayi tana dariya yace "Allah kin kara nauyi sosai,
Uhmm ai gara na kara kar nayita cin abinci ba'asan yanda yake tafiya ba."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial158 Chapters
The Misplaced Dungeon
The gods on four worlds were in trouble, or rather the clique that had taken over those worlds development and refused to listen to the established but less powerful gods already in power were in trouble. Their mismanagement was causing four previously lush and pleasant worlds to become harsh and inhospitable. So taking another leaf out of world building 301 they arbitrarily decided to seed the worlds in question with new dungeons they could control or at least influence. One fine day Azurea, self declared Goddess of dungeons on those four worlds discovered a fascinating world; it was teeming with life, literally overburdened with teeming billions of sophonts. Even better in her view many were atheists and due to the rapidly expanding population many of those were brand new souls. So without further ado she soulnapped one hundred of them for her cliques experiment. This is the story of one of the randomly selected beings, a sixteen year old girl with anger management issues, in fact Mary Silvestre has been diagnosed a borderline psychopath by a lazy school system. NB: This story uses UK English spelling.
8 196 - In Serial23 Chapters
Rain Sabbath
Weeks before graduating highschool, Marie Weiss encounters the transfer student Felix Conti; a strange boy claiming to be on a research mission in the oceanic town of Sapphire Isle. In the following days, strange phenomena occur in alarming intensity. Monsters stalk the night, shadows come to life, and an invisible storm looms on the horizon. Out of everyone, Marie has the most reason to worry. No town is big enough for two witches, after all. Updates every Saturday at 5PM EST. Note: This is the first draft. Expect some fumbling and numbling and fiddly dunwhoozithowers here and there. Apologies in advance.
8 129 - In Serial10 Chapters
Genesis: Journey of the Creator
after drifting away in the void for who knows how long, a lonely soul finally decided to create a world base on his memories, follow his journey to enjoy his own creation.###############$##############################meh. its my first time so its crude, if you find it unacceptable, you can just drop it if you want.
8 450 - In Serial36 Chapters
Infestation
The world is being overrun with 'hives', corrupting buildings into nests for monsters. The unlucky people in a building when a hive emerges either die, witness someone die, or gain otherworldly power. The latter are known as 'users'. Charlotte, a recently emerged user with the rare power of precognition, has found herself stranded with little to no support and a desperate need to get some money. She's weak and so teams up with a stranger to clear hives together but life quickly falls into disarray as her situation and paranoia compound.
8 160 - In Serial6 Chapters
Trùng Sinh Mạt Thế Truyền Thuyết - Hòa Xuất Thú Thú
Thể loại : ngôn tình, trọng sinh, mạt thế, dị năng, tùy thân không gian, nữ cường, hoàn.Sơ lược :Trong mắt ngươi mạt thế là dạng gì?Biến dị, thây ma, dị năng, người sống sót? Thân nhân, người yêu, cừu nhân, người xa lạ?Nhiễm Minh chưa bao giờ nghĩ tới bên cạnh mình có một ngày đầy dẫy quái vật, lại chưa nghĩ tới so với quái vật đáng sợ hơn chính là người bên cạnh. Âm mưu, dương mưu, giết chóc, phản bội, tử vong, trùng sinh ······Giống nhau mạt thế, không đồng dạng như vậy chuyện xưa, hoan nghênh đi vào mạt thế truyền thuyết.Một câu nói giới thiệu vắn tắt: Đây là mỗ nữ mang theo tiểu đệ khắp nơi đánh quái vật thăng cấp đập bãi chuyện xưa!
8 198 - In Serial13 Chapters
to Learn about a Lucy. (Fairy Tail Fanfic)
A watching the future fanfic. It's currently X781, three years before canon. A group of Fairy Tail mages find themselves in a large building, with no known way out.They sit down, and they watch the future.-to learn about a lucy (with a look into the future.)© Hiro Mashima
8 144

