《ƘADDARAR RAYUWA》K page 101
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 101
Kwana biyunda Sawwama tayi wajan mahaifiyarta ba karamar nutsuwa ta samu ba domin taji dadi sosai dik wata damuwarta takau, dadin dadawa ga yaranta da suke kara debe mata kewa."
Yareema kam yana gidan Hajiya amma gabaki daya hankalinsa yanaga Sawwama azamansu ba hira sukeyi ba ba kuma sun wani shaku bane amma kewarta yakeyi sosai Allah-Allah yakeyi kwana biyun sucika yadauki matarsa suyi tafiyarsu,
Itakuwa Sawwama nata wajan ba hakan bane domin tafi sakewa wajan mahaifanta kwana biyu dake hankalinta yana kwance har wata yar cika tayi,
Shikuwa tunda yakaita bai sake komawa ba amma gabaki daya hankalinsa yana can yasan bata sakewa da zarar ta ganshi takebi dik ta takura kanta hakan yasa yabata sarari nadan kwana biyun ko zata samu nutsuwa amma hankalinsa gabaki daya yana gareta,
Ana washe gari zasu tafi gabaki daya hankalinta yatashi Mama ta lurada hakan tazauna tayita mata nasiha amma dukda haka tana cikin damuwa gashi Sassafe zasu tafi dan zamanda tayida Yaranta na kwana biyu sai takeji wannan karon kamar bazata iya tafiya tabarsu ba ga Muhammad ma wajanta yake domin dashi tataho daga gidan Hajiya."
Bayan tayi Sallar asubahi bata koma bacci ba domin tasan da sassafe zasu tafi kamar yanda yafada mata kafin yakawota Aikuwa Sassafe sai gashi yazo Allah yaso tagama shirinta tun kafin lokacin Baba ma dake yasanda tafiyar sai baiyi gaggawar ficewa kasuwa dawuri ba,
Yana tsaye a kofar gidan bai san yanda zaiyi ya shiga ba domin shi baima da waya saida yazo nan yasiya kuma baida Number dinta Aysha ta matsa zata biyoshi yaki zuwa da ita daya sani dayazzo da ita tashiga ta sanarda zuwannasu yana tsaye mai adaidaita ya iso ya tsaya yana kallo yadaga waya yayi kira bada jimawa ba sai gashi yara sun fito daga gidan sanye da kayan makaranta ajikinsu suka nufi wajan keke napep din, dasauri ya nufi wajan yaran Hindatu tana kallonsa tasaki fara'a domin taganesh mijin yaya Sawwama ne dan ranar daya yakawo Sawwaman sun gaisa tasan cewa shine mijinnata kafin ya karaso itama tafara nufar wajannasa tagaisheshi ya amsa cikin sakin fiska batareeda yayi magana ba tace "kazo mushiga ciki tayiwa mai keke napep magana sannan tajuya tafara tafiya zuwa cikin gidan babu musu yabita abaya tayi masa iso har cikin falon Sannan tashiga a sanarwa Sawwama ta zuwannasa sannann tafito tasameshi zauna tace "Yaya Sawwaman na zuwa, yayi mata godiya ta fice domin ana jiranta,
Sawwama bata dauki lokaci ba ta fito koda ace Hindatu bata sanarda ita yana falo ba jikinta yabata domin daga shigowarsa kamshin turarensa yayi mata maraba,
Mayafi tayafa tashigo falon da sallama ta zauna can gefe dashi idanuwansa yana kanta ita kuma bata yarda sun hada idoba,
Gaidashi tayi ya amsa yana mai sakin murmushi, muryarta cike take da sanyi barinma idan tana tare dashi ya lura tafiyin sanyin gani yakeyi kamar wacce take tsoransa dar-dar takeyi idan tana kusadashi,
Advertisement
Shiru ya biyo bayan gaisuwar tasu a falon suna zaune ahaka na tsawon lokaci karan AC dake falon kawai akeji,
Hameeda ce tafara shigowa falon sai Hamdan yabiyo baya Hannunsa rikeda muhammad,
Yaran su dukansu suka nufeta ta zaunar dasu gefenta ta zabga tagumi kawai tana kallonsu jimamin tafiyarta tabarsu takeyi hakan yasa tahanasu Hameeda tafiya makaranta Yareema ne yayiwa yaran magana suka tafi wajansa banda Hameedah dake jikin mahaifiyarta, Muhammad kawai yasani matsayin danta amma wadannan ma alamu ya nuna masa yaranta ne domin suna mugun kamada ita,
Mikewa tayi ganin yaran sun sake a wajansa ta nufi wajansu Baba a falo ta samesu ta sanar dasu zuwannasa sannan tajuya,
Tare mama da Baba suka shigo yana ganinsu yakoma kasa ya zauna babu yanda basuyi yakoma ya zauna kan kujera ba amma haka yaki zama,
Cike dajin nauyinsu ya gaidasu suka amsa sannan
Baba yayi musu yan nasihohi hakama Mama,
Baba yadubi yadubi Sawwama yace "saiki tashi kutafi koh rana tanayi, Allah ya kiyaye hanya,
Nan danan idanuwanta suka ciko da hawaye dakyar ta iya maidasu tatashi tadauko jakarta zallan Muhammad suka dauka nan Hameeda ta kankameta ta fashe da kuka danta fahimci uwar tafiya zatayi ananne itama takasa tsaida hawayen nata,
Mama tace "ji shahanci wajan Hafsatu ko menene abun kukan?"
Baba shi kansa yaji babu dadi ganin Sawwama tana hawaye daan yasanta ba komai ke daga mata hankali harta nuna ba,
Shi kansa Yareema tabashi tausayi hakan yasa yadubi baba kansa yana Kasa yace "Baba idanda Hali zamu tafi da yaran dukansu,
Baba ya girgiza kai yace "Babu hali domin sai annemi izinin mahaifinsu abari tukunna daga baya duk yanda ake ciki zan sanar daku,
Ni Mama takarbi Hameeda tanata tsala kuka Sawwaa tafice ko Sallama bata tsaya sunyi ba domin idanta tsaya itama kukanne mai karfi zata saka,
Godiya yareema yayi musu sannan yafito dauke da Muhammad a hannunsa,
Ajikin motan ya sameta tana tsaye ta kifa kanta daga can ya bude mata motar tana jin anbude ta shiga ta zauna shima ya shiga yaso yararrasheta amma ganin baiga fuska ba saiya hakura yaja motar Muhammad yana kan cinyarsa,
Ahaka suka isa har zuwa gidan Hajiya kai tsaye part dinta yawuce yayi parking motar saida ta tsaya ta dai-daita nutsuwarta kafn tafito,
Shima yafito yarufa mata baya amma bawani rata bane tsakaninsu domin daga nesa idan ka hanga zaki iya cewa tarema suke,
Hajiya na zaune a falo tagama shirya musu duk wani abunda zasu bukata a tafiyarsu harda Ma'aikaciya guda daya wacce kusan koda yaushe da ita Hajiya take tafiya duk yanda zataje,
Daga nesa ta hangesu saita saki murmushi babu wanda zaice Yareema bashine mahaifin Muhammad ba saboda irin kamarda sukeyi tanadan gaba dasu kadan shikuma muhammad ya lafe kafadarsa kamar wanda yake bacci,
Karasawa tayi wajan Hajiya ta gaidata Hajiya ta amsa tana fadin kun kusa kuyi latti domin sha daya jirginku zai tashi yanzu nake shirin kiranku,
Yareema ya karaso yana fadin gamu mun iso yanzu in sha Allahu zamu tafi babu bata lokaci, yaso su tafi da muhammad kozai dauke musu kewa amma shima Hajiya tace sai daga baya, ransu bai soba amma babu yanda suka iya,
Advertisement
Alokacin aka fara fita da kayayyakinsu aka shigar motarda zata kaisu airport kafin 10:00 sun fice agidan sun nufi airport di."
_____________
Sadam yafito ma suna tsaye a wajan yana jira yaga daddy yadaga waya yakira anzo anshiga dasu sai yaga yatsaya shima sai ya tsaya yana jiran abunda daddyn zaiyi,
kasancewar ranar Baba bai samu yafita kasuwa dawuri ba sai wannan lokacin yasanya ya riskesu a tsaye suna neman wanda zaiyi musu iso, da fara'a Baba ya karasa wajansu sukayi musabaha,
Sadam yasha matukar mamaki dan daga dady har Najeeb babu wanda ya fada masa su Sawwama sun canja gida,
Baba yace "Ashe kuna tafe bismillilah mushiga mana sadam kansa yana kasa domin nauyin Baba yakeji Baba kuwa yasake kamar komai bai faruba,
Suna shiga palour Baba ya kwalama mama yakira Tashigo hannunta daukeda Hameeda wacce har lokacin kuka takeyi,
Yace "Ummi kawo musu ruwa mahaifinsu hameedane sukazo,
Sadam kuwa bin yarinyar Yayi da kallo ta girma sosai tayi wayo,
Dady yace "rikici take tabawa kenan? Naganta a hannu sai jan zuciya takeyi,
Baba yace " rikicin kenan wai mahaifiyarta tatafi shine take kuka,
Jin an ambaci Sawwama saida gaban Sadam yafadi Dady yace "Oh Allah sarki,
Mama ta dauko ruwan da abun sha ta kawo babu yanda batayi Hameeda tasauka su gaisa ba amma taki,
Saida tatafi baba yajuya suka gaisa Sadam jiki a sanyaye ya gaidashi ya amsa sannan ya hada da bashi hakuri,
Baba yayi murmushi sannan yace" Babu komai Sadam wannan kaddarace da Allahya rubutata kuma saita faru sannan bayan haka kai masoyin Mama nace inaji a abunda yafaru kai kafita jin zafi haka Allah ya rubuta,
Dady yace "hakane shiyasa yanzu mukazoda kokon bararmu ataimaka tadawo dakinta su raini yaransu gabaki daya su taso a hannunsu,
Mun dakata ne saboda zafin mutiwa bai gama barin jikinta ba, idan Allah yasa da rabon komawarsu sai kaga an koma kuma anzauna,
Baba yayi shiru kamar mai nazarin wani abun suma duka sukayi shiru suna kallonsa,
Sadam jiki na rawa yace "Baba nayi maka alkawari in sha Allahi bazan sake bari wani abun ya sameta ba dauketa ma zanyi mubar kasar tayi zamanta acan,
Baba ya nisa yace "Ba wannan bane matsalar baban Yan biyu Mamana ta rigada tayi aure,
Dumm sadam yaji kamar anbuga masa guduma har wani dushi-dushi yake kallo,
Baba yaci gaba da fadin "kanin mijinta mai rasuwa da aura da mahaifin shi yaron da mahaifiyar marigayi ciki daya suka fito,
Wani muradadden lamarine wannda Allah kadai yabarwa kansa sani,
Da kunzo dawuri toda zaku samesuma dan basu dade da tafiya ba,
Sadam yakasa magana dady dakyar yabude baki yace" Allah yabasu zaman lafiya, Baba ya amsa da amin
Dakin yadauki shiru sai dady yayi karfin halin cewa Idan babu damuwa munaso rikon yan biyu yadawo hannun mahaifinsu,
Baba yayi shiru sannan yace "toh dama yanzu muka gama magana dashi mijinnata akan yanaso yaran su dawo hannunsa toh nace bamuda wannan ikon saina sameku munyi magana dama ko baku zoba nima zan je can din,
Dady yayi shiru sannan yace "nima zanso ace yaran sun girma gaban mahaifiyarsu toh amma wani lamarin ya gifta dama tun farko na sanar daku har lokacinda mahaifinsu zai bukaci yaransa zan barsu wajanku,
Ita Sawwama ta iya yiwuwa zata haifi goma bayan su amma shi bahaka bane,
Baba ya kalleshi da rashin fahimta,
Dady yacigaba da magana Haihuwa awajan Sadam sai wani ikon Allah domin bazamu cire rai da rahamar ubangiji ba,
Dady ya zauna ya fayyacewa Baba yanda lamarin yafaru har yanda akayi rabuwarsu izuwa abunda likita ya fadi,
Sai yanzu baba yasan ainihin dalilin rabuwar dakuma dalilin dayasa Sadam bai dawo maida Sawwama ba ya tausayawa masa kwarai da gaske,
Baba ya jajanta lamarin sosai sannan yabashi hakuri yace masa in sha Allahu zai dawo masa dasu dakansa kafin yakoma amma yanzu yakara masa sati guda akai,
Jiki a sanyaye suka tafi Baba ma suka barshi da sanyin jiki,
Bai iya fita kasuwa ba bayan fitarsu Mama tashigo ya sanarda ita jijjiga kai tayi tace "kaga muguwar mata abunda ta jawowa danta koh?
Tana ganin muta kuntatawa ashe a kanta ta kuntatawa,
Allah ya kyauta Baba ya amsa da amin tafiya kasuwarda baiyiba kenan."
—————
Mummy duk yanda taki jinin Sawwama saida ta tausayawa Sadam,
Abida kam har tsalle tayi da labarin ya risketa, Hafsa itama taji dadi amma sadam yabata tausayi, jin cewa Sadam zai kwaso mata yaran tayi murna sosai dan dama abunda takeso kenan,
Tunda sukazo kasar Cikin matan Sadam babu wanda ta taka zuwa gaida mummy ita Hafsa tsoro takeji jin labarin mummy shiyasa ta yanke shawara bazata jeba, Abida kuma fushi takeyi da ita, danko mahaifin Abida ya yanke alaka da mummy,
Sai itace tataka taje gidan tasamu Abida a falo tana kallo tunda tace mata sannu ko kallon yanda take bata sake yiba daga baya kuma tatashi tabarta zaune,
Mummy bakin ciki ya na cita aciki, ga Hafsa kanma ko idonta bata ganiba, itakanma batasan wainarda ake toyawaba dan bacci takeyi,
Har mummy tagaji tatafi,
Takira Sadam ta shaida masa tabbas baiji dadin abunda yafaru ba amma sanin halin mummy ya sanya bai tankaba saboda yasan zata iya fada masa abunda ba shine ba ya tambayi matan su fada masa wani abin daban,
Yanaso yagyara alakarsa tsakaninsa da mahaifiyarsa bayason wani abunda zata sake yi da zai sake nuna rashin kirkinta kiri-kiri shiyasa ko abu tafada bayabin diddigi,
Gashi cikin matan babu wacce tayi masa complain shiyasa shima bai tankasu ba,
Yana sane babu wacce taje ta gaidata yasann tsakaninsu da Abida a halin yanzu Hafsa kuma baisan yanda Mummy zata karbeta ba, shiyasa bai kaitaba."
Toh Alhamdulillah mungama exam in sha Allahu bazamu tsayaba sai mun gamashi gabaki daya,
Ina matukar jin dadin yanda baku gajiya dabin labarinann dukda yanayin yanda yake zuwa baku daina nuna masa kauna da Bibiyarsa ba jzkllhu khairan nagode matuka🥰🥰
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alab
Advertisement
Fierce Ex-wife: President, Please Be Careful
Zhou Youlin, a famous ice queen of the special forces. During an accident in her mission, she was betrayed by her squad mates and was shot twice. She died on the spot. When she woke up again, she became the useless madam of a rice family and was a resentful wife who was neglected by her husband.
8 861The Rise Of A Porter
Do read my WSA 2021 novel **Alone: Tale of a Monster Hunter**.
8 883tales from the multiverse
stay stories that are from the multiverse of my mind...they are good, but I can't really make whole books out of them, maybe I will continue them at later parts, but this is just short peeks into various stories.
8 201They Who Hunt the Forest
As a rule of nature, breaking a wave before it peaks halts and disperses built-up energy. Unfortunately, Fate doesn't play by the rules of nature. The cost of a Fourth war: an equal number of lives, a thousand thousand generations of lost futures, and one infinitely unspeakably tortured soul of a child never given chance to be one. Or, the one where some power-hungry immorals decided to put the words "bijuu," infinite," "natural energy," and "psuedo" together in one sentence, not necessarily in that order. Naruto Fanfiction, please excuse the tags. AU ANBU OC, 3/4th Hokage era. Originally posted on Fanfiction.net Current release rate: 1 per week until caught up to Fanfiction.net Goal release rate: 1 per 1-2 months Actual release rate: 1 per 2+ months Explanation: average word count per chapter ~10,000+
8 186War of Auras
In a medieval world full of kingdoms and conflicts, everyone is born with so-called auras, powers derived from the monsters that once inhabited the land. In this world, a boy named Akin was born with a minimal and weak amount of aura, making him much weaker than everyone else. Even with these delimitations, Akin is determined to become the strongest person. He will meet many people with different goals, stories, and powers in his adventure. He will also have to face villains along the way. How will Akin make it? He's definitely going to need a lot of help.
8 69Senior Year
Summer is over and school has started. It's y/n's last year of high school. There will be Friday night lights, pep rallies, school dances, college decisions, and some unexpected surprises. This book shows what y/n and the cast will be doing during the time between the Scorch Trials and the Death Cure. This is the second book in the Once in a Lifetime Opportunity series!
8 105