《ƘADDARAR RAYUWA》K page 99

Advertisement

*ƘADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by

zaynab bawa

#Follow me on

"

Marubuciyar

*BIBIYATA AKEYI*

* Y'AR FARI*

* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 99

Mai martaba yacigaba da fadin "Lallai wannan abunda ya faru al'amarine na ubangiji haka ya tsara lamarinsa tun farko koda kuwa a shekarun baya muka sanski to haka ya tsara dole ta wannan hanya zakizo garemu,

Iya namu mu baki hakurine domin anyi miki rashin kyautawa ta hakika, yanke shawara da abunda zai faru da rayuwarku nan gaba yana hannunki bazan tirsasa mikiba idan kinji bazaki iya ba ki sanarda mijinki, saiya duba lamarin kiyi hakuri Allah yahuci zuciyarki,

Kiran Sallahr azahar aka farayi hakan yasa mai martaba ya takaita bayaninda yakeyi,

zuwa lokacin Sawwama tadan tsagaita da kukanta, mai martaba ya mike dakyar saboda yanayin jikin tsufa yace "in sha Allahu komai yazo karshe daga yanzu babu wani abu makamancin wannan da zai sake faruwa,

Zan dauki matakinda wanda ya aikata wannan abun bazai Kara tunanin sakewa ba yanzu haka wannan fitarda zanyi da zarar anyi Sallah zan nemo bakin zaran na karasa warwareshi in sha Allahu, yana gama fadin haka yace "bari naje naji ana kiran Sallah su duka sukayi masa fatan sauka lafiya banda Sawwama da Yareema wanda kowanne da abunda yake tunani,

Dakyar Umma ta iya bude baki jiki a sanyaye tafara magana "Hafsa dafarko dai zance kiyi hakuri ki yafewa Yareema amma dan Allah karkice zaki rabu dashi domin hakan ba mafita bace,

Kizauna kiyi hakuri ki yafe masa dukda cewa ya aikata miki babban laifi Amma ba'a cikin hayyacinsa yakeba kuma wannan ba hujjar da zaisa akasa tuhumarsa bane ki tuhumeshi kiyi masa hukunci yanda ranki yaso amma kada ki barshi karki rabudashi zuwanki cikin rayuwarsa gabaki daya KADDDARAR RAYUWARSA ta warware bazance nan gaba bazai fuskanci wata Kaddara ba amma ina roka masa ubangiji ya kasance wannan itace kaddara babba mafi muni daya fuskanta kuma bazaj sake fuskantar makamanciyarta ba,

Idan takama har mahaifanki mu zamubi mubash hakuri dukda nasa abun dole zaiyi musu girma amma bbu wata mafita face ayi hakan har indai zaki hakura ki yarda ki zauna adakin mijinki,

Yareema yakasa cewa komai yamike agaba Sawwama dayake zaune jiki babu kuzari yace "umma zan tafi Sallah ta dago ta dubeshi tadade ahaka sannan tayi masa murmushi irin wanda yakeyi mata cikin murya mai cikeda gwarin guiwa tace "kafita da gwarin guiwarka da addu'a ka sanya kafarka a waje cikeda tsoron ubangijinka shi kadai babu wani wanda ya isa yayi maka wani abun batareda yardarsa ba ka sanya aranka cewa shine kadai zaiyi maka wani abun, Asiri gaskiya ne amma hukuncin ubangiji shine babban gaskiya,

Kaje masallacinka ka dawo Allah ya kareka idan kayi Sallan kayi addu'a sannan karka dade kadawo kanemi gafarar matarka ka roketa harsai ta yafe maka,

Murmushin karfin Hali kawai yayiwa mahaifiyarsa ya juyarda kansa yayi waje,

Fitarsa daga shashin Umma gabaki daya ya hautsina mutanen wajen mutanen kallonsa kawai sukeyo kallo mai cikeda mamaki,

gashi kafofinsa ji yake kamar yayi musu nauyi bazasu iya daukansa ba ahaka ya daure ya sake takawa, da sauri fadawan dake wajan duka suka zube kasa suna kwasar gaisuwa cikeda mamaki sai suna ganin kamar shi kamar kuma bashiba,

Advertisement

Hannunsa harde a bayansa yayi murmushi hadefa shakar wata iska mai sanyin kamshi ya lumshe idanuwa ya budesu akansu kamar wanda yake nazarin wani abun akansu danya kura musu idanuwa na tsawon wani lokaci,

Cikin maganar mai hadeda hikima ta fannin wanda ke sauraro zai gane mai maganar yana yinta cikeda ilimi dakuma hankali yace "Natashi lafiya kuma ina lafiya wannan zaman zaisa murass Sallah ko zamu iya wucewa yanzu?

Dasauri suka mike cikin motocinsa aka dauko daya bayada lafiya tsawon shekaru amma a dik lokacin da aka sake sabuwar mota kirarda yakeso sai mai martaba ya sanya an canja masa ita da sanya ran wata rana zai samu lafiya,

Kallon motar yayi sosai tayi masa kyau sai dai bai taba kallon mota deisgn dinta ba, Yareema baisan shekara kusan goma yabar duniya abaya ba😅 ina nufin anyi abubuwa dayawa da baisan dasuba, hattada yanayin rayuwarda yasani abaya yanzu kusan duk ta caccanja,

Bude masa motar akayi ya shiga duk yanda suke wuce kallonsu akeyi domin tsawon lokaci wadannan fadawan basuyi tafiya cikin fada a mota ba, nan danan cikin fada tadauki dumi har izuwa isarsu masallaco sun samu ba'a kaiga shiga sallar ba, fotowarsa a mota zuwa shigowarsa masallaci mutane sunga abun mamaki da al'ajabi,

Wasuma fasa sallar sukayi nan fada ta dauki zafin da gaske cikin mintuna kalilan magana tafara spreading cikin fada,

Cikin masallacin babu wanda baisha mamaki ba sai mai martaba zallah domin shi kadai yasanda farkawarsa,

Mutanen masallacin sai suke ganin kamar ba Yareema ba wanda akace musu yana kwance yana jinya tsawon shekaru kusan tara,

Domin fatarsa ta murje tayi wani kyau hardan cikowa yayi kamar wanda ya tafi hutu, idan aka kallo fatarsa tabbas za'asan tayi shekaru bataga rana ba,

Waziri ciki ya duri ruwa suma tsaye yayi domin ko amafarkinsa baitaba yin makamancin wannan ba sai yakeji kamarma mafarkin yakeyi,

Yareema dakansa yaja Sallar kamar yanda yasaba har indai yananan toshi kejan Sallah, mai martaba kuwa ransa yayi fari kall,

Bayan idarda Sallah gabaki daya wajan ya kacame da murna amma wasu na ciki na ciki,

Bayan sun dan jima a masallacin sai suka wuce shashin mai martaba bayan sun isa ya sanya aka kawo masa wannan matar tambayar duniya sunyi mata amma taki tabasu amsa kawai kuka take,

Mai martaba yace "nasan dole bayin kanki bane wannan lamari domin Yareema babu wani abunda ya tare miki a rayuwa face kyautatawa da yakeyi miki ki sanar dani wanda ya sanyaki sannan ki amshi hukuncin daya dace da laifinki,

Hukunci zansa ayi miki batareda ya wuce mizanin aikinda kuka shuka ba,

Matarnan tana kuma tace "Ranka shi dade na gwammaci na karbi hukunci kowane irine daga gareka domin kare ahlina,

Mai marta ya tambayi abunda take nufi tace "idan kai ne ni kadai zaka hukunta amma sukuma wanda nayiwa aiki harda iyalaina zasu hukunta,

Mai martaba yace adauketa ayi gaba kawai ayi mata hukunci dai-dai laifin,

Suka tasa keyarta agaba suka wuce da ita,

Yareema duk yashiga damuwa, mai martaba ya dubeshi yace "Khaleefa kaje ka huta sannan kabawa matarka hakuri kayi mata ba dai-dai ba,

Mutanen nan ba karamin shiri sukayi ba karka saka damuwarsu cikin ranka,

Advertisement

Ganin mai martaba ya fahimci damuwarda yake ciki ya sanya ya maida damuwar tasa hadeda lullube fuskarsa da murmushi,

Yace "Abba kaine mai bukatar Hutu ai yanzu nikam tsawon shekarunda nayi ina hutu ya isheni amma shekarunsa bazasu dauki wannan stress dinda kake saka kanka cikiba kadaina bincikenann kabarshi wanda suka aikata wannan abun inada yakinin Allah bazai barsu hakaba,

Mai martaba ya kalleshi zuciyarsa ta cikeda nutsuwa saida ya kishingida kamar wanda zaiyi bacci ganin haka yasa yareema ya mike zai gyara masa fillon kujerarda yake, mai martaba yace "zauna abunka bawai baccinma zanyiba abunka da jikin tsufa zaman yakanyi mun wuya shiyasa yanzu banma cika fita fadanba kona fita bana jimawa,

Cikeda tausayin mai martaba yareema ya zauna gefansa a hankali yafara matsa kafarsa mai martaba yace "kanaji da kanka Khaleefa dakaje ka huta kawai abunka,

Yareema bai kulaba yaci gaba da matsa masa kafar kuma yanajin dadin hakan sosai ahaka har baccin ya daukeshi sannan ya zame a hankali bai gyara masa kwanciyarba saboda yasan yana tabashi zai mike yafita sannan yacewa masu kukada sashin karsu bar kowa ya shiga su harsai shida kansa ya nemesu suka amsa umarnin nasa kai tsaye shashin ya wuce yasamu Umma duk sun tafi nasu wajan Saura Sawwama wacce tunda ta idarta sallah takekan Sallaya jiki a sanyaye ya isa ya zauna kusada ita ta dago ta dubeshi amma bata yarda sun hada idoba ta saukarda kanta kasa,

Hafsa! Ya kira sunanta kamar yanda yaji ana kiranta bata dagoba bata amsaba,

Jikinsa yayi sanyi ganin taki amsawa ya daure yafara fadin

"Dan Allah kiyi hakuri ki yafemin na hadaki da girman Allah banda wani dalili ko hujja da zan kare kaina koda inada itama bazanyi amfani da itaba domin na cancanci hukunci daga gareki dan Allah ki yafemin na cuceki na tarwatsa rayuwarki sannan na sanyaki cikin kuncin rayuwa,

Kanta yana kasa tabashi takaicecciyar amsa "Babu koma,

Da mamakk yake kallonta dan baiyi tunanin zata sauka dawuri hakaba yacigaba da kallon fuskarsa danya gano da gaske take babu komai din kokuma tanaso ne kawai yabarta ya sanya tafadi hakan,

Da gaske kike babu komai kin yafemin har cikin zuciyarki?

Kin yafemin bazaki hukuntani ba kenan?

kamar bazatayi maganaba sai kuma ta daure tafara fadin

"Kamar yanda mai martana yafada zan iya yarda asiri ne amma koda asiri ma akwai Allah ya isata akanka,

Gabansa saida yafadi dan bai fahinci abunda take nufiba,

Tacigaba da fadin "inada tabbaci Allah ya hukuntaka da Allah ya isata wacce akoda yaushe nakeyi mata babu rana babu dare,

Toh Allah yayi maka hukunci da kansa ni menen nawa da zance bazan yafe makaba saina sake hukuntaka na tabbata duk wani hukuncin da zanyi maka bazai kai kwatankwacin wanda ubangiji yayi maka da kansa ba,

Idannace zan hukuntaka iyakaci na daina yimaka magana konace bazan zauna da aurenka ba idan nayi haka banyiwa kaina adalciba ama cire zancenka aciki dan hakan na nufin ban shirya gujewa KADDARAR RAYUWATA ba kenan, ni kaina banzanzo nasake wani aurenba wwannan aure danayishi tun lokacin na sakawa raina sannan na roki ubangiji yasa ya kasance aure na karshe da zanyi a rayuwata,

Allah yaga zuciyata abaya na kuntace ka dukda rashin sanin kokai waye kuma naroki sakayya a wajan Allah kuma inada tabbacin ya sakamin dan haka yanzu har cikin raina nakeji na yafe maka abunda yafaru bazan sake kuntatar wani kamar hakaba saboda na dauki ishara akanka,

Inacan inata amfani da fushine ina mika maka muggayen addu'oi kaikuma kananan alhali bakada masaniya akanma abunda ka aikata,

Allah yagani na yafe maka kuma har cikin zuciyata nake fadan hakan ka juya ka fuskanci rayuwarka da abubuwan da zasuzo nan gaba na Alkhairi kona sharri, Allah yabaka ikon cin jarabawarka,

Tunda take magana ya shimfide fuskarsa da wani kasaitaccen murmushi jin yayi shiru batasan abunda yake ciki ba ya sanya ta dago tayi arba da wannan murmushin nasa wanda takeda tabbacin halayyarsa kenan kawarda kanta gefe tayi a hankali ya furta nagode Allah yasaka miki da alkahiri yacire miki kuncin cikin rayuwarki gabaki daya,

Amin ta amsa a hankali, sun dauki tsawon lokaci ahaka kamar wacce bakinta yake ciwo tace "fatana kawai nayi daraja a wajanka dukda ina ganin kamar hakan bamai yiwuwa bane,

Dasauri ya ce "dan Allah kidaina fadin haka Allah sannan yace "yunwa nakeji ki taimkamin da abinci,

A hankali tatashi tanufi hanyar fita,

Umma duk a kunneta taji zancenda sukeyi domin tagama abinci a tashigo ya shiada musu sufito sai ta tarsa zancen,

Tunda taji wannan abunda yafaru ta yanke shawarar daga yanzu dakanta zatana musu abinci har zuwa yareema su tare da matarsa dn tasan tabbas mai martaba zaiyi musu gini, kokuma ruma ko Ummi idan kuma Allah yakawo miji sai Ruma tayi aurenta,

Tayi sallama sawwmaa dake shirin fita ta amsa Umma ta shigo bayan Sawwama tabata izini,

Daga tsayen da take tace "kufito na shirya abinci a falona,

Sawwama wacce haka kawai takejin nauyi da wani irin kunyar Umma ta sunkuyarda kanta tace "Toh kawai,

Umma ta juya tafice,

Harya mike ya isa wajanda take bata motsaba saida taji ya kamo hannuta da sauri da dago ta dubeshi ya sakar mata murmushi ta kawarda kanta gefe yace "muje saida ta zare hannunta dake cikin nasa sannan tafara tafiya a hankali yana biyeda ita abaya harsuka karasa wajan dining din ya zauna Umma tabata umarni akan tayi serving mijinta jiki babu kala tatashi ta zuba masa abincin sannan ta zuba nata Umma kam dana ta rigada tasaka Ruma ta zuba musu tun kafin su shigo, takasa cin abincin shikuwa gabaki daya hankalinsa yana gareta saida yayi magana sannan tataba kadan tatashi."

Waziri Allah-Allah yake agama abunda sukeyi afada yashiga wajan hajiya babba yanzuma dan bayason azargi wani abunne dacan zai wuce,

Kuma yasan labari bazaije mataba dan bata wani kowa shiga shashinta awannan lokacin,

Ana gama abunda akeyi bai zarce ko inaba sai shashinta ganinda tayi masa ahaka batareda yajira isoba ya tabbatar mata babban al'amari yake tafe dashi."

Kawatace billy S Fari 💎 tace bazan gama book dinnan a 100pges ba harda rantsuwarta😩😩 nidai banaso tayi kaffarane amma da wannan ma a half page zaizo gobe na karasa🥺 nayi hakuri zai wuce 100pges din koda da guda dayane😕."

✔️ote

Comment

Follow

Share plss

To be continued

Zaynab Alabura

💞

    people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click