《ƘADDARAR RAYUWA》K page 97
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 97
Tun acikin toilet din bayan ta taimaka masa ya tsarkake jikinsa ta fuskanci sauyin yanayi a tattare dashi,
Wani irin kallo yake mata wanda takasa gane na menene sai lumshe ido yakeyi kamar wanda yakejin bacci,
Numfashinsa yana fita da sauri da sauri ganin haka ya sanya ya janyoshi kawai suka fice daga bandakin,
Suna fitowa daga toilet din sai taga jikinsa gabaki daya ya mace kamar wanda ciwon yake shirin tashi gabaki daya ya canja yanayi ya isa gadon batareda yasake kallon yanda takeba ya kwanta a gefensa na dama, dasauri ta bude wadrope din taciro sabuwar jallabiya da sabon boxer kamar yanda tagani suke kowanne cikin ledarsa gabaki daya wadrope din abjnda yake cike kenan dam kuma dukansu sabi fill, taga dai wanda yana cirewa fita dasu akeyi, ahaka dai ta taimaka masa ya sanya amma a yanda ta sanshi a kwana biyunnan zata iya cewa yanzu kamar wanda aka sauyashi kamar wani daban bashiba,
Da sauri yakoma yasake kwanciya a gefensa na dama ta dauko ruwan addu'a tabashi ya sha ya sake komawa ya kwanta ha lumshe idanuwansa,
ganin haka ya sanya itama ta kwanta gefensa shikuwa yana kwanciya kamar wanda baccin yake jira ya daukeshi, ba ita tafarka ba sai asubahi a yanda ya kwanta ko kwakkwaran motsi baiyiba saida ta mirginashi ta canja masa wajan kwanciya sannan ta tashi tashiga toilet tafito daureda alwala taga yakoma kamar yanda ya kwanta a barin damarsa,
tabarshi a hakan ta gabatarda Sallah dake anrigada anshiga ta dade zaune akan Sallaya bayan addu'oi tayita karatun alqur'ani saida taji bacci na neman daukarta a zaune sannan tatashi ta dauko ruwan addu'an da mai martaba ya aiko ta tasheshi amma kamar baya jinta ko matsawa baiyiba nunfashinsa dai yana sauka a hankali ganin haka ya sanya kawai ya shafe masa jikinsa dashi sannan ta kwanta a gefen gadon,
yau kam bata kai kamar jiyaba dawuri tatashi tashiga tayi wanka sannan tafito ta canja kayanta tafita bataga kowa a falonsu Umma ba dan haka tawuce izuwa kitchen wanann matar ta jiya tagani wacce Umma tace mata itace wacce takeyin komai na kitchen din,
Da mamaki take kallon Sawwama domin batasan abunda yakawota kitchen dinba batama taba kallonta ba ko batasan bakowa ke shiga kitchen dinbane?
Sawwama ta kalli matar taga ita take kallo ta juyarda kanta gefe batareda ta kalletaba ta bude baki zata gaidata sai taji matar ita tafara gaisheta nauyin amsawa taji sai kawai ta maida mata da gaisuwar itama matar bata amsaba dan tasan cewa batada damar amsa wannan gaisuwa ko ba'a fada mataba tasan cewa itadin watace shigar jikinta zai nuna hakan,
Jin bata amsaba ya sanya Sawwama bata sake tankawaba tajuya tafara abunda ya kawota saboda taji Umma jiya tace ayimasa faten dankali da kifi sanna asaka alayyahu akai hakan ya tabbatar mata da yanaso ne,
Advertisement
Saida ta tanadi duk wani abunda takeda bukata sannan tafara aikin itadai matar kallonta kawai takeyi bataso ta hanata kuma taje tayi laifi tunda batasan ko wacece ba,
Sawwama bata matsa a wajanba saida tagama komai ya jure sannan tabar kitchen din,
Iya wanda zauyi amfani dashi ta deba da ajiye sauran akan dining dinsu Umma,
Har lokacin yana bacci hakan yasa ta debi nata taci sannan ta rufe masa nasa ta zauna takira mama Sun dade suna hira samnan ta kira haleema saida suka dauki tsawon awa suna waya bayan sun gama takira hajiya suka gaisa,
Baba kam tasan yana kasuwa hakan yasa batama kirashi ba,
Har wajan shabiyu bai tashiba tana zaune tana danna waya taji Sallamar Umma amsa Sallanar tayi sannan tace tashigo ta karaso ciki ta gaidata ta amsa tana tambayarta mai jiki tace "Alhamdulillhi
Umma ta zauna tana kallonsa da mamakin irin kwanciyar dayayi,
kwana biyu har wani dan cika yayi,
Saida tanemi waje ta zauna sannna ta maida hankalinta kan Sawwama wacce tayi kasada kanta tace "ya tashi kuwa? Ko har yanzu bai farkaba?
Sawwama tace "tun jiya dai daya kwanta da dare bai tashiba na tasheshi yasha wannan ruwan da aka aiko amma har yanzu bai tashiba,
Umma ta jijjiga kai tace toh kwanciyar fa tun jiya haka ya kwanta?
Sawwama ta dago ta dubeta dan bata gane yanayin tambayarba,
Umma data fahimci haka sai tace "ina nufin a hannun damansa ya kwanta?
Eh a hannun ta kwanta koda na mirginashi sake dawowa yayi,
Umma da nisa zuciya cikeda damuwa danma yanzu damuwartata ta ragu cikin karyayyiyar murya tace "kuma naga jiya baiyi baccinba Allah dai yasa bawani sabon abun bane kuma,
Sawwama ta amsa da amin,
Suna zaune ahaka Ummi tashigo ta samesu sa'i-sa'i suke taba hira amma ita bata sanya musu baki saboda akwai rashin sabo,
Saida akayi azahar sannan su Umma suka fita don gabatarda Sallah itakuma aciki tashige toilet tayi alwala ta gabatarda nata sallan ta zauna akan sallaya tanata addu'oi,
Umma ce tasake dawowa ta sanarda ita mai martaba zai shigo dama da hijabinta jikinta sauya wajan zama kawai tayi, Umma ce tayi masa iso yashigo da sallama Sawwama ta amsa murya kasa-kasa yashigo kai tsaye yayi kan Yareema saida yayi masa addu'oi yaduba jikinnsa sannan ya juyo ya zauna a sopa dake dakin Sawwama ta gaidashi kanta yana kasa ya amsa yana tambayarta jikin yareema tace "dasauki,
Sun dauki tsawon lokaci ahaka mai martaba yakara mata yan nasihu sannan yace "aduk lokacinda kuke zaune kada bakinki yagaji da tofa masa addu'oi kuna zaune kiyita fadin
"*HASBIYALLHU LA'ILAHA ILLAH HUWA ALAIHI TAWALKALTU AHUWA RABBUL ARSHIL AZEEM*
*A'UZU BIKALIMATILLAHI TAMMAH MIN KULLI SHAIDANIN WAHAMMA WANIN KULLI AININ LAMMA*
Ki lazimci karanta *A'UZU BIKALIMATILLAHI TAMMAT MIN SHARRIN MA KHALAQA*
*LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU NIMAL THALIMIN*
In sha Allahu Allah zai dubemu sannan sai yaye mana damuwarmu,
Sawwama kanta yana kasa tace "in sha Allahu yacigaba da bata addu'oi na tsari dana kariya,
Ya dan dade a wajan Sannan yayi sallama yatafi,
Advertisement
Yana tafiya Sawwama tahau yin addu'oin tana shafa masa dama tunda can ita bakinta bamai zama shiru bane idan tana zaune toh akwai abunda takeyi acikin ranta kamarsu *Istigfari, Su Hasbunallhu wani'imal wakeel, La haula wala kuwwata illah billah*
Har akayi la'asar Yareema yana wannan baccin yanzu kuma abun yafara bata tsoro dan bata tana kallon baccin nasa hakaba,
Tayita kokari ko zai tashi amma ko motsi bayayi idan taga haka zai takoma ta zauna tacigaba dayi masa addu'a."
———————————-
Cikin week din Sadam ya shirya dawowa kasarsa akaro nafarko bayan wasu shekaru,
Hafsa ganin dagaske tafiya zasuyi su barta ya sanya itama tace binsu kawai zataje,
Abida kuwa cike takeda zumidi dan rabonta da gida itama tun tahowarsu da Sadam banda aurensa da Hafsa ma da wayartama kwacewa yayi,
Kowaccensu na ciki na ciken kawai amma ita Abida dake bata iya boye abunda yake cikinta sai ta fiddoshi haka yasa bata iya boye damuwarta dake ciki na dawoda Sawwama dayace zaiyiba tasan irin sonda yake yiwa Sawwama bata nanma bata isheshi kallona bare kuma ace yanzu tadawo,
Tanada yakini cewa idan yanzu Sawwama tadawo toh zaiyi mata soyayya ne fiyeda yanda yayi mata abaya zai riketa gam kuma ba mummy ba koma wacecce bazai yarda tasake rabashi da itaba,
Ita dai wannan lamari sam baiyi mata ba tafiso ace yakaro wasu matan da ya maido Sawwama,
Sun gama shiri tsaff lokaci suke jira suyi airport domin tashin yamma zasuyi,
Yana zaune adakin Abida amma hankalinsa yana can gida gani yakeyi kamar lokaci bazaizoba yakoma yaje aiwatarda abunda yakaishi, yasake duba agogo akaro na ba dadi mtsww yaja tsaki ya furzar da wata iska yana karkada kafa,
Abida da fitowarta daga wanka kenan ta tsaya tana kallonsa cikeda takaici,
Kasa karasawa gaban mirror tayi ta nufoshi saida tayi magana kafin yasan da isowarta, yana kallonta daureda towel yace "me kikeyi anan da bazakije ki shirya ba?karki bata mana lokaci, tabe baki tayi tace "saura awa biyu harda rabi kafin jirginmu yatashi idanma kayi hakuri lokaci zaizo amma cikin kwanakinnan duk wanda yaganka sai yaga wani zumudinda kake ciki ita kanta waccar uwar kwainanayen bata isheka kallo ba,
Zaunawa tayi gefensa ta canja murya tace "Sadam dan Allah kafasa zance dawoda Sawwaman gara ga auro wash matan daban,
Wai na mamajo kika maida nine abida? Kullum zancenki na auro wasu matan daban ance miki ra'ayin kainane tara mata kema sanin kan,,,, daga masa hannu tayi cikeda takaici tace kafada yafi sai arba'in dan haka banada bukatar ji, kai kanka kasan idanma yanzu kana kokarin kamanta adalci a tsakaninmu tana zuwa zaka daina ka canja gabaki daya saboda kasmau abunda kakeso dama abunda kake fada shine katara mata ata dalilin rashinta, kaga kuwa kdan tazo mundawo hoto,
Sadam yayi shiru yakasa bata amsa dan yasan a wannan karon kam dole saiya danni kansa ayanda yake jin daukin Sawwama idakuma ba hakaba toh za'ayi babu dadi tsakanin matansa,
Mikewa tayi ta isa mirror ta shafa mai sannan ta shirya ko kallonsa batayiba yaja trolley dinta tayi gaba,
Bude dakin hafsa tana zauna akan bed ta alamu tagama shiryawa jiransu kawai takeyi, yana kallonta itama ya fahimci tana cikin damuwa,
Sake murfin kofar yayi ya karasa ciki ya zauna gefe ta cikin sigar lallashi yace "amaryata ne yake damunki haka?
Hmmm nikam aina kusa sauka a wannan matsayin tunda ga wata amaryar zakayi, yayi murmushi dan yasan kishi ke dawainiya da ita yace "Au na manta ashefa yanzu itace zata kasnace amarya toh nacanja uwargida, tabe baki tayi tatashi cikeda damuwa zatayi waje hannunsa ya sanya yakamo hannuta ahankali ya jawota tadawo baya akan cinyarsa ya daurata, ya sanya bakinsa a dai-dai wuyanta ta lumshe idanuwa, a hankali yafara magana "Hafsa karkiyi kishi da Sawwamaty idan kikayinin haka bazanji dadi ba,
Sawwama tanada kwayun hali zakiji dadin zama da ita, nisawa tayi cikeda damuwa tace "amma fa sonda kake mata yayi yawa kaduba kaga kwanakinan kowa yaganka sai yasan kana cikin nishadi,
Kimin afuwa sannan kimin uzuri akan Sawwama nafara sanin menen so kaddara tazo ta rabani da iga bawai dan nadaina sonta ba na hakura da ita yanzu Allah yabani damarda zan maidata dole nayi farin ciki,
Sawwama nada kyawun hali sosai itace macenda nasan menene so akanta mun dauki tsawon lokaci muna tare da zancen aure amma haka Allah ya rubuta abida zan fara aura koda na sanarda ita bata kullaceniba bare ta kullaci abida,
Kinga batada hayaniya sam tanada halaye masu kyau zakiji dadin zamada ita har indai baki bata mastsalaba inada tabbacin bazaki samu matsala a wajanta ba,
Jikinta yayi sanyi sosai har kunya taji toh meyema abun kishi da Sawwama bayan wajan mijinta zata dawo?
Amma ai dole tayi kishi tunda tana sonsa kuma tanada masaniya akan sonda yake yiwa Sawwama,
Nisawa tayi ta turo baki tace "amma fa karka manya kayimin alakawarin zaka bani twins na rikesu,
Sadam yayi shiru kamar mai nazarin wani abun sannan yabude baki yace "eh toh nayi alkawari zan bakisu amma yanzu tunda mahaufiyarsu zata dawo saina shawarceta tukunna dukda nasan bazama tahana ba sai abaki hamdan saboda saboda zakubi jituwa dashi dan yana bawa mahaifiyarsa ciwon kai saboda ita batason hauaniya, Hakeeda kuma kamar yanda na fada miki batada maraba da mahaifiyarta hattada kamanninsu da halayensu,
Uhmm kawai tace sannan ta mike tana fadin "muje time, a falo sumu Abida tacika tayi famm danma yayi mata dokaciya akan kada takara shigo musu daki idan suna ciki komai zatayi tajira har sai sun fito, kuma ranta yana bace sam batajin yin laben shiyasa bata labe danjin abunda ya zaunarda suba, suna fitowa fuuu tafice tayi waje."
taxi suka kira ta daukesu har zuwa airport, suna isa bata sukabi duk wani matakin daya kamata bada dadewaba jirginsi ya daga."
Saukar cikin dare sukayi Amma dukda haka Sadam bai yarda sun sauka gidan Mummy ba gidansa suka sauka ahakan aka tattare abunda za'a tattare suka kwanta har Allah-Allah yakeyi hari ya waye yaje yaga Sawwama da yaransa."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial326 Chapters
Epic of Ice Dragon: Reborn As An Ice Dragon With A System
A young man that was always cautious with his life ended up dying in the most random way possible, buried by an avalanche.As he died, within his last moments, he heard several mechanical voices resonating inside of his head, and he was granted many wishes in the form of Skills, Fortunes, and a new Body.Now, reborn as an Ice Dragon, he is thrown into a world of fantasy that seems way too much like Norse Mythology named Yggdrasil, which is also, somehow, a Cultivation World?What a weird mashup of concepts!Accompany him as he explores this world, survives against the deadly monsters that roam this world, and fights to find a place to belong to, and a purpose to this new life.However, he is not the only Reincarnated who was given wishes, and soon enough, the world he was thrown into will be engulfed in complete chaos.
8 2451 - In Serial147 Chapters
The Great Core's Paradox
Book 1 available on Kindle, KU, and Audible! Name: Paradox Species: Snake, ? Description: A tiny snake with great potential. That was who I was. That was what I was. A tiny snake with great potential. The sole creation of the Great Core. It was just us, the Great Core and I, tucked away in our little corner of the World Dungeon. Together, we hid from the bad-things and the Coreless of the world outside - safe from the horrors that would consume us. Until, one day, the Coreless found us. Until they tried to steal away my creator. Until, with no other option, I swallowed the Great Core that had made me. Only after that did I become what I was always meant to be. At last, I became the Great Core's Paradox in more than name. [The Endless Cycle] began. Thus begins the story of a little snake zealot and his journey to greatness.
8 247 - In Serial7 Chapters
Necromancer King
Sometimes, you just want to release your pent up anger form real life. And one of the best places to do it is in a game. Ever since its launch, World of Aingarrth allowed players to fulfill their wish. Do you want to be an asshole? Go ahead. Do you want to be a shiny white knight? You do you. Players are free to choose and define themselves in the brand new VRMMORPG. It takes the world by storm. Not only by how unique the MMORPG is, but also because there is roleplay mode. It allows people to set their own settings, either fantasy towns, schools or even graveyards. Then, choose scenarios that are going to happen, like getting married or saving a princess. They would then play as the main character, and the story adapts to their decision. Kei, a 29-year-old corner store clerk, decided to try it out. He has enough of his plain boring life, where many people treat him like trash. Each time after work, he would spend hours playing the game, even if it means he must sacrifice his sleep. He sometimes plays the roleplay mode, but he is more attracted to the MMORPG mode His passion inspires a certain guild leader, who takes him in and makes him his vice. With his help, the guild slowly builds up, until it gets to be the biggest villains guild in the server. One day, after work, Kei is about to launch the game when he fell asleep. When he opens his eyes, he is surprised to find himself laying on a pedestal in a tomb. With a girl kneeling beside him. He didn't realize he was transported to another world. Nor that there were others who were transported there too. A/N : The story is being rewritten. Photo by Mike Ko on Unsplash
8 131 - In Serial71 Chapters
A Side Villain’s Ballad.
Reincarnated as a meager villain in a swords and magic novel. It is as much as one would expect. Perhaps less. On Hiatus
8 152 - In Serial10 Chapters
The Code of Life - Epic Fantasy/Scifi LitRPG Series
Strange new worlds with monsters and beasts, some to tame, some to slain. Some to make friends of as you realize you're a bigger monster than they could ever be... And you have to move and progress. Learn and survive. Only that can unlock the boxes of secrets and provide answers to the ultimate of riddles. Seemingly randomly selected, thirteen people of diverse backgrounds are given access codes to the MOLI. It offers a strange new experience that looks very seductive and engaging, with stunning graphics and alluring species, just utterly mindblowing and addictive. But, it seems nobody knows what MOLI actually is, a whole new level in VR gaming or an inexplicable transference to another universe with different worlds and their own laws and customs. The experience feels so real it’s difficult to be certain. But they have to find the answers fast because people soon start to die. *** This is not intended to be a typical litRPG series, although it uses a lot of its elements to help create the whole setting. Planning to publish a chapter a day, so be warned of the editing mistakes that are certain to sneak through. Hope to keep on fixing them as I go along.
8 168 - In Serial36 Chapters
Ganda’lfr – The Left Hand of God
The eight year old Vectre lay unconscious in his bed. He collapse because of the sudden burst of information entering his brain. The memories of his past life was now unburied and he was being made to remember who he was. An inhabitant from another world. He was from a world where monsters and magic did not exist, where advance technology ran rampant. Huge amount of information are now being process by his brain. Including his ability.
8 177

