《ƘADDARAR RAYUWA》K page 92
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 92
Kwanansu hudu agarin amma gabaki daya garin ya isheta damuwarta kawai taganta agida Hajiya kanta ta fahimci hakan shiyasa ta yanke shawarar kwana biyar kawai zasuyi su koma hakan yana nufin saura kwana daya kenan,
Hajiya Sam batason ganinta cikin yananyin damuwa har irin haka,
Ta lura idan suna zaune ita shiru kawai takeyi tana tunani idan aka sakota cikin zance sai tayi murmushin yake kawai,
Yareema kuma gabaki daya ya hanata sakatt kuma baya taba yiwa kowa magana sai ita baya sakewa da kowa sai ita idan tabar wajan ya ringa musu tijara kenan bata samun lokacin kanta sai dai idan yayi bacci,
Har su umma hakuri kawai suke bata domin sun san ta takura dayawa amma babu yanda zasuyi,
Aranar Hajiya ta snaar musu cewa washe gari zasu koma nan kuma sai hankalinsu ya karkato kan lamarin toh idan suka tafi wani hali yareema zai kasance aciki?
Karfa akoka gidan jiya, su kansu shaidane baya taba yarda ya zauna waje idan bata a wajan kuma har lokacin bai saki jiki da kowa ba sai ita, yaya zasuyi kenen menen mafita?
Izuwa yanzu basu hango mafitar ba amma da ace zau kara koda wasu yan kwanakine tabbas za'a samu mafita,
Hajiya zaune gaban mai martaba kanta yana kasa bayan sun gama gaisawa sannan tace "Abba dama nazo na sanarda kai ne cewa gobe idan Allah yakaimu zamu koma gida,
Mai martaba saida yaji gabansa yafadi a tunaninsa zau dan kwana biyu,
Shiru yayi sai can yace "Bazaku dan kara wasu kwanaki ba? Tunda kinga yanda lamarin ya kasance kada kutafi kuma abu yazo ya baci azo akoka gidan jiya azuwa yanzu bamuda wata mafita amma nasan idan kuka kara kwanaki tabbaas zan nemo mafita,
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke sannan tace "Abba nima naaso nakara kwanakin tunda dama bada niyyar kwanakin danazoba kenan naso nafi haka amma Abba hafsatu tana takure matuka tana cikin damuwa ganinta a wannan yanayin baiyimin dadiba Abba kar garin son zuciyarmu ita kuma mu tauyeta tunda mijinta ya rasu na yi alkawarin bata farin ciki dai-dai gwargwado yana daya daga cikin dalilin dayasa nazo da ita nan,
Kar yazamnaa ni banbata farin cikiba kuma na sakata a damuwa batajin dadin zaman nan idan muka koma can duk wani abunda ake ciki sai a yanke, tayi magana yanda mai martaba ya fahinceta sosai,
Advertisement
Dan haka baija wani zance ba,
Mai martaba ya nisa sannan yace "hakane maganarki kinyi tunani mai kyau shikenan yanzu kuje in sha Allah zamusan abunyi,
Hajiya tayi masa godiya sukayi sallama da fadin gobe zatazo yimasa Sallama,
Sawwama jin zasu tafi washe gari taji dadi sosai sai take ganin kamar gobenma bazata yiba,
Washe gari jirgin 12:am suka biyo suka dawo gida sai asannan sawwama taji sanyi aranta,
A gidan Hajiya suka wuni zubur sai yamma likis kafinnan tasaka driver yakaita da muhamnad da tsarabarda suka zo da ita,
Babu wanda tabawa labarin abubda yafaru agidan tacigaba da rayuwarta kamar yanda tasaba, amma sai dai wani abu guda daya shine tausayin Yareema takeji aranta ko menene ya sameshi ya kwanta ciwo haka tsawon lokaci?
Menene alakarta dashi wacce ita bata saniba? A iya tunaninta tayi amma batasan wani abunda yataba hadata dashiba.
Nisawa tayi sannan afili tace "Allah yabaka lafiya dan har cikin ranta tana tausayinsa."
Yareema yasake shiga wani hali a hankali-hankali ciwon yake dawowa yanaso yakoma kamar na baya mai martaba Umma da sauran hankalinsu ya tashi ganin abunda yake shirin sake faruwa,
Mai martaba ya rigada yagama yanke hukunci cikin zuciyarshi dai dai har izuwa yanzu bai fadawa kowa Bayan yazo ya duba jikin yareema yafito falo yasamu su Umma suna zazzaune suna kallonsa gabaki daya suka mike shikuma ya zauna akan kujera sannan suka zauna a kasa,
Yadubesu zuciya cikeda Damuwa yace "Ga dukkan alamu abunda banaso shine yake shirun sake faruwa jikin yareema yanaso yasake dawowa kamar nabaya,
Bamuda tabbacin abunda yake faruwa gameda wancan yarinyar (Sawwama) amma inada yakinin cewa akwai wani abun dake kulle tasakanin wannan ciwon dakuma ita yarinyar bamu saniba ko Allah ya rubuta cewa warakarsa na tareda ita shiyasa tsawon lokaci mukayita neman magani Allah baiyiba amma gashi a mintuna kadan da haduwarsu sai Allah ya nuna mana ikonsa, yanzu gashi tatafi abu yanaso yadawo,
Shiru yayi sannan yacigaba da magana "narigada na yanke hukunci cikin raina amma yazama dole na shawarceku matsayinku na mahaifansa zan tafi dakaina har can garin na nema masa auran wannan yarinya domin hakan shine kawai mafita,
Umma wacce itama ayanzu tasan batada wata mafita data wuce wannan dari bisa dari tabawa mai martaba goyon baya,
Amma sai dai ita yarinyar basusan ko cewa zata aminceba, amma zasu fara tunkarar Hajiya da maganar kafin akaita gaba,
Mai martaba yace "idan Allah yakaimu gobe zan tashi natafi can kuma inaso har naje nadawo babu wanda zai san abunda yakaini,
Advertisement
Da mamaki suke kallonsa da sukaji abunda yafada wai gobe zaije can, mai martaba da kansa zaije akan wannan maganar shida bama mutumbe mai son tafiya ba, barinma da akace yareema ya kwanta rashin lafiya sam baya nisa da gida saboda tsoron abunda zaije yazo,
Umma cikin ladabi kanta yana kasa tace amma Mai martaba daka tura wani basai kaje da kanka ba koda wasu daga cikin amintattunka katura za'aje kuma zasuyi abunda yakamata,
Mai martaba cikeda damuwa yace "wannan lamari yanada muhimmanci sosai a wajena bai kamata ace nayi wasa dashiba bayan ku nan dana sanar daku babu wanda zai san abunda zai kaini, kuma na gargadeku karkowa yasani,
Umma tace "in sha Allahu babu wanda zai sani, mai martaba yace "Allah yayarda akowani lokaci yana fada musu su boye samun lafiya da ciwon Yareema bawai dan yana tunanin zasu fada ba sai dan kawai yanaso yasake jaddadawa."
Da dare Hajiya na zaune wayarta tafara ruri tana dubawa taga mahaifinta da sauri takai hannunta taja ta amsa kiran cikin ladabi ta gaidashi ya amsa cikin hikima mai martaba ya zayyana mata abunda yake shirin faruwa da kuma wanda yafaru m bayan tafiyarsu,
Hajiya tayi shiru sai can tace "Abba ni aganina hukuncin daka yanke bayida laifi hakan yayi yareema danane ni kaina mai bashi aurene ya aura ko aysha akace a aura masa a yanzu banida jaa zan bashi zuciyata daya kuma hankalina kwance amma dubada condition dinsa a yanzu bana tunanin Hafsa zata amincewa auren kokuma zatayi farin ciki da auran Abba rokon danakeso nayi maka guda dayane in sha Allahu gobe zan kirata muyi magana kafin kazo amma har indai bata amince ba inaso kayimin wannan alfarmar kada a tilastatta ko abi ta wajan mahaifanta yanda zasu sanyata ta amince, inaso tayi farin ciki tayi aurenta zai sanyata farin ciki tasamu nutsuwa fiyeda yanda tasamu wajan Abubakar lokacin yana raye,
Shiru mai martaba yayi jim kadan sai kuma yace "toh shikenan Allah yakaimu goben nayi miki wannan alkawarin babu wanda zai tilastata, amma kifara magana da ita tukunna kafin na iso jirgin rana zamubi bayan azahar in sha Allahu zamu iso,
Hajiya tace Allah ya kawoku lafiya sannan sukayi Sallama."
Wa she gari ta sassafe Hajiya tafara aikan abubuwan da za'ayi na bukatar wanda za'a tarbi baki dasu,
Wanda zatayi ordernsu kuma tun adaren jiya tarigada tayi karfe tara takira Sawwama tace tanason ganinta batareda wani tunani ba Sawwama tadauki muhammad dake su Hamdan suna makaranta tataho,
Ganin ayyukan da akeyi ya sanya tmdaga zuwanta itama tashiga aikin cikin kankanin lokaci suka gama tangamrmen falon Alhaji na tarban baki aka sake gyarawa dukda koda yaushe acikin gyara yake aka jere abubuwan acan lemu kuma da na kanti da wanda suka hada da kawunansu aka sanyasu a cikin firiji,
Sai bayan angama aikin Sawwama tasamu zama Hajiya kam bata samu zamaba domin tasa anata gyaggyara ko'ina dan mai martaba wannan karonne zuwansa na biyu gidanta da rasuwar Abubakar sai wannan ko auran yaranta yazo daga zaran an gama daurin aure daga can yake wucewa,
Shi kansa alhaji ya kansile duk wasu schedules dinsa na ranar ya gayyaci wasu daga cikin abokanansa kawai suna jiran zuwan mai martaba."
Hajiya babba tana zaune rohoto ya isota cewa mai martaba zaiyi tafiya da garinda zaije amma sai dai basusan abunda zai kaishi ba Hajiya Babba tashiga taraddadi sosai domin mai martaba baya tafiye-tafiye shi sam idan yabar gari kuwa toh zaije Kasar saudia ce, sai kuma wani Babban lamari dan haka gabaki daya hankalinta baikawo mata cewa wai zaije nemawa Yareema aure bane amma duk da hakan ta sanya ayi mata binciken abunda zai kaishi garin."
Saida sukayi sallar azahar sannan Hajiya tasake wanke ya shirya cikin Lace tazauna a dakinta sannan ta nemi ganin Sawwama,
Sawwama tamikr tabar muhammad wajan Aysha dan tasan maganace mai muhimmanci tunda a uwar daki za'ayita,
A zaune tasamu hajiya akan Sofa dake cikin dakinnata saida gabanta yafadi dan wata iriyar kama da Hajiya tayi mata da Abubakar, gabaki daya shima kamanninta ya dauko,
Dakyar ta iya saita kanta dan hawaye ke son gangarowa a idonta ta maidasu sannan ta isa da Sallama Hajiya ta amsa tana sakar mata da murmushi zama tayi kasa nan kan carfet kanta yana kasa tace "Hajiya gani,
Hajiya tadade tana kallonta ahaka takasa furta komai jin shiru yasa Sawwama tadago taga ita Hajiyan ke kallo saita maida kanta ta sunkuyar Hafsatu! Hajiya ta kira sunanta a hankali ta amsa da fadin "Na'am,
Iska Hajiya ta furzar Sannan tace."
Nayi test jiya shiyasa jiya da shekaran jiya kuka jini shiru na tsaya na dan taba karatu, Allah ya taimakemu baki daya ya biya mana bukatunmu na Alkahiri nagode sosai da Hakurin da kukeyi da yanayin typing dina in sha Allahu komai yakusa zuwa karshe nahuta kuma ku huta. Sai dai comment dinku yayi kasa sosai😩😩 dan Allah kudaure kuna comment dayawa ko zan samu naji karfi nagama tashi daya."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial60 Chapters
Goblin Progenitor
Jon was finishing up another horrible date, one among many, thinking about how alone he felt now more than ever. When suddenly fate shined its bright headlights of Resurrection onto him.Lighting up a path to never feeling alone again! In a goblin horde!? As the mythical Goblin Progenitor! I would like to apologize in advance for the first few chapters - as they are not super coherent in grammar or past present tenses. I try to improve as I go, the further chapters I feel are a lot better. I will keep striving to improve the story and fix things when the chance presents itself
8 588 - In Serial13 Chapters
True.Love.Crossing.Worlds. (TLCW)
Before TLCW A Meeting of Souls, there was just TLCW The story is the previous draft that I took down before I started posting the rewrite. This has been told me from a number of sources, that I should still have my previous draft posted, but with the notification that it's being rewritten. So, for those of you are new to the story, enjoy, but please check out the rewrite as well. Harry Potter has lived nine lives, each time failing to complete his true destiny. However, the fault doesn't lie solely with him. Betrayed, manipulated, and eventually enslaved by those he loved and trusted, success was always beyond his reach. He knows something has to give. He's willing to do just about anything, even if it means changing everything. But he can't do it alone. He'll need allies, and perhaps a real shot at love if it's not too much to ask. Follow Harry as he navigates the afterlife and gears up for the Final Attempt to save his world.
8 71 - In Serial6 Chapters
How a Skeleton Became The Ruler Of The World
A game and anime geek dies and ends up in a fantasy world as an undead. Upon awakening, he hears a voice:"[Mission - conquer over 80% of the world]," read and experience along with the hero his adventures on his way to world domination. The MC is intelligent and can be cruel. You will see the change he goes through after being reborn and who he will become to dominate the world. It will be a combination of fantasy and kingdom building, but there will be no shortage of adventures as he will have to raise his levels to advance his kingdom. The world in this novel is huge as you will find out in the book itself. I ask all readers to leave comments, ratings and followers. I respect and expect constructive feedback but it's worth reminding you that like some, I'm just a novice writer.
8 109 - In Serial8 Chapters
Optic Mage
Aiken, 25, gets summoned to another world as a 15-year-old student mage with a unique ocular ability. In his pursuit to figure out how he can go back home, he realises he must ensure an old prophecy comes true. However, this prophecy requires him to join the bad guys and bring about the destruction of the new world. If he doesn't, it may spell doom for the old world he wishes to return to. [Credit]Photo from Bruno Felixhttps://instagram.com/iambomani/ Check out my edgelord book:https://books2read.com/u/mgg7dD
8 165 - In Serial16 Chapters
Wattpad India Awards 2020
Welcome to Wattpad India Awards 2020An annual celebration of the diverse, creative, and empowering stories from Indian writers. A celebration of stories that open our hearts and change the way we think.This is the second year of the Wattpad India Awards, and we're excited to announce that the submissions for the awards will open on 26th October 2020, 2 PM (IST).
8 117 - In Serial28 Chapters
10 things I love about you | Benedict Bridgerton
A Bᴇɴᴇᴅɪᴄᴛ Bʀɪᴅɢᴇʀᴛᴏɴ Sᴛᴏʀʏ𝙒𝙝𝙚𝙣 𝙀𝙡𝙚𝙣𝙖 𝘽𝙚𝙣𝙣𝙚𝙩 𝙛𝙖𝙡𝙡𝙨 𝙞𝙣 𝙡𝙤𝙫𝙚 𝙛𝙤𝙧 𝙩𝙝𝙚 𝙛𝙞𝙧𝙨𝙩 𝙩𝙞𝙢𝙚"I didn't know what to write, so I listed 10 things I love about you."𖡼.𖤣𖥧𖡼.𖤣𖥧𖡼.𖤣𖥧𖡼.𖤣𖥧
8 95

