《ƘADDARAR RAYUWA》K page 91
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 91
kwance yake yana bacci ahaka baza'a taba cewa yanada matsala ba da bataji ana zancen bayida lafiya ba toh da sai tace baccin jin dadi kawai yakeyi fatar jikinsa sheki kawai takeyi irin wacce hutu ya amsheta,
Da dukkan alamu wannan fata tadauki lokaci bataga ranaba Ta tsura masa idanuwa tana kallonsa,
Bazata taba cewa majinyaci bane ahaka domin bbu alamun jinya ajikinsa, kallonsa takeyi tun daga sama har kasa ta tsaida idanuwanta a yattsun kafarsa sai kuma tasake dago kwayar idanuwanta har izuwa zara zaran gashin idanuwansa, sai take ganin kamar tasan fuskarsa awani waje,
A'ina kenan toh? Mutumin da akace yayi tsawon shekaru yana jinya kwance baimasan yanda yakeba,
Sai dai idan yayi mata kamada wani wanda tataba kallo,
Zama sukayi gefen gadon da yake dukansu ita kuma tazauna a side drawer dake jikin gadon kamshin turare taji mai masifar dadi tun shigowarsu takejin wannan kamshin gabaki daya rayuwarta sau daya ta taba jin turare mai dadinsa,
Umma tadubi Hajiya tace kinga dannaki koh? Gashinan yana baccinsa yanzu haka zancen danake miki yakai 1week yana wannan baccn
Sai jiya da jikin yataba shi hakanma bai bude idanuwa ba yanzu baifi yafarka sau daya a sati ba,
Kuma abun mamaki ba wata na'ura aka sanya masa da zata taimakeshi ba iko kawai na ubangiji ne,
Koda ya tashi sai dai ihu kawai yakeyi banda ihunsa shekara da dama banji muryarsa ba,
Hajiya tace "Allah ka dubi lamarin wannan bawa naka kabashi lafiya su duka suka amsa da amin,
A hankali Sawwama ta furta Allah ya yaye masa yabashi lafiya Umma tadubeta tadanyi murmushi sannan tace Amin,
Sun dade a zaune sunayi masa addu'oi sannan suka mike da niyyar fita itama Sawwama ta mike tafara tafiya a hankali,
Caraf taji an cafke hannunta atsorace ta juyo tadubeshi idanuwansa suna kulle kamar yanda tabarsu amma hannunsa yana rike danata gam,
Jan hannun tayi a hankali amma taji shi gam danba rikon wasa yayi mata ba,
Dayan hannunta ta sanya tayi amfani dashi dan raba hannusa da nata amma ko gizau hannun baiyiba, ganin bata tahowa ya sanya Hajiya juyawa tayi mata magana sai taga abunda yake faruwa ta kalli hannun sannan ta dubi Sawwama ta sauri ta karaso wajan ganin tajuya yasa hankalin Umma itama yakai wajan hardasu Ummi da aysha suka juyo,
A hankali umma tace "kiyi hakuri sannan ta sanya hannu zata raba hannu Gam taji hannun arike,
A fili ta furat "Yareema! Yareema! Yareema ka farka ne? Tayi magana ne duk da tasan cewa bazai san metake yi ko cewa ba,
Sake mata hannunta Yareema kaji?
Shiru dai bai motsa ba, a hankali ta sake kama hannun zata cire ta karfi ya jawota ta fado kansa da sauri tafara komarin mikewa sukam mutanen dakin tsayawa kawai sukayi kallon ikon Allah,
Umma tsoronta karya shaketa kamar yanda yataba shaketa shekarun baya dasuka wuce dan haka ta isa ta rikota tana shirin kwacota daga hannunsa kamar wanda aka tsikareshi ya bude ido, akan Sawwama ya saukesu,
Advertisement
Itama shi din take kallo idanuwansu ya hadu waje daya murmushi ya sakar mata Sannan cikin mamaki da al'ajabi ya furta kinzo? babu abunda sukayi miki?
Umma dake tsaye akansu saida ta zauna dabass akasa dan tsakanin mamaki rabonda taji muryar danta yayi magana an doshi kusan shekara tara,
Hajiya ta karaso dasauri tana fadin yareema! Yareema Alhamdulillahi kana jina? Kana cikin hankalinka kallonta yayi da alamun rashin sani a fuskarsa bai kulataba ya juya ga Sawwama yace "babu abunda sukayi miki
Sawwama sai tayi amfani da wannan damar tace "eh babu sakeni na tashi na zauna dasauri yakai kallonsa wajan hannunta daya rike sannan gata kuma kwance a ajikinsa, saketa yayi dasauri a fili ya furta kiyi hakuri,
babu komai tace sannan ta mike,
zata zaune can gefe yayi saurin rike hannunta yace "ki zauna anan tsoro nakeji karsu sake zuwa sutafi dake babu musu ta zauna dan har ita cike takeda al'ajabi yanzu mahaifiyarsa tagama fadin rabonda taji muryarsa yafi shekara takwas yanzu kuma gashi nan yana mata magana garau zatt mai hankali kai hakan yake nufi kenan?
Dakyar Umma ta iya mikewa daga yanda take tazo jikinsa ta rumgumeshi sosai tana kuka tana yiwa Allah hamdala saida tagama kukanta bai kulataba tayi masa magana yaki amsawa hankalinsa yana kan Sawwama gabaki daya,
Daga karshema hannunta yasake kamaw yarike gam kamar wacce za'a kwaceta,
Kowa yayi masa magana adakin yaki kulawa ko dagowa bayayi ya dubesu, itadai Sawwama ita kanta bazatace ga halinda take ciki ba a yanzu tarasa abunda yake faruwa gabaki daya takasa gane komai kanta ya kulle,
Umma tacewa ruma takira mai martaba da sauri tafice tashiga mota lokaci kalilan ta isa shashinsa batareda an tsayarda itaba aka barta tashige saida tazo shiga falonda yake a zaune sannan akayi mata iso a falon tasamu Hajiya Babba shiyasa batayi gigin sanar da mai martaba abunda yake faruwa ba, ganinta a birkice ya sanya mai martaba yadauka jikin yatashi dan haka yabiya suka wue can kai tsaye,
Hajiya Babba kuwa taji dadin wannan lamari domin itama a zatonta jikinne yatashi shiyasa akazo neman mai martaba, yan wahala tafadi bayan fitan mai martaba ta rigada tasan wahalarda kansu kawai sukeyi amma Yareema bazai tana samun lafiya ba,
Sashinta takoma saboda tasan idan jikin yatashi mai martaba yatafi to acan yake raba dare,
Abunda yaje ya samu yasha bambam da abunda yayi tsammani mai martaba yayi murnar wannan canji da aka samu daga wajan Yareema haaliafa kuma ya gargadi,
Amma sai dai abunda yakasa sani shine menene akalarsa da Sawwama? Menene Alakarta da ciwon Yareema da yana kallonta kaso Hamsin daga cikin ciwon da sukayi shekara tara suna magani bai kauba sai yanzu?
Mai martaba yaje ta dayan gefen ya zaune yace "Yareeema yaya jikin kana jina?
Ance kayi magana nima kayimin magana naji,
Yareema ya kalleshi sanna ya juyaga Sawwama yace "karki kulasu mugayrn mutanen ne zasu cutar dake,
Sawwama ta girgiza masa kai tace ba muggaye bane kuma bazaku cutarda kowa ba yan uwanka ne idan sunyi maka magana kana amsa musu,
Dagowa kansa yayi ya dubi Umma dasauri tazo tazauna kusa dashi tace "Eh eh yareema mu yan uwankane ba zamu cutarda kaiba, ni mahaifiyarka ce nima haifeki ka kalleni kayimin magana ko zanji dadi,
Advertisement
Kallon Sawwama yayi yanaso ta gaskanta masa zancen kai ta daga masa alamun eh dagaskene abunda Umma tafada,
Murmushi kawai yayiwa umma Mai martaba yace "yareema kallo ni nan ka gane ni waye?
Ya juya wajan Sawwama yace" wannan fa shima ba mugu bane?
Sawwama tace eh ba mugu bane, waye shi? Ya tambaya shiru tayi dan batasan menene alakarsa da mai martaba ba,
Mai martaba yace "ni kakanka ne nine mahaifin babanka, ina baban nawa yake? ya tambaya,
Allah yayi masa rasuwa, jijjiga kai kawai yayi hannunsa yana cikin nata firr yaki sakinta tagumi kawai tayi da dayan hannun tana kallon ikon Allah,
Ajiyar zuciya ya sauke yace "ashe bamasu cutarwa bane toh amma mutanneda suka kamaki ina suke?
Sawwama da batasan amsar tambayarsa ba tayi shiru kawai tana kallonsa duk cikinsu ma babu wanda yasan abunda yake nufi,
Mai martaba yace kuzo muje waje nagano wani abun dangane da abunda yake faruwa yanzu,
Yacewa Sawwama kiyi hakuri ki zauna anan yanzu zamu shigo kai kawai ta gyada musu Umma tace "kana ganin babu matsala idan anbarsu su kadai?
Yace "babu komai, fita dukansu sukayi yana kallon sun fice ya sake rike hannunta da karfi yace kiyi hakuri kinji bazan sake bari wani abun ya sameki ba bazan sake hannunki ba,
Sawwama kallonsa kawai takeyi tarasa abun cewa,
Suna fita Mai martaba ya dubesu yace su sallami duk yan aikin da suke ciki babu bata lokaci duk wasu masu hidima na sashin Umma aka sallamesu yarage saura Umma, ummi, Hajiya Aisha, ruma dashi kansa mai martaba,
Yadubi Umma yace "toh Alhamdulillhi inaga ciwon Yareema yakusa zuwa karshe dan yanzu zamu iya cewa hamsin cikin dari na matsalar takau tunda har yayi magana kuma alamu ya nuna yasan me yakeyi amma saidai wannan yarinyar ita kadaice acikin tunaninsa da rayuwarsa dole akwai wata alaka data taba hadasu akwai alaka kai karfin gaske a tsakanin wannan lamari,
Mun dade muna magani Allah bai kawo sauki ba ashe saukinsa yanaga gareta sai yanzu Allah ya turo manada ita,
Ba shakka sun san juna kafin wannan abun ya sameshi,
Hajiya tace Abba bana tunanin haka saboda har yanzu ko shekara ashrin da daya ina tunanin bata ida rufawa ba kaga lokacin da wannan abun yafaru kenan tana karamar yarinya kuma bata taba zuwa nan garinba koda sau daya zanyi mamaki idan akace sunsan juna,
Mai martaba Yace " yanzu kishiga kiji ta bakinta mikewa tayi dan cika umarnin mahaifinta,
Bayan tashiga kamar yanda tabarsu haka ta taddasu yana makale da ita,
Zama tayi gefen Sawwama ta dafata cikin kulawa tace Hafsatu kiyi hakuri da abunda yake faruwa,
Murmushi karfin Hali kawai Sawwama tayi Sannan tace "bbu komai,
Hajiya tace "Hafsa ko kin sanshi ne?
Sawwama tayi shiru sai kuma ta girgiza kai tace "bansanshiba Hajiya,
Amma kiyi tunani baki taba kallonsa wani wajeba?
Sawwama tace bantaba kallonsa ba nima saida nayi tunanin haka amma bantaba kallonsa ba,
Hajiya tace "ikon Allah kenan shi kadai yasan abunda yake kulle a acikin wannan lamari,
Zuww tayi ya sanarda mai martaba yanda sukayi,
Mai martaba yace "toh itama batada amsar wannan lamari yanzu haka amsar da zata warware wannan abu tana wajansa dan shikam tabbas yasanta ayanayinda yake yanzu bazamu samu amsaba,
Amma muci gaba da addu'a sannan ayita zamuci gabada magani bazamu tsayaba har muga yanda Allah zaiyi damu sannan basaina fada mukuba bayan mu da muke nan banaso wannan zance yafita ko'ina,
Yanzu kukoma ciki saboda zamanta ahaka zataji babu dadi har muyanke abunyi,
Mai martaba yatafi ransa cikeda jin dadin wannan hali dayaga jikannasa aciki,
Ahaka suka koma suka samesu yana nan rikeda ita ya dubi Sawwama a hankali ya rada mata yunwa nakeji,
Umma dake gefensa taji abunda yace "dasauri ta mike dakanta tayi dining ta debo masa abincin da aka jere musu danyin dinner ta daukoshi a plate jikjnta har rawa yakeyi ta zauna gefenaa tadauki spoon ta debi abincin sannan takai bakinsa,
Batareda gardama ba ya bude bakin ta zuba masa a hankali yake ci tana bashi harya koshi,
Bayan yagama yadubi Sawwama yace "bakyajin yunwa ne?
Murmushi kawai tayi bata bashi amsaba,
Hajiya tadubi Aysha da ruma tace "ku kawo mana abincin gabaki dayanmu nan sai muci, suka mike suka debo abincin Sawwama kasa ci tayi saida Hajuya tayi magana tadan tsakura kadan tabari muhammad dama shikam yana jikin hajiya ita ta bashi harya koshi,
Yasaba da ita sosai hakan yasa bai nemi zuwa wajan mamarsa ba,
Anan suka raba dare murna da farin ciki bai barsu sun iya rintsawa ba barinma umma datake ganin kamar idan tatafo zai sake komawa bacci,
Saida bacci ya daukeshi Sannan sawwama tasamu da zare hannunta, wani daki dake cikin sashin suka ta kwanta amma bata iya bacci ba,
Tunanin abunda yafaru dakuma wanda yake shirin faruwa kawai takeyi amma takasa gane komai domin kwakwalwarta ta tsaya cak tadaina wani kissafi,
Tashi tayi tadauro alwala tacigaba da Sallah akunnenta aka kira a sallatu har aka kira sallah tayi raka'atanil fijr sannan ta gabatarda sallar asubahi sai asannan bacci ya dauketa,
7:am Yareema ya tashesu yana neman yanda take aysha tazo ta tasheta, taje tasamu halinda suke ciki yana ganinta kuma sai ya lafa, breaskfast kanma ki yayi kowa yabashi sai ita zallah,
Haka suka wuni a zaune tagaji tazama ji takeyi kamar tafashe da kuka da ita dayace adakin tasan kuka zata saka tayi mai isarta,
Yanzuma taki magana domin tana kallon idan tafara kukane zai kwace mata,
Wai meyake shirin faruwa da itane? Menene hadinta da wannan yareeman da baya samun nutsuwa sai idan tana wajan?
Zuciyarta azalzalarta kawai takeyi ji take kamar tayi tsuntsu takoma gida dan bazata iya zama irin wannan zama maras makama da alkibila wanda sun kansu basusan me suke ciki ko wane hukunci zasu yanke ba."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial114 Chapters
Sir Crabby (Progression Litrpg)
It was just another day at the coast when a life was changed forever. What started as a prank for a young girl resulted in the elevation of a crabs existence. Now, wrenched from it's happy life at the beach, the crab..... HAS AWAKENED. Sir Crabby, a mundane Ghost Crab, finds himself thrust into sapience. Into a world filled with creatures both mundane and magical, a world where Evil lurks beneath the waves. Join Sir Crabby as he travels beneath the ocean; discovering power, adventuring forth and searching for his young friend as he's thrust into the Eternal Conflict of Arthos. Reviewer's rave: "It's like Thundercats, but with crabs." Release Schedule: Currently MWF, with a return to M-F within the coming weeks. This is my first novel, and I'd love any feedback.
8 161 - In Serial7 Chapters
A Soothing Melody for the Bleach-Stained Ego
You have been cordially invited to an interview and meeting with yourself. Please, do not relax - there's still plenty work to be done.
8 188 - In Serial45 Chapters
Rome on Middle Earth (ROME)
The legions of rome were about to go back to their camp after recently winning another battle when a flash of light from the sky blinded everyone, next thing they knew there is mist around them and 13 dwarves and an old man with a pointy hat running towards them with a horde of goblins chasing them. Watch the Legions of Rome fight their enemies as once again they make the world tremble as they participate in earth shaking battles, Battle of the six army, Battle of Helms deep, Battle of Minas Tirith, and Battle of the Black Gate. Cover Art Credit: Leo Karpacz I do not own any characters and images in the story.
8 154 - In Serial7 Chapters
Survival Mage
When ken was a young boy, he became insatiably fascinated by the arcane. The unknown to be more precise, and he loved anything mythical. Like any young boy, he was fascinated by the legends of dragons and gods. But where others were content with the bedtime stories, he was not. When Ken accidentally unlocks his innate talents one day, he starts regretting his curiosity. While a whole new world of magic opens its doors to him, he realizes being a mage isn't all its cracked up to be. In order for new mages to control their newfound powers, they are forced into an academy to learn control and to provide better growth for their ability. Alas, there is an entry exam one must pass. But not all who enter will leave. Depending on overall score during the exam, your allotted a certain amount of resources at the academy. How do you gain more points? By killing your peers, or providing enough entertainment. Author Note: Unsure where this is going yet, just having fun writing. PS, The cover is from Google. I don't know whos it is, but it looks awesome and fits the theme. If anyone does know, or it is yours, please don't sue me. On the other hand, if anyone sends me a fanart version, that'd be cool too.
8 189 - In Serial31 Chapters
Alpha Caine
#1 IN INTENSE January-March of 2019FIRST BOOK OF THE ALPHA SERIES"I will have you, Amira," Caine's hand slides from my hip where it is grasped up my side. I shiver at the sparks that trail behind his touch. His lips are close to my neck, hovering right over that one spot. That one spot that is meant for him and only him, but I still don't want to give it to him, I still hate him. Yet I'm not pushing him away...His breath is hot on my neck as he whispers seductively in my ear again. "I will have you, and you won't be so damn stubborn about it," his lips dip down into my neck and my body disobeys me as I shiver again. His voice is low and gruff once more. "You'll be screaming my name so loud, you won't need a mark for people to know you're mine."***************Contains suggestive language, swearing, violence, and minor alcohol use.UNEDITEDPart of an ongoing series.
8 233 - In Serial13 Chapters
The Will Of The Cat
A young boy must work through the hardships of training and being an average kid whilst trying to learn about a raging war with spirits. One problem: his teacher's a talking cat that is near omniscient and wants nothing to do with him. The young boy has to prevent the war, but how will he do it without any knowledge of what to do?
8 179

