《ƘADDARAR RAYUWA》K page 88
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Page 88
Sadam yayi iya tunaninsa yadauka kawai abban hafsa zaiyi masa kashaidi koya rokeshi yarabu masa da yarsane,
Hakan yasa ya shirya yatafi kiranda yake masa,
Zaune yake gaban mahaifin Hafsa bayan sun gaisa kansa yana kasa, shikuma yanata kallonsa kamar wanda yakeson gano wani abun gamedashi, gyaran murya yayi sannan yafara magana "Sadam Hafsa tayimin bayani akanka kuma ta gwadamin kaine wanda takeson aura,
Tun lokacin da take kasarmu tafadamin cewa tasamu wanda zata aura daga karshe tadawo nan da zama saboda yaron yanuna shi baida ra'ayin aurenta,
Wata rana kawai take shaidamin cewa tasake haduwa dakai anan kasar batasan abunda ya kawoka ba aikine ko karatu,
Ko ranar da ta nemi ganinka kazo da amincewarmu amma sai dai tazo mana da wani zance na daban munyiwa zancen duba da idon basira mungane cewa wannan bawani babban al'amari bane da zaisa akiyin aure ta dalilin,
Sai dai kai gar ila yau baka amince da aurenta ba,
Ni nayarda zan barta ta aureka tunda tana sonka amma har indai kai baka sonta bazan iya bari ta aurekaba saboda farin ciki nake nema mata banaso azo ayi abu ita bata samu kwanciyar hankali ba, idan hankalinta bai kwantaba muna namu bazai kwantaba,
Sadam kansa yana kasa yace "kayi hakuri baba bawai naki takaba amma sai inaga kamar baidace ya sanya rayuwarta a cikin wannan kadaicin ba abunda nake nufida kadaici shine nida ita gabaki dayanmu kananun yarane idan tayi aure zata tara zuri'a nikuma ayanzu ga jarabawar da Allah yayimin amma sai dai ni inada yarana itama wata rana zataso taga nata,
Dariya abban hafsa yayi sannan yace "itafa rayuwa ba tara yara bane kawai yake cikinta akwai al'amura dayawa wanda yanzu nasan kafara fahintar hakan, idan ita taji zata zauna bana tunanin za'a samu matsala da ita idan kana sonta ka amince da wannan auren Allah ya sanya muku albarka,
Sadam yarasa yanda zaiyi shi harga Allah bayason wannan auren shi yanzu zaifi gane yayi rayuwarsa babu mai takura masa dan bai dauki abida a matsayin abunda zai daurawa kansaba a halin yanzu,
Kansa yana kasa yace "zanyi magana da mahaifina in sha Allahu yanda mukayi dashi zan sanar maka,
Abban hafsa yace "hakanma yanada kyau amma inaso kasani kaine yakamata ka yankewa kanka hukuncinnan dan kai zaka zauna da matarka,
Amma yanzu tunda haka ka bukata kaje kayi shawarar ni inajiranka duk yanda ake ciki saika sanar dani,
In sha Allahu kawai ya'iya fadi,
Da sanyayyen jiki Sadam yabar gidan
Bayan yatafi Abban Hafsa ya sameta,
Yace mata tacire ranta akan Sadam idan Allah yasa mijintane zai aureta idan kuma ba mijinta bane babu yanda ta iya danya lura cewa babu ra'ayin auren a ransa,
Hafsa tashiga damuwa sosai jin furucin mahaifinta umminta tayita rarrashinta itama tana gwada mata cewa tacire Sadam aranta kawai dan bayason auren shikuma namiji ba'ayi masa tilas,
Ki kyaleshi idan yana sonki da kansa zai dawo wajanki kibashi space na kwana biyu kiga gudun ruwansa,
Advertisement
Sannan wannan rawar kai da zumudin da kike gwadawa akansa yakamat kina boyewa ki kama kanki, kin rigada kin nuna kina sonsa wannan ya isa idan abun yafi haka zaiyita miki feleke shi namiji haka yake sau dayawa idan kika nuna kindamu dashi zaiyita basarwa amma da zarar kin shareshi zai fara shiga taitayinsa,
Hafsa tace "amma ummi wancan karonfa fana shareshi haka shima ya shareni ko sau daya bai nemi yanda nakeba,
Wancan karon daban da wannan,
Wancan yanada wani option wanda yafiki awajansa wannan karon kuma babu, kibarshi yayi shawarar kamar yanda yace zaiyi kuma karki nemeshi harsai shida kansa yaji ya nemeki kinji?
Hafsa ta amince bazata nemeshi ba amma bawai dan ranta yaso hakanba."
Sadam yakira dady awaya yayi masa bayanin halinda ake ciki, dady yace "toh Sadam yanzu kaine wanda yakamata ka yankewa kanka shawara shin zaka zauna da ita? Zaka aureta?
A halin yanzu ka kai matsayinda zakayiwa kanka zabi babu wanda zai sake takuraka kayi abunda bakaso idan kaji kana sonta toh Alhamdulillahi idan baka sonta ka hakura Allah ya hada kowa da rabonsa,
Kazauna kayi tunani kayi addu'a,
Sadam yarasa tacewa danshi atunanin daya tunkari mahaifinsa zai samu mafita sai yaga ba hakaba,
Samada 2weeks bai nemi Hafsaba itama bata nmeshi ba,
Yarasa wanda zai tambaya shawara bazai taba iya tambayar mummynsa ba dady kuma yabar masa zabi a hannunsa,
Ya yanke shawarar ya nemi najeeb ya ji nasa ra'ayin,
Ringi biyu najeeb ya dauka batareda yayi Sallama ba yace "dan iskan mutumi sai ayita nemanka baza'a sameka ba,
Sadam yace "kaga ni ba shirme na kiraka kayimin ba idan banda kai dama anan kasar ba'acika samuba ba sai dai idan nina nemeku,
To me yake hanaka neman namu? Tunda kasan zan nemaka, ko a whatsapp saikaga dama kake amsa magana,
Mtswww yaja tsaki kai kaga banza nifa kiranka nayi danjin koke kokenka ba,
Najeeba cikin kulawa yace "ai kai dama ba'a abun arziki dakai inata nemanka amma ka tsaya kanmun iskanci mai yasa ka kirani? A whatsapp ma sako sai yayi 2days baka budeba duk kadawo wani iri amininka sai kayi kwanaki baka tuna dashiba,
Dame nace maka bana tunawa dakaine sai kayimin wannan shirmen,
Yanzu yaya matarka da baby?
Lafiyansu kalau Najeeb ya fadi adakile,
Shiru sukayi nawani lokaci sai can Sadam ya kare shirun nasu da fadin kasan meke faruwa kuwa?
Bansaniba tayaya za'ayi nasani batareda ka sanardaniba?
Sadam yace "kawar matarka hafsa muka haduda ita anan kasar kuma tadawo da zancen aurena duk wani bayanin daya kamata nayi mata nayi amma itada iyayenta sun amince zata aureni ahaka,
Narasa yanda zanyi ni gani nakeyi kamar muhakura da maganar auren kawai zaifi,
Najeeb yace "ka tsaya kayi tunani ka yankewa kanka shawara,
Cikin zafi sadam yafara fadin "wai meyasa kukemin hakane? Dady yace natsaya nayi tunani na yankewa kaina shawara kaima kafadi haka shin ni kundaina bani shawara kenan?
Bazaku duba kugani kucemin haka yakamata kayiba,
Nisawa Najeeb yayi cikin sanyin murya yace "kaga abunda yafaru arayuwarka nafarko har izuwa yanzu bada son ranka ka auri abida ba amma ga irin illar datayi maka arayuwa, bamaso ace mun fada maka wani abun kabi batarda son ranka ba asake samun matsala dukda bama fatan hakan amma ni aganina ka amince da auren yarinyarnan zaka samu sauki tunda bazaka zauna babu mataba tunda ita waccar kayi mata yaji kuma bazata tabayin fari a idonka ba ta rigada ta bakanta kanta,
Advertisement
Ita kuma Sawwama kace saboda farin cikinta bazaka dawo da itaba,
Ka aureta kawai Allah yabaku zaman lafiya,
Ajiyar zuciya Sadam ya sauke yarigada ya yanke shawarar auranta amma dayake bai samu wanda yabashi goyon bayaba sai abun ya yakasa kwanciya a ransa yanzu kuma dayaji opinion na najeeb hankalinsa ya kwanta kuma yanzu ya yanke shawarar zai aureta,
Har sunyi sallama zai kashe yajiyo Najeeb yna fadin Sawwama n lafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali,
Lumshe idanuwansa yayi ya budesu saboda yanda yaji zuciyarsa tayi mas dadi na kasancewarta cikin kwanciyar hankali,
Afili kuma yace na tambayake ne?
Banace karka kuskura koda sau daya kaje wajan da kasan zat ganka ba?
Najeeb yace "to wai meyasa?
Idanta ganka zata tuna dani zuciyarta zatayi babu dadi ta iya yiwuwa farin cikinda tasamu ya gushe na wani lokaci nikuma bazan iya jurara hakanba,
Najeeb cikn sanyayyar murya yace "ni bamu haduda itaba tana gidan mijinta ina zan ganta?
Kawoa dai inajin labarin yanda take rayuwa,
Kuma kaina nasan zakaso kasan halinda take ciki shiyasa nake neman sani,
A hankali yace "nagode
Najeeb bai kulaba sukayi Sallama,
Saida yayi 2days da waya da najeeb kafinnan ya kira Hafsa tana kallon kiransa ta washe baki cikin murna sai kuma ta hade rai, tatsaya jan aji bata daukaba saida yakusan katsewa sannan taje zata danna bata kaiga amsawaba ya katse,
Wani haushin kanta taji cikin takaicin jamaaa ajin da tayi,
Tajira ko zai sake kira shiru samada awah daya bai sake kiran ba, gabaki daya tabi tadamu kawai saita yanke shawarar kiransa yana dagawa tace "lafiya? Naga missed call dinka,
Babu gaisuwa kawai kifara tambayana lafiya?
Ina wuni tafadi adakile, lafiya ya amsa,
Cikin subutar baki tace "kai idan kakira mace sau daya shikenan dan bata daukaba bazaka sake kiraba?
Oh dama kina kusa kikaki dagawa kenan? Na kyauta kuwa da ban sake kiraba,
Ni nace maka ina kusa? Nazone kawai naga 1missed call
Dariya yayi kawai dan yasan cewa tagani,
Menene kuma na dariyar? Nace maka fa banganiba,
Toh ni nace wani abunne? Dariya kawai fa nayi ko itama dariyar laifine?
Shiru dukansu sukayi anata wajan kuma sai tura baki takeyi,
Shiya kare shirun da fadin zanzo yau kina gida?
Har zabura tayi cikeda farin ciki tace "eh ina,,,,
Shiru tayi ta hade rai kamar wanda yake ganinta tace "menene me zakako kayi?
Inaso muyi maganane amma idan bakya gida shikenan saurin cewa tayi ina gida babu yanda zance kazo,
Murmushi kawai yayi yace toh,
Toh? Toh kawai zakace?
Toh me zance nace toh zanzo,
Uhm! kawai tace "yana kashe wayar tatashi harda tsalle addu'a kawai takeyi yakasance cewa zaizo mata da zancen ya amincewa aurantane."
Hafsa taci kwalliya tana jiran zuwansa bai isoba sai yamma likis lokacin yatashi a aiki,
Tayi murnar ganinsa amma sai wani shan kamshi takeyi, cikin basarwa tace "menene ya kawoka wajena?
Ka yanke shawarra bazaka aureni ba shine kazo ka fadamin,
Dariya kawai Sadam yayi yace "yaya akayi kikasan abunda nazo sanar dake?
Zaro ido tayi tace au dagasken zuwa kayi kacemin bazaka aureniba?
Ko menayi maka da baka sona?
Shidai kawai kallonta yakeyi saida tagama yace "nadauka ke kika yanke shawarar hakan tunda baki jira kinji abunda ya kawomi ba,
Ba zuwa nayi nace bazan aurekiba zuwa nayi nace na amincewa auranki,
Dan Allan da gaske tafadi tana zaro ido,
Kai ya gyada mata tatashi ta saka ihu hadeda daka tsalle, shidai Sadam yana mamakin wace irin soyayya take masa haka, da gudu tafice adakin taje tasamu umminta yana Ummi! Ummi! Kiji waiya amince da aurena, baki umminta tasake tace ke banason shashanci ke wace irin wawiyace? Agban nasa haka kikayi wannan ihun kina murna?
Baki taturo tace "ummi ke bakiyi murna ba dayace zai aureni?
Nayi murma mana nayi murna sosai amma ke inaso kiyi hankali fada sosai ummi tayi mata, nan danan tashiga hankalinta takoma wajansa saida akayi magrib yatafi."
Amma saida yakarfi no mahaifinta,
Bayan yakoma yakira dady bugu biyu yadauka bayan sun gaisa yake cewa "dady na amince zan aureta kayi farin ciki?
Har indai kayi farinciki Sadam nima nayi farin ciki, zanturo maka Nunbern abbanta sai kuyi magana dashi,
Dady yace "shikenan saika turo,
Dady yakira abban hafsa sunyi magana da fahimta kuma ya amince zai bashi aurenta amma yace "yaje yasamu dan uwansa wanda take wajansa suyi magana, dady yaje ya sameshi aka tsaida magana aka bada sadaki ansayan aure wata biyu masu zuwa anan kasar za'ayi zasu tattaro suzo ayi biki su koma,
Sadam baiso hakaba yaso kawai ayi auren sunacan basai sun dawoba,
Aurensu saura 1weeks su duka suka dawo daga wancan kasar,
Walima kawai akayiwa bikin babu wani shagali aure da 2weeks sadam da amaryarsa suka koma can kasar dama yabar Abida acan yabar mata duk wani abunda zata bukata bai snaarda ita yanda zaije ba."
Bayan sun dawo Allah yayiwa mijin Sawwama rasuwa dady da kansa ya toshe duk wata hanya da Sadam zai sani danya tabbata zai shiga wani hali na tausayin Sawwama matarsa kuma bazata samu kulawaba hankalinsa zai rabu kashi-kashi,
Dady yadauki mummy sukaje yiwa Sawwama ta'aziyya itama batasan cewa Sadam yayi aureba dan batada ta yanda zata sani ayanzu damuwarda take ciki kawai tafi karfinta."
Dafarko ba gidanda sukeba Sadam yafara sauke Hafsa daga baya suka ya yanke shawarar hadesu waje daya dan hafsa ba kamar Sawwama bace tsaff zata gyarawa abida zama,
Kwanasu biyu cikin gidan abida batasan dasuba saboda koda yaushe suna daki amarcinsu kawai suksha sun barta hoto,
Yanzu hakama ji tayi kamar hayaniya kuka-kuka cikin dakinsa kanta tsaye ta tura kofar dakin tashiga."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial179 Chapters
Isekai'D Shoggoth
It begins as a usual isekai story.No, wait. It's worse. It's otome isekai. And I'm the villain.Of course, there must be some kind of cheat to make up for it. It's that kind of story.And my cheat is... being a shoggoth. Which apparently includes being a genius with setting up all sorts of production. Because "engineered to be universal labor" backstory for that race, I surmise.So... Screw it, full steam ahead. Let`s see what I can make out of this world and it's ikebana-based magic. (This is a mirror. Original was posted at https://www.scribblehub.com/series/117113/isekaid-shoggoth/ - As of Sept 2, this copy had been fully synchronised with original posting.)
8.09 2755 - In Serial113 Chapters
The Doorverse Chronicles
John Gilliam, the Faceless Man, is one of the premier assassins in the world. His skills are legendary, and he's never failed in a mission. When a job goes wrong, though, he discovers that there's an entire universe beyond what he knows, one where magic and monsters exist and his skills and talents are frail shadows of the powers that be: the Doorverse. Now, John has a new job. As an Inquisitor, he's tasked with traveling the Doorverse and righting the balance on the worlds he finds. Each world is unique, and John has to learn how to survive anew every time he passes through another door. Led by his AI guide, Sara, he'll have to become more than a killer-for-hire, and more than just a human if he wants to survive the Doorverse!
8 523 - In Serial29 Chapters
Ascension of Singularity
In realms where Immortals are gods and devils among men, a Post-Human descended. Hailing from a distant realm, the Post-Human was ordered to conquer it all. But when desires and morality intersect, what is sin, what is justice? A sage can be a butcher, a tyrant can be a saviour. Only victors shall write history! A/N: Story type is largely Xuan Huan and will have irregular update schedule. Chapter length range from 2 - 3 K words each and may have some grammatical errors. While this fiction isn't my first work, I intend to continue it for some time. I hope readers understand that there will be lot of mistakes.
8 145 - In Serial19 Chapters
Valdarus Burning: Rise of Spirits
Kywen and Sundeera are nexum, soul-bonded, and they have their hearts set upon finding the second Scroll of Jakuta, unseen by the living and whispered about by the dead. The girls live on the southern tip of Hindar, and they know nothing but the centuries of peace made possible by the Jaliff Treay, the precious agreement forged by the Elemental, Spirit, Flora, and Fauna clans of seasons past as they faced the destruction of the Endless Ravage.Sundeera has just returned from a half-season of Inaru training while Kywen finds herself planning to bid the rumor-shrouded Wiovan Order at the Collaboration, a festival celebrated every two seasons with an arena for each discipline of magic: Crystal, Shade, Wild, and Root. Half performance and half test, the Collaboration allows boys and girls to bid for apprenticeships with previously warring clans, and for the first time, the celebrations are being held far from the Watcher of Clans' protected territories of the Capital.After a chance encounter with Jorrel Airmala, the second heir to the Watcher of Clans, and a shocking attack that leaves more questions than answers, Kywen, Sundeera, and Jorrel are thrust into a whirlwind of adventure, danger, and mystery that bring them face-to-face with the unthinkable.
8 519 - In Serial19 Chapters
The Immortal Supreme
On the huge and vast planet named Zhou that lies near the edge of the universe, there lay 4 continents surrounded by an ocean even bigger than all the continents combined. There is the Teolim continent in the East, the Cold North continent in the north, the Hu continent in the west, and the ever prosperous Heaven Reaching continent in the south. Every continent is wracked with conflict as cultivators roam about searching for their own good fortune to achieve Ascension and venture further in towards the center of the universe. However, good fortune does not end up in the hands of whoever wishes for it. It comes to the destined few, the Chosen of their generation such that they may surpass their predecessors and bring more prosperity to their family through their own strength. However, there are still mortals who live normal lives in the 4 continents. Every one of which have the choice to walk the path of cultivation or to continue with the peace that eternally sleeps with them in their mortal lands. This is the story of how a young boy who steps into the bloody world of cultivation willingly and realises that it was not what he hoped it was. Witness as he slowly changes his attitude towards cultivation and the meaning to be a cultivator. Watch as he slays those that determined it right to slay him. Await his rise to fame as he achieves his Ascension and ventures towards the centre of the Universe, where he will make his name known to all the Immortals and reign supreme over them! Author's note: This is my first novel and as you had expected from the title, it's a xianxia novel. It's going to take a couple years to finish so stay a while. I will need your continued support to stay strong and finish this as fast as I can for all of you. Each chapter will have 2000 words at least. Posting schedule: 1 regular chapter a week. There may be an extra one so watch out for that. There may be a few errors here and there so I would like your assistance in spotting them. Thanks for reading! P.S the cover isn't mine, you can find it here. I just edited it a bit. https://www.dandwiki.com/wiki/Sword_Specialist_(3.5e_Prestige_Class)
8 77 - In Serial76 Chapters
Sired To The Vampire King [The Series]
[MATURE AUDIENCES](Editing Stage) A 19 year old girl named Veronica Adams takes a walk through the woods and ends up seeing a vampire and she bites his neck getting killed in the process by the creature of the night , by mistake she's turned into a vampire and something else..but there's only one catch she's sired to himAce thinks she's falling for him because of the Sire bond , but this time he could be wrong. There's a prophecy going around about Ace finding his mate , but he just doesn't realize she's right in front of him.
8 343

