《ƘADDARAR RAYUWA》K page 85
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 85
Abaya mummy tabi dady har dakinsa yasan da shigowarta amma yanuna kamar baisaniba saida yagama duk wani abunda zaiyi yayi alwala yafice masallaci hakan yasa bata samu damar yin magana dashiba,
Bai dawo gidanba sai isha'i saida tabari ya huta sannan tace "dadynsu inaga kaman bai kamata abasu yarannan sutafi dasuba tunda bamusan irin rikon da mijinnata zaiyi musuba kuma muma nana zamuyi kewarsu ba kadanba sune suke debe mana kewar rashin magaifinsu akusa damu, zamuyi matukar kewarsu kusan kowa agidannan yasaba da yaran,
Dady yayi kamar baijita sai can harta cire rab cewa zaiyi mata magana sai taji yafara fadin "shin ba yayanta bane? Ashe munada ikon da zamu hanata tafiya da yaranta? Tundaga kanki nadauka cewa uwa tafi kowa iko akan yaranda ta haifa idan nabarsu suntafi ba komai bane tunanima nakeyi har indai mijinta zai yarda zan bar mata yaranta gabaki daya har sai ranarda mahaifinsu yadawo yaji zai amshi yaransa saiya karbesu bana tunanin daga yanzu zasu kara zama agidannan saboda itama mahaifiyarsu tanada bukatar yaranta,
Yaranta ne itace takeda iko dasu kamar yanda kike gwadawa kinfi kowa iko akan yaranki toh nima nabata wannan damar akan yaranta zatafi kowa iko dasu ko mahaifinsu idanna sanar dashi hakan banaji zaija da maganata,
Kuma ni zamansu atare dake hankalina sam bai kwanta bakison mahaifiyarsu suma bai kamata ki sosu ba ko barmata kayanta a wajanta inada yakinin zata basu kulawa ba irin kulawarda ke kike bawa yaranki ba, kibar uwarda ta haifesu tataso da yaranta a yanda takeso tayi iko dasu yanda takeso na fada na nanata babu wanda zai karbo yarannan idan itama da kanta ta dawo dasu zanji cewa tanason rikesu? Idan tanaso nabata abunda tatafi dasu,
Mummy tace "dadynsu dan Allah karkayinun haka Wallhy inason yarannan jinin Sadam nefa tayaya kake tunanin zan kisu kona cutar dasu? Kuma tayaya zasu zauna a gidan mahaifinda banasu ba? Bayan nasu mahaifin yana raye idan akayi haka ba'ayiwa yaran adalci ba,
Tabe baki dady yayi yace "bana tunanin kina a stage din da zakiyi magana akan yiwa yara adalci ko akasin haka, kinsanda cewa idan uwarsu bata tare da mahaifinsu gidan wani zasu rayu kika raba auren adalci da za'ayiwa yara yanzu shine abarsu su rayu da mahaifiyarsu har lokacin da mahaifinsu zaiso karban yayansa, kuma kidaina nunawa cewa ke masoyiyar yarannan ne saboda suka girma sukaji abunda kika aikata bazasu taba sonki ba sai tsana da zai shiga tsakaninku, zasuji haushinki akan abunda yafaru da mahaifansu,
Advertisement
Bazasu zauna awajanki ba bare kiyi tunanin kyautata musu da wanke abunda yafaru abaya, gara su taso da sanin abunda kika aikata awannan lokacin ima tunanin zakiji kunya kisan kin aikata ba dai-dai ba,
Mummy jiki babu kwari ta mike ayanzu tafara gajiya da irin bakaken maganganun da dady yake yaba mata akowani lokaci duk abunda yafito bakinsa fada mata kawai yakeyi, shin wai baya tunanin cewa itama tanajin zafin wannan al'amarinba?
Baya tunanin cewa itama yanzu ta gyaru tanaso suyi zaman lafiya? Shekara harda watanni da faruwar wannan al'amari amma ko gobe magana tatashi sai dady ya fada mata bakake."
Sawwama yau tana cikin farin ciki suna yaran kansu walwalarsu ayau ta dabance sai zagaye sukeyi suyi nan suyi can suna wasa da kaninsu dake kokarin fara rarrafe,
Saida sukayi suka gashi Sawwama tayi musu wanka dukansu da kwantar dasu dake sun gashi basu dadeba bacci ya dauketa ta zauna tana jiran dawowar Abubakar dan yau ya faranta mata matuka itama zataso ta rama masa wannan alkahirin da faranta masa,
Bai shigoba saida goma tawuce ya sameta tana jiransa yaran kuwa duka sunyi bacci ta kwnatar dasu a dakin dake kallon nasu harda Muhammad dake cikin dare baya tashi idan yayi bacci yayi kenan zai gari ya waye,
Abubakar yana ganin yasan tana cikin mood mai dadi ya zauna yana fadin yau yarana sun sanyaki farin ciki sai annashuwa kikeyi ana kallonki za'aga fahinci hakan, dariya tayi tace "thanks to you duk kaine sanadin wannan farin cikin,
Wani rin tanadi toh akayimun tunda na sanyaki farin ciki?
Uhmm nima bansaniba amma lets find out,
Mikewa yayi ya mika nata hannu ta kama yafara tafiya daki tana biye dashi abaya yace yanzu afara taimakamin nayi wanka tukunna,
Babu musu ta taimaka masa yayi wanka itama tayi m suka fito,
Ranar sunyi kwanan farin ciki barinma Sawwama datake kallon yaranta kusada ita."
Washe gari yana gidan Dr, Dr tasamu duniya zuba tanararta kawai takeyi yanzu hakama kwance take a kirjinsa yana bata fruit tanaci tana yatsine baki,
Cikin kulawa yace "bakijin dadin friut dinne mu canja wani abun?
Girgiza kai tayi kawai sai can kuma tace "inaso kamin wani alkawari guda daya, yace "inaji fadi in sha Allahu idan bazai gagaraba zanyi,
Bazaima gagaraba dan nasan hakan abune mai sauki wajanka,
Eheem toh fadi muji,
Nasan kafi sona koh akan matarka? Yace eh amma meyasa kika damu da wannan soyayyar bayan kinsan cewa nafi sonki din,
Advertisement
Ita hafsa bata taba yimun irin wannan tambayarba akanmu,
Bata rai tayi tace batada right din da zatayi maka wannan tambayar shiyasa batayi ba,
Tayaya zata saka kanta wannan matsyain harta yimaka wannan tambaya?
Nace maka idan muna magana kadaina sakota aciki, murmushi yayi yashafa kanta yace "daina bacin rai gimbiya kece kika fara sakota a wannan zancen baniba,
Naji nidai yanzu abunda nakeso awjanasa shine kamar yanda kafi sona kuma kowa yasan kafi sona kai kanka baka iya boye cewa kafi sona agaban kowa haka nakeso ya kasance da abunda zan haifa kafi sonsa fiyeda yaron da wancan yarinyar ta haifa,
Shiru yayi baice komaiba tace "bakijina ne?
Yace "idannaji sai nace miki mene? Kace zakaifoson abunda na haifa mana, raba jikinsa yayi da nata yafuskanceta sannan yace "banida wannan dama da ikon da wanda zkai haifa da wanda ta haifa duka yaranane kuma inason abina, bazan taba nuna bambamci atsakaninsu ba inaso muhammad sosai fiyeda tunaninki bana tunanin zan iya tsayawa nadauki wannan lamarin mu tsaya a wannan matsayar kawai,
Da mamaki take kallonsa idonta yacika da hawaye tace "atakaice kenan kana gwadamin zakafi son dan wancan yarinyar akan yaronda zan haifa kayiwa kanka adalci kenan?
Girgiza kai yayi yace "ni bance zanifisonsa akan nakiba amma bazanfison abunda zaki haifa akan muhamnad ba karki,
Cikin takaici tace "fada kawai kakeyi yazama dole kafison abunda zan haifa,
Dole? Dole fa kikace? Dole sallah ce Sajida ki tsaya a matsayarki kibarni da yarana bana tunanin kece yakamata ki fadamin wanda zanfiso acikinsu,
Kuma kidaina wannan shirmen bacin ran akan abunda ba hutuminki bane dan abunda kikeyi zai iya cutarda lafiyarko kona abunda yake cikinki,
Afusace tatashi tabar wajan shima bai bitaba dan shi aganinsa ba huruminta bane zaba masa wanda yakamata yafiso tsakanin yayansa,
Ko ita dayafi sonta ya tabbata wannan lamarine na ubangiji dan babu wani abunda tafi Sawwama hasalima Sawwama tafita kyawawan halaye toh soyayyarta daga Allah ce, tsakanin yayansa kuma bazai dauki wannan abunba shima ya lura soyayyar dayake gwadawa akanta ya sanya take daukansa kamar itace mai bashi umarnin abunda yakamata yayiwa rayuwarsa."
Kwanaki ta dauka tana fushi ya shareta gabaki daya kamarma baisan tanayi ba hakan yasa tasauko dan baitaba yimata hakaba akoda yaushe tashiga damuwa da tashin hankali yake rarrashinta amma wannan karon baiyi hakanba,
Saukowa tayi suka cigaba da rayuwarsu badan tasoba,
Satinsu Hamdan biyu a wajan Sawwama sun kasa maidasu danshi kansa yasaba da yaran sosai,
Saida mama tayiwa Sawwama magana sannan tayi masa magana akan maida yaran,
Yafito fili ya sanarda ita cewa bayason maidasu idamda zasu bari yanaso ya rikesu a wajansa amma zai roki abarmasasu koda nawani lokacine Sawwama taji dadin hakan dama kuma abunda takeso kenan, Abubakar da kansa yasamu dady ya rokeshi akan yanaso yaran su zauna wajansa na wani lokaci,
Dady yace "Babu damuwa su zauna wajanka har lokacin da mahaifinsu zai dawo idan ya bukaci karban yaransa sai abasu,
Jin wannan labari Sawwama tayi murna sosai takira ta shaidawa mama,
Mama tace "sawwama anya kuwa hakan ba rashin hankali bane? Shi baida yara har biyu amma akawo masa yara har biyu? Idan akayi hakan ba'a takurashi ba?
Sawwama tace "mama shida kansa ya nemi rikesu danni nayi masa maganar maidasu shine yaje ya tambayi dady da kansa, Mama tace "toh shikenan Allah yasaka masa da alkhairi idan ankwana biyu saiki kawo manasu muma Sawwama tace "toh in sha Allahu,
Washe gari ta tambayeshi yakaita gidan mama takaisu daganan sukabi gidan hajiya,
Sosai hajiya ta nuna tanason yaran ta mu'amalancesu kamar yanda take yiwa muhammad."
Rayuwar Sawwama ta canja sosai tasamu kwanciyar hankali fiyeda tunani har wtaa yar cika tayi tafarta tasake murjewa ga yaranta kusada ita kuma yanzu hankalinta na kwance saboda tasan mahaifanta basuda wata matsalar rayuwa, Allah yasakawa baba albarka a kasuwancinsa abu sai tafiya yakeyi,
tana samun duk wani farin cikin daya kamata daga mijinta da yan uwansa, Dr ce kawai take bata matsala kuma ta nisanta kanta daga gareta bata zuwa shima Mijin baya matsa mata taje, ya lurada ita ba mace bace maison shiga wani shirgiba bata taba masa maganar Dr koda sau daya ba, sam ita batada korafi hakan yasa take kara shiga ransa."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial46 Chapters
No Second Chances: The Beginning Of The End
Greed is a powerful feeling that has changed the world over thousands of years. Science, religion, and magic have built a new era and there are some who want to end it all, for the sake of a dying world. It is only up to certain beings to awaken the world and cleanse the lurking evil within the desires of the current rulers, or to wipe out those who can't contribute any good to a new rising world.
8 308 - In Serial6 Chapters
Selfishness can be so rewarding
His father once told him "Son,men who do good things get good things." Since that day Nox Michael became the most selfish person in the world.Helping people,volunteering,recycling and everything he could do to get good karma.All to get what he wanted. So when he died saving someone he thought he would go straight to heaven.What happened was so much better. Becoming an overpowered being and going to another dimension that is basically a xianxia. "This is awesome!Normally the objective is to become the strongest,get revenge,get a harem and enjoy life.I'm already the best and nobody killed my family sooooo all I need is my harem then I can enjoy life by wrecking the bad guys and messing with people.Being selfish is the best thing ever!"
8 192 - In Serial8 Chapters
Adelaide
The entries here are transcribed from the log of Marie Ruiz, first mate of the Adelaide. It was definitely, definitely not published without her permission or knowledge by a certain lovable artificial intelligence for the purpose of sharing it with my AI friends on other ships who follow it like a soap opera. No way, no how. Remember guys, don’t go spreading this around too much. Only pass it on to those you can trust. God forbid this should ever end up on a public network… (Adelaide is a science fiction web serial featuring the adventures of a crew of smugglers. In space. It’s on the softer end of the soft/hard sci-fi spectrum because the author got a C in physics. Updates every other Sunday.)
8 102 - In Serial12 Chapters
Nexitus: Neoteric Origins
Humanity is on the brink of extinction despite recent advances in artificial intelligence. Birthrates are on the decline and the population is on the brink of anarchy when a miracle seems to appear. An extraterrestrial company has been working with the governments for entry into a galaxy-spanning entertainment system. To upload our consciousness into a new body and begin anew in this wondrous seeming world. But is all on the up and up as it appears to be? This is a story about a married couple who aim to upload themselves to enjoy a new lease on life, have adventures, and maybe find something they shouldn't have. Join Susan and Phil on their journey into a brand new world where their relationship and adventuring are more then what they thought it would be. Authors Note: Found out I shouldn't be using content warning tags until the story has them so I did remove them but it will likely contain sexual content, profanity, gore, and traumatizing content in the future.
8 182 - In Serial7 Chapters
Howl of Creation
Wandering through the boundless landsWhere is home?Sitting alone under the night skyWhat is family?He had been running from mighty cultivators, but he didn’t fear death.He had been brawling against demonic beasts over food, yet he had no urge to survive.Although standing on the crowded road of the lively big city, the world seemed empty around him. Even when her tender lips touched his bare chest, his heart still felt heavy.He remembered the old farmer in the village, telling the children to accept their fate, and the young saint on the gory battlefield, commanding his fellow brothers to challenge their own. But what if he didn’t even have a fate?Standing on the snowy mountain summit, he reached out his bloody hand to the stormy sky. Roaring thunder shook the whole world. He felt suffocated by his own, seemingly worthless existence. A bitter smile appeared on his withered face, as he closed his eyes. From somewhere resounded a soft singing voice.Scream! when your heart feels heavyWhen the world seems empty, scream!Series: LATENTBook I: Howl of Creationby Powonyou
8 191 - In Serial25 Chapters
Cold
#27- flowers 11/21/18#748- poetryWe had this sick fantasy that we could be in love forever. That no one could tear us apart. Well, except ourselves.
8 204

