《ƘADDARAR RAYUWA》K page 84
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 84
Dr sai zagaye takeyi a gidan tarasa wacce irin murna zatayi tabbas yau ta sake tsinkewa da lamarin ubangiji idan ya rigada ya tsara abu toh babu wani tsumi ko dabara sai wannan abun yafaru babu wani shortcourt da za'a yiwa lamarin har sai iya lokacin da Allah ya tsaga,
Jikinta yayi sanyi tunowa da tayi aranarda zata samu wannan ciki babu irin wulakancin da bata yiwa Abubakar ba aranarda tasan cewa bazai saiki sawwama ba aranar tasamu wannan ciki har cizonsa saida tayi akan kada ya kusanceta batasan cewa rabo bane yake kiranta daya biye mata ya rabuda ita kamar yanda taso da bata samu wannan cikin ba, bayan daya kusanceta wannan lokacin saida tabada tazarar 2month bata bari yasake kusantarta ba, fushi tayi dashi mai tsanani ko yanzu bata gama sauka ba sai wannan lamarin ciki ya bullo,
Hawayenr yagangaro a fuskarta tasanya hannu ta share wani irin kunya, nauyi, da tausayin Abubakar ya kamata a iya saninta bata taba ganin mutum mai son kyautatawa da sanyin halinsa ba duk wani abunda take masa saboda tasan yanada sanyin haline kuma zai iya dauka amma koda sau daya bata taba taka kafarta ko tasanya wani yaje mata wajan malami ko boka da sunna ta mallakeshi ba, a ganinta soyayyar dayake mata kawai ya isa ta juyashi sai akaci sa'a soyayya ta haduda sanyin hali sai take amfani da hakan tanayi yadda taso."
Kai tsaye gidan Dr ya nufa, a tsaye ya sameta tanata zagaye falo takasa zama, tanajin sallamarsa tayi saurin jin bakin kofa kafin yakaiga shigowa cikin falon ta isa zuwa wajansa,
Rungumeshi tayi sosai sai kuma tasaki kuka amma yanayin kukanta ya bambamta da irin kukan dayake yawanyi wannan kukan anaji za'asan da farin ciki kunshe akasansa,
Shima rumguneta yayi yana shafa bayanta cikin sigar lallashi amma baice komaiba tadan jima yana kukan sannan ta dago da murmushi dauke a fuskarta hannunsa taja suka zauna kan kujera murmushi kawai takeyi takasa furta koda kalma dayane shima baice mata komaiba jira kawai yakeyi ta furta abunda takeson furtawa, rabonsa daya ganta cikin farin ciki haka yadauki tsawon lokaci kuma rashin farin cikinta ba karamin daga masa hankali yakeyi ba, yanzu kuma daya kalli fuskarta cikeda farin ciki sai yasamu kansa cikin yanayin dadi,
Ciki nake dashi ta fado zancen cikin sauri,
Tsayawa Abubakar yayi sai yakeji kamar wanda kunnensa baiji masa dai-dai ba yace "ciki? Dr ciki gareki? Alhamdulillahi Allah nagode maka ya rumguneta tsam ajikinsa shi kansa saida yayi hawaye domin kullum burinda da fatansa baiwuce itama Dr taga jininta kamar yanda shima yaga nasaba,
Yayi murna sosai ita kanta Dr dagata yanda yake farin ciki sai take ganin kamar ita bama farin ciki tayiba,
Kula ta musamman Yafara bata sannan ya hanata daga koda cup ne ya sanya ta dauki hutu a asibiti yace "takula da abunda yake cikinta kawai, Dr har mamakin irin sonda Abubakar yake nuna mata takeyi duk ta kasancewa shiba bako bane wajan nuna mata soyayya amma ta wannan karon dabanne, ya fadawa Sawwama itama tayi murna sosai har taje ta dubata rashin samun kasewar fuska ya sanya bata sake komawa ba."
Advertisement
Hajiya ma daya fada mata sai tace Allah ya sanya alkahiri ya sauketa lafiya,
Bayan Haka kuma sai tace "yaushe zaka kawo anty hafsa? Ta kwana biyu bata zoba inaso naga maigidana, dan yake yayi sannan yace Hajiya bazakice yaushe zan kawo miki Sajida ba?
Baki hajiya ta sake sannan tace "koh meyasa zance ka kawomin ita? Idan itada kanta tayi ra'ayi tazo kasan bazan koreta ba amma haka kawai bazan ce tazoba tunda ita batada kirki,
Ko azatonka dan kace tanada ciki zan fara haba-haba da ita?
Toh nafadaa maka zan kara fada maka bantaba kin wannan yarinya dan bata haihu ba saidai dan munanan halinta ko yanzu idan bata canja ba inanan nima bazan canja ba,
Allah ya amfana mata abunda zata haifa ita rabonta mai nisane shiyasa takai har wannan lokaci bata samuba yanzu da rabonta yazo Allah yabata hali kuma nanan ajikinta idan ta canja tayiwa kanta fada idan takk taje tayi rayuwarta muma muyi tamu,
Shiru Abubakar yayi bai iya cewa komaiba,
Washe gari yakai Sawwama ta wuni wajan Hajiya, Hajiya tace mata tashirya in sha Allahu watan gaba zasuje garin yan uwanta tagansu suna su ganta."
Abubakar yanzu idan yana gidan Sawwama baya dawowa sai dare sosai saboda yana wajan Dr yana kula da ita amma yaga laulayinta ma ba irinna Sawwama wanda tayi bane ita bata wani laulayi sai kawai tsirfe-tsirfe irinna ciki,
A falo ya samu Sawwama tayi wanka sanyeda sleeping dress tana jiran dawowarsa Muhammad kwance a cinyarta da sallama ya shigo ta amsa ya kasar mata murmushi itama ta maida masa hadeda yimasa barka da zuwa ya amsa hadeda karasawa ciki muhamnad ya dauka cikeda soyayya yayi masa peck agoshi yace "Babana yayi bacci baiga dawowar babansa ba, Dariya tayi sannan tace "aikuwa dai ya jiraka dan baima dade dayin baccin ba,
Rumgume yaron yayi yana fadin "banji dadiba na tsaya wajan Dr ne kuyi hakuri murmushi Sawwama tayi har cikin ranta batajin zafin dare dayake kaiwa wajan Dr ita da ya aureta abaya ma ya kulada ita sosai alokacinda takeda ciki toh inaga Dr auren shekara goma sha?
Babu komai nasan yanzu tana bukatar kulawa so yakamata a yanzu kabata kulawa, nagode Allah yayi miki albarka yafadi sannan ya shfo cikinsa yace "yunwa nakeji mikewa tayi ta tanadar masa abunda zaici bayan yagma daida yadan huta sannan yashiga wanka bayan yafito Sawwama har tayi shirin kwanciya ta kwanatrda muhammada akan gadonsa itama ta kwanta,
Turare kawai ya fesa shima yabita gadon ya kwanta jawota jikinsa yayi a kunne ya rada mata nayi missing dinki kwana biyu bana samun nutsuwa gabaki daya al'amura sunyi yawa ga zancen shiyasa ga kuma Dr dake butata kusada ita, lumshe ido kawai Sawwama tayi tana jinsa yana magana ita kanta tasan tayi missing dinsa dan sam yanzu basa samun lokaci, saukoda bakinsa yayi daga kan kunneta zuwa lips dinta ya dauki tsawon lokaci yana kissing dinta sanna ya sauko zuwa wuyanta yana kissng yanabin kowani sako yana shakar kamshin turarenta,
Kowani lokaci da salon turaren da yakeji ajikinta, wani dan tsokaci karki kasance kullum da turare daya kike amfani kikasance lokaci-lokaci kina amfani da varities na turaruka kamshi daya akowani lokaci yanada gundura wasu lokuta dayawa maza sunson sabon abu sabon yanayi,
Advertisement
Akwai mutanenda turare ya rigada ya kama jikinsu kowani irin turare kikayi amfani dashi sai wannan kamshin jikinnaki ya fito ki kasance wacce mijiki yanajin kamshin jikinki zai gane bawai da kalar turare ba, ina nufin kamshi na jiki idan kika sanya turare sai ya bada wani samfarin scente mai dadi,
Karki kasance amfani da turare daya kullum mijinki idan yaji sauyin turare a wajene kawai wata tazo wucewa yaji turarn ya masa kamshi no ki kasance mai canja turare lokaci-lokaci mijinki zai kasance mai tunanin yau da wani rin kamshi zaiyi arba, idan kika saka turare kamshin baiyi masa ba toh gaba sai akiyaye kada a sayi turare irinsa amma idan kamshi yayi masa koda gaba bayan kinyi amfani da wani zaki iya canjawa ki sake sayo wancan."
A kasalance ya dago idanuwansa suna lumshe yace "wannan wani irin turare ne? Kamshinsa yayi dadi yafadi hakan hadeda maida hancinsa wuyanta yana shakar kamshin, shiru Sawwama tayi dan batasan mai zata ce masa ba domin turarene hadeda humra kala-kala da kamshin ya hadu saiya bada wani irin kamshi mai armashi,
Kamar yanda ya fada dagaskene yayi missing dinta danya nuna mata hakan da gaske,
Kwanciya tayi ajikinsa itaba bacci takeyiba tadaiyi shiru yanayinda suka kasance dan lokaci kalilan daya wuce yana dawo mata,
Hafsa taji yakira sunata, uhmm ta amsa cikin muryar bacci,
Babu wanda zaice kin haifu a zahidir da kuma badini, a kallon fuska dakuma jikinki murmushi tayi batareda ta bude idanuwanta ba tace yara har uku kuwa, tana fadin haka sai kuma tayi shiru jikinta yayi sanyi,
Murmushi yayi sannan yace "koda sau daya baki taba zuwa kin dubasu bayan aurenmu ba kuma nima baki taba sanyawa naje na dubasu ba bakya tunanin yaranki zasu tashi da jin haushinki a ransu?
Ko saboda mahaifinsu ne ya sanya baki zuwa ki dubasu?
Jiki a sanyaye Sawwama ta girgiza kai kamar bazatayi magana ba sai kuma tace "ko daya ba saboda mahaifinsu bane kawai dai banason zuwa na dagawa yaran hankali nima na daga nawa hankalinne mama tana zuwa dubasu duk sati kuma idan taje takan kirani,
Kayi hakuri bawai ina yabon mahaifinsu agabanka bane amma shi baiyimin komai da zaisa nakasa zuwa duba yarana ba, koda yayimun ma hakan bazaisa na kasa duba yarana ba, koda narabu dashi bazan taba mantawa da taimakon daya yiwa rayuwata ba, idan bama tare zan daukeshi matsayin dan uwana na kadan daga cikin abubuwan da Sadam yayi mata ta sanar dashi amma saida yaji jikinsa yayi sanyi,
A sanyaye yace gobe zamuje dubasu idan Allah yakaimu,
Tace Allah ya kaimu, tashi ki gyara jikinki ki kwanta dan naga bacci kike kokarin yi, mikewa tayi ta yi bandaki shima yabita abaya maimakon suyi wanka kai tsaye kamar yanda suka shiga saida ya tabbatar ya sake sama musu nutsuwa kafin sukayi wanka suka fito,
Washe gari bayan yaje ya duba Dr ya dawo gidan sawwama da yamma yace ta shirya suje duba twins,
Shopping suka wuce yace tayi musu shopping abubuwan da zata kai musu, wasu yan tsirarrun abubuwa ta dauka ganin haka ya sanya da kansa yashiga debe musu kaya,
Saida yacika butt na mota da seat na bayan motan tass sannan suka tafi,
Sawwama sai taraddadin yanda zataga yaranta takeyi dukda kasancewar mama kullum taba fada mata irin kularda yaran suke samu,
Sun samu mummy da yaran agida dady yana wajan aiki itama mummy batajin dadi ya sanya bata fitaba,
Sawwama tadauka yaran zasu manta da ita amma saitaga yanda suka makala mata saida suka kusan sanyata kuka,
Mummy jiki a sanyaye hakama Sawwama banda gaisuwa babu wani abunda waninsu yakara cewa
A sace mummy ke kallonta gabaki daya ta canja tadawo wata hamshakiyar yarinya bazaka taba cewa tayi aureba,
Za'a dauka yanzu take karagan yan matanci, sai wani yalyali takeyi, kana ganinta zaka tabbatar hankalinta a kwance yake,
Abubakar bai shigoba yana waje shiga muhammad yace kawia ya fito masa da yaran ya gansu
Saida tadan jima kadan sannan ta ce zata tafi amma zata fitawa mijinta da yaran ya gansu mummy toh kawai tace Sawwama takaisu a Abubakar yadaukesu yanaji kamar shine mahaifinsu yacewa Sawwama gabaki dayansu kamarki sukayo nan gaba nima idan zaki haifamin yara zaki haifo masu kamarki ne,
Dariya kawai Sawwama tayi saboda tasan yanzu su Hameeda da hamdan sunyi wayan daukan magana dan suna surutu,
Hassana da Hussaina suka fito karban yaran Abubakar yace sufara shiga da kayan kafin yaran saida suka gama shigarda kayan gabaki daya mummy tana zaune ta zabga uwar tagumi kawai kallon kayan takeyi sai kace wani wanda zasu bude shgo,
Dakyar ta iya bude baki tace kuje ku karbo yaran dannasan yanzu suma sunaso sutafi,
Suka koma karbosu amma yara fir sunki zuwa wajansu har mummy tafito dakanta sunki zuwa wajanta,
Mummy satan kallon Abubakar takeyi aranta tana fadin irin mijinta Allah yabawa Sawwama kuma kenan yanzu?
ahaka dady yazo ya samesu bayan sun gaisa dady yace toh kushigo ciki mana, mummy tace ai sunma fito tafiya ne yan biyune sukaki barinsu su tafi,
Abubakar yace idan babu damuwa da anbadasu muntafi dasu idan suka kwana biyu sai nadawo dasu tunda yanzun sunki, batareda wani tunaniba dady yace shikenan babu damuwa kuje kawai, da mamaki mummy ta kalleshi ko kallon yanda take baiyiba godiya sukayi masa suka shiga mota suka tafi,
yawuce ciki batareda yabi takan mummy ba,
Sawwama taji dadin wannan abun sosai shi kansa saida ya fahimci hakan kai tsaye gida yakaisu ya zubasu sannan yawuce sallan magrib daganan zaiyi wajan DR."
Zuwa jimawa in sha Allahu zan karo wani
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial18 Chapters
Necrobyte
Within a valley of a ruined Earth, lies the last remaining bastion of humanity. Survivors of the war only knew capitalism. The exchange of goods and services, to work under a company, to pray for employee benefits. The free market must be allowed to exist. Every last human should work under the Company. Under the all-encompassing corporate overlords, are millions of employees. One such employee is Gin, a boy who looked far younger than normal. How will he survive in such a world? Would he be able to achieve the dream of every employee? To have enough money to become a capitalist? To retire early and to enjoy the boons of life? Only time can tell.
8 139 - In Serial151 Chapters
An Upgraded Soul
Aditya, a 16-year-old teenager dreaming of becoming a professional Formula racer, currently studying in an international school is dealing with the biggest crisis of his life. He had been informed by the police that his parents have gone missing leaving no clue behind. To add on to his misery, Aditya has been sleeping 14 hrs a day due to an unknown reason for the past two weeks. He had been dreaming an alternate world where the 'other' Aditya lives the exact same life as him. But, things became more intriguing when the events in his dream started diverging from his real-life events. For one, his parents did not go missing in his dreams. They were safe and sound. Later in his dream life, Aditya went on to continue his studies in Europe and later became an F1 racer just like he aimed for, while in real life, he got himself expelled from his school and started working in a garage as a mechanic. A world of difference.Accompany Aditya on a journey filled with many impossibilities as he comes in contact with many hidden truths the world is unaware of, in his quest of rescuing his parents.The setting is mainly focused in IndiaTags: Action, Adventure, Missing Parents, Smart Protagonist, Kind Protagonist, Romance, Harem, Friends, Subordinates, Futuristic technology, Biologically Modified Humans, Cyborgs, Genius, Mafia, Firearms, Military Technology.
8 447 - In Serial36 Chapters
Ash. The Legends of the Nameless World. Progression Gamelit Story
"The Legends of the Nameless World cycle" includes the stories of key characters of the "Dragon Heart" saga. "Ash" is the first of the prequels to the "Dragon Heart" series. It can be read as a stand-alone book.Even before Myristal went out, before the battle of the Heavens and the Earth broke out, before the Black General was imprisoned on the Mountain of Skulls, a wizard had wandered the endless expanses of the Nameless World in search of his past and his future. This is the legend of Ash, the Master of a Thousand Words, the Bloody General. What’s true and what is fiction is up to you to decide. But this is how his story was told to young children, so that they wouldn’t be afraid and have nightmares, back when the legends of the old world were still remembered.
8 219 - In Serial22 Chapters
Dust 2: A New World Order
It can always get worse… A new world order is coming, one that will pit one species against another. Life is about to become very hazardous—for anyone who gets in Dust’s way. With every day that passes, Dust is more afraid of what he will become. His powers are growing far beyond what he can predict, and he is reluctant to tell his make-shift family that he isn’t sure when—or if—it will ever stop. His goal is to get to Portland, Oregon and find his aunt and uncle. Ideally he would get there alone, because he’s far too much of a danger to the people around him, but they aren’t willing to give up on him, and an old enemy isn’t far behind. When they reach Portland, Dust discovers a line has been drawn between those who have been changed and the unchanged ones who want to control them. Can Dust protect his new family from being used or will the power within him become a force that will not only destroy his enemies, but the ones he loves?
8 452 - In Serial17 Chapters
Raising Phoenix From Today
Its an Isekai reincarnation in a Sword and Sorcery magic along with a system. Sachi Nakamura is reborn in a world of Sword and magic. She is an above average mage however a near death incident changes her life as she awakens her system entering the rebirth Island where she is the master of the sacred beast Phoenix. She is in a different universe and the system gave her Phoenix with different elements, some she heard some new. It is set in a similar universe of Raising dragons. Hope fans and readers like it and comment on it.
8 86 - In Serial7 Chapters
Love at last. (SEQUEL TO SATISFACTION BEING)
With Brooklyn's father being in jail, Mother Has a restraining order will Brooklyn and August have a Happy ever after? Will Brooklyn's parents find their way back into her life somehow??
8 150

