《ƘADDARAR RAYUWA》K page 82
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 82
Gajeruwar nakuda Sawwama tayi Allah ya sauketa tasamu danta kyakkayawa mai kamada mahaifinsa, alokacin su dukansu suna asibitin aka fito musu da yaron itakuma Sawwama ana kimtsata,
Hajiya tafara karban yaron tana hamdala saida tagama yimasa addu'a sannann ta mikawa mahaifinsa, yana karbansa bai kai idonsa kan yaronba yadubi doctor din da takarbi haihuwar yace "yaya jikin mahaifiyar yaron?
Tayi murmushi tace "Alhamdulillahi tananan lafiya yanzu hakama ana gyarata ne za'a kaita daki ta kwanta ta huta,
Sai alokacin ya samu sukunin kallon yaron kana kallonsa kamanninsu sak daya,
Shima addu'ar yayi masa sannan yasake mikawa Hajiya wani irin dadi yakeji aransa baisan lokacin da hawaye yafara gangara a kumatunsa ba shafa bayansa Hajiya tayi tace "A'a kull Abubakar godiya zaka yiwa Allah ya daga hannuwanka ga yabawa kyauta da ni'ima irin tasa kayi masa kirari da jinjina, kai dai gashi Allah yasa kaga jinki wanda Allah bai basuba ina rokon Allah ya azurtasu da zuri'a dayyiba idan kuma rashin samun alkahirin agaresu Allah ya sanya hakan yazaman silar shigarsu aljanna,
A hankali ya amsa da amin yanajin zuciyarsa tanayi masa wani iri yakasa fassara wani irin yanayine, yanada tabbacin cewa farin ciki yake ciki amma baisan tayaya zaiyi ya fidda wannan farin ciki ba domin ya cika masa zuciya gabaki daya, neman hanyar fidda wannan farin cikin dake cikin zuciyarsa yake ko zai samu sauki,
Daki aka kai Sawwama tasamu bacci, su dukansu dakin suka nufa Hajiya na rumgume da yaron shikuma Abubakar ya karasa bakin gadon yana kallon Sawwama, nisawa yayi a zuciyarsa yana tausayawa mata saboda yanda yaga tayi nakudar mai zafice amma lokaci daya,
Hajiya tace kayi waya akawo mana abubuwan da zamu bukata daga gida dan zuwa gaggawane amma inaji ma da zarar ta farka suka ga babu wtaa matsala zasu sallamemune mutafi gida sai dai kawai ina tunanin koda sun sallamemu zamu bari gari yawaye saimu tafi,
Waya Abubakar yayi cikin kankanin lokaci aka kawo duk wani abunda zasu bukata dama wanda bazasu bukata ba,
Awa uku Sawwama tayi tana bacci kafin tafarka duk wani abunda yakamata hajiya da kanta takeyi mata zuwa safiya kuwa suka wuce gida,
Agidan Hajiya suke duk wani kula itada jaririnta suna samu gashi Abubakar gabaki daya ya zauce akansu sai bajinta kawai yakeyi kaya saida Sawwama tayi masa magana akan adaina kawowa shigowa goma zaiyi gidan to da abunda zai shigowa yaron dashi, Hajiya tacewa Sawwama tabarshi yayi aida baiyiba yanzu kuma yanayine dan nuna farin ciki da godiyarsa ga ubangiji,
Mama sau daya tazo taga Sawwama ganin irin kulawarda ake bata sai hankalinta ya kwanta sosai,
Halima ke zuwa kullum tana wuni awajanta,
Har akayi 3days da haihuwa Abubakar bai sanarwa Dr haihuwar ba,
Dr na asibiti zancen haihuwar ya isketa da gabanta yahau faduwa nan danan ta rude aia taji gabaki daya babu dadi wani irin kishine ya shigeta bata taba danasanin hada aurenba kamar yanzu datasan haka zataji idan Sawwama ta haihu toda bata fara wannan zancen ba,
Advertisement
Mikewa tayi ta sanya a sanarwa duk patients dinda sukazo ganinta su komai sai gobe akan wani abu urgent yataso,
Gida ta nufa takira Abubakar tace tanason ganinsa yau za'ayi duk wacce za'ayi amma yau saiya rabuda Sawwama tunda tarigada tayi abunda aka aurota dan tayi,
Yana jin kiran jikinsa yabashi tasan abunda yafaru,
Yasamu harda isa gida jiransa kawai takeyi,
Yana shigowa tafara fadin tun datsu na kiraka aina ka tsaya?
Kallon agogon dake hannunsa yayi yace "baki wani dade da kirana ba kawai inaga kin matsune shiyasa kike ganin kamar na dade,
Sharewa tayi ta nemi waje ta zauna shima yabi bayanta ya zauna,
Naji ance Wannan yarinyar ta haihu shin hakane? Ta jefo masa tambaya, saida gabansa ya fadi amma ya dake yace "eh tahaihu
Da mamaki ta kalleshi tace shine baka gayamin ba? Bayan kasan ta haihu din kuma me kake jira? Ko karigada ka saketa ne?
Shiru yayi na wani lokaci baice komaiba tace "kaifa nake sauraro nakasa gane kanka kwana biyunnan hakuri kawai nakeyi yanzu hakama ta haihu baka sanarda niba menene nufinka?
Kuma zamanne takeyi da auranka har yanzu?
Da ka saketa tun lokacin da takeda ciki da yanzu tayi idda tunda ta haihu,
Abubakar baikaiga bata amsaba wayarsa tafara ruri mikewa yayi yace "minti biyu Alhaji na kirana daukan wayar yayi yafice,
Dr tanata jiransa yadawo taji shiru abunda bata saniba shine yafice daga gidan gabaki daya wayarsa takira tajita akashe kuka ta zauna tasaka batasna me abubakar yake nufi daitaba,
Tasan yana tsoron mahaifansa ne shiyasa bai saketa ba amma dukda haka sai ya saketa tasan halin mijinta tasan irin sonda yake mata, hakan yasa take ganin babu da yanda za'ayi yaso Sawwama saidai yaki sakinta saboda yan uwansa,
Abubakar aranar haka yaki dawowa gidan saboda baisan abunda zai taras ba."
Yan uwan Alhaji sunata zuwa duba Sawwama da yaronta
Itakuma hajiya nata yan uwan ba yan gari bane shiyasa basu zoba ta iya yiwuwa sai daga baya,
Washe gari yaje duba su Sawwama yar uwar Alhaji datazo dubasu tace "nikam Abubakar matarka bazatazo taduba yaronnaka bane? Kullum agidannan nake wuni amma banganta tazoba ko a yaronma halinnata zata nuna?
Hajiya tace A'a barta kartazo tayi zamanta ni duk irin wannan baya damuna,
Abubakar yaji dadin yanda Hajiya ta kashe zancen a wajan da zaisuyita juya maganar tadawo wani abun daban."
Wasan buya suka farayi shida Dr yama daina zuwa gidan gabaki daya jiransa kawai takeyi yazo,
Kwanata biyu bataje wajan aikiba tana gida hankalinta atashe, dataga abun yana neman fin karfinta ta kira mahaifiyarta tana kuka, Mahaifiyarta tace tazo tanason ganinta,
Bayan Dr tagama yiwa mahaifiyarta labarin abunda yafaru kawai saijin saukar mari tayi, a tsorace ta dago ta kallo mahaifiyarta dama matar daga kallonta zatayi masifa,
Itama Sajida gudun halin mahaifiyartata ya sanya batayi shawara da kowaba ta aikata wannan abun,
Fada mamarta tafara tana fadin ashe bakida hankali?
Kanki kalau kuwa sajida zaki aikata wannan abun ke waya fada miki ana wannan abun dana miji gashi nan kina kallo zai baki kunya,
Advertisement
Sajida tana kuka tace "Ni nayarda da irin sonda yake min mama bazai taba son wata mace bayanniba inada yakinin mahaifansa ne suka hanashi sakinta,
Dalla rufamin baki wawiya namijin?
Namijinne zakiyi masa wannan shaidar?
Dan yana sonki sai akace miki bazai so wata bayan keba?
Sakarya kawai ni tashi kibani waje tunda ke kika daukowa kanki masifatoh kije takare miki, kina kallo uwarki bata zauna da kishiya ba amma ke zaki zauna da ita,
Mikewa Sajida tayi tace nayarda da Abubakar bazai taba son wata ba kuma zakice na fada miki sai dai idan babu yanda ya iya yana tsoron mahaifansa amma wannan yarinyar kam bazai sotaba,
Harde hannuwa mamanta tayi tana karkada kafa ta maida hankalinta kan TV bata sake kulata ba mikewa itama tayi tafice cikeda jin haushin mahaifiyartata tasan ko za'a fada mata wani abun da yarda amma badai abubakar yaso wata ya mace ba bayan irin sonda yake mata."
Takira wayar Abubakar tataura masa message harta gaji,
Da dare Sawwama na daki itada wata matarda take kulada ita tana kallon yashigo tafice tabasu waje zaunawa yayi Sawwama ta dubeshi tace "Sannu da zuwa, murmusawa yayi yace "yawwa, shiru na wani lokaco babu wanda yasake magana, tafahimci akwai damuwa atattare dashi cikin kulawa tace "mai yake damunka naga kaman kana cikin damuwa, nisawa yayi yace "Dr sai kuma yakasa cewa komai bayan hakan,
Sawwama tace "dama dole asamu matsala amma in sha Allahu komai zai dawo dai-dai bayan munjure duk wani abunda zai biyo baya,
Murmushi kawai yayi yakasa fadawa Sawwama cewa baima sanarda dr dinta sai yakejin nauyin hakan,
Ganin yaronsa dayayi ya kudirta cewa yau komai zai faru zai snaarwa Dr halinda ake ciki."
Sai dare sosai kafinnan yatafi,
Gidan Dr ya wuce baiyi mamakin ganinta batayi bacci ba dan yasan halinta damuwa tana hanata bacci kuma yasan babu abunda taki jini irin kishiya dole wannan abun ya dameta sosai, wani irin tausayinta ne ya shige ransa yasan bai kyauta mata ba amma itama Sawwama idan yarabu da ita bai kyauta mataba kuma ya zalince ta,
Tana kallonsa ta nufeshi da sauri ga mamakinsa sai yaga tayi masa murmushi da fara'a a fuskarta take fadin yaya anyi nasara koh? Sun bari ka saketa?
Aidama nasani nasan cewa kaki zuwane harsai kashawo kan wannan matsalar kafin ka fuskanceni,
Shina murmushin yayi mata amma na karfin hali yace "zauna tukunna muyi magana,
Zama tayi tana kallonsa jira kawai takeyi yace yasaki Sawwama,
Shieu yayi Dr tace kai nake sauraro Yaya akayi?
Sunkuyarda kansa yayi yace zan fara da baki hakuri Dr tace babu komai duk wani abunda kamin yawuce har indai ka saketa na yafe mata,
Dr bansaketa ba,
Meyasa? ta tambaya hadeda bata rai
Shiru yayi tace kaifa nake sauraro ko meyasa baka saketa ba?
Bazan iyaba Dr kiyi hakuri bazan iya sakinta ba zanci gaba da zamada ita matsayin matata,
Mikewa tayi tana fadin karya kakeyi wallhy karyena baka isaba, me zaisa kacigaba da zamada ita? Nasan ba sonta kake ba nikadai kakeso kuma ni kadai zakaso har karshen rayuwarka kai ka fadamin hakan, idan abunda ta haifa kakeji Idanni ban rikeshiba Hajiya zata rikeshi Hannu bibbiyu karka damu, duk tana wannan maganar ne cikin kidima,
Nisawa yayi yace "duk ba wannna dalilin bane yasa bazan saketa ba sonta nakeyi inaso na zauna da ita a matsayin mata,
Kuka Dr tasake tana fadin wallhy karya kakeyi baka sonta ni kadai kakeso, idan kana sonta ni kadaina sona kenan?
Girgiza kai yayi yace "ni bance miki nadaina sonki ba hasalima sonda nake miki bana mata kwatankwacinsa kuma bana tunanin har abada akwai mace ta aure da zansota irin sonda nake miki amma bazan iya zaluntar rayuwarta ba inason zan zauna da ita, ihu tasaka tana fadin kakara fadin kana sonta Allah ya isa,
Rikota yayi tana faucewa yace "kiyi hakuri bazan sake fadaba in sha Allahu har abada bazan sake cewa ina sonta a gabaki ba amma Sajida ki saurareni kinsan bazan taba yin hakan danna cutar dakeba inasonki ke kanki kinsani,
Kokarin kwacewa take tana fadin bansaniba ai yarda da sanin sonda kakemin yasa na yarda bazaka taba son wata mace bayan niba ashe kai bahaka kakeba ka sakeni wallhy bazan zauna da itaba saina kasheta har indai kace zaka zauna da ita,
Kankameta yayi yanda bazata iya kwacewa ba yace bazaki iyaba Dr nasan wacece ke bazaki taba iya cutarda wani ba kidaina fadin haka duka tafara kai masa tana fadin ya saketa yaki saketa,
Daga karshema wani abun daban yawuce dashi atunaninsa ko zai sama mata kwanciyar hankali,
Har cizonsa saida tayi amma yaki barinta kawai dan ya rarrasheta,
Shiru tayi ta lafa ajikinsa tana kuka kasa-kasa shafa bayanta yakeyi yace "kiyi Hakuri sajida kiyi hakuri nasan nayi miki laifi, bazan fasa baki hakuriba dannasan laifinda nayi miki har abada bazai gogu a zuciyarki ba amma inaso ki sani Hafsa tanada halayya masu kyau zakiji dadin zama da ita bazaku tana samun matsala ba, kuka ta fashe dashi tana fadin Allah ya isa idan kakara yabonta agabana,
Shhhhssshhh sorry bazan karaba in sha Allahu ko sunanta idan bakyaso nakira a wajanda kike bazan kiraba a kufule tace karka kira, toh kawai yace,
Shi yayi tunanin rikicin natama zaifi haka."
Ranar suna yaro yaci sunan alhaji muhammad, Alhaji ya hana a yiwa sunan barko yace akira yaro da sunansa yanda sunan bazai bata ba,
babu wani abu na jin dadin rayuwa wanda basu tabadawa Sawwama da yaronta ba,
Sawwama taga soyayya iya soyayya yan uwan hajiya kalilanne daga ciki suka hallara yan uwan alhaji shnfi yawa a wajan,
Sunane akayishi kanar wani gagarumin biki duk wani kudinda Abubakar yake kashewa ko kadan baya jinsu a jikinsa, komai yagani sai ya sayawa yaronnan harna wanda bai ganiba nema yake ya saya,
Anyi suna angama cikin girmama juna da mutumtawa."
Vote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial29 Chapters
The Hero Raised by a Monster
Have you ever woken up in a strange fantasy land for no discernible reason? Don't worry, I know you haven't. But I did! Before we go any further, full disclosure: I am a monster. At least, that's what people tell me. Now, you don't need to be too worried about that because I've got a hero around to make sure I don't cause too much trouble. Well she isn't really a hero yet, but I'm going to make sure she becomes one. After all, I'd really rather not be hunted down just for being what I am. Or maybe it's the murder and property damage? I'm not really sure what it is that sets people off.
8 155 - In Serial50 Chapters
Celeste Academy
The boundary between Valemnia and Earth has been breached by demons. Although knights who go by the name Celestes have managed to take things back under their control, demons who escaped to Earth have to be hunted down. When fate decided to turn at the wrong time, seventeen-year-old Valeriana Kerrigan ended up in the clutches of a demon she escaped from at a price—her choice. Her unfortunate involvement served as wind in her sail to leave neutral waters, hence, she reluctantly steps into the chaotic shores of a different world where the only way to leave and live is to enter and learn to fight. Even so, Valemnia’s problem with demons may take more than just learning how to wield a sword and getting along with its element-bending locals. To keep the boundaries strong between her world and the other, Valeriana would have to learn how to let go of her humanity. Literally. But is this world worth losing it for?
8 102 - In Serial58 Chapters
Beginning from Nothing: Book 1 of The New Age
Global warming. Overpopulation. Pandemic. Supernovas and meteoric extinctions. The universe is coming to an end, and the powers above have decided to pull the plug on this version. But not anytime soon. Two young men and a young woman find themselves among the 500 humans recruited as Beta Testers for the next version of the Universal Code, the magitech workings that power reality. Updates for humanity include: Patched Tongue Biting glitch Decreased acne spawn rate And Magic Not all the changes are positive however. Monsters, foul magic, nobles, and politics all conspire the prey upon these new citizens. Asher, Elijah, and Li must gather their strength and prepare for humanities migration to this new reality, or witness their people cast into servitude.
8 278 - In Serial17 Chapters
Ambition
"Will there ever be a world of peace?" This question rings across the continent for generations, until it is heard by one. This tale follows, the one who will usher the world into an era of prosperity and peace. The only one who is capable. The ambitious, the illustrious. Minamoto Yama. [wip]
8 62 - In Serial32 Chapters
The Mage returns to being an Archer
In medievel time, a mage in a hero's party has expended all his mana to save the lives of his teammates when being pressed hard by the Demon Lord's army. Unable to utilize any spells, he is forcibly removed from the hero's party and is looked down upon as below a human being. Fortunately for the mage, he is not your average human, as he is a reincarnator from Earth. As he slowly recalls his former life's knowledge, he begin his new adventure with a new profession, an archer. Watch as our protagonist sets out on to reclaim his lost honour and prove himself once again against the Demon Lord army, to aid humanity again in its darkest hour.
8 216 - In Serial46 Chapters
daggers
- do not read !- main au is on twitter, i'm just using wattpad for the narrations
8 58

