《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 80
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 80
Kulawa ta musamman Sawwama ke samu daga wajansa gabaki daya ya manta da komai ya dauki hankalinsa ya maida akan komanta,
Idan ya sameta ta zauna tana tunani kuwa zaiyita janya da hira har sai ya kwantar matada hankali,
Idan kuma ya fahinci dalilin damuwar nata yakance mata tadaina tunani dan batasan yanda Allah zaiyi dasuba abun yana daure mata kai dan baifito ya fada mata abunda yake nufi da wannan kalmar ba amma akwai abunda maganar ta dosa bataso ta sakawa ranta cewa yana fadin hakanne saboda bazai saketa ba, idan kuma yazo ya saketa tashiga damuwa, ta tasan irin wannan hali Abubakar yake dashi to da bata fara bari tasake dashi ba, gabaki daya ya sabar da ita dashi koda yaushe yana manne da ita har labarai yake bata naban dariya kawai dan yaganta cikin farin ciki duk yanda take tunanin Abubakar a nuna kulawa abun yawuce nan, a yanda ta fahinceshi yana daukan dan adam da darajar gaske mutum ne shi mai kyawun hali, itakam zatace tayi sa'ar maza da sukasan menene kulawa wanda sukasan yanda ake tafiyarda ƴa mace,
Chewing gum yadawo mata ko fita bayayi sai dai idan zai daukesu ne su fita tare, sai dai zama dashi sam bayida gundura saboda mutumne mai ilimin gaske yayi nisa a fannin boko kuma masanine na addini shiyasa duk kalamansa suna fitowa a mizani kuma a yanda duka dace, komai nasa abun burgewa ne kama daga kalan fatarsa kyawunsa da surarasa kai hatta muryarsa wani lokacin idan yana wani abun tsayawa kawai takeyi kallonsa sai ya lakaci hancinta tukunna,
Hajiya ne tace "yanzu yakamat sudawo haka tunda laulayin da sauƙi itama tasamu kulawa ta iyaye a kusada da ita."
Lokacin dawowa suka sanya ita tanata murna amma shikam sai yakeji kamar su ƙara daɗewa dan baisan yanda zasu kaya da Dr ba."
Hajiya ta tanadar musu komai kafin isowarsu sauƙa tayi musu na musamman, tasanya aka kai can gidansu,
Saida ya huta sannan yanufi gidan Dr daƙaye yashwo kanta ta haƙura da fushin da takeyi dashi danko wayarsa tadaina ɗauka,
Albihir yayi mata da cikin da Sawwama takedashi amma yakasa gane shin murna tayi ko akasin haka,
Cikin wani yanayin da yakasa kintata tace "yanzu amfaninta yaƙare ka sawwaƙe mata kawai taatfi,
Cikin lallashi yace "ai bazamu yanke shawara haka dawuri ba mubari ta sauƙa mana! Bazan iya bari ta sauƙa ba yanzu nakeso ka sawwake mata tunda munrigada mun samu abunda ƴan uwanka sukeso bazai yiwu kacigaba da zama da itaba,
Nisawa yayi yace "idansu Hajiya suka tambayeni dalilin Sakin me kikeso nace musu? Ko yaya kibari musamu wata mafaka kuma ni inaso na raini yarona tare dani, idan bata tare dani kinga hakan bazai yiwu ba,
Baƙin ciki ya sanya tabar masa ɗakin gabaki ɗaya,
Kwanansu biyu da dawowa yakaita ta gaida Hajiya yanzu tabar laulayi sai azabar ci arana sai sAwwama taci abinci sau biyar,
Advertisement
Sawwama ta kawowa hajiya da Alhaji tsaraba sunyi murna sosai,
Dama tun acan Abubkatar ya shaiadawa mahaifansa cikinda Sawwama take dashi, Tun kafin su dawo zance yarigada ya ratsa dangi kowa yasan da zancen cikin, Hajiya kullum burinta ɗaya su dawo tacigaba da kulada lafiyar Sawwama."
Alhaji yana shigowa Hajiya ta sanar dashi zuwansu Sawwama, Alhaji dama ya rigada yagama tsara kyautar da zaiyi mata, takardun gidanda suke ciki alhaji yabata, dungurum gun,
Sawwama sai take ganin lamarin kamar amafarki, hawayene yafara gangaowa akan fuskaarta na tausayin kanta da mahaufansa tasan zasu shiga wani hali idan sunsan irin aurenda sukayi dakuma sharaɗin auren, dasunsani da basu ɓarnatar da dukiyarsu, akanta ba,
Tayiwa Alhaji godiya sosai da fatan alkahiri."
Bayan sun koma ta ɗauki takardun tabawa Abubakar amma yace mata wannan natane halak malak alhaji yabata ta ajiyesu a wajanta ko takai gidansu a ajiye mata,
Washe gari yakaita gidansu da mamakin Sawwama tasamu mama ta haifu Jaririnta kuma ko a waya babu wanda ya faɗa mata, dama ita duk ganin da take yiwa mama kamar mai cikine amma bata kaiga tambaya ba,
Haihuwar Halima kawai tasani itama ta haifi yarinyarta,
Mama kuma kunyace ta hanata Bayyanawa duk da cewa bawai tawani girma bane amma tana ganin yaranta suna haihuwa itama na haihuwa, ko taron suna basuyiba, yaci yaci sunansa Muhammad,
Sawwama tayi murnar ganin mahaifanta cikin walwala sunata godiya suna shaida mata irin abun alkahirin da mijinta da danginsa suke aiko musu dashi gabaki ɗaya sun canja sun dawo shar dasu,
Cikin dake jikin Sawwama kuwa suma sun rasa shin murna zasuyi ko fargabar auren ƴarsu daya kusa mutuwa, sudai yanzu sun zubawa sarautar Allah ido kawai suna jira suga yanda lamarin zai kaya."
Washe gari Sawwama taje taga Halima Abubakar da kansa yakaita, dama tun kafin su tafi ta aiki mai aikinta kasuwa tayi mata sayayyar kayan yara dana manya,
Halima tayi murnada ganin yanda Sawwama ta canja ita kanta haliman ta canja sosai saboda tana samun kula sosai,
Saida ya tsaya suka gaisa da Halima sannan yawuce Halima tace "yaya Sawwama a ido wannan mutumin kamar mutumin kirki, Harararta Sawwama tayi tace "dama ance miki mutumin banza ne shi?
Halima duk yanda kike tunanin kirkin mutuminnan toh yawuce nan kamar yanda kamanninsa yake haka zuciyarsa take, taɓe baki Halima tayi tace"komadai menene yaya Sawwama bai kamata ya biyewa matarsa su aikata wannan abunba wannan cutane zasu cutarda rayuwarki dana abunda zaki haifa saboda son zuciyarsu,
Murmushi Sawwama tayi sannan tace "Halima kenan inaji ajikina wannan mutumin bai waureni dan ya rabuda niba, mekika gani yasa kikace haka? Inji Halima, Sawwama tace "akoda yaushe nayi masa maganar rabuwa yakance nabari zuwa lokacin saboda bamusan yanda Allah zaiyi damuba wallhy kirkinda yake dashi yawuce yanda zakiyi tunani bantaɓa tunanin za'a samu mutum mai dukiya haka da azabar kirki ba, amma ni banaso na sakawa raina hakanne yazo kuma ba haka bane, kuma saboda matarsa komai zata iya aikatawa dan tarabani da mijinta,
Nisawa Halima tayi tace "nima ina fata ace bazaku rabuba yaya Sawwama Allah yasa kamar yanda yakeda ƙyawun fuska haka zuciyarsa take kyakkyawa gameda ke, itakuma matarsa karki damu da ita har indai mijinki yanuna yanasonki kuma zaici gabada zama dake toh ki toshe kunnuwanki, duk wani abunda zatayi taje tayi ai ita tafara, kuma dama irin wannan lamari ba'a cika farashi aƙareshi yanda rai yasoba, shiyasa karma ayi kar afara."
Advertisement
Sai magrib kafin yazo ya ɗauketa wannan lokacin Halima ta sake masa ba kaman ɗatsuba jin kalamansa akan yayartata."
Satinsu guda da dawowa amma baiji Dr tayi masa magana akan yafara ƙwana gidan Sawwama ba ranar haƙurinsa ya ƙare ya shaida mata cewa zaije wajan Sawwama saboda ba ita ɗaya bace yanzu tana buƙatar kulawarsa kusada ita,
Dr tace atafir batasan zance ba ita ai dole tunda yanzu tasamu ciki bazaije wajanta ba tunda anrigada ansamu abunda yasa yakeson zuwa wajannata, babu irin lallaɓin da baiyi mata akan tabarshi taƙi,
Cikin lallami yace "Dr kowane irin aure fa mukayi da ita inaso ki sani cewa itaɗin matata ce kuma akwai hakkinta akaina Allah zai tambayeni duk wani rashin adalcin dana mata banaso na kasance mutum maras adalci, alokacin da zan yanke igiyar aurena akanta shine kikeda ikon hanani zuwa wajanta, amma banda yanzu saboda ahalin ynzu tanada buƙatar na kasance kusada ita,
Kuka Dr tasaka tana faɗin kaci amanarta, idan baka mantaba kafin ka aureta saida nasaka kayimin alƙawarin cewa da zarar ta samu ciki bazaka sake kusantarta ba kuma bazaka taɓa sonta ba idan lokaci yayi kuma zaka saketa,
Abubakar yace"duk nayi miki waɗannan amma na gwammaci na saɓa miki akan na saɓawa mahaliccina, dan haka mu yanke wannan alƙawarin zanje gareta duk bayan ƙwana biyu kuma zan kulada lafiyarta har izuwa ta sauƙemun abunda yake cikinta, yana dauriyanr kawai yana faɗa mata haka amma yana cikin tashin hankali ganin kukanda takeyi, aranar haka baisamu zuwa wajan Sawwama ba amma kamada daga washe gari yafara zuwa babu irin rikicin da Dr batayi ba amma haka yaƙi sauraronta,
Ganin yanda yayi watsi da alƙawarin dayayi mata yasata ɗauki zafi sosai da lamarin, sau biyu tana zuwa yiwa Sawwama warning."
Duk abunda takeyi ko sau ɗaya Sawwama bata taɓa maida mata martani ba abun har mamaki yake bawa Dr da Abubakar, basusan haƙurin Sawwama ba tazauna da wacce tafi Dr hauka (Abida)😅
Cikin Sawwama sai sake girma yakeyi tana sake samun kulawa daga kowanne ɓangare,
Cikin yana shiga 9month Hajiya ta sanya Abubakar yadawo da ita gidanta da zama gabaki ɗaya, itake kulawa da ita yanda ya dace,
Sai fama takeda fargabar abunda zai faru bayan haihuwarta dan ahalin yanzu tama wufe EDD ɗinta,
Har bataso ta haihu kullum kuma da fargabar ko aranar zata haihu take,
Abubakar ne yashigo amma Aisha kawai yasamu a falo zama yayi ta gaidashi yana tambayarta ina hajiya, tana side ɗi alhaji tabashi amsa, "Hafsa fa? Ya tambaya, tana ɗakinta muna kallo tatashi tashiga,
Inadao lafiya ya tambaya?
Inaga lafiya amma bazan iya kintataba tunda dama kwanakinnan batajin daɗi, miƙewa yayi yanufi ɗakin da dake,
Azaune ya sameta bakin gado ta yi nisa cikin tunani harya ƙarasa ya zauna bata ankaraba ba saida ya riƙo hannunta, Arazane ta juyo sai kuma ta sauƙe ajiyar zuciya,
Jawota yayi jikinsa ta ƙwantarda kanta luff zuciyarta babu daɗi,
"Ko zan iya sanin abunda yake damunki? Ya tambaya cikin kulawa,
Runtse idanuwanta tayi bakinta ya kasa furta komai, cikin kulawa yacigaba da faɗin tunani baida ƙyau a lafiyarki a halinda kike yanzu,
Hajiya ce ta ƙaraso falon bata zaunaba taga babu Sawwama a zaune yanda tabarta duban Aisha tayi tace "ina kuma Anty Hafsa tayi? Aisha tace "tashiga ɗaki yaya Abubakar ma yazo yana wajanta, juyawa Hajiya tayi zuwa ɗakin Sawwama,
cakk ta tsaya daga bakin ƙofar ɗakin jin Sawwama cikin sanyin murya tana faɗin "Dole nashiga damuwa awannan yanayin koka manta cewa da zarar na haihu mun rabu dakai kenan?
Ko kasan yanda nakeji? Ni kenan rayuwata kowanne lokaci da irin ƙaddarar da zata zomin dashi, meyasa ka aureni? Da tun lokacin baka yarda da aurena ba saboda zakazo kayi dana sani bayan rabuwarmu,
Ni Dalili ɗaya yasa bazanyi dana sanin aurenka ba shine samun lafiyar ƙanwata, kuma nasamu kwanciyar hankali daga gareka, da san wannan kulawar zaka bani daga karshe kazo ka tsinketa
Da akwai yanda zamuyi da ban aureka ba domim ni duk wani ƙyaleƙyelen duniya bai dameni ba amma inason koda sau ɗaya arayuwata na samu kwanciyar hankali inason kwanciyar hankali mai daurewa ba wannan wacce kake bani mai iyaka ba, yanzu mai zan cewa abunda na haifa? Wani irin aure nayida mahaifinsa? Shin abunda na haifa idan ya girma zai fahimceni?
Ga mamakin Sawwama Abubakar murmushi yakeyi saida yabari da ida sannan ya sanya hannunsa ya share mata hawayen dake gangara akan kumatunta cikin kulawa yace "Ga dukkan alamu kin fara sona kamar yanda nima nake sonki, ni ban aureki da niyyar da nasakeki ba koda kin haihu Sannan kuma koda baki yarda da aurena ba tunda ta faɗamin nayi niyyar biyawa kanwarki kuɗin magani, naje asibiti sau biyu na ganki kuma na bibiyi rayuwarki ta baya naji abunda yafaru duk wasu halayanki na sansu da irin haƙurinda kike dashi, niba karamin mutum bane da zan yarda kawai nayi aure batareda bincike ba hakan bamai yiwuwa bane, alokacin dana daura niyyar aurenki tun daga lokacin nasakawa raina ko na aureki bazan rabu dakeba saboda Hali irinnaki kaddara ce kawai zaisa wanda ya aureki yarabu dake,
Zan iya cewa mutane masu hali irinnaki sabuda yawa, toni wane gigin zai kaini narabu dake?
zamana dake ya sake tabbatarmin da ke wacece, macecece ke mai sanin yakamata haƙuri da rashin son abun duniya samun mace kamarki is very rare sai dace, bani kadaiba kina tunanin akwai wanda zai samu kamarki kuma yarabu da ita?
Ban damu da abunda Sajida zata aikata ba dan nasan na wani lokaci ne amma bazan rabu dakeba zamu zauna ki haifamin yara masu kamada ke, yanzu ki kwantarda hankalinki kinga halinda kike ciki,
Hajiya dake jiyosu alokacin jikinta duk yabi ya mutu tambayar kanta takeyi shin mai yarannan suka aikata? Mai kunneta yake jiye mata? Ganin batada amsar wannan tambayoyin sai daga garesu ya sanya ta."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial10 Chapters
The Dawn of Blood
As the saying goes, "Ignorance is bliss." That is a good way to describe us. We are constantly seeking to improve, to evolve. Coming up with laws and theories to better understand the world around us. But what if it was all for naught. What if what we think is truth is nothing more than the actions of higher beings, far beyond our reach. Upon the discovery of an entire new reality, remaining ignorant is certain death. The only way to live is to grow, to evolve, to adapt. This is my first novel so any feedback and criticism is greatly appreciated. I hope that I'm able to grow as a writer through this and hope that people enjoy my work. Credit for the cover image goes to Richard Luong. Check him out at https://tentaclesandteeth.deviantart.com.
8 138 - In Serial53 Chapters
Samurai NOT
By his master's request, Tadayoshi ended his life. Now he must look for the reason behind the request.
8 204 - In Serial28 Chapters
Beyond Floating
Muse thought her life had ended twenty years ago because, well, it had. Existing aimlessly for two decades as a ghost, she finds herself yanked along in a rip-tide of strange events. Thrust unwittingly into the midst of a group of paranormal hitmen-for-hire led by a man named Isaac. Michael, a normally rational and righteous holy soldier of God, succumbs to revenge and hatred, sacrificing everything in the fight to destroy Isaac and everyone who associates with him. Muse, by virtue of her inadvertent association with Isaac, is on that list. This is actually my first 'finished' fiction that I've ever written, which I completed about 8 years ago. I dug it up recently and I'm posting it as I thought people here might get a kick out of it. So, take that for what you will. Chapters will be released daily at 6:00pm EST.
8 101 - In Serial71 Chapters
The Victims⦻
People's interesting encounters/experiences with the SlendermanThis book is the best material for researching. Everything (especially encounters )in this book is very handpicked. I only chose ones that can intrigue you.I recommend this book if you do the 'Real research' about paranomal and mystery or even creepypasta.(which the slenderman is concluded)I saw a lot of books which describe their own experience but I hardly saw collecting books. So I made it.
8 245 - In Serial35 Chapters
YOU ARE MINE
In which a father sells her daughter to a Mafia kth support me.💜💜💜 "YOU ARE MINE "a ff about a rich man Kim taehyung, who owns his own gang and a loan shark company.He then falls madly in love with a daughter of one of his clients.Then y/n the girl who stole the mafia's heart gets sold by her father to taehyung.What will happen to the 19 years old virgin girl in the mansion of the mafia taehyung all alone........
8 88 - In Serial26 Chapters
Guitar Cry: A Cody Simpson Love Story
He looks at her as his best friend.She looks at him as the boy that she is in love with.The world looks at them as Hollywood's youngest couple.
8 199

