《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 79
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 79
Suna cikin meeting alhaji ya kirashi awaya bai samu ya ɗaukaba sai bayan yafito ya kirashi Alhaji yace masa yazo yana nemansa,
A ƙanƙanun lokaci ya isa wajan mahaifunsa bayan sun gaisa yake sanar dashi cewa yanaso suje saudi shida matarsa amarya sannan kuma suwuce wasu ƙasashe guda biyu itama ta buɗe idonta kuma duk tafiyarku ni zan ɗauki nauyinsu gabaki ɗaya,
Naga aurenku wata huɗu amma haryanzy bakada niyyar yin hakan, kuma mahaifinta basuda ƙarfi izuwa yanzu yaci ace kafara taimaka musu wannan nabar makane kai dakanka kayi kasamu ladan sirikanka da kanka,
Kansa yana ƙasa yace "in sha Allahu alhaji zanyi,
Alhaji yace "saiku fara shirin tafiya nanda wani lokaci,
Godiya yayi masa sannna yawuce wajan Hajiya ya faɗa mata abunda Alhaji yayi,
Hajiya tace "eh munga kai bakada niyyar kyautatawa shiyasa, wancan matarda ka aureta wace ƙasace bakujeba amma yanzu wannan aure wata huɗu kazauna kayi shiru, ko tsoronta kakeji shiyasa ita wannan kakasa kyautata mata?
Ƙasa yayi da kansa bai iya cewa komai ba, Har Hajiya tayi faɗanta tayi shiru, Sannan daga ƙarshe tace yakawo mata sawwama ta kwana biyu bata gantaba, ya sama da cewa zai kawota amma sai gobe,
Hajiya tace toh Allah yakaimu,
Taraddadin yanda zai gayawa Dr wannan maganar yakeyi dan baisan yanda zata ɗauki abunba,
Saida yabari ya daidaici lokacin da suke cikin farin ciki sanna ya dubeta cikin wani yanayin da bazata iya karantar mood ɗinsa ba yace "Alhaji ya nemi ganina 2days back so naje yake sanardani cewa yabiya mana saudi nida Hafsa and kuma bayan nan zamuyi tafiya zuwa wata ƙasar daban kuma komai shine yaɗauki nauyin hakan bansan yaya zaki ɗauki lamarinba shiyasa ban sanar dake ba amma yaya kike ganin zamuyi, tunda yafara magana tasake baki tana kallonsa, bazaku jeba tafaɗa ataiace sannan ta ɗaura da faɗin ai bawai an aurota bane dan taji wani daɗi tasake dakaiba meye nawani har zuwa wata ƙasa kabari idan ka saketa saika biya mata saudi tubda tarigada tadawo uwar ɗanka,
Shafo kanta yayi yace "Alhaji su duk basusan da hakanba sun ɗauki wannan aurene kamar kowani aure kuma bazan iya mayarda ƙyautarsa garenu ba saboda bansan wane dalili zance masaba kinsan Alhaji kinsan yanayin tsaurins bazan iya bijirewa maganarsa ba,
Advertisement
Kuma dana zauna nayi tunani sai naga mai zai hana mutafi da ita ɗin kema mutafi tare amma kibiyomu daga baya, bansan ko acan idan babu idonki zan iya kusantarta ba,
Fauce hannunta tayi tace nace maka A'a bazkaa tafi da itaba idan bazaka kusanceta ananba kabari kuma kasan a irin wannan lokaci da nakeda patient dayawa bazaiyiwu natafi nabarsu ba kawia ka janye zancen tafiya da ita,
Amma dai kinsan bazan iyaja da maganar Alhaji bakoh? A fusace tace ni ka saketa kawai, ka saketa tunda dama ni nace ka aureta yanzu nafasa,
Miƙewa yayi yace wai yaronki kika maidani? Duk wani abunda kikace kinaso shi nakeyi saboda na faranta miki amma ke kullum sai kiringa yin abunki da isa kinsan banason haka kuma akanki bazan ɓatawa mahaifana ba, yana gama faɗi yafice a gidan bai dawoba sai dare a ɗaki ya sameta ta zauna tayi zugum zama yayi a gafenta cikin sanyin jiki jawota yayi jikinsa yafara bubbuga bayanta yaɗauki tsawon lokaci ahaka sannan yaɗagota hawaye yagani a fuskarta cikin rawar jiki ya sanya hannu ya share mata hawayen, Haba haba Sajida wai har meyayi zafi haka baki yarda dani bane?
Soyayyar da nake miki yasa nake biye miki a komai da kikeso wanda yawancinsu daga ƙarshe muke zuwa muyi danasani, farkon aurenmu babu yanda banyi dakeba akan ko yaro ɗaya mu haifa amma kikaƙi kikace karatu haka soyayyarki ta sanya na amince dukda raina bayaso,
bayan kingama karatu haka kikace aiki yayi miki yawa nanma na biye miki, har mahaifana lokuta da dana nakan bijirewa maganarsu saboda ke meyasa duk wannan abun bazaki iya fahintar sonda nake miki bazai bari naci amanarki ba?
Yanzu ni banaso wani abun yasake haɗani da mahaifana ta dalilinki inaso a yanzu komai dake tsakaninku ya dai-dai ta kinsani sanin kanki cewa ke kika fara saɓaw ada ƴan uwana su basu nuna miki wani haliba basu taɓa nuna miki wani ƙi ta dalilin baki haihuba abunda kike mus yasa suka canja miki kuma hakanma ban goyi bayan dangina ba ke nabi baya, kinsani kinsan dangina mutanen kirkine bzasu taɓa ƙinki da baki haihu ba, kuma laifin rashin haihuwarmu duka laifimmu ne mun biyewa son zuciyarmu,
Toh yanzu ma idan bakiyi hankali ba koda wannan tatafi wata zasu sake sawa na auro kinga nikuma bazan zama sai auri-sake ba,
Advertisement
zan zauna da wanda zasu auramin nan gaba har indai baki tsaya kin kwantar da hankalinki Anyi komai kamar yanda aka tsara ba, maganar tafiya kuma zamu tafi da ita idan hankalinki bai kwantaba ki biyomu amma bazan saɓa umarnin Alhaji ba,
Lumus tayi ajikinsa tana sauraron abunda yake faɗa komai tasan ta aikatashi shiyasa tayi shiru dan itama duk zafin zuciyarta bata iya juran ɓacin ransa nan danan take shiga damuwa ko tafara kuka dake tasan baya iya jure ganin hawayenta."
Jin yayi shiru da maganar yasa Alhaju yasake tun tuɓarsa yace Alhaji inaso zanyi clearing schedule ɗina na month ɗin gaba gabaki ɗaya sai mutafi zuwa wancan month ɗin,
Alhaji yace toh hakanma yayi Allah yakaimu."
Sawwama na gaban mirror ta fito daga wanka ɗaure da towel ta zubo gashin kanta abaya tajiyo shigowarsa amma bata juyoba tacigaba da abunda takeyi tabaya yazo ya rumguneta janye gashin kanta yayi gefe yayi mata kiss abaya murmushi tayi tace sannu da zuwa, ƙara rungumota yayi ya saka kansa a wuyanta yana kallonta ta cikin madubi yace albishir,.
Goro tafaɗi tana sakar masa murmushi Hajiya tace nakaiki tun jiya amma bansamu dana nazo nakaiki ba idan kuma taga driver ne yakaiki zatayi faɗa yau zamuje saiki yiwa Alhaji godiya ya biya mana zamu tafi saudi, juyowa tayi tana kallonsa dan son gasgakatar da abunda yake faɗa,
Ganin babu wasa a fuskarsa ya sanya ta raba jikinsa da nata ta isa izuwa gado ta zauna bin bayanta yayi da mamakinsa sai yaga batayi murna da hakanba
Bai yanke mata hukunci ba dan baisan dalilinta ba ya isa bakin gadon shima ya zauna,
Kamo hannunta yayi cikin kulawa yace"mai kuma yafaru? Maimakon kiyi murna sai naga akasin haka, sunkuyarda kanta tayi hawaye yanason zubowa tana ƙoƙarin maidashi tace "duk waɗannan abubuwan bamasu ɗaurewa bane kabari kawai nagama abunda ya kawoni natafi banajin daɗin wannan muguwar shaƙuwa dake shiga tsakaninmu,
Kamo hannunta yayi ya sakar mata murmushi sannan yace nikuma inaso, karkiyi judging komai yanzu bakisan yanda Allah zaiyu damu nan gababa, kedai yanzu ki shirya muje kiyiwa Alhaju godiya,
Gabaki ɗaya takasa gane yanda maganarsa ta dosa amma saboda batason sakawa kanda damuwa kawai saita share tayi masa godiya,
Yakaita tayiwa Alhaji godiya kuma yaji daɗi sosai."
Acikin month ɗin suka fara shirye-shiryen tafiya
tun awaya ta sanarwa mama kafin taje ta sanar msu Mama akan cewa zasuje Saudi kuma daganna zasu wuce wata ƙasar,
Mahaifanta sunyi murna sosai dan sunce zuwa saudi komadai menene a auren ai alkhairi ne,
Saudi suka fara zuwa dayake yazo ɗaya da lokacin aikin hajji,
sukayi aikin hajji wtaansu ɗaya acan suka wuce wata ƙasar,
Tarairaya da kulawa sosai Sawwama take gani a wajansa, zuciyarta takan yabi irin kulawa da tarairaya dayake mata, wata zuciyar sauta haneta tace karta fara ta faɗa domin gaba zatasha wahala kuma duk abubuwan dayake bawai dan yana sonta yakeyi mata na sai dan neman cikar burinsu shida matarsa, Amma ahaka idan kukaga irin kulawarda yake nuna mata saiku rantse auren soyayya sukayi,
Shikansa yanajin daɗin zamansu da Sawwama sosai domin ta kuwa ta iya zamada mutane iya zamansu bazai iya faɗin wani halinta da takeyi wanda bayaso ba, komai nata a nutse tajeyinsa Sam batada hayaniya gashi tanayi masa biyayya akan duk wani abunda yakeso,
Satinsu biyu acan Sawwama tatashi da zazaaɓi ya matsa sutafi asibiti tace dasauƙi basai sunje ba, ƙwana biyu da samun lafiyarta still wani ciwon yasake dawowa wannan lokacin kam dolenta saida tayarda sukaje asibiti, likita sun shaida masa tana ɗauke da ƙaramin cikin na wata ɗaya, Alhamdulillahi kawai yake faɗi yana godiya ma ubangiji,
Ita kam Sawwama tarasa wani irin hali take ciki shin murna zatayi? Kokuma baƙin cikin takusa rabuwa da mijinta?
Shi kansa saida ya fahimci halinda take ciki sai tabashi tausayi yasan koda ace bata sonsa sai taji wani iri idan tayi tunanin cewa da zarar da haihu zata rabu dashi saboda shi kansa yanzu bazai iya cewa baya sonta ba bare ita mai sanyayyar zuciya,
Kwantar matada hankali yayitayi harya samu ta ɗan sake tadawo kamar yanda suke."
Tunda Aka tabbatarda cikinne kuma sai jinya laulayi kala-kala, shidai yanan yana kulawa da ita kamar ƙwai saida cikinta yakai 4month kafinnan ya sanarwa su hajiya lokacin harya ɗan fara fitowa laulayin kuma yayi sauƙi sosai."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial37 Chapters
The Reluctant Court Wizard
When Jason graduated top of his class in the Magnus Academy he thought he'd have his choice of jobs. Unfortunately, a royal decree asked for the top graduating student to be sent to the capital to serve as the new court wizard. Left with little choice, Jason took the job, reluctantly. As a commoner, he knew he'd be at a disadvantage in the politics driven royal court. Jason expected that his new job would test his wits as he'd have to struggle to fit in and keep himself out of trouble amidst all the intrigue. What he didn't expect was that the kingdom would quickly fall into crisis soon after he takes the post. Cover art generously donated by JackOfHeart - Thank you so much.
8 213 - In Serial18 Chapters
Stolen
A child stolen from his parents, subjected to torture and misery for 6 years before his mind finally shattered into pieces, his once sole control over his body stolen, now shared with unknown beings that are as puzzled as he is over their existence.Finally escaping the home he knew, how will he survive with these voices in his mind that takes over his body from time to time? Strictly for mentally mature readers, story depicts gory and psychological related mental issues in detail and is relatively depressive with a maniac of a Main Character.
8 177 - In Serial35 Chapters
The Devil's Parcel
Throughout known history, men have been trying to attain Everlasting Peace in this world, but all attempts ended up in war. Lilith and her friends are trying to get by in this world and complete their goals, but it's hard when people are trying to destroy it at the same time. Lilith will have to face challenges to reach her goals, but can she do it?
8 216 - In Serial40 Chapters
Masked Girls
Rifton Girls' High School is the most elite all-girls school in the city. With a strict scholarship-only admission, a grand school campus and plentiful funding from its wealthy alumni, it is no doubt that the already-talented young ladies within its halls will develop further into future leaders. Unfortunately for some of them, one outcast concealed in the shadows will soon ruin their plans when she tears apart the facades of select students in the name of revenge. From the perspective of a troubled teenage mind, a story of merciless revenge unfolds - and all MASKED GIRLS will be exposed. ❝DO NOT UNDERESTIMATE THE POWER OF THE PAWN.❞© 2018 maskedst. All Rights Reserved.ACHIEVEMENTS | #2 in #thriller, zodiac awards honorable mention, the teen fiction awards 2018 finalist, added to 'bright young minds' reading list on @mystery.
8 122 - In Serial90 Chapters
Mianite- The Alternate Heroes' Journey
The untold story of the alternates' journey in the Realm of Mianite. From the POV's of Alyssa, Jeriah, Mot, and Spark, this book describes the many events, both good and bad, that everyone went through.
8 115 - In Serial41 Chapters
Haiku
A collection of haiku.Note 1: all of the haiku posted are mine, please don't share them anywhere else without my permission and proper credits. If you want to share them anywhere else, please DM me about it. Note 2: if you see any mistake, be it a spelling/grammar/syntax/ error or a haiku that isn't 5-7-5, please just let it slide. This book is years old - there is no need to point a mistake out as I do not intend to fix any of them. Note 3: this book was written when I was around 13 or so. Obviously, the haiku will reflect the writing skills of a 13-year-old. So, if you choose to defame me over that, your comments will be deleted or reported when necessary.
8 166

