《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 78
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 78
Mikewa tayi cikin nutsuwa ta isa fridge ta dauko masa kunun aya wacce ita ta hada da kanta data gajida shan drinks na company saita hada kunun ayah, ta hado da lemon coke da kawo da cup tsugunnawa tayi agabansa ta ajiye ta sanya hannu zata hude coke yace no bani na jug din nafison wanda aka hada a gida, cikin nutuwa ta zuba masa kunun ayan ta mika masa hadawa yayi da hannunta ya rike kofin ya zuba mata idanuwan jin yaki sakin hannunta ya sanya ta dago ido kwayar idanuwansu ta hadu murmushi yayi sannan ya saki hannunta dama abunda yakeso kenan, ya kalli cikin idanuwanta saboda wani ruwan kyau dayake kallo a ciki, kasa tayi da kanta taja gefe ta zauna yakai cup din bakinsa saida ya lumshe idanu saboda dadin dayaji ahaka saida ya shanye jug dinnan tass sannan aka fara kiran la'asar yadubeta yace zanje nayi sallah idan kinyi sallah ki shirya zamuje gidan Hajiya,
Kai ta gyada masa kawai yatashi ya fice ta tattare kayan tashiga tayi sallah akwatin turaruka ta bude ta debawa Hajiyarsa sannan ta dauki atmpha da lace acikin kayan da akayi mata,
A bags tasaka takawo palour ta ajiye sai sannan yashigo, sai taga kuma ya zauna maimakon yace sutafi, yadubeta yace idan akwai kunun ayannan ki debe mukaiwa hajiya tanaso sosai,
Sawwama tace babu amma idan babu damuwa kabani 10minute yanzu zan hada, kai ya jijjiga mata ciki karamin lokaci tagama hadawa sannan tajuya a bottles dayawa tace masa tagama masu aiki ya sanya suka debo kayan suka kai mota,
A hankali yake driving motar komai nasa gwanin burgewa da sha'awa daga kallonsa kuma ya kasance mutum mai tsaftar gaske komai nasa Ƙal-ƙal,
Dake da dare aka kaita gidan shiyasa baya luraba yanzu ta kare masa kallo tangamemen gidane mai kyauwn gaske girmansa kamar wanda zuri'a guda suke rayuwa aciki,
Suna isa yace "masu aiki suhuga da kayan yana gaba tana biye dashi abaya, hajiya tayi matukar murnar ganindu ahaka gwanin sha'awa sai albarka take sanya musu,
Hajiya tana zaune saidata shanye kunun aya gora daya tacewa Sawwama harkin tadonun da kwadayin awara duk.lokacin danake cin awara da kunun aya nake hadashi,
Sawwama cikin kunya tace sai nayi miki ai yanzu tunda kinaso, hajiya tace kayya mamana barshi kawai zan saka masu aiki suyi soyawa kawai zasuyi akwaishi a fridge,
Sawwama tace saina soya miki inane kitchen? Duk yanda Hajiya taso Sawwama ta hakura amma taki haka saida takira masu aiki suka sadata da kitchen duk wani abunda take buƙata suka tanadar mata dashi,
Bayan tashiga hajiya tace kagani koh abunda nake faɗa maka Abubakar yanzu nasan kayi aure ka auro yarinyar datassn mutumci, kaduba kaga abunda ta kawomin tasandai nafi ƙarfinsa amma dake tanaso ta kyautatamun haka ta kawomun kuma naji daɗin hakan ƙwarai da gaske ta nuna inada daraja,
Shiadai shiru yayi mata daga karshe ma fita yayi yace zai dawo ya dauketa,
Irin yanda jama'ar gidan suke nunawa Sawwama soyayya saida tayi hawaye, Hajiya sai santun Awarar Sawwma takeyi tana faɗin tunda nake bantaɓa cin awara mai daɗin wannan ba, nikuwa nace ba dole ba Su Sawwama antuno tsohuwar sana'a😅
Advertisement
Da Eggs ta soya sannan tayi liver sourse tayi smashing na kaza tasaka duka a source ɗin,
Sai bayan isha'i yadawo shina yazauna yaci awarar cin gaske yayi mata saida ya koshi, yakai hannu zai taba kunun ayan Hajiya tayi saurin buge hannun tace"naga matarkace tati ta kawomun shine zaka shanye? Kaje gida tabaka naka nama, dariya yayi Sawwama ta dago kai ta kalleshi yayi matuƙar yin kyau shi komai kyau yakeyi masa,
Yace Hajiya ai duka aka kawo miki, Hajiya tace najidai bazaka shaba,
Sai 9:pm suka tafi Hajiya tayita saka mata albarka sannan kuma tace masa "idan ya sabawa matarsa bata yafe ba."
Sawwama taji daɗin kasancewa da Hajiya har taji taɗan sake damuwar dake ranta tafita gida yafara kaita ya ajiyeta sannan yawuce wajan Dr yasamu tadawo tayi fushi sai cika takeyi akan yaje ya zauna ko ina yaje? Batayi tunanin ma yana tareda Sawwama ba saboda bata kawo zai iya zama inuwa daya da itaba."
Abinci tasa masu aiki suka kawo masa yace ya koshi yaci abinci gidan hajiya, taɓe baki tayi saboda ba yau aka fara hakaba kullum yaje gidan hajiya acan yakeci ya koshi."
Rarrashinsa ta zauna tanayi akan ya taimaka ya kwanta da amaryarsa na wani lokaci yayi ya sauwake mata, ita batasan afili ne kawai yake nuna bazaijeba amma cikin ransa Allah-Allah yakeyi yasamu yafita wajanta, tace masa gara katafi dan yau inada threatre da dare kuma bazan dawo ba sai 12:har sai wanda nayiwa ya farka, jijjiga kai yayi ya nisa baice komaiba,
Haka ya nuna mata badan ransa yasoba yatashi yatafi, yana shigowa gidan tun baikaiga shiga shashinsu ba kamshinsa ya sanarda ita yashigo gidan
Saurin kwanciya tayi ra rufe idanuwanta kamar mai bacci dakinsa yafara shiga ya yi wanka ya canjo kayan jikinsa sannan yashiga dakinta da sallama ciki-ciki a zuciya ta amsa yand bazaiji ba isa gadon ya kwanta gefenta ko motsi batayi ba akan bataso yagane ba bacci yakeyi ba,
Ahankali ya mirgino da ita tadawo jikinsa nunfashinsu yana dukan na juna zuciyarta tana bugawa da karfi sakamokon tsintar kanta awani hali datayi, luff tayi ajikinsa tana shakar kamshin turarensa mai dadin gaske, kansa ya saukar dai-dai lips dinta ya hadesu waje daya cikin nasa salon yafara kissing nata, saida yayi mai isarsa ya saketa pretending na baccinta bashi ya hanata maida masa abunda yake mata ba, shima kuma ganinta tana bacci bai hanashi aikata abunda yayi niyya ba,
Yau tasake tabbatarwa da cewa wannan mutumun mugune,
Kuka tayita sharɓa ahaka bacci ya dauketa shikuma yatashi ya gyara jikinsa yadawo ya gyara mata kwanciya,
Shima kwanciyar yayi ya luka cikin tunani mai yasa yake bawa wannan yarinya wahala dayawa, mai yasa yake sauke gabaki ɗaya bukatubsa akanta, sonda kake yiwa Dr ne yasa baka iya takura mata da buƙatunka wannan kuma dake ba sonta kake ba shiyasa baka sarrara mata sai kakai ga cimma buƙatarka zuciyarsa tabashi amsar tambayoyinsa,
Ahaka bacci yayi gaba dashi saida aka kira sallah yatashi sannna itama ya tasheta koda tafarka yafice wanka tayi ta yi sallah ta dauki Ƙur'ani tana karantawa ahaka yashigo ya sameta yana sauraron muryarta mai daɗi cikeda sha'awa saida ta idda sannan ya kwanta ya rufe ido a hankali itama tazo ta kwanta,
Advertisement
A hankali ya jawota zuwa jikinsa yayinda gabanta yaketa faɗuwa abunda take tunanin kuwa shi ya aikata sai dai wannan karon yasaka tausayi aciki."
10:00am tatashi ta haɗa musu breakfast sannan tashiga dan tashinsa tsayawa tayi akansa takasa taɓashi ahaka ya nuɗe ido akanta tayi saurin juyawa zatabar wajan ya cafke hannunta ya jawota ta faɗo kansa a kunnr ya raɗa mata meyasa kike kallona daburburcewa tayi sannan tace dama uhmm breakfast na haɗa maka shine nazo tashinka,
Riƙeta yayi ahaka yace toh jira na watsake duk da ƙagu ya saketa tatashi sai can ya saketa tayi saurin yin palor brush yayi sannan yafito yazaun aya karya sha ɗaya yabar gidan yakoma gidan Dr,
Shabiyu da mintuna tashugo gida,
Sannu yake mata ta zube a kujera yafara mata massage tana lumshe ido"
Idonta arufe tace Yau amma tare kuka kwana? Nisawa yayi yace yauma hakane ni kadai na kwana,
Ajiyar zuciya ta ƙara saukewa sannan tace "karka damu zan samo mana wata mafita dan wanna inaga bazatayi aiki ba,
Shuru yayi domin a fuskarsa yana ganin tsantsar farin ciki idan ya gwada mata cewa bai kusanci Sawwama ba,
Miƙewa yayi ya yishiga ciki wanka yayi yafito, ɗaure da towel da wani ƙaramin towel yana tsantsane kansa turus yaja ganinta azaune akan bed sai kuma yaja ya fuske da kallon tuhuma ta bishi ya basar kamar baiga irin kallonda takeyi masa ba,
Wanka Kayi? Ta jefo masa tambaya, murmushi yayi yace Dr akwaiki da son tambaya bayan kinsan amsarta, nisawa tayi sannan tace naga ka wanke harda kanka kuma wanka a irin wannan lokaci baka saba ba,
Zargin wani abu kikeyi kenan? Ni kowanne lokaci lokacin wanka nane kuma kullum ina wanke kai inaga saboda zuciyarki na wani wajene yasa yanzu wani abu ya ɗarsu miki arai,
Jijjiga kai tayi sannan tace yawuce."
Haka rayuwa tayita tafiya har aurensu yakai 2month duk juma'a Sawwama takanyi abinci akaiwa mahaifiyarsa dan kyautatawa kuma tanajin daɗin hakan,
Kewar Mama da Baba ya isheta tana zaune tunanunsu kawai takeyi,
Ahaka yazo ya sameta da safe dan yanzu yadaina zuwa ya kwana a cikin rana yake zuwa aduk lokacin daya samu dama,
Amma a hakan sai Allah ya sanya shaƙuwa a tsakaninsu har idan yawuni baizo gareta ba bayajin daɗi, amma ita Sawwama da wani abu daban ta alaƙanta zuwannasa,
Bayan yagama abunda ya kawoshi take sanardashi tanaso taje wajansu mama,
Yace ta shirya idan zai fita sai ya ajiyeta, dama ashirye take Hijab kawai tasaka taɗauki yaja da ƴar tsarabarta tafito, Dake baisan gidanba saida tayi masa kwatance Mamaki je yankamashi ganin gidansu bai taɓa ɗauk rashin nasu da ake faɗa har yakai haka ba kuɗi yaciro mai yawa yace tayi musu tsaraba dashi kasa karɓa tayi ta tsaya tana kallonsa girgiza kai tayi tace A'a kabarshi kawai gashi na taho musu da wani abun ta faɗi tana nuna masa jakar hannunta, wancan nakine wannan kuma nawane ki karɓa babu kyau maida hannun kyauta still bata karɓa tace toh karage yayi yawa, kamo hannunta yayi ya danƙa mata sannan yace ki gaidasu godiya tayi masa sosai yaji daɗin hakan tafita yana kallonta jiki a sanyaye harta shige gida, duk wani abunda yaje zato akan yarinyarnan sai yasamu hakan saɓanin hankalinsa, wani abunda ya lura da ita duk da cewq basuda hali amma kuɗi bai rufe mata idanuwa ba kuma yana tabbacin cewa da dan kuɗine bazata taɓa yarda da ƙudurin Dr ba tayi hakanne kawai dan babu yanda ta iya tanason ceton ƴar uwarta, gata da sanyin hali kuma zamansa da ita ya fahinci yarinyace mai tsantsar Haƙuri,
Nisawa yayi zuciyarsa cikeda tausayinta yaja motarsa yawuce,
Mama tayi murna ganin Sawwama sosai gashi taga tayi kyau kuma tayi kumari daga kallo hankalinta a kwance yake dukda abunda suke tunkara a gaba amma ita kwanciyar hankalin da ɗiyarta tasamu na wannan lokaci kaɗai yayi mata daɗi,
tsarabar da takawo mata ta miƙa mata mama tayita yimata albarka,
Sawwama saida takasa ɓoye irin soyaytar da ƴan uwansa suke nuna mata ta faɗawa mama,
Mama tace "Allah kenan Sawwama can mahaifiyarsa bata sonki shi yana ƙaunarki nan kuma mahaifiyarsa
na matuƙar ƙaunarki amma shi bai aureki dan yana sonki ba, Allah yayi miki zaɓi mafi alkhairi acikin rayuwarki,
Sawwama ta amsa da Amin,
Kuɗin daya bata ya miƙawa mama tace wai gashi injishi,
Mama tace duk wannan kuɗi masu yawan na menene Hafsatu da baki karɓa iya wannan ɗawainiyar da sukayu damu ma mungode Sawwama tace "mama nima banyi niyyar karɓa ba amma ya matsa mama tace toh idan babanku yadawo sai abashi,
Sawwama ta lurada mahaifiyarta tunda tazo sai tofe tofen yawu takeyi abun yayi mata kamar wacce takeda ciki amma bata furta ba dan tasan mamansu yanzu saita hau faɗa."
Har dare Sawwama takai agidan shida kansa ya dawo ya ɗauketa ya maidata gida sannan yakoma gidansa,
Dr yasamu ta dawo daga aiki amma daga kallonta tana cikin ɓacin rai zama yayi akan kujera yace waya taɓamin sarauniyata ce?
Cikin ɗaga murya tace ashe munafuntaat kakeyi?
Kamar yaya? ya tambaya! Ancemn anganka da ita yau amota ina kukaje?
Iska ya furzar yace ni nadauka wani abunne yadaru kika ɗaga hankalinki haka,
Wani abunne mana yafaru tunda ance anganka da ita a mota,
Gidansu fa zataje na kaita, kuma waye yazo ya faɗa miki sanyawa kikayi a ringa faɗa miki duk abunda nakeyi kenan?
canja topic din tayi da faɗin amm ai baka faɗamun cewa zaka kaita anguwa ba ka sanya driver yana kaita duk yanda zataje mana,
Nisawa yayi yace Dr kinsan banason ihu soyayyar da nake miki yasa nake gudun ɓacin ranki, meyasa kikeson sanyawa ranki cewa ni zanci amanarki kenanma baki yarda da soyayyar danake miki ba kenan?
Dawowa kujerarsa tayi ta zauna cikin tafara lallashinsa domin ta yarda dason da yake mata bazai taɓa wani da zai ɓata mata rai da ganganba,
Washe gari badan ransa yasoba ya nemawa Sawwama driver sannan yace duk yanda zataje tatafi kawai basai ta sanar dashiba, tawani wajan taji daɗin hakan domin zata samu ganin mahaifanta akai akai,
Amma wanu wajan bataji daɗi b adan hakan yana nuna mata baidamy da itaba kenan."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial38 Chapters
Vampire Genesis
Zuheil hurt anyone she could until the consequences of her actions caught up with her when she was murdered in retribution. In the depths of hell, she came upon an entity that had use for her in its perpetual war with the light. She was sent to a world different from her own, to fulfil its vague purpose. Zuheil awakens in the body of a Beast of great power. She must now learn how to control it and, in time, use it to dominate.
8 165 - In Serial41 Chapters
Once More
"Trouble is brewing, the world of Karridor is hurtling toward an inevitable doom, and no matter how long I ignore it nobody else seems willing to fix it!" Follow the lazy and capricious "Goddess" Alexandria as she struggles to find someone who can solve the big problems so she doesn't have to. After all Alexandria knows involving herself with the affairs of the outside world is a losing proposition that always ends in heartbreak, it's a lesson she's learned again and again, but maybe it's time to learn it once more? ===== a/n: project mostly dead, sorry folks *cover commisioned from Juan Miguel - thanks so much!
8 176 - In Serial11 Chapters
Evolved
in 2021 a secret government facility underneath a chemical plant is housing gene 175 aka the evolution gene. when the chemical plant blows up, it unleashes gene 175 upon the world. after laying dormant for a year, gene 175 activates; thus begins the apocalypse. people either evolve to gain power, or they deviate becoming abhorred. ten years into the apocalypse Noah Brookhart, who lost his family, now loses his life. in the ten years he experienced the apocolypse, he never once "awakened" his powers. after dying he wakes up nearly 10 years in the past (about a month after the apocolypse started,) after which, he evolves to stage 2 (which he never managed to do before,) discovering his power. now that he has a new found streangth can he avoid his bleak future?
8 137 - In Serial7 Chapters
Super Spies
Corey is enlisted at the Dark Moon spy network as a novice, and gets to know the beautiful and mysterious top super-spy, Nadine. What will fate throw in their paths? Will it throw them on a mission together? Will Corey's love for his heroine be reciprocated? What will Corey think if he finds out she was raped by a monster?
8 122 - In Serial39 Chapters
La Loi du Mystère [French]
L'équipage de l'Imbattable est loin de se douter que le naufragé repêché en pleine tempête est l'un des derniers utilisateurs de la magie, un art interdit par le Mysterium et ses inquisiteurs. Mais quand il revient à lui, le naufragé a perdu la mémoire. Qui est-il et comment s'est-il retrouvé là? C'est ce qu'il va devoir découvrir par lui-même.
8 185 - In Serial32 Chapters
Kita Shinsuke
You were always just the third Miya child until... he came. I do come back and read comments that you send and please don't write any mean or rude comments to my writing or to other people's comments because I will either address it or delete the comment. Hopefully it's getting better and my spelling is shit. I do not know what it is like to have cuts or how to deal with them. Sorry if this is inaccurate. Also I do not own any of these characters or the anime. IM ALWAYS READING WHAT YOU SAY!!!Thanks so over 52k reads!! WTF TYSM!!!!
8 170

