《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 76
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 76
Cikeda murna mahaifansa sukazo nema masa auren Sawwama batareda sunsan da wata kulallayiya a kasa ba,
Sun nemi aure cikin karamci suka bata sadaki a wajan suka yanke lokacin aure sati biyu kawai,
Ba baba kadaiba har mahaifinsa saida ya tsorata ganin Gomna mai sauka da manya manyan mutane a gidansa sunzo neman auren jikarsa,
Mahaifinsa yace lallai Abubakar yayi sa'ar iyayen mata masu karamci ina fata wannan aure yazame musu alkhairi gabaki dayansu Allah yasa mutuwa zata rabasu,
Jin haka yasanya jikin Baba yayi sanyi yanzu ya sake tabbatar da cewa mijin da matar kawai suka shirya lamarinsu,
Malam sa'adu ya amsa da amin."
Bayan sun tafi Yaya zakari ya dubi Baba yace "Hamisu kaikam kanada sa'a yanzu nikam na yarda ajikin yaranka take auran masu hali, dakuma nufi na ubangiji idanba hakaba yaushe zamu taba tunanin wadannan mutanen zasuzo wajanmu su kaskantar da kansu a neman aure, gashi yanda suka mu'amalancemu kamar babu wata bambamci tsakaninmu dasu.
Malam Sa'adu yace "Allah ya zaunar dasu lafiya dan gaskiya munga karamci a wajansu."
An sallami Hindatu daga asibiti bayan angama mata treatment dinda yadace amma duk bayana sati zata dinga zuwa ganin likita sannan an daurata akan magani,
Dr Sajida dakanta take musu duk wani abu hatta magani kawo musu kawai tayi sannan tace everyweek akwai wanda zata sanya ya ringa daukosu yana kawosu taga likita,
Mama tace abunda kikayima haka mungode basai an sanya mai daukomu ba, in sha Allahu da zarar sati yacika da kanmu zamuna zuwa."
Dr tace "toh shikenan tunda hakan kuke bukata saiku na zuwa dakannaku nikuma zan sanya muku ranarda zakuna ganina."
Alhaji da yakira yaronsa ya shaida masa yanda sukayi cewar ansaka biki sati biyu masu zuwa.
Abubakar ya sanarwa Dr, kyabe baki tayi tace toh shikenan babu damuwa duk wani abunda yakamata muyi sai muyishi cikin lokacin,
Halima dataji zancen auren da Sawwama zatayi kuka ta ringa yi tana fadin yaya Sawwama dan Allah karkiyi wannan auren ke kenan bazaki kasance cikin farin ciki ba? Mai yasa zaki sadaukar da taki rayuwar saboda rayuwar wasu,
Sai lokacin Sawwama tayi magana da fadin lallai Halima niba saboda rayuwar wasu zanyi wannan abunba saboda rayuwar Hindatu ne kuma kowaye a matsayina inajin abunda zai aikata kenan banajin na aikata wanj abu ba dai-dai ba,
Kuma ni ba koda yaushe bake cikin kunci ba rayuwarda nayi da Sadam nayishi cikin kwanciyar hankali yabani kulawa da soyayya maras misaltuwa wacce bazan taba mantawa da itaba,
Dafata Halima tayi sannan tace dukda haka Yaya Sawwama dan Allah ki janye maganar auren wannan mutumin ni hankalina bai kwanta da auranba tunda ta rigada tabiya anyiwa Hindatu aiki muce musu zamu biyasu kudinsu kawai,
Hmm lallai Halima toh idan mukayi haka ya zamana mune marassa kirki kingani kiyi shiru da wannan zance kawai tacika mana alkawari kamar yanda ta dauka yarage namu mu cika mata,
Mama wacce zancen karshe taji kawai shigowarta kenan tace halima anya kinada hankali?
Advertisement
Tayaya za'a fasa wannan aure bayan su sun cika nasu alkawarin?
Da zuciya daya mu zamuyi wannan auren Allah yasa hakan ya zame mana alkahiri gabaki dayanmu,
Mama nifa rayuwar yar uwata ne banaso yashiga cikin wani garari tayaya zata yarda bayan ga wasu sharuda na banza data kafa mata?
Mama malam Rabi'u fa lauya ne zai iya tsaya mana dan ko shari'a mukayi dasu bamuda laifi mun amince musune kawai dan munason ceto Yar uwarku,
Baba wanda shigowarsa kenan ya tsinci zancen a sama yace "ke Halima kinsan wani irin mutane ne su kuwa? Manyan mutane ne yanzu haka babansa shine gomna daya sauka, har kina tunanin zamu iya ja dasu? Toh maganin kar ayi karma afara, Allah ya zabar mana mafi alkhairi kuma banaji ajikina iyayensa zasu yarda yarabu da ita basusan da lamarin saki bayan haihuwa ba, karkiso kiga yanda iyayensa suke murna da aurenann sai fata kawai sukeyi ace mutuwa ce zata rabasu,
Mama tace nima haka nake fata amma wannan matar tasa yar bala'i ce kanaji sharudan data gindaya da zarar tacika musu burinsu, Baba ya nisa sannan yace toh ai mu muna namu shina Allah na nashi kuma nasanne gaskiya toh dukanmu mu zubawa sarautar Allah ido."
Shiru halima tayi jin yanda dukansu suka dauki lamarin amma da dan itane da fasawa za'ayi."
Sawwama bata sake tanka musu ba ita abarta da ahunda yadameta guda daya ma."
Da dare Sawwama da kanta taje wajan Mama da Baba ta maganar tanaso amaida Hameeda da Hamdan wajan iyayensu,
Mama tace haba Sawwama tayaya zaki maida yaranki wajan da ke ba sonki suke ba, dan kinsan zaiyi wuya ya kasance bawa mahaifiyarsa za'a barsu ba wancan matar tasa bazata taba iya rike miki yara ba a idonkima ta lahamtasu bare babu idonki,
Sawwama tace Mama nida aganina hakan shine yafi dan bazan iya zuwa dasu can gidanba, Baba yace bazai yiwuba kam dama ace auran baida wani sharadine toh sai kitafi da yaranki ya rikesu.
Kuma Baba banaso nabarsu a wajanku idan nabarsu wani nauyine na sake daura muku,
akaisu can babu yanda ta iya dasu dan jininta ne,
Baba yace toh idan hakan kika gani sai amaidasu din, mama tayi shiru itadai yarnta baiso maida yara yan shekara goma sha ba,
Baba yace Sawwama ta maidasu tace bazata iyaba sai dai Mama takaisu,
Mama da kanta ta shiryasu da kayansu ta nufi gidan dasu,
Anci sa'a weekend ne Dady na gida bayan sun gaisa da Mummy adarare sai ta nemi ganin dady natasan mummy ta shiryu ba batasan yanda zata dauki abunda shiyasa ta nemi ganin dady,
Bayan sun gaisa dady bai ganeta ba ko ince baima santaba saida mummy tayi masa bayani,
Cikin hikima Mama tace ga Hameeda da Hamdan nan nakawo mukusu, hakan bawai dason ran mahaifiyarmu komu gabaki dayanmu ba amma babu yanda muka iya saboda ita mahaifiyarsu zatayi aure kuma yafi dacewa ta maidaosu gidan mahaifinsu da ace an kaisu gidan wani daban ko yaya zasufi samun sakewa cikin danginsu,
Saida ta ida Sannan Dady yafara magana yace toh dama tun farko abunda yasa banyi tunanin karbosu ba saboda zasu daukewa mahaifiyarsu wata kewar toh amma tunda kun kawosu Alhamdulillahi,
Advertisement
Kunya da takaicin abunda muka aikata muku ya hanani zuwa nabaku hakuri dan bansan da wani ido zan kalleku ba bayan irin laifin da muka muku,
kun bamu auran yarku cikin mutumci batareda laifi ko wata matsalaba mun dawo muku da ita gida tanada kananun shekaru,
Mama tace ai mungodewa Allah daya kasance ba wani laifin tayiba, dama kyawun zamantaka shine a hadu cikin mutumci arabu ahaka bare mu yanzu bamu rabuba zuri'a ta kullu tazama guda daya, albarkacin wadannan yara andawo yan uwa,
Dady yace Allah yamausu albarka yakuma rayasu itakuma Allah yabata zaman lafiya tsakaninta da mijinta wannan aure da zatayi Allah yasa mutuwa kawai zata rabasu,
Mama ta amsa da amin,
Mummy kuwa ta kunshe jikin kujera kamar wata munafuka tkasa cewa komai,
Ganin irin kallonda baba yake mata yasa tayi saurin cewa laifi kam anyi muku laifi amma ku gabarcemu Mama tace "babu komai atakaice, girgiza kai Baba yayi yarasa wani irin hali mummy kedashi yanzu haka zata nemi yafiyar wanda tayiwa laifi?
Tabbas da sauranta zai ya kara gyara mata zama duniya bata gama goganta ba tukunna."
Mama ta kunce hamedda dake goye ta mikawa mummy tayi saurin karbarta ta mika Hamdan saiga hawaye yafara bin kumatunta ji takeyi kanar tajuya da yarannan kada tabarsu anan,
Mummy ta rikesu gam-gam dake bacci sukeyi basusanma a hannun wa suke ba,
Da mama zata tafia Dady yayita mata godiya Sannan yace idan Auren yatashi dan Allah su ako masa zaizo, mama tace "in sha Allahu tafita cikeda kewar yaran."
Yaran mummy wuni tayi inaka saka inaka aje dasu sai lallabinsu take gashi Hameeda sai kuka take bata saba da itaba gara Handan baya kuma amma bai sakeba,
Sanin cewa batada hope na samun wasu jikokin daga tsatson Sadam nan gaba yasa ta rike yaran zallar soyayya take nuna musu."
Sawwama har zazzabi saida tayi na rabuwa da yaranta gabaki daya takeji duniyar bata yimata dadi, gashi aure sak shirye-shiryensa akeyi,
Hajiya ta sa aka sanarda daurin auren a gidajen yada labarai kamarsu tasoshin TV gidajen radio da sauransu,
Nan danan labari ya karade ko'ina, dady a gidan TV yaji sanarwar ya sanya aka kira mummy bayan tazo yayi mata alamu da takallo TV zama tayi tafara kallo saida tajira har aka kara mai maitawa sannan dady yayi magana yace "kingani koh?
Kinga Sawwama saboda yar gidan talakawa gashi yanzu zata auri attajiri Dan gidan attajirai wanda dukiyarsa bada kwatanci da tamu mu bakomai mukedashi agabansu ba,
Yanzu fadamin ke kowa yarinyar wace taci riba? Waye mai kudi da takala a halin yanzu?
Mummy takasa gaskata abunda kunnuwanta sukeji abu sai kace al'amara,
Dady ya sanarwa Sadam Auren Sawwama da wanda zata aura, Sadam yagani a kafafen sada zummnta amma bai taba dauka cewa wai Sawwamarsa bace,
Ranar bacci gaggararsa yayi shikenan Sawwama ta manta dashi zata auri wani, duk wani ya auri Sawwama da irin kyawawan halayanta a halin yanzu shine yaci ribar aure,
Har kuka saida Sadam yayi yanajin zafi da kuna acikin ransa, ya tabbata Sawwama tajirashi tajira dawowarsa, amma bai dawoba kuma a yanzuma yasan dole akwai dalilin dayasata yin aure da wuri,
Fatansa kawai ta rayu cikin farin ciki maras adadi,
Duk wani al'ada da akeyi na aure sanda familyn mijin Sawwama sukayi abun harya yiwa Sawwama wani iri dan ita aganinta tunda bawani auren dadewa bane duk wasu abubuwan ba'ayisu ba,
Dr hankalinta kwance ganin mijinta tareda ita ko alamu baya gwadawa cewa zaiyi aure,
Yanzuma haka zaune suke shida ita Dr tace yakamata afara gyara yanda amarya zata zauna kaga lokaci sai tafiya yakeyi,
Murmushi yayi yace aigama gyara yanda zata zauna, cikin mamaki tace dayaushe danni ban ganiba,
Nisawa yayi sannan yace bani nayiba Alhaji ne yasa aka gyara daya daga cikin sabbin gidajen daya gina yace anan zata zauna,
Zaro ido Dr tayi cikin mamaki tace what? Kasan da hakan shine baka sanarda niba? Tayaya za'ace zata zauna a sabbin gidan Alhaji bayan kowa acikin zuri'arku gidajen suke hari har wani gata tasamu haka awajan alhaji? Aurenda ba dadewa zaiyiba,
Murmusawa yayi yace sanin ba dadewar zaiyiba shiyasa bandamu ba, kuma kinsan Alhaji, girgiza kai tayi tace "koma yaya kasan yanda zakayi tadawo nan da zama ina kallon komai a idona hankalina zaifi kwanciya,
Bazan iyaja da maganar alhaji ba bayan haka kuma sonda nake miki bazai iya barina nayi tarayya da wata mata while kina gidanba,
Dr tace naji amma ba wannan gidanba ka nema nata wani gida can daban wanda bai kan wannan ba, tayaya zata zauna awannan gida?
Kamo hannunta yayi cikin sigar lallashi tace me kikeso nacewa alhaji? Matarda zan aura batakai zama a wannan gidanna ya canja mata wani bakyaganin zasu fahimci wani abu?
Har ranta taji zafin ambatar matarda zai aura da yayi, a fili tace amma meyasa baka sanar dani dawuri na cewa a gidan zata zauna?
Saboda banyi tunanin hakan zai zama damuwa ba tunda ba wani dadewa zatayi ba yabata amsa,
Shiru kawia Dr tayi amma sam ranta baiso abunda yafaru ba."
Kudi sosai danginsa sune kashewa na shirye-shiryen wannan auren Kuma ba abnun mamaki bane idan akayi la'akari da kasancewarsu manyan mutane bayan haka kuma abunda suka dade suna buri kenan,
Al'adu kala-kala sukeyi yau akawo wannan gobe akawo wannan Mama har tagaji da abubuwan da sukeyi idan taga yanda yan uwan suke murna da rawar jiki ramta baci yakeyi kasancewar tasan auren abune mawuyaci ya dade."
Kayan aure kuwa da aka kawo bayan yan uwan da suka karba mama bata kira kowa yagani ba dan abun yafita a hankali, daki guda aka zubesu aka rufe, Mama batayi kasa a guiwa wajan gyara Sawwama ba dukda tasan cewa bawani aurene nason rai ba, amma dukda hakan bazata barta ba."
Biki saura kwanaki aka aiko masu lalle daga gidansu ango akayi mata harda kitso, duk wannan abunda akeyi dangin ango ko mutum daya baisamu sanya Sawwama a ido ba bare susan yaya kalarta take."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial16 Chapters
Pangea: A New World
What is the system? What is its purpose? Who made it? All three are questions that have been debated throughout the ages, and yet to date the answers remain unfound. However, some irrefutable fact exists. The system expands, grows and enables. The system seeks to expand its reach, grow its influence and enable those under it to flourish. A Beginners Guide to the System, Germain Fitzgerald This is a story not of the system but of an individual who suffers, flourishes and ultimately evolves under its influence. Follow the growth of Jacob Lockerby from a normal teenager granted access to a world of his dreams and watch as this previously ordinary individual becomes extraordinary. Herein lies the tale of he who would become a legend. Update Scehdule: Every Sunday 10pm GMT. I appreciate this is a rather slow schedule but this is my first attempt writing and I am doing this for fun while trying to juggle my final university year workload with writing this. I hope you stick with the story and feel the chapters are worth the wait. Lastly just a shameless beg but please do rate and comment, feedback is always welcome and will help me improve my writing.
8 203 - In Serial40 Chapters
Embracing Tears
An innocent little girl was being ostracized and persecuted in her small village. People refer to her as a daughter of a Demonic Witch. With the death of her mother, her entire life came plummeting down. Her fate was turning for the worse. Her future was grim. Life was not fair to the innocent little girl. However, things began to change when she met a particular young woman and a Dragon. Will they be the stars that will light the little girl’s path towards a brighter future? Cover Image Source: https://pin.it/7LAMHP6
8 251 - In Serial13 Chapters
Every Hateful Instrument
Hail-and-Farewell Vinright is a pirate, ferrying drugs and weapons across the galaxy. When he discovers that the headaches he's been plagued with are not a sign that he has a brain tumor, and are instead the rare God-given gift of the power, one in a million psychic abilities, Hail sees the opportunity to help his family profit. Only people with the power can build the stardrives at the core of every ship, and the market for them is controlled by the Imperial government. Pirates would pay huge sums for one, so Hail's family enters the market. Aymon Sandreas is the least likely candidate to take the Imperial throne upon the retirement of his master, First Herrault. When Aymon steps too far out of line, his master sends him away to find the pirates who are flooding the galaxy with stardrives, destabilizing the Imperial government and the spacefaring Guild. Expecting an easy but boring task, Aymon's interest is piqued when the mysterious stardrive maker proves a clever and capable adversary. When Hail and Aymon finally come face to face, Aymon offers Hail an opportunity: work for me, in exchange for your life. But Hail wants nothing more than revenge, and he's willing to play the long game to get it...
8 157 - In Serial10 Chapters
Le roi fou des hommes-arbres - Aventures des Arbolarbres(FR)
Histoire Fantastique pour adolescents et jeunes adultes Dans un pays où la magie est influencée par le cycle des saisons végétales de l'Arbé, de la Poussé, de la Germé et de la Floré, un jeune homme arbre (Arbolarbre) appelé Oak Quercus découvre son don de pour la magie, celui-ci provenant de sa longue lignée. Cependant, sa magie sera-t-elle suffisante pour arrêter le Roi Fou du peuple Arbolarbre, celui qui a enlevé toute sa famille pour les punir d'avoir élevé la voix contre ses impôts injustes ? Taxes qu'il cherche à utiliser pour lever une armée afin de conquérir les Royaumes Animaliers et assouvir sa faim de chair et sa quête d'mmortalité, s'opposant ainsi aux enseignements sacrés de l'Arbre-Dieu et de la Foi Végétale ?
8 169 - In Serial31 Chapters
Broken [FINISHED]
An adopted by Lin-Manuel Miranda fanfictionDenise is a normal girl. She is not popular, but not an outsider either. She wears normal clothes, and goes to a normal school. To put it shortly, she's a perfectly normal girl. Or is she? Some secrets remain truly secret. Some scars aren't visible on the outside. Some people are Broken.Author's Note:I have been reading a lot of these "Adopted by -" fanfictions lately. I wanted to write something different. Take the cliché concept, and change it in something original.
8 232 - In Serial5 Chapters
❄️My Yuki Academia(bnhaxnaruto)❄️
After the events of the reanimation jutsu during the Fourth Great Shinobi War. Haku and Zabuza had thought that their time in the land of the living is over. But then just before they ascended to the afterlife, they were met by the Sage of Six Paths and given the chance to be teleport to leave live in a new world, a world of heroes, villains and quirks as long as they take a plus one...Highest Tags:#3: Hakuyuki- August 2, 2020#6: Narutoxbnha-August 2, 2020#7: Bnhaxnaruto-August 2, 2020#8: SageofSixPaths-August 2, 2020
8 128

