《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 75
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 75
Sawwama tayi kasa da kanta tace "kudinne ko miliyan daya bai haduba amma yanzu baba yafita bamusan yanda Allah zaiyi ba,
Murmushi Dr tayi tace abune mawuyaci ace yahada wannan kudin acikin karaminn lokakaci haka,
Sawwama batace komaiba likita tace idan babu damuwa inaso insan dalilin rabuwar aurenki,
Da sauri Sawwama ta dago ta dubesta ta gyada mata kai irin eh haka nake nufi, kawarda kai Sawwama tayi tace babu dalili, murmusawa tay sannan tace akwai wani abunda yake faruwa babu dalili kuwa Sawwama?
Ki saki jikinki dani ki fadamin bawai haka kawai nakeson sanin sirrinki ba inaji ajikina zan taimaka muku da rashin lafiyar kanwarki, Sawwama ta dago da sauri tace "da gaske jijjiga kai tayi tace "eh amma saikin saki jikinki kin sanar dani dalilin mutuwar aurenki,
Jijjiga kai Sawwama tayi sannan tace "bawani dalili bane kamar yanda na sanar dake mahaifiyarsa batason auren mukuma muka nace so akarshe saida ta raba auren ko rabuwarmu ma babu dalili itace ta sanyashi, wasu yan kalilan abubuwa Sawwama ta sanarda ita,
Jijjiga kai tayi sanna tace "toh nima dai idan wannan matsalar uwar mijinne ina fama da ita dan bataki itama taga ya sakeni ba,
Sa'ata daya danta yana mugun sona dan bazai iya rabuwa daniba saukin dana samu kenan, ni gabaki daya danginsa ma ba sona suke ba, amma tunda mijina nasona toh baidameni ba basu nake aureba."
Shiru tayi na wani lokaci sannan tace "toh ni Sunana sajida kumani likitace kamar yanda kika sani,
shekarata sha takwas da aure amma har yau bansamu haihuwa ba, Shekararki nawa? Ta jefawa Sawwma tambaya, "sha tara Sawwama tabata amsa atakaice,
Da na haihu farkon aurena da yanzu yarinyata tayi kamarki Dr tafadi tana kara nazari akan Sawwama,
Murmushi kawai Sawwama tayi Dr tacigaba da fadin,
"Dafarko mu muka tsaida haihuwa lokacin ina karatun likitanci kinsan babu yanda za'ayi mu hada karatun likitanci da haihuwa, nagama kuma alokacin aiki yayi mini yawa muka kara tura haihuwar zuwa wani lokaci toh yanzu kuma haihuwar muna nemanta amma babu,
Idanda nida mijina ne toh babu wata damuwa danmu zamuyi rayuwarmu ahaka cikin farin ciki,
Amma banda danginsa, danginsa sun matsa akan sunason ganin jininsa,
Mijina yanada kudi sosai babban dan kasuwane yanzu kuma yashiga harkar shiyasa sannan kuma shidin dan gidan manyan mutane ne mahaifinsa yayi gomna a garinnan shekara goma da suka wuce,
Danna wayarta tayi ta nuno mata hoton wani mutum kyakkyawan gaske matashi da bazaifi 40yrs ba, mika mata wayar tayi Sawwama ta amsa tana kallo, kallon wayar tayi sannan tajuya ta kalleta fuska cikeda tambayoyi, amsan wayar tayi tace "kin ganshi koh? Mijina kenan, mijinki? Nikuma meya hadani da mijinki Sawwama ta tambaya!
Murmushi tayi sannan tace ina kaiki zamuzo wajan,
Shi wannan da kika gani Mijinane Sunansa Abubakar Muhammad Dabi,
Inasonsa sosai shima yana sona fiyeda tunaninki, ina matukar kishinsa sanin hakan dayayi ya sanya bai yarda ya kara aureba duk kuwa da takurin da hajiyarsa take masa akan aure, yanzu gabaki daya ta tsaneni gani take ni na hana danta aure, eh tabbas ni na hanashi aure saboda bazan taba iya zama dashi da wata mace ba, amma naga tsananin da mahaifiyarsa take sanya masa yanaso yazama katanga tsakaninsa dashi,, domin yanzu bai samun zama kwata-kwata saboda a kullum maganarta ya kara aure yayi aure yayi aure, maganar bata wuce haka, hakan yasa sam baya zama a kasar yake nisanta kansa da ita don wannan dalilin,
Advertisement
Kamar yanda na fada miki soyayayr dayake yimin ya hanashi kara aure, nima kuma bazan iya bari yayi aurenba toh amma tunda Iyayensa haihuwar sukeso suga yayi shine na yanke wani shawara tun lokacin dana fara ganinki,
Inaso ki auri mijina zaro ido Sawwama tayi cikin kidima tace "na auri mijinki awani dalili? Ni nace miki aure zanyi? Mijina yananan zai dawo gareni bana bumatar naki mijin, mikewa Sawwmaa tayi zata bar mata wajan ta kamo hannunta tace dawo ki zauna ai bakiji karashin zancen ba,
Zaunawa Sawwama tayi Dr sajida tacigaba da fadin nima bawai ina nufin ki auri mijina ki zauna dashiba dan bazan iya barin hakanba, kawai inasone ki aureshi na wani lokaci ki haifa mana yaro daya kacal saiki fita,
Da mamaki Sawwama ke kallon wanna mata shin meta maida ita tukunna?
Hawayene yafara gangarowa a kumatun Sawwama,
Dr tacigaba da fadin "bayan kin haifa mana yaro daya zaki iya tafiya ki komawa mijinki, dan nasan cewa mahaifansa suna daff dayi masa aure, yaronda zaki haifa bandamu ace dana ko dankiba kowanne a kirashi har indai dai dan mijinane toh da sauki domin zai ruguzamin duk wata barazanar da take cikin rayuwata, bazna iya zamada kishiya ba amma zanyi hakuri na zauna dake na wani lokaci kafin kurabu, dangin mijina ba kananun mutane bane da zan iya ji dasu dole muyi yanda sukeso amma ta wata hanya daban, har indai sukaga jininsa nima zasu barni na sarara."
Zamuyi contract dake zan biya kudin aikin kanwarki gabaki daya da nauyinta sannan duk wani kudinda jinyar zataci nice wacce zan biyahsi ko shekara nawa Zatayi tana shan magani ni zan dauki nauyi harsai ta warke idan takama na fita da ita kasar gabaki daya toh zan fiddata amma in return zaki haifawa mijina yaro guda daya rak kinga farkon haihuwarki twins kika haifa idan mukaci sa'a muma zaki iya haifa mana su, Yanzu ke zaki yanke hukunci Shin zakibar kanwarki tamutu? Ko zaki yarda da abunda nafada miki? Nasan kinada halinki zakiyi zabinda yadace da rayuwarki, kije idan shawraa zakiyi da mahaifanki kiyi amma abunda kike dashi gabaki daya bai kai kwana daya ba."
Sai dai wani abu guda daya danakeso kisani shine bazan taba daukan cin amana ba akan mijina babu wani abunda bazan iya aikatawa ba da zaran kin haifi yaro daya bana fata ki sake zamamin acikin gida ni kadaice zan kasance matarsa har mutuwa."
Mikewa Sawwama tayi jikinta a mugun sanyaye tanufi dakin da suke mana tana kallonta cikin damuwa tace wani abunne ya faru da hindatun koh?
Girgiza kai Sawwama tayi sanna ta zauna takasa cewa komai,
Har Baba yadawo, ganin Sawwama a cikin damuwa sosai Baba ya dafata yana fadin Mamana ayi hakuri amma zancen kudi kam duk yanda nake tunani naje ba'a samuba na sanya gidanmu a kasuwa idan Allah yasa ya sayu sai abasu wani abu daga cikin kudin subimu sauran,
Sawwama tace baba karka damu za'ayi mata aikin kamar yanda suka bukata,
Baba yace toh Abunne ba'a cewa komai,
Mama tace toh tun datsuma kika dawo daga wajan likita amma kinki sanar dani yanda kukayi da ita,
Shafa kan Hundatu Sawwama tayi sannan tace mama baba muje waje muyi magana, suna fita bayan sun sami waje sun zauna Sawwama ta shaida musu yanda sukayi da likita sannan tace na yanke shawara baba har indai Hindatu zata samu lafiya zanyi abunda sukace ba yaro daya ba idanma goma sukeso zan haifa musu, kuka mama tasaka Baba yace A'a Sawwama dan ceton rayuwar daya yarinyata bazan saka rayuwar daya cikin garari ba,
Advertisement
Murmushin dole Sawwama tayi sannan tace Baba ni Karka damu dani narigada na yarda da cewa ni Haka ƘADDARAR RAYUWATA take, mama takasa cewa komai tasan a wannan halinda ake basuda wata mafita data wuce hakan,
Baba ma saida yayi hawaye yace "yanzu maganar ƴan uwansana cewa yana saida ƴaƴansa da kudi,
A fili kuwa bbau abunda take futawa sai Allah yayi miki albarka,
Mama ma hakan tafadi,
Jiki a sanyaye Sawwama takoma office ɗinta ta sanat da ita cewa sun amince da abunda tafaɗi,
Takarda tabawa Sawwama tace gashi ki sanya hannu anan, ba akan komai ba sai akan cewa da zarar kin haifi yaro ɗaya zaki rabu da mijina idan kuma bahaka ba toh zanyi miki duk wani abunda nayi niyya,
Batareda damuwa ba Sawwama ta sanya hannu naɗe takardan tayi ta sanya a jakarta sannan tajuya ga Sawwama tace saiku fara shiri gone za'ayi mata aiki dama already nagama tanadar komai domin nasan zaki amince,
Daga karfe sha biyu na daren yau karta sake cin komai gobe 12am za'a shiga da ita aiki,
Sawwama tarasa godiya zata yimata kokuwa haushinta zataji, babu yanda ta iya afili ta furta mungode."
_____
Dr Sajida tana shiga gida da murna take sanarwa mijinta yanda sukayi,
Nisawa yayi yace "Wai dole sai anyi wannan abunne?
Jijjiga kai tayi tace "hakan zaisa idon hajiya ya sauka akanmu tabarmu mu sarara ko kasamu kadaina yawan tafiye-tafiye mukasance tare,
Amma mamin alkawari daya cewa bazaka tana sonta ba, kuma tana gama aikinta zaka saketa tatafi,
Sannan banaso kayi mata sakewar da har zasu shaku da ita, daga zarar tayi ciki kuma shikenan tunda abun nema yasamu saika daina kwana da ita dan kaima nasan dolece zata sanya ka kusanci wace macen wacce baniba,
Kuma yarinyace shekararta sha tara iyayenta basuda karfi, idan kaji zaka taimaka musu wannan ban hanaka ba amma ni nayi nawa iya abunda zan iya yimusu,
Cikin mamaki yake kallonta yace ni? Nine zan auri yar shekara sha tara?
Gabaki daya har nawa take da zatayi aure?
Bata fuska tayi tace karka manta ina shekara sha takwas ka auroni, dafa da yanzu ba daya bane kigane mai zai hana ki canja wata wacce tafita shekaru,
Raba jikinta da nasa tayi cikin bacin rai tace nafasan mai nakeyi so kake na nemo mai yawan shekaru tazo naga ba dai-dai ba?
Ita wannan dai ita nagani kuma ita zaka aura, ganin ranta yabaci yasa ya amince badan yaso ba, amma yana dan shekara arba'in tayaya zatace zai auri yar shatara,
Ganin ya sauko yasa tace saika sanarda su hajiya cewa zakayi aure sai hankalinsu ya kwanta za'a kawo musu abunda ransu yakeso abarni nasha ruwa."
Shiru kawai yayi batareda ya amsa ba dan ransa bayason yawan aibata danginsa datakeyi."
Zaune yake gaban wata mata wacce ana kallonta za'a fahimci ta hada jini da jinsun fararen fata da alamu ruwa biyu ce,
Ganta yana gefe batada alamun amsa gaisuwarsa,
Rangwabar da kayi yayi yace hajiya, Hannu ta daga masa tace "idanba da zancen aure kazoba toh kaje abunda kawai nayafe gaisuwa, murmushi yayi yace "Dama da zancen auren nazo amma tunda kince kin yafe barina tafi,
Saurin rikio hannunsa tayi tace "zo dawo nan zauna kace aure zakayi? Jijjiga mata kai yayi dagaske yafada alokacin da fara'arta take fadada, nanma kara jijjiga kansa yayi, Sumbatarsa tayi a goshi hadeda fadin Alhamdulillahi, Alhamdulillahi,
A'ina matar take?
Murmushi yayi yaji dadin yanda yaga fara'a akan fuskar mahaifiyarsa a fili kuma yace a cikin garinnan amma fa iyayanta basuda karfi hajiya,
Kara murmusawa tayi tace su masu kudin su sukayi kansu? Komu da mukeda dukiya mu muka bawa kamu wannan duk nufine na ubangiji, har indai tanada tarbiya kuma gidansu gidan mutumci toh Ahamdulillahi,
Kamo hannunta yayi yace Hajiya sai a sanya alokaci a tamabayrmun aurenta idanda hali ayi komai lokaci daya agama,
Hajiya tace aiko dolenmu ma muyi sauri tunda shekara nawa muna fama yau bada wayonmu ba Allah ya tsagi bakinka kace zakyai aure,
Yanzu Alhaji zan jira yashigo yatafi meeting yana fitowa saika fada masa a fadawa yan uwa kowa ya hallara za'ayi babban taro,
Hajiya aure bana fariba wane taro kuma?
Kawai inaga kaman Alhajin da dan abokanansa suke su karbamin auren yafi,
Bata fuska hajiya tayi tace kul haka bazai yiwuba ai aure aurene idanma na karshene sunansa aure."
Bayan fitarsa yan uwansa hajiya ta ringa kira tana shaida musu zancen auren,
Bayan mahaifinsa ya dawo ma ta sanar dashi shima yayi farin ciki,
Bayan yakoma yake sanarda Dr yadda sukayi da hajiya cewar tanaso ta hada taro, tabe baki tayi sannan tace rabuda ita ta hada kabarsu suyi yanda sukeso yanda zasu gamsu da auren muma nan muna namu shirin."
Mahaifinsa ya kirashi akan yayi masa bayanin mahaifam yarinyar babu bata lokaci ya sanar masa komai dan shima Dr ce ta sanar dashi,
Washe gari akayiwa Hubdatu aiki da taimakon likitoci daban-daban Dr Sajida ta jagoranci aikin, har likitocin da bata lissafa ba saida ta gayyatosu domin har indai burinta zai cika ta shirya kashe ko miliyan nawa ne,
Anyi aiki cikin nasara awanni ya daukesu suka gama suka fito wannan karon wani daki danan aka kaisu Amenity dake cikin babban asibitin dakin yayi kyau matuka, daganan akaci gaba da basu kulawa ta musamman."
Yan uwansa da mahaifansa sunyi mamakin yanda akayi baba ya kudi mai tarin yawa a kankanin lokaci har akayi aikinnan, kowannensu zuciyoyinsu cike take da tambayoyi."
Cikin kanakinin lokaci mahaifinsa yasa aka masa bincike akan mahaifan Sawwama kuma sun samu yabo sosai,
Cikin wani dan lokaci yace ashirya zasuce nema masa aure,
Yakoma gida ya sanarwa Dr Sajida itakuma ta sanar musu,
Baba dakansa yayi mahaifinsa bayani bai boye masa komai da dalilin aurenba, mahaifinsa yace hakan da tayi shine dai-dai don ceton yar uwarta,
Dan kowama a matsayinta hakanne zai aikata amma ni ina fata cewa Allah yasa wannan aure da zatayi ya kasance ta samu farinciki maras misaltuwa Allah yasa wannan aure mutuwa ce kawai zata rabasu,
Baba cikin jin dadi ya amsa da amun,
Malam Sa'adu yace ka turosu wajena zan sanarwa yan uwanka babu bukatar sai anyi musu bayanin dalilin auren kubar wannan sirri atsakanin mu da ita matarsa da mijin dan bana tunanin koshi mijin dangainsa sun sani bazai iya tunkararsu da wannan zance ba,
Baba yace in sha Allahu, dama shi bawai yanada niyyar fada musu bane dan yasa rashin fahimta irin tasu baisan yanda zasu dauki lamarin ba."
Sati biyu da yiwa Hindatu aiki jiki yayi kyau sosai ko abinci Dr ce take aiko musu komai nasu ta dauke maimakon abun ya burgesu sai sukejin rashin dadi da da hali da sun dakatar da ita da wannan hidindimun da bazasu burgesu ba itadai tayi musu abunda suke bukata itama zasuyi mata abunda take bukata."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial20 Chapters
Strongest Sorcerer
Tens of years, thousands... even millions! Deaths, rebirths... none shall hinder me. To find you... to see you... to hold you in my arms! Nothing shall block my path even if I go against the "will" of the heavens again! -The Strongest Sorcerer- This story is about a mysterious mage named Gin, in his journey through the vast realms of the Myriad worlds in search for the reincarnated soul of his beloved. From betrayals to conspiracies that involve the heavens and the hells, enslaving ancient dragons, killing gods and facing the first fallen.
8 211 - In Serial10 Chapters
I Shall Prevail
Creatures roam the lands, the skies and the seas. Races from noble elves to stubborn orcs can be seen. Strong prey on the weak since as long as time has been. The gods, giants and titans are no more but urban legends long since forgotten. Here, strength is key, for he with strength can survive and protect his loved ones. "I will grow strong no matter the cost, my sweat, blood, and tears will be the only ones falling, for I, myself, will rise. I won't quit! I won't give up! I will give it my all, I shall Prevail!" - shouted a young boy atop a hill as tears dropped from his eyes, he wasn't going to allow life to hurt him anymore. He would protect his loved ones, he would control his own fate.
8 65 - In Serial62 Chapters
IROKO - An Elsewhere Naruto Fanfiction
Five years after the Fourth Great Ninja War, in the peaceful Village Hidden in the Leaves, 13-year old Iroko Nakata dreams of surpassing his hero, Naruto Uzumaki, and becoming the ultimate ninja! As he teams up with the eccentric-for-a-sensei Hisao, the quirky Yuura Kairi and the mysterious Asami Senju, Iroko competes with childhood rival Kazue Katsumi in a series of trials and ordeals that come with being a ninja! This is an Elsewhere Naruto fan fiction that focuses on several OCs of my own creation as I seek to expand the world of Naruto and try to create plausible events that would have occurred during the Blank Period and could (maybe) potentially co-exist with the canonical storyline. Disclaimer: I do not own the Naruto franchise or any part of it whatsoever, all rights go to their respective owners.This story is also on Wattpad, AO3, and Webnovel.com **New chapter once every month.
8 160 - In Serial31 Chapters
He is a Cricketer!!!!!!! ✔
Cricket is Sanskar's life at the same time Swara hates it like anything. Read to know the story of Dr. Swara Malhotra And Cricketer Sanskar MaheshwariWARNING: ERRORS AND ERRORS!
8 106 - In Serial32 Chapters
Art of Betrayal
Violence created them, and violence brought them together. After an attack on the capital of Er Rai, Arcturian commander Varia discovers a larger conspiracy, one that propels him into the company of his nemesis, Maddox. A forbidden and tenuous relationship blooms between the two, but the love they have found is threatened by the truth of Arcturus’ betrayal, a monumental secret, and an ocean of blood between them. Two men plagued by war must put aside their hostilities in order to find peace.
8 278 - In Serial11 Chapters
10 Myths about Introverts
Introverts! Unite separately at your own homes.
8 327

