《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 74

Advertisement

*ƘADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by

zaynab bawa

#Follow me on

"

Marubuciyar

*BIBIYATA AKEYI*

* Y'AR FARI*

* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 74

A baya Baba take biyeda ita har suka isa office ɗinta dake cikin babban asibitin lab-cord ɗin jikinta ta cire da ajiye sannan ta isa izuwa kujerarta ta zauna ta lanƙaye,

Da hannu tayiwa baba alamu ya zauna ya Ƙaraso ya zauna a kujerar ganin likita alkalami taciro ta fara rubutu ajikin wata katarda mai ɗauke da tambarin asibitin ajiki, saida tagama rubutun sannan ta rufe kan alkalamin ta ɗan turarda takardar gefe sannan ta sanya hannunwanta ta takare haɓanta a hankali tafara magana,

Malam Hamisu kaine Guardian na Hindatu koh? Kai mahaifinta ne? Baba ya gyada kai cikin kaguwa da son jin dalilin kirannasa,

numfashi mai nauyi taja ta fitarda sanyayyar iska a bakinta sannan tace " toh dafarko dai kasan matsalar dake damun hindatu munyi iya bakin ƙokarinmu mun ɗaurata akan magani da sanya ran za'a dace ta rabuda wannan lalura, toh amma abun baiyiwuba, ina tunanin ciwon ya dade ajikinta kafinnan yafara nuna sign, idanba hakaba a stage din da kukazo asibitinnan ayanda muka duba magani iya zai warkar dashi dukda option biyu nabaku gameda hakan idan magani baiyi ba we'll undergo sugery, unfoturnately magani baiyi aikiba yanzu bamuda wani option daya wace muyi mata aiki,

zuface tafara ketowa baba ya sanya hannun rigarsa yana sharewa yayinda zuciyarsa take bugu da sauri da sauri, likita tacigaba da fadin "Malam Hamisu muna bukatar yimata aiki a gaggauce dan kowanni lokaci ciwon kara cin jikinta yakeyi bamuda ishesshen lokaci ina tunanin 10days ne iya tsayinda zata iya kaiwa araye batareda wannan aiki ba, am afraid idan aka wuce wannan lokaci ba lallai tayi making ba, amma idan akayi aiki in sha Allahu muna saka ran zata samu lafiya zata dawo kamar ma batai ciwo ba har indai akabi komai yanda ya kamata kuma sai anyi hakuri dan hakan zai dan dauki lokaci,

Baba cikin tashin hankali yace ashirya yimata aiki nawa ake bukata naje na kawo zuwa gobe ayimata yana maganane cikin kidima,

Huuuuuuu ta fuskar da wata iska sannan tace toh ba anan gizo yake sakar ba wannan aikin ba karamin aiki bane likitocin da suke yinsama bamudasu awannan asibiti ni kaɗaice, sauran hayansu akeyi daga manya-manyan asibitoci na kasarnan,

Kowanne kuma sai anbiyashi and mutane dayawa basa iya affording aikinann haƙura sukeyi su sallama yayinda wasu suke neman taimako su samu ayi musu wannan aiki, ni matsayina na likita yakamata na sanar dakai dan bamusan yanda sa'a takeba ta iya yiwuwa kahaɗa kudaden acikin kwanakin ayi mata aiki, amma nanda 5days yakamata komai ya kammala dan booking dinsu akeyi idan yawuce wadannan kwanakin abune mai saukin gaske yazamana suna engaged so kaga aiki bazai yiwu ba,

Baba baki na rawa cikin tsantsan tashin hankali yace "kamar nawa ne kudin aikin?

Takardar da tayi rubutu dazu ta jawo gabanta ta mika masa, karɓa yayi yakai kallonsa ga takardar,

Baba kansa ya kulle sosai yakasa fahimtar shin zero nawane ajiki kuma nawa hakan yake nufi, cikin rashin fahimta ya dago ya kalleta ta gyara gilashin idonta sannan tace "aiki zaici samada 3million banda kudin magani da sauran treatment bayan aiki akalla zatayi 2years tanashan magani kuma maganin ciwonta are very expensive kai kanka you can tell da irin yanda kuke kashe kudi, duk wani expenses abarshi a 5m gaskiya zaiyi wuya ku kashe kasada haka,

Advertisement

Dushi-dushi baba yafara gani maganarta yafara jiyowa nesa-nesa sai wani kara daya biyo baya batayi auneba taganshi ya zube akasa,

Cikin hanzari takira likitoci suka bashi taimakon gaggawa ya farfado amma jikinsa babu kwari hakan yasa aka daura masa ruwa amma shi yana ward na maza,

Sawwama jin haka ba karamin tashi hankalinta yayiba kuka tayitayi, Baba dake kwance a asibiti shike lallashinta ana gayawa Mama itama tadawo babu shiri dama su Laraba mahaifiyarsa suna nan basu tafi ba,

Baba yanajin dama-dama ya mike dan baiga ta zama ba ya tara iyalansa bayani yayi musu yanda sukayi da likita laraba ta saka salati tausayin danta ya kamata Mama da Sawwama kuwa kuka sukeyi Hindatu kanwar Baba na basu baki, Baba yace "zan fita zanje inyita nema ko Allah zaisa adace, Laraba tace "ai nima banci tazama ba zanje wajan mahaifinka namasa bayani sai yatara yan uwanka kowa yakawo abunda zai kawo sai ahada, mama tarasa na cewa dan tasan duk yanda zasuyi bazasu taba iya hada kudinann ba, koda kuwa gidanda suke ciki zasu saida kudi bazai taba haduwa ba, Sawwama ta duba account dinta yafi sau goma duk wani kudinda yake ciki sun cinyeshi kaff a jinyar Hindu wanda ya saura baifi 50k ba, shima tasan nanda wasu lokaci zai kare babu irin tunanin da batayi aranta ba takasa samo mafita."

Antara yan uwan baba kowa da kowa ya hado abunda zai hado amma bai ida cika dubu dari biyar ba, tashin hankali kam suna ciki likita kuwa bata fasa zuwa dubasu ba kullum takanyi musu tuni da lokaci,

Gabaki dayansu sun fada sun fita hayyacinsu idan ka gansu duk sun zabge, abincima basamun cinsa sukeyi yanda yakamataba, nema kuma basu hakura da nema ba dan abune mawuyaci iyaye da yan uwa su hakura suna ganin nasu ya mutu sai dai dan babu yanda suka iya.

Likitan da take duba Hindatu zaune a wani kayataccen falo yasha kayan alatu kujeru set biyu ne a cikin palourn kowanne fanni akwai tv dinsa, a daya daga cikin set din kujerun take zaune TV yanatayi amma hankalinta baya kan tv din tayi matukar zurfi a tunani, ajiyar zuciya ta sauke yayinda wani abu keta yimata yawa a zuciya,

Ta rigada ta gama yanke shawarar abunda zata aikata kuma hakan shine dai-dai da tsarinta,

Tarigada ta sakawa zuciyarta abunda takeso kuma suma tasan ta zarar taje musu da muradinta basuda wata mafita face su amince mata shikenan burinta na shekara da shekeru zasu cika,

Wani kayataccen murmushi tayi sannan ta dauki wayarta bugu biyu akayi picking fara'ar fuskarta ta fadada alokacin da akayi sallama, cikin tsantsan kulawa da nuna soyayya da wanda ake magana dashi ta amsa sallamar, bayan sun gaisa daga cikin wayan naji yana fadin "wani abun farin cikinne yafaru da Sarauniya ta? Najiki cikin farin ciki, dariya tayi sannan tace "inaji ajikina matsalarmu da shekara goma sha takwas tazo karshe, cikin murna shima naji yana fadin Alhamadulillahi kada kicemin munyi samuwa kenan?

No bamuyi ba sai dai inaji ajkina munkusa cika burinmi dakuma kawarda kowacce matsala a cikin rayuwarmu, cikin daurewar kai yace "bangane ba ko zaki iyamun bayani dallah-dallah?

Girgiza kai tayi kamar wanda yake ganinta sannan tace "A'a ido da ido nakeso na sanar dakai, oh toh kice gobe na biyo jirgin sassafe kenan?

Advertisement

Murmushi tayi sannan tace toh ina zuba idanuwa zan kuma shirya tarbarka dan nayi kewarka, shima anasa wajan yace "nima nayi kewarka tafadi cikeda kaunarsa."

—————

Dady na zaune a palour ya aika Hassana takira masa mummy, ba bata lokaci mummy ta iso dan rabonda dady ya nemi ganinta tun kafin faruwar wannan lamari yana yi kamar baimasanda tana rayuwa a cikin gidanba,

Dady saida ya dan dauki lokacinsa kafin ya dubeta yace "inaso yau kuje ki dubo yarinyar nan da yaranta sannan ki basu hakurin abunda yafaru,

Mummy cikin rashin fahimta tace "wace yarinya?

Kamar bazai amsaba sai can kuma yace matar Sadam da yaransa, gaban mummy ya fadi tayay zata iya fuskantar Sawwama da iyayenta?

Dataga dai dady baida niyyar kara cewa komai akai kawai saita mike,

Da yamma ta shirya dasu Hassana zuwa gidansu Sawwama sai dai sunje basu samu kowa ba dan suna asibiti haka suka dawo ta shaidawa Dady shidai baice komaiba dan baima yarda da cewa tajeba,

Sadam kuwa anasa wajan sunanna da Abida kamar yanda suke sai dare yake dawowa gida alokacin ta rigada tayi bacci,

Yauama kamar kullum yadawo da dare a zatonsa tayi bacci amma yana shiga yaganta zaune a palour tana jiransa yadawo bata rai yayi kamar baigantaba zai wuce tayi saurin shan gabansa tureta yayi gefe tayi saurin kara shan gabansa tace "bakasan ka ajiye mata bane agidannan da zaka tafi kana barina batareda kasan halinda nake cikiba,

Kallon mamaki sadam yayi mata sannan yace "mata dama inada wata matace anan? Abida cikin gadara tace kwaarai kuwa tunda gani gabanka, tabe baki yayi sannan yace "toh ya rabata yawuce binsa abaya tayi, batareda yanuna yasan tana dakinba ya rage kayansa yashiga wanka yafito yayi shirin kwanciya cikin rashin kunya Abida tace kai nake jira hakkina nazo kabani,

Da mamaki Sadam ya kalleta sannan yace "akwai wani hakkin daya wuce abinci da abin sha dana ajiye miki,

Tabe baki tayi tace ba wannan ba idan wannan ne zan iya tanadarwa kaina kuma kasan me nake nufi, kwanciya sadam ya gyara hadeda fadin "toh bazan iyaba,

Bazaka iyaba kamar yaya?

Bangane me kake nufi ba? Bayan rashin haihuwar itama mu'amala ta auren bazaka iyata ba?

Toh wallhy baka isaba, bakani takardata da passport dina dan bazan zauna ba, ka sakeni tunda ba'aure dole."

Dariya sadam yayi yace "aiko ana aure dole tunda aurenki idanba dole da akayimin ba toh bazan aureki ba,

Cikin masifa tace "toh tunda dole akayi maka saika sakeni yanzu banaso,

Juyawa sadam yayi gefe domin yanzu babu wani abu da zai saka aransa ya bata masa rai, tunda yarabu da Sawwama sannan ya cirewa ransa damuwa toh babu wani abunda zai saka aransa ya dameshi, cikin kwanciyar hankali bacci ya daukeshi yabarta tanata surfa bala'i, karasawa tayi ta tabashi taga ashema mahaukaciya ya maidata danshi yayi baccinsa,

Dakin tayita dube-dube gabaki daya saida da hargitsa tana neman wayarta ko passport dinta amma bataga komaiba hakan yasa kawai tafice cikeda haushi da bakin ciki."

______

Karfe goma na safe jirginsa ya sauka a Nigeria ita da kanta taje daukoshi, tun amota yake tambayarta abunda takeso ta fada masa tayi masa alamu da driver dake tukasu a mota, shiru yayi har suka isa gida bayan yayi wanka ƴan aiki suka shirya musu breakfast sunaci cikeda kulawa take tarairayarsa bayan sun gama yace "yanzu kam saiki fadamin ina sauraronki,

Gyara zama tayi ta gama zayyano masa abunda ta yake faruwa da kuma shirinda da shawarar data gama yankewa,

Shiru yayi ya nisa na wani lokaci Sannan yace "banki takiba amma kina ganin hakan zai yiwu bazai haifar da wata matsala ba?

Murmusawa tayi sannan tace daga wajan Hajiya kasan baza'a samu matsala ba abunda take burine na tsawon lokaci,

Girgiza kai yayi yace "bahaka nake nufi ba ita yarinyar nake nufi, murmushi tayi tace ni nasan mai nagani shiyasa na kawo wannan dabarar, ina kallon mata dayawa meyasa bantaba yardaba sai wannan?

Itafa yarinyar danya shadaff ce karamar yarinyace bana tunanin zamu samu matsala daga gareta harma da iyayenta saboda yanzu basuda wani hanya data wuce wannan kuma karka manta ai ba tawata mummunar hanya bace,

Shafo fuskarta yayi cikeda soyayya yace "yanda kikeso hakan za'ayi har indai hakan zai sanyaki farin ciki toh ashirye nake da baki goyan baya dari bisa dari amma inaso kiyi tunani dakyau sosai banason wannan abun ya zame miki matsala ko wani bacin rai,

Bata rai tay tace "baka yarda da kanka ba kenan? Shafo fuskarta yayi sannan yace idan nine bakida matsala kuma kema kinsanda hakan, irin sonda nake miki bazaisa na iya zama da wat,,,,,, shsssshhh ta sanya hannu ta rufe masa baki tace "na yarda dakai

basai kayi dogon bayani ba, yanzu gobe zan shiga Asibiti duk yanda mukayi saina dawo na sanar dakai amma inada yakini baza'a samu matsala ba."

Washe gari ya cika kwana biyar kenan Baba yayi fafuguka amma akan dubu dari biyar kadan aka daura,

Baba ya kawo kudin asibiti sun zauna jigum-jigum anan mama takawo shawarar su saida gidansu su koma gidan Baba Sa'adu da zama ko su kama haya, baba yace koda mun saida gidanmu bazai kai zallan kudin aikin bama bare ace na magani da sauran treatment,

Mikawa Sawwama kudin Baba yayi yace ki ajiye barina fita naga abunda Allah zaiyi,

Karba Sawwama tayi cikeda damuwa, suna zaune wata nurse tashigo tace Sawwama taje office na Dr tana nemanta,

Cikin sanyin jiki Sawwama ta tashi ta nufi office na likitan,

Da sallama ta isa Dr ta amsa bayan ta sameta zauna a kujerarta ta likita, idonta ne ya sauka akan Sunan dake makale gaban teburin likitan DR SAJIDA SALMAN cardiologist, a zuciyarta ta nanata sunan,

Dr ta amsa sallamar sannan tataso fuskarta cikeda fara'a, karasawa tayi sopa dake katoton office din ta zauna,

Da hannu tayiwa Sawwama alamu da ta zauna gefenta karaswowa tayi ta zauna sannan ta gaidata,

ta amsa sannan tace ina twins?

Sawwama kanta yana kasa tace suna wajan mama,

Gyara zama Dr sajida tayi sannan tace "ko kuna sane da cewa yauce ranar karshe da zamu iya karban kudin aiki?."

✔️ote

Comment

Follow

Share plss

To be continued

Zaynab Alabura

💞

    people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click