《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 73

Advertisement

*ƘADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by

zaynab bawa

#Follow me on

"

Marubuciyar

*BIBIYATA AKEYI*

* Y'AR FARI*

* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 73

Izuwa wannan lokaci Sawwama ta kwantar da hankalinta sai dai baza'ace babu wani abunda take damunta gabaki ɗaya ba, Mama da Baba suna iya kacin ƙoƙarinsu wajan ganin basu barta da wata damuwa ba duk wash buƙatunta suna ƙoƙarin biya mata, daɗin ɗaɗawa abunda ya ƙara ɗauke mata hankali shine ciwon Hindatu domin wata damuwar ta kori wata,

Kullum yawon asibiti sukeyi amma da zarar ansamu canji na lokaci ɗaya jiki zai sake dawowa sabo,

Ga cin kuɗi da jinyar take musu taimakonsu ɗaya Kuɗin dake account na Sawwama wanda Sadam ya tura mata dashi suke amfani, hakanma yanzu abubda yarage baida wani yawa."

Sadam yanacan jiki anata ganin canji yayinda dady ya daɗe da dawowa yabarsu acan sunata jinya, ya farfaɗo hhat yana magana kuma sam bai nunawa mummy komai ce domin a cewarsa iya wannan abunda yafaru dashi ma darasine ne daga wajan ubangi, Sawwama kuma ƙoƙarin yakiceta yakeyi da aransa dan bazai iya dawo da its cikin rayuwarsa yanzu a wannan hali dayake ciki ba, hhat indai yayi mata haka baiyu mata adalci ba,

Bayan haka bayaji ajikinsa mummy tayi shuryiwar da zata barsu su zauna lafiya, duk wani abunda yafaru yanaji laifinsa ne daya kasa daina sonta alokacin da mummy ta furta batason aurensa da ita, da yayi haƙuri da ita wancan lokacin to da bai jefata cikin damuwa ba toh amma yaya zaiyi? Bai isa jaa da abunda Allah ya rigada ya ƙaddara ba, ya ɗauki ƙaddararsa ya rumguneta Hannu bibbiyu kuma zaiyi koƙarin yin rayuwa batareda Sawwama ba awannan lokaci, bazai iya sake jefata cikin wani halin ba,

Zai nesanta kansa da its gwargwadon yanda zai iya hhat yaga yanda Allah zaiyi dasu,

Watansu biyar yasamu lafiya ya warke sai dai likitoci sun shaida masa abune mawuyaci ya sake haihuwa, amma basusan wani hikima na ubangiji ko yaya zaiyi dashi man gaba ba, bazasu ce masa kwata-kwata bazai haihu ba dan ni'imomi da ubangiji da yawa take,

Murmushi Sadam yayi a fili yafurta idan wannan ne ni banida damuwa dan yara biyu sun isheni rayuwa fatana kawai Allah ya rayaminsu."

Dady ta kansa yaje tafowa dasu likita yayi masa bayanin halinda ake ciki Dady yashiga tashin hankali matuƙa dagaske,

Bayan sunbar asibitin izuwa masauƙinsu yanda mummy da Abida ke zaune dady ya tarasu gabaki ɗaya ya dubi Sadam cikin tausayawa yace" cikin hikima da rahma ta ubangiji yau gashi Sadam ya miƙe kamar baiyi jinya ba, amma sai dai abunda likita ya sanar dani ya matuƙar ɗaga mini hankalina,

Ya dubi mummy yace"duk wani abunda yafaru da yaronnan ke kika jawo, duk faɗin duniya babu wanda ya takura miki agidan aurenki amma ke kin takurawa ɗanki, sunkuyarda kai mummy tayi dady yacigaba da faɗin yanason matarsa amma kin hanashi zaman lafiya da its gashi yanzu halinda kika jefashi, likita ya shaidamin abune mawuyaci ya ƙara haihuwa, Salati mummy ta sanya sannan tafashe da kuka dady zaro ido Abida tayi afili ta furta bazai sakw haihuwa ba?

Dady yace kwarai kuwa kuma kune sila keda uwarsa, nayi danasanin barinta danayi ta tilasta masa akan aurenki, aurenki bai zame mana alkahiri ba Aurenki bai ƙari ɗana da komaiba keba mace bace ta rufin asiri dalilinku ku biyunnan kun tarwatsa rayuwar ɗana kuma ban yafe muku ba, sakayyar abunda kukayi masa tananan biyowa baya banajin zan iya zama da ke ya nuna mummy sannan ya dubi Sadam yace "kai idan zaka iya zamada matarka ban hanaka ba, kuma daga yanzu duk wani hukunci daya shafi yarana babuke aciki zamu yankeshi ne daga ni sai su,

Advertisement

Bazan hanasu zuwa yanda kike ba amma bazasuyi rayuwa tare dake ba, domin son zuciyarki da son duniya zaisa ki jefasu cikin wani hali, dady yadubi Sadam yace Sadam ka yafemin nima nasan danawa laifin acikin abunda yafaru domin bana dakatar da mahaifiyarka ni atunanina bazata sanyaka aikata abunda zai cutar dakai ba, ashe ba haka bane hasashena baizo dai-dai ba,

Sannan kuma kaje kadawo da matarka in sha Allahu bazata sake takura maka ba,

Sai alokacin Sadam yayi magana yace "Dady kayi hakuri dan Allah karkace zaka rabu da mummy kamin wannan alfarmar, zaka iya mata wani hukunci na daban amma karla rabu da its kodan DARAJAR ƳAƳANTA, nasan mummy tayi ba dai-dai ba amma hakan bazaisa na yanketa matsayinta na uwa ba, matsayinta nanan so bazanso wani abun ya cutar da itaba, zanyi matuƙar jin baby daɗi idan kuka rabu ta dalilin abunda yafaru,

Sannan zancen Sawwama kuma Dady bazan maidata ba tacigaba da zamanta Allah yamata zaɓin daya fini alkahiri zanyi hakanne bawai don bana sonta ba saidan soyayyar danake mata zaisa na nisanta kaina da ita banason tasake iron rayuwar da tayi abaya, .kuma dady ni yanzu ba kamar da name ba zama da ita zai mana na cutar da it bazan iya jure ganinta ta cutu ba,

Zancen Haihuwa kuwa koda ace bantaɓa haihuwa ba wallhy bazan damuba na fawwalawa Allah komai shine majiɓanci duk wash lamurana, bare inada yara hhat guda biyu toh Alhamdulillahi nagode Allah da wannan baiwar,

Abida kuma bazan saketa ba can zauna da ita ahaka ko yaya zatayi kuma bazan taɓa sakinta ba dalilinta wannan abun ya faru So tazauna ta shuke abunda ta girba,

Kawo wannan lokaci kuka sosai Mummy keyi tama kasa buɗan baki ta nemi yafiya wajan ɗaya daga jikinsu, Allah idan yasoka da rahma ne zai baka ikon neman yafiyar laifinda ka aikata,

Ga mamakinsu kuka sosai Abida tasaka tana faɗin wallhy ni bazan zauna dakai ba haka kawai dannice bakaso saika cutar dani, ko cemaka akayi ni banason na haihune wallhy saika sakeni,

Dady ya dubeshi yace Sadam bazan tursasa makaba amma gani nake kaman rabuwa da itan shi yafi dan bazata yarda ta zauna ba, Ka sawwaƙe mata Allah zai baka wata wacce zata zauna dakai tsakani da Allah."

Ɗage kafaɗa Sadam yayi yace toh karta zauna mana dady! Ni narigada na yanke shawara tatafi bangon duniya nima bason zama da itan nakeyi ba kawai dai igiyar aurenne bazan sakeba,

Mummy jin maganganun Abida yas ata tsaya da kukan da dakeyi tace "Sadam ɗinne kikr cewa bazaki zauna dashiba dan lalura ta sameshi?, Abida tace kwarai da gaske bazan zauna da maras haihuwa ba,

Ƴar dariya Sadam yayi yace aini inada zuri'a ko yau na mutu nabar baya amma kefa? Ke koda ban bar kowa ba nasan na shuƙa abun kirki wanda zaiyita bibiyata, Rabuwa dake kuma bazanyiba zakiyita haukarki ki dawo ki daina,

Yanzu haka ni da kika ganni bama zanbar nan ƙasar ba haka zaku koma bandani,

Idan kinji zaki bisu saiki bisu amna igiyar aurena guda biyu na kanki,

Jin abunda Abida tafaɗi yasaka zuciyar Mummy ƙara karyewa tace lallai Abida ke butulu ce duk wannan abun danayi nayishi ne danke, amma yau kika rufr ido ni kika watsamin ƙasa anawa, tashi Abida tayi tabar wajan dan bazata iya mata rashin kunya ba bakuma zata iya tsayuwa taji kalamanda zata faɗa ba,

Advertisement

Murmushi Sadam yayi yace "mummy kingani koh?.na tabbata da Sawwama ce wani abun ya sameni bata dalilinta bama bazata taɓa iya guduna ba zata tsaya mu fuskanci koda wani iron ƙalubalene tare,

Mummy cikin muryar kuka tace "toh kadawo da ita ku zauna ta kula dakai, murmushi Sadam yayi yace "bazan iyaba,

Tsaki dady yaja yace "ashe bakida kunya? Dama aakwai rabarda zaki buƙaci taimakon abunda kike wulaƙantawa? naɗauka ƴar gidan talakawa batada wani abunda zata iya miki,

Nanma kuka kawai mummy tasaka,

Abida tana shiga ɗaki takira mahaifinta ta shaida masa abunda take faruwa, bala'i yahauyi yana faɗin ai kuwa bazata saɓuba nima inaso naga jikokina ko yaso ko yaƙi dolensa ya sakarmun ke."

Washe gari su dady da mummy suka koma gida akabar zallan Sadam da Abida,

Saida tayi kwana uku bata sanyashi a idanuwanta ba balle tayi masa rashin kirki tasa ya saketa."

Mahaifinta yanajin labarin dawowar su Dady ya kira mummy tazo yanason magana da its,

Mummy wacce ko kallon arziki bata samu wajan dady taje a ɗarare ta sanar dashi nema yayanta take mata, dady baiko juya ya kalleta ba yace "tace masa shi yazo ya sameshi,

Mummy ta sanar dashu yanda sukayi da dady, hhat gida yazo ya samu dady yace yanason takardar Abida,

Cikin rashin damuwa Dady yace aini aurenta ba akaina yakeba Sadam zaka samu da wannan maganar sannan kuma banajin zai iya saketa saboda duk halinda yashiga dalilinka ne da its yarinyar dakuma uwarsa,

Kai matsayinka na babba ka biyewa mata kuka aikata ɓarna ko nice son zuciya da nuna son naka afili, itakuma uwarsa dake shashasha ce kia ka nuna son ƴarka itakuma tabada nata ɗan toni a wajena ba haka abun yakeba, ina son ɗana sosai kuma zan iya komai dan tsaya masa, banajin yanda nakesonsa kanason ƴarka, So yanzu kowa zai nuna iron soyayayyar dayake yiwa nasa, awannan lokaci kome Sadam ya yanke ina bayansa kuma zan goya masa baya ɗari bisa ɗari,

Dady ya ɗaura da faɗin kana kallonsu suka aikata abunda suka aikata amma baka hanasu ba, gashi yanzu Abun yadawo man ƴarka, shiyasa akace kawa zai gina ramin mugunta ya gina dai-dai kansa."

Kaca-kaca sukayi da mahaifin Abida kafin yabar gidan, Mummy kuwa tsananin mamaki ya hanata cewa komai, wato ita suka maida doluwa tayiwa ɗanta rashin kirki amma gashi su afili suke nuna son nasu yarinyar,

yana fita yakira abida Yace ta tattaro tadawo zai turo mata kuɗin jirgi,

Abunda bata saniba shne Sadam ya ɗauke passport ɗinta kamar wanda dama yasan da faruwar hakaan"

Bayan dady ya shaida masa yanda sukayi da mahaifinta nanma yabi ya ƙwace wayarta iyakacin abunda ya barmata shine abunci,

Batayi gigin fitaba saboda tasan ƙasar idan ta kuskura ya fita ba passport aka kamata toh ba ƙaramin tashin hankali bane tattare da hakan."

Sai dare liƙis Sadam yake dawowa gida yana zuwa sai kulle ƙofar ɗakinsa yayi wanka ya kwanta bacci baya taɓa neman yanda Abida take."

______

Bayan sungama karin kumallo mama tadubi Baba tace baban hafsa naga baka shiryawa fita kasuwa ba, ko bazaka fita dawuri bane? Baba yace "yau gabaki ɗaya banajin can fita kasuwa jikin yarinyar man jiya da dare yabani tsoro gara mamana ta shirya mukaita Asibiti ke seki zauna agida duk yanda ake ciki ma buga miki ways, Mama tace "da katafi abunka kawai naga jikin da dama yanzu hakama bacvi takeyi, idan yaso zuwa jimawa saimu kaita asibitin,

Baba yace A'a jikin nata abun ba'a cewa komai ko naje kasuwa hankalina bazai ƙwanta ba gara nakaita da kaina,

Kicewa mamana ta shirya sai tabar yaran wajanki muje,

Mama tace toh tatafi ta faɗawa Sawwama akan tashirya sai suwuce asibiti,

Cikin ƙanƙanin lokaci tayi wanka ta shirya suka tafi,

Suna zuwa aka basu gado taimakon gaggawa aka fara yimata kafin likitan da take gani tazo,

Ƙwanansu uku a asibiti sannan Baba ya sanarwa ƴan uwansa da yawansu daga ciki zunzo dubata, mama da Sawwama ke karɓe-karɓe idan wannan tahuta sai wannan tazo,

Mama ce ta kwana a wajanta sai Sawwama tazo ta karɓeta Mahaifiyar Baba laraba ce tacewa baba yazo yakaisu asibitin itada Ikilima ƙaramar ƙanwarsu da Hindatu dan basusan wajan da yarinyar takeba,

Baba yazo yayi musu jagora har izuwa ɗakin sun samu likita na dubata hakan yasa suka zauna a gadon dake gefen na Hindatu,

Sawwama ta gaidasu suka amsa Baba cikin kulawa yace "sannu Sannu mamana Allah yasaka miki da.mafificin alkahiri, ko zaki koma gida tunda gamunan saimu ƙarɓeki?

Girgiza kai Sawwama tayi tace A'a baba ban daɗe dazuwa ba mama takoma gida,

Laraba tace toh madallah tare kuke jinyar kennan? Baba yace eh karɓe-karɓe suke da mahaifiyarta,

Laraba tace ita tunda ƴar uwarta takama jinya tadawo gida kenan? Dan kullum akan cemin anganta agida,

Shiru baba yayi dan duk cikin danginsa bai faɗa musu mutuwar auren Sawwama ba,

Jiki a sanyaye yace auren nata ne ya mutu shiyasa take gida,

Taɓe baki laraba tayi tace nasa arina ai ƙwarya tabi ƙwarya ina ƴarka in auren wannan mutanen?

Kaƙi jinika da zai rufa maka asiri ka zaɓesu gashi sun kwance maka zani a kasuwa, kuma auren ya mutu kaƙi faɗa mana mu maƙiyanka koh?

Hindatu ƙanwar Baba tace ko menene abun yayatawa a saki mama?

Dan lay kibar wannan zancen kibarshi yajida abunda yake damunsa yanzu,

Sawwama wacce kanta take ƙasa ko ɗagowa takasa yi,

Likitan dake duba hindatu wanda dama gun ɗazu su take sauraro, taso ta fahinci cewa Sawwama batada aure ganin yanda take zirga-zirga a asibiti bata sake gaskatawa ba sai yanzu,

cire abun kunneta tayi tadubesu face dan Allah ko zaku iyayin wane? Asibiti ba wajan irin wannan magamganun bane kubar maras lafiya taji da abunda yake damunta, dukansu suka miƙe laraba harna tuntuɓe zasu fice Dr tace Bandake Sawwama ki zauna ki kulata ita, kaikuma ka biyoni ta nuna baba."

Dukansu suka fice a ɗakin Baba yabi bayanta Sawwama kuma tazauna kusada Hindatu."

✔️ote

Comment

Follow

Share plss

To be continued

Zaynab Alabura

💞

    people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click