《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 72
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 72
Taɓe baki Abida tayi haɗeda sakin murmushi sannan ta raɓa ta gefenta tawuve, saida ta isa man kujera ta zauna sannan tadubi Sawwama wacce itama tajuyo itan take kallo,
Tsawon lokaci suna ahaka Sawwama afusace tace idan bbu abund ya kawoki zaki iya fitarmin a gida bana gayyar rashin hankali da rashin imani,
Abida harta buɗe baki zatayi zaki sai kuma tayi shiru, dariya ta sanya kamar wata mahaukaciya tace Au gidanki? Wai gidanki kikace? Labari bai iso gareki ba kenan? Ai yanzu ni dake matsayinmu ba ɗaya ba kuma nan ba gidanki bane,
Sawwama cikin rashin fahimtar abunda take nufi tace koma menene naji amma tashi ki ficee,
Na ɗauka kinyi danasanin abunda kika aikata ne yasa kima biyo sawu ki bada haƙuri ashe ba haka bane rashin hankali ya kawoki, toh bazan ɗauki rashin hankalinki ba dan haka kificemin agida gun dawuri,
Abida tace sai dai ke ki five amma baniba dan yanzu nice mallakin gidannan dakuma wancan gidan danni kaɗaice matar Sadam,
Sawwama tace"shiyasa nace kin fara hauka dan haka kifita kibani wuri,
"Au wai baki yarda ba? Cewar Abida hannu tasaka ajakarta taciro wata takarda ta mƙa mata, ƙin karɓa tayi Abida ta ɗage kafata tace "baki iya karatun bane I guess so barina karanta miki,
Ni Sadam na saki matata Sawwama saki ɗaya
batareda ta aikatamin wani laifi ba sai dan bin umarnin da zai zame mana maslaha gabaki ɗaya,
Sawwama na ƙarasa jin haka ta isa wajan da sauri ta fauce takardan kuma abunda abida ta karanta shine arubuce ajiki kuma tabbas wannan rubutun Sadam ne,
Cikin rashin Gaskata abunda tagani ta juya ga Abida da kallon tuhuma, Abida tace "mijinki zaki kira ki tabbatar danni nagama aikina,
Wurga mata Sawwama tayi face shirinki bazai taɓa aiki akainaba kuma nasan Sadam bazai taɓa sakina ba har abada dan haka kitashi ki fita,
Miƙewa Abida tayi ta shure takardar gefe tace "ki ajiyeta ke zata yiwa amfani sannan please idan antashi tafiya kar ayi mana sata dan nasan kayan Mijina ne ya saya
ficewa tayi bayan gama faɗin hakab tabar Sawwama jiki rawa,
Tana fita Sawwama ta ɗauki wayarta tafara kiran Sadam amma bai shigaba takira yafi say ashirin duk baya shiga, zama tayi tana kuka
Abunda yafaru ne yasa Mummy ta saka ya saketa kenan ita akaiwa laifi kuma ita za'a hukunta?
Adakeka ahanaka kuka kennn,
Har dare Sawwama takai tana kiran layinsa amma bai shigaba
Washe gari taga zaman bazai kaita ba ta ɗauki yaranta da takardar tawuce gida,
Bayan sun gaisa da mama take cewa wanu abunne yafaru naganki duk kin koɗe, kuka Sawwama tasaka tabawa mama labarin abunda yafaru mama ta zauna jigum takasa cewa komai,
A lokacin takira Baba yadawo daga kasuwa suka shaida masa abunda take faruwa Baba yakarɓi takardar ya karanta sannan yace nagodewa Allah daya kasance ba laifin komai kikayi masa ba, Allah ya zaɓarda mafi alkhairi ki kwantar da hankalinki kishiga ɗaki kihuta,
sai kuje ki ɗebo kayan sakawanki mu zuba ido muga hukuncin ubangiji."
Sati guda kenan da faruwar wannna lamari amma sam wayar sadam bata shiga,
Mummy har izuwa lokacin tana gidansu, lokaci-lokaci Sawwama tana neman wayan Sadam amma baya shiga,
Advertisement
Har yanzu tana cikin damuwa dan gani take idan baby Sadam bazata iya rayuwa ba,
Wani lokacin kuka zata zauna tayita yi,
Mama takan rarrasheta wani lokacin kuma idan haushi ya cikata saita barta tayita kukan,
Ranar ma haka tashirya zata fita kai Hindu Asibiti dake jikinnata har yanzu tashiga sanar da ita akan tatafi, ta sameta tanata rausa kuka, mama ta tsaya akanta tana faɗin Hafsa haka zamuyi dake?
Kin takura kanki kin hana kanki sukunu akan namiji idam babushi bazakiyi rayuwa ba kenan?
Ke bazaki ɗauki Ƙaddara ki fawwalawa Allah komai ba? Shin wannan kukan zai sama miki mafita ne?
Toh barina faɗa miki ke yanzu uwa ce yakamata ki zama jajirtacciya sakin sure ba akanki aka fara ba, idan da rabo atsakani zaku komawa aurenku, amma kukanku bai is aya canja rubutaccen all'amari ba, ki sawa kanki salama ki tsaya ki kulada yaranki su kansu sun rame, Duk kinbi kin fita hayyacinki,
Sharae hawaye Sawwama tayi tax "mama ba haka bane ni rashin samunsa da ake a ways ne abun take damuna kar wani abunne ya sameshi,
Mama tace ki kwantar da hankalinki hafsa in sha Allah baby abunda ya sameshi shima yana cikin zullumin rabuwar aurenku ne shiyasa yayi nesa daku,
Kibashi lokaci in sha Allahu bbu wani abunda yafaru dashi,
Murmushin yaƙe Sawwama tayi sannan tace fita zakiyi yanzu? Mama ta amsa da faɗin Yauce ranar komawarmu asibiti da Hindatu yanzu hakama tafiya zamuyi,
Miƙewa Sawwama tayi tace "barina shirya muje tare, mama tace "ke ki zauna bazamu bar gidan babu kowa ba,
Sawwama ta girgiza kai face A'a mama mutafi kawai dannima zaman nawa ni kaɗai bazanji daɗinsa ba,
Mama tace "toh kimtsa kifito karmuyi latti mikimin wannan yaron na goyeshi saiki goyi ƴar uwarsa, mika mata hamdan tayi itakuma ta shirya ta goyi hameeda suka nufi asibitin,
Wash gwaje-gwaje aka sake rubuta musu sannan aka basu ranarda zasu kawo sakamako,
Sawwama duk ita tayita jigilar biyan kuɗi da sauransu saida sukayi gwaje-gwajen sannan suka koma gida mama nata mita tana faɗin "yanzu dai zuwa asibiti yazama wahala sai gwaje-gwaje kawai suke rubutawa yarinya tanata jin jiki amma bazasu bata wani abun da zata dan samu dama-dama ba, wannan ai idan yazo da ƙarar kwana sai arasa rayi,murmusawa Sawwama tayi tace "ai mama idan ba'ayi gwaje-gwajenba ba'asan akan wani irin magani za'a ɗaurata ba, sai sunyi kafin su game abunda take damunta, taɓe baki mama tayi tace uhmm,
Sun dawo gida agajiye liƙis bayan sun huta Sawwama ta ɗaura musu abinci,
Bayan tagama tacigaba da kiran wayar Sadam amma taƙi shiga haƙura tayi ta kira ta ajiye wayar zuciyarta cikeda damuwa fall,
Tausayin kanta takeji tana tunanun shin zata iya samun mutum irin Sadam mai sonta da tausayunta?
Hindatu sunata komawa Asibitu an gano wani ciwone a zuciyarta sun daurata akan magani da saka ran ciwon zai baje idan kuma hakan bata faruba sai dai aiki,
Sati biyu da fara shan maganunta anga sauyi sosai."
Tun suna ganin lamarin kamar wasa yanzu abun ya wuce tunaninsu,
Suna jira Sadam zai kira ways yaune? gobene?
Shiru saida akayi sati uku,
Mummy mahaifanta jin takaicin abubda t aaikata ya sanya ko neman dady basuyiba,
Yanzu haka zaune take da wayarta a hannu ta rafka uban tagumi, wata dattijuwar mata tafito tana ta tsaya akan mummy dake zaune a babban fall da rafka tagumi,
Advertisement
gyaran murya tayi mummy ta kalleta, murmushi tayi irinna manya tace ai baki fara damuwa ba da saura,
Kuka mummy ta sake tace ni momma da wane zanji
da ɓatan Sadam ko dadynsu da yaƙi saurarena kema wajanki danake tunanin zanji sanyi kullum magana kike yaɓamin,
Dariya ƴar dattijuwar tayi tazauna idonta naga Tv kamar bazata tanka ba sai kuma face "aishi ba yaro bane zai dawo kawai ya raba kansa da fitinarki ne, kin tabka babban kuskure kina ƙoƙarin gyaran auren wata ke kina shirin tubuƙe naki, gashi yaronki ma ya nesanta kansa dake, idan kina ganin kin ruguza rayuwar aurensa ko naki kika ruguza,
Banda rashin basira ke kina ƙuntatawa ɗanki kina farantawa ran wasu gashi kina gani dai yayanki tunda kikazo gida ko say ɗaya bai tambayi daliliba baima damu ya saniba tunda shi aurrn ƴarsa ya gyaru na kowa ma ya ɓaci,
Bansan a'ina kika ɗauko wannan baƙin halin naki ba ni ai kina kallo nida matan ƴaƴana kamar ni na haifesu,
Amma ke kin fitina yara gabaki ɗaya kin hanasu zaman lafiya shiyasa nace miki ai bakiga komai ba sakayya tananan agaba,
Muƙus mummy tayi tanajin mahaifiyarta nata yimata faɗa tasan ko menene ma yafaru toh ita ta jawowa kanta."
A halin yanzu duk wani wanda yasan da ɓacewar Sadam yana cikin matsananciyar tashin hankali domin kuwa wayarsa Sam bata shiga dady ya saka har garinda yaje an nema ba'a sameshi ba,
duk abokanansa an kirasu bbu wanda yasan yan yake, har najeeb duk kusancinsu amma bai sanar dashi yanda yake ba,
abun da yaƙici yaƙi cinyewa dady da kansa ya tafi garin nemansa a ganin babu yanda ba'a bincika ba ba'a sameshi ba yasa dady yace ayi tracing na layin man ma akashe iyakacin wajanda aka kashe layin ya sanar dashi daff da za'a shigo gari,
Police dady yasa a maganar suka nemansa har yanda layin yadaina aiki sunje, wajanma ba wajan mutane bane jejine daff da za'a shiga gari,
daga ƙarshe Asibitoci suka shiga dubawa cikin ikon Allah kuwa sami Sadam yayi accident tsawan sati uku bai farfaɗo ba sannan kuma babu wanda yazo nemansa yasa suka barashi basu wani damu dayi masa magani ba,
Dady har kuka saida yayi ganin halinda Sadam yake ciki yana can wani ɗaki kamar maras gata ɗakin hhat wani wari take da dukkan alamu marassa lafiyan dasuke wannan ɗaki ba wani cikekken kulawa suke samu daga likitocin ba,
Dady yayi faɗa kamar me gabaki ɗaya likitocin suka taru haƙuri kawai suke bashi sanin cewar idan magana tayi nisa su kansu zasu samu matsala saboda sakacin da sukayi da maras lafiya,
A ranar ya nema transfer suka koma gida kai tsaye babban asibitin dake garin aka wuce dashi,
likitoci sun taru sunyi iya bakin ƙoƙarinsu amma basu samu ya farfaɗo ba,
Sun alaƙanta hakan da rashin kula daya samu alokacin daya samu hatsarin, bai samu immediate treatment ba,
Satinsu biyu a asubiti amma baby wani canjin kirki mummy tazo tayi kuka harta gaji tayi danasanin abunda ta aikata,
Ba'a wani ganin canji gameda lafiyarsa hakan yasa likita yabawa dady shawara akan yafita dashi ƙasar waje domin ayi masa magani,
Kullum mummy a asibiti take wuni wajan Sadam amma dady ko waiwayen yanda take bayayi, yace shi bazai hanata jinyar ɗanta ba, zai barta tazo tayi jinyarsa kodan tayi hankali nan gaba."
Abida ma tashiga tashin hankali ba ƙarami ba ganin halinda suka jefa Sadam, kullum zuwa asibitin kusan koda yaushe tana tare da Sadam ko fita batayi sai dare take komawa tabar mummy."
________
Yanzu damuwar dake damun Sawwama taɗan ragu dan har tana fita suyi hira da mama kasancewar Hindatu babu lafiya koda yaushe tana gefrnta,
Kamar kullum yauma suna zaune da mama cikin gida sai sukaji Sallamar Halima,
Tana ganin Sawwama ta ƙaraso da sauri ta zauna tana faɗin yaya Sawwama kema ashe kina hanya naji daɗin ganinki, inata so naje gidanki amma a cikin satinnan zan zoni, murmusawa kawai Sawwama tayi,
Mmaa tace Halima dududu yaushe akayi auren da har zaki fara yawo? Har yaushe akayi bikin yabarki kika fara fitowa, Halima face wallhy Mama nayi ƙoƙari kusan wata biyu fa kennan ban ganku ba,
Mama wata uku akeyi kafin a fara fita a zamanin yanzu kenan ma zamanin iyayanmu kuwa sai sun shekara kafin suje gida, Dariya dukansu suka saka sannan ta gaida mama da Sawwama, ganin Hindatu a kwamce yasa ya tambayi abunda ya sameta, mama ta faɗa mata kuka Halima tayitayi wai ba'a sanarda itaba, haka dataji mutuwar auren Sawwama ma saida tayi kuka, tace Yaya Sawwama zamanku keda Yaya sadam gwanin sha'awa yana sonki sosai, amma wannan shu'umar matar saida ta rabaku in sha Allah baku rabuba sai sun koma, mama tace kull Halima karna sake ji uwartasa ce shu'uma, Halima tace toh mama fisabillahi me yaya Sawwama tayi har haka da zafi?
Rabuda its zata gani a ƙwaryarta amma banaso nasakeji kin aibatata, Kubarta da halinta amma uwa ce a girmama ta kota wannan dalilin, Ko karamci irinna Sadam kaɗai ya isa ya wanke laifin mahaifiyarsa, duk wani abunda ta aikata kanta ta cuta abarta da fitowar rana da faɗuwarta zataga sakayya akanta in Sha Allah."
Sai dare sannan Halima tatafi."
maganin Hindatu yaƙare hakan yasa Sawwama ta shirya domin rakata ganin likita,
Likitan da suka saba gani suka samu, macece da bazata wuce shekaru 36 ba tanada kirki sosai,
Bayan sun gama ganin likita ta rubuta musu magani acikin asibitin suka says sannan suka fito,
Suna daff da fita daga asibitin taga su mummy suna ƙoƙarin shigowa, saurin juyawa gefe tayi dan bataso su ganta, aranta idan tace batajin zafin mumny tayi karya,
Tana ganin motar tawuce tajuya suka koma gida."
Da mummy dady da abida aka tafi can ƙasar amma dady zai dawo bayan yaga yanda treatment ɗin zai wakana na wani lokaci."
Yanzu jikin Hundatu yana ɗan tashi lokaci-lokaci duk da cewar tana ƙarban magani,
Yanzu harta kaiga ana basu gado a asibiti a sallamesu idan jikin yatashi a sake dawo da its,
Likitan na nuna musu kulawa sosai barinma ga Sawwama da yaranta,
Tanason yara sosai koda yaushe tashiga asibitin saita ɗaukesu."
Wani lokacinma offices take wucewa dasu."
watansu Sawwama Huɗu da rabuwa amma hhat yanzu mikin son Sadam yananan acikin zuciyarta
Kuma har yanzu wayarsa bata shiga, dady akai-akai take mata aika amma ba'a taɓa sanarda its halinda sadam yake ciki ba."
Twins kuma sun cika shekara dan shirin yayesu ma takeyi dake bawani shan nonon sukeyi ba, abinci kuwa kowani iri ci sukeyi."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial437 Chapters
Magical Academy: Rise Of The Supreme Magic Craftsman
[ The book is reaching its end so the author started a new novel that you may want to check out "Reclaiming the Demon's Curse" is the title. Thank you! -xltnz ]
8 1157 - In Serial7 Chapters
Faery Knight - A Mirai Suenaga Adventure
On the colonized world of Pantheon, where humanity is lorded over by the enigmatic Archons, Mirai Suenaga survives the vicious invasion conducted by the alien Genjitsu, but the price she and humanity pay is high.Ten years later, as a teenage girl attending her second year of high-school in the city-state of Pan Pacifica, Mirai is a member of the Crimson Force Team, training to qualify as a fully fledged Faery Knight. Taking part in the Summer Tournament, where the various teams of the academy compete for dominance using their Battle Faeries, Mirai faces obstacles and adversaries as she aims for victory. But she will face her greatest challenge outside of the battle arena, when the Genjitsu choose to invade Pantheon yet again, and crush humanity once and for all.A sci-fi action adventure featuring the creation of Danny Choo, Mirai Suenaga.
8 183 - In Serial13 Chapters
Aether Online
This is the story of Katherine Veldorbell, Daughter of the richest and most successful woman in human history. Without any real relationship with her mother, she sets out on making a name for herself in her mother's creation: Aether Online. A game where anything is possible, Where the less than fortunate in life can succeed. Loan Shark? Mass Murderer? Prostitute? It's all yours to enjoy. What to Expect: A bomb ass story with interesting devices, cool enemies and a nice cast of supporting characters.
8 179 - In Serial9 Chapters
Gray Hour: The Cursed Coin
"Would you fall in love with your murderer?" Diana wakes up and finds that instead of only five minutes to live, she has now twenty-four hours. She needs to find the reason and ‘cure’ for her endless cycle of deaths. But, when there are infinite numbers of possibilities, suspects, and a boyfriend – or should she say a fiancé? – who is the reason for her deaths ninety-percent of the times, it becomes complicated.
8 158 - In Serial10 Chapters
Life After The End Of Times
What would you do after waking up in a world of magic and monsters with no memory?
8.18 112 - In Serial11 Chapters
The Forest's Guardian
Follow Iago, a man with a past unknown even to himself, who has dedicated his life to defending the Beasts of the Awakened Forest - sentient creatures with magical abilities highly sought after by poachers. He must battle Mages and foot soldiers alike, all while attempting to gain the trust of the Beasts as a whole, and grappling with his own motivations for what he does. Things were looking up for the Forest, until a new threat emerged, and the poachers gained far greater resources and numbers than ever before. Now he must face off against an Archmage - and the support of the Forest is not guarenteed. Old powers must be persuaded to assist, or the Forest will fall forever. I'm writing this for fun and don't think it's particularly good, but it's fun to write so I figure I may as well upload it here! If you give it a read, thank you, and I hope you enjoy! Trying my best to release a chapter every other day, barring most weekends/holidays (though I will still try to get them out, but I make no promises) [participant in the Royal Road Writathon challenge]
8 92

