《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 70
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 70
Halima na zaune a barandar mama tana tankaɗen garin tuwo, yarone yayi Sallama yace wai ana Sallama da Halima awaje,
Mama dake gefe kan tabarma zaune tace kaje kace tana zuwa,
Kallon Halima tayi tace "tashi ki gyara jikinki ana sallama dake kije,
Tashi Halima tayi ta wanke jikinta ta shiga daki ta canka kaya sannan tasanyo hijab tafito, ajikin motarsa ta sameshi ta karasa cikin nutsuwa ta gaidashi ya amsa yana kallonta sun dan taba hira sannan yayi mata sallama yawuce."
Yanzu Malam rabi'u da Halima sun gama fahimtar juna saura kawai ya rage magaba su shiga maganar."
Washe gari malam rabi'u yazo yasamu baba, yana neman izini akan yanaso yaturo magabatansa a tsaida magana amma sai Baba yace "ya dakata tukunna sai yaje yasamu yayyunsa da mahaifinsu saboda bayaso asake samun matsala kamar yanda aka samu a lokacin auren Sawwama da Sadam yanaso ya gyara Alakar dake tsakaninsa da yan uwansa,
Ranar Laraba Su baba suke taruwa da yan uwansa a gidan mahaifinsa domin tattauna al'amuran rayuwa, ya yanke shawarar aranar idan suka taru zaiyi musu maganar auren Halima."
Ranar laraba da safe Baba bai fita kasuwa ba bayan yagama karin kumallo yayiwa mama sallama yawuce wajan mahaifinsa,
Malam Sa'adu zaune shida iyalansa baki daya,
Sai laraba matarsa dake cikinsu ana tattunawa,
Bayan sunyi Sallar azahar sun dawo Baba ya dubi mahaifinsa yace" Baba dama wani yaro ne yake neman auren Halima toh yazo ya sameni nikuma nace yabari idan nazo nasamu mahaifana da yan uwana mukayi magana duk shawarar da muka yanke sai nasanar masa idan kun amince saimu yanke masa ranarda zai turo magabatansa,
Malam sa'adu yace "Toh Alhamdulillah angodewa Allah, hakanma da kayi yayi kyau yanzu ga yan uwanka nan saisu yanke zuwa yaushe suke ganin za'a basu damar zuwa,
Yaya zakari kamar wanda dama jira yake yace "Baba badaniba bazan kara saka baki aduk wani abunda yashafi gidan hamisu ba aina faɗa maka kuma tunba yanzu ba, tunda haka yaga yafi masa toh yaje yayita aurarda yayansa awaje sai yajeshi yayi kayansa shi kadai batareda ya nememu ba ni narigada na cire hannuna a duk wani lamuransa ai duk wanda zaiƙi naka a duniya ba masoyinka bane, a lokacin danazo nayi maganar hada auren yar wajansa da yarona rufe idonsa yayi yace allanfir ba haka ba toh ni kuma mai zai gayamin? Allah na tuba meye nasa zai taso ya sameni na tsaya masa? bare yafi ɗan uwa awajansa sai yaje bare ya rufa masa asiri,
Yaya Ahnadu ne yace ai Hamisu yayi wauta a wannan zamani ace anason naka za'a aura amma kaƙi? Duk wanda zai auri yarka ai asiri ya rufa maka, barinma kai mai Ƴaƴa mata gabaki ɗaya, haka ka rufe idanuwanka alokacin mukuma ka watsa mana ƙasa anamu idon,
ai duk wani mai son naka ba abun ƙi bane taruwa akeyi arufawa ajuna asiri,
Advertisement
Yaya jamilu yace ku kuna zancenku ne aishi Hamisu kuɗi yagani ya sanya bazai iya bawa ɗan yaya zakari aure ba ya karɓi maƙudan kudi ya bada ƴarsa baidamu yakaita yanda zatafi samun kwanciyar hankali ba,
Kuma shi idan kukaga ya nememu ta wata huƙatarsa ce tataso yanaso mu rufa masa asiri anan take sanin amfaninmu,
Mahaifiyarsu tace kaji koh Hamisu? ina dai kanaji da kunnenka? Ai duk abunda ƴan uwanka sukayi maka kai ka jawo wazai ƙi nasa yaso bare? Abunda ya shiga tsakaninka da ƴan uwanka kai kajawo da tun farko kayi abunda yamata da haka bata taso ba."
Baba shidai baice komaiba ya sunkuyarda kansa ƙasa yana jira suyi su gama har indai hakan zaisa su huce su sauƙa a fushinda sukeyi dashi,
Shi koda say ɗaya bai taɓa danasanin ƙin basu aureba, bai taɓaji cewa yayi ba dai-dai ba auren Sawwama da yayi da Sadam,
Ya tabbata da yabawa Yaron yaya Zakari auren Sawwama da yanzu wani zancen mai muni akeyi ba wannan ba, yasan bazasu taɓa fahimta ba duk wani there're na duniya sai yagani,
Ƙanwar baba mai suna Hindatu ne ta amshe zancen da faɗin "Mama gaskiya bai kamata kishiga wannan zancen ba idan su sun kasa fahintar yaya Hamisu ke yakamata ki fahinceshi, yayiwa wasu alƙawarin aurrn ƴarsa tayaya lokaci ɗaya zaizo ya canja bayan kunsan matsayin alƙawari, shi yaron yaya zakari mai ya hanashi tun dawuri yanuna yana sonta ba sai bayan wani yace yana sonta daga farko, Abunnan shekara kusan biyu kenan amma kulkum aka tashi zance sai kun tado dashi, kunsan yaya hamisu nada Haƙuri ne amma cikinku ba kowanne bane zai zauna ana faɗa masa kowacce irin magana yana shiru,
Sosai Hindatu tayita magana sanda jikinsu yayi sanyi ,
Malam Sa'adu baice musu komai ba har suka gama maganganunsu, domin wancan karon sun nuna ya goyi bayan Baba Hamisu,
Malam sa'adu yace kacewa yaron ya turo magabatansa wajen sai muyi mgana."
Dukansu sunyi mamakin da mahaifinsu bai tanka komai gameda maganarsu ba har sukayi suka bari karshema wani zancen ya canja na daban."
Sai bayan isha'i sunci tuwo sannan kowannensu yakama hanyar gidansa."
Washe gari da dare bayan Baba yadawo a kasuwa yake cewa mama tayiwa Halima magana akan ta sanarwa saurayinta ya turo magabatansa,
Amma ta isarwa da Halima saƙon Baba amma kunya ya sanya ta kasa sanar dashi hhat saida mama tasake tuna mata sannan ta faɗa masa,
Ya shaida mata in sha Allahu zai sanar dasu idan yakoma gida dake ba agarin suke da zama ba."
Sadam yana fita sallan azahar daganna yawuce gidan mummy,
Acan yasamu abida yana kallonta ya tabbatar ƙararsa takawo,
Haɗe rai yayi yashiga ya zauna ya dubi abida yace"da izinin wa kika fito?
Mummy tace ungo man Sadam kana shigowa zaka fara yiwa mutane masifa toh da iznina ta fito ni nace tazo,
Saboda rashin hankali yana damunka jiya kasan ka barta cikin ɓacin rai saika tafi abunka wajan lallashin wancan matar, Wato mata so koh?,
Advertisement
Kuma ta faɗamin hhat zaginta tayi toh mudai kaff danginmu bbu mahaukata sai dai idan itace mahaukaciya, in banda kai wawa ba Sadam ta shanyeka shin mace zata ƙira danginka da mahaukata ne kuma kaci gabada zama da its?
Aiko zaka zauna da ita toh lallai ka hukuntata dai-dai da abunda ta aikata,
Sannan ga wata kuma fitsararriya Na mamajo zaka dawo? Kana yaronka kayita tara mata, agabanka ta wulaƙanta matarka amma kakasa cewa komai saima haƙuri kabata toh wallhy karnaji karna gani Sadam,
Faɗa sosai mummy tayiga yiwa sadam shiru yayi baice komaiba ransa yana masa ƙuna,
Mumny tana gama faɗanta yabar gidan batareda ya bi takan kowa ba."
Abida kuwa ya shaida mata cewa duk ranarda ta sake ta ƙara kai shi wajan mahaifansa da sunan ƙara shi kans baisan abunda zai iya aikatawa ba."
_________
Bayan wani lokaci malam rabi'u ya turo mahaifans aka gama magana, an saka sure wata uku masu zuwa lokacin baba zai samu yayi shirye-shiryensa a hankali,
Lokaci yana ƙaratowa Su Sawwama anata hidima duk wasu abubuwan da suka kamata anyisu,
Sadam yabata tasa gudumawar wanda ya taimakawa su Baba sosai da wash abun,
Ƴan uwan Baba kuwa bbu abunda suka masa hakan ya nuna masa basu sauƙa da fushinda sukeyi dashiba."
Alokacin da sukaga ƴan uwan Malam rabi'u dake sunada hali baba yasha maganganu dan cewa sukayi baya aurarda ƴaƴansa sai a masu hanu da shuni ya maida yaransa jarinsa,
anafara gudanarda biki amma bawata hidima sukayiba kawai walima ce, agarin zasu zauna mijinta tunda aka fara biki Sawwama samu zama ba sai da aka gama aka kai amarya ɗakinta,
Bayan biki da ƙwanaki Hindu wacce take biye da Halima tafara Zazzaɓi dafarko sun ɗauka gajiyar hidimar bikine amma sai sukaga abun ba haka ba
Chemist Baba yakaita akayi mata ƴan gwaje-gwaje daganan akace malaria ke damunta, magani aka rubuta mata
Abida kuwa hhat lokacin bata sake kaiwa Sadam ƙara ba dan maganganuna sun shugeta tana tsoron abunda zai aikata idan tasake kaishi ƙara, yayinda tsanar Sawwama da yarnta yananan acikin zuciyarta da mummy, kullum gani takeyi Sadam yana fifita Sawwama akanta."
Yaran Sawwama sunata girma har sun fara tsayuwa lokacin suna 8month,
Lokaci-lokaci sunkanje gaida mummy bawata tarɓa suke samu ba, saima baƙaƙen maganganu da take rakosu dashi, hakan yasa saita ɗauki lokaci bata jeba,
Kamar yau kusan 3month kenan bata je ba Sadam yace tashirya zuwa gobe zasuje su gaida mummy batajin daɗi,
Washe gari tunda safe ta shirya baizoba sai bayan azahar ana daf da za'ayi la'asar dake gidan a abida yake,
saida sukayi la'asar Sannan suka kama hanya,
Kamar kullum Sawwama saida tayiwa mummy dan bata taɓa zuwa hannunta haka,
Tafiyar lokaci ƙalilance takaisu gidan mummy bayan sun shiga kusan 30minute suna jiranta shi dama Sadam yana sauƙesu ya sanarwa mummy suna falo ya juya,
Sai can suka fito ashe harda Abida a gidan Sawwama cikin girmamawa ta gaida mummy, mummy ta amsa adaƙile, tambayarta tayi jiki mummy tace "naji sauki sannan ta ɗaura da faɗin ku ganinku wato sai idan mutum yana ciwo sai a leƙo adubashi, sai tsawon watanni bakisan da ina raye ba, tunda banci daraja da uwa ba yau gashi naci darajar zazzaɓi anzo an gaidani,
sunkuyarda kai Sawwama tayi sai taji babu daɗi wato ita mummy ko batada lafiya sai tayi bala'i,
Abida taketa tae baki tace "mummy ai laifin mijinta ne daya nuna mata darajarki da bazatayi ba, ya nuna mata zata iya taɓa kowa tazauna lafiya kinga dole tayi abunda takeso,
Mummy tace shiba maras hankali ba idan uwartane ai bazatayi mata hakaba,
Cikin sanyayyar murya Sawwama tace mummy kiyi haƙuri in sha Allahu zan kiyaye, taɓe baki tayi tace uhmmm toh Allah yasa danni bansa akaba aiba girin girinba dai tayi mai,
kular dake gaban Sawwama ta miƙa mata haɗeda faɗin maummy gashi, hararar kular mummy tayi tace "menene wannan ɗin? Badai yauma abincin kikayi ba? Kullum bakida aiki sia girka abinci idan zakizo gaisheni ko kin ganni da yunwa ajikinane?
Dariya Abida tasaka tace kai mummy toh ba'a samu agida ba yanzu ta samu ana facaka shiyasa idan zatazo take dafa miki taɗauka kowama na cikin halin yunwa, taɓe baki mummy tayi batace komai ba,
Dan sai dai ta faɗa haka afili dan taɓatawa Sawwama rai amma tanajin daɗin abincinta saboda ta iya abinci sosai."
Hawaye ne ya fara zarya a kuncin Sawwama."
Mummy tace kaga yarinya Au kuka kikeyi? Mijinki yazo ya ce an miki ba dai-dai ba koh? Yau naga makirci,
ƙasa dakanta tayi dan bazata iya hanasu saƙƙowa ba,
Yaran suka fara mutsil-mutsul sunaso su sauƙa mummy ta galla mata harrara tace sai ki sauƙesu ai, tunda nan gidan ubansu ne jikanuna ne idan awajenki banida kima su jinane,
Abida wacce idan taga yaran kamar tamutu takejin baƙin ciki, ko ɗan kulawar da mummy ke nunawa akan yaranma baso takeyiba,
Ganin mummy ta ɗauki yaran ya sanya ta tashi tayi ciki cikeda ɓacin rai aranta tunani take mezata yiwa yaran dan tasamu sauƙi acikin ranta,
Suna palour hhat akayi Sallar magrib, mummy ta dubi Sawwama tace"ni zan shiga Sallah ki ɗebi yaran kishiga dasu kema kiyi sallah karki barsu sumin ta'adi dan ƙiriniyarsu tayi yawa barima shi namijin ubansu kuwa baiyi ƙiriniya ba,
Ɗan murmusawa Sawwama tayi kawai jin yanda mummy take maganar kamar wanda aka sakata done, ko bbu komai tasamu sauƙi acikin ranta, koda mummy bazata sota ba har indai zataso yarnta toh Alhamdulillahi,
Ɗaukansu tayi ta shige ciki dasu a ɗakin tasamu abida bbu wanda yakula wani acikinsu Sawwama tazuba yaran tashiga toilet ta ɗauro alwala,
Hamdan yanata wasansa har ya'isa wajan abida yatsan ƙafarta ya taɓa yana ƙoƙarin kai bakinsa ta sanya Hannu ta tureshi baya dariya ya saka sai ya kalli kamar wacce take masa wasa ya ƙara zuwa wajan ƙafarta ya saka hannu ya kama a fusace Abida tayi wulli dashi can gefe cikin jin haushinsa, haɗeda zagin uwarsa, hakan yayi dai-dai da fitowar sawwama daga toilet."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial23 Chapters
Nobody's Way
Foreign Thorn: Book 1 For eight centuries, the people of Isla have wanted for nothing. The Creator, Maere, uses Her power not only to keep them healthy and fed, but also to map the direction of each person's future Path - their vocation, role in society, and even the partner they'll spend their life with. In a world where infighting once threatened the very survival of humankind, the old texts say that Maere personally stepped in to help guide Her creations to harmony. All is not well among the people of the northern lands, however, as Jian discovers when she receives her own long-awaited Path. The Creator has chosen to favour some towns, but not others, leading to anarchy and unrest in the east, and fierce distrust between the neighbours who enjoy Her protection and those who don't. After many nights of disturbing premonitions, visions of a face uncannily familiar to her, and a voice beckoning her to "Homeland," Jian decides she needs to find answers for herself. She hires Madrigal, a surly young traveller hailing from an "unblessed" village, to take her to the southern lands. The swordsman is on the run from something, or someone, but Jian has no choice but to trust him. When the two leave the safety of the familiar and meet Quinn, a mysterious boy who seems to know more about Jian than she does about herself, it becomes clear that there are forces besides the old magics, forces completely unknown to the people of Isla, in play. Madrigal and Jian aren't sure if Quinn can be trusted, but they're certain he knows more than he's letting on...
8 101 - In Serial45 Chapters
SOULMATES.
━━ MATTHEW TKACHUK!❝ After all, soulmates always end up together.❞ mainly social media- messages, instagram, ect. [calgary flames] [matthew tkachuk] © nazemkadri 2017
8 168 - In Serial13 Chapters
Fade Away [Reapertale]
What could go wrong when your living among Gods?
8 90 - In Serial101 Chapters
100 Short Scary Stories
*Featured on the Wattpad fright and Ghost profile!*Read these stories at your own risk. Some of them have gore and many are rituals you can perform. Others are tips and tricks to escape demonic activity or maybe even how to get out of a coffin while you're alive... Highest Rank: #1 in horrorThese stories are a mix of both mine and stories found off the internet.
8 189 - In Serial32 Chapters
hope not, blackpink
... as if nothing happened, i will smile if i see you© dilemmarz | 2020
8 204 - In Serial44 Chapters
Please Stay[Stray Kids × Reader]
(Y/N) tried to avoid the music industry as much as possible. However with fate, her twin brother Hyun Tae got into a car accident forcing her to disguise as him and continue the steps of her brother with the stage name of "Alex", being one of the members of STRAY KIDS, a new JYP boy group to soon have a debut. Will she be able to succeed?(Rewriting)04/19/19 - 10/05/20 [Completed]
8 135

