《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 67
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
page 67
Ɗakin dake daff da nasu ta shiga ta shinfiɗa hameeda saita ta tabbatar baccin nata yayi nisa sannan tafito izuwa falo, Sadam na ɗauke da hamdan yana masa wasa yayin da shikuma yaketa ɓalɓala dariya kallonsu ta tsaya yi daga nesa gwanin sha'awa, a hankli ta taka ta ƙarasa wajanda suke zama tayi gefensu sannan tace "miƙomin shi yyaa Sadam dare yayi sosai gara shima yayi bacci kamar ƴar uwarsa, ɗago yaron sadam yayi ya yi masan peck a both kumatunsa sannan ya dubeta yace "yaronnan nada sabo sosai bawani daɗewa nayi tare dashi ba amma ya sake dariya kawai yake min, murmushi Sawwama tayi sannan tace"su yara haka suke ko yau suka fara ganinka idan suka sake dakai zaka ɗauka tun dacan sun sanka idan kuma sunada ƙuiwa ko kullum suna ganinka sai sunyi maka ƙuiwa, daɗin daɗawa kaifa mahaifainsu ne dole su sake dakai sosai ba kamar sauran mutane ba,
Miƙa mata shi yayi ta ƙarbeshi ta kimtsashi sannan ta bashi mama alokaci ƙalilan shima yayi bacci kamar ƴar uwarshi ta kaishi ta kwantar dashi saida tayi musu addu'a sosai sannan tafito duk wani abunda yakamata ta tattare saida ta tattareshi suka kulle ƙofa sannan suka shiga daga ciki, Suna shiga sawwama ta isa izuwa ma'ajiyar kaya ta ɗauki kayan bacci ta saka sannan ta ƙarasa gado ta ƙwanta ta lumshe idanuwanta shima rage kayan jikinsa yayi sannan yace "zo muje muyi wanka, Sawwama tace ni bacci nakeji kaje kayi kawai nayi wanka daff zamu fito daga gida,
Kamo hannunta yayi yace"no wannan na dabanne wancan daban noƙe kafaɗa sawwama tayi tace "oh oh nayi wanka bazan ƙara wani ba mura nakeyi"
"aida ruwan zafi zamuyi yafaɗi batareda yajira ta ƙara faɗin wani abunba ya ɗauketa cakk zuwa banɗaki, tsawon lokaci suka ɗauka wajan wanka sannan suka fito, wannan dare gabaki ɗaya sun rayashine a farantawa junasu yaransu basu farkaba sai asubahi, Sawwama tana jiyo kukansu tatashi ta nufi wajansu shikuma ya wuce zuwa masallaci a ɗakin yaran tayi sallah saida ta tabbatar sun koma bacci sannan takoma ɗakinsu tasamu har yadawo daga sallah, komawa bacci sukayi basu suka tashi ba sai 10:00am sai bayan ta farka tagama duk wasu abubuwan da yakamata har izuwa lokacin su hamdan bacci sukeyi, bayan tagama shirya gidan ta haɗe breakfast sannan tashiga wanka tafito sanye da towel wanda iyakacinsa cinya, batayi auneba taji sadam yashigo ɗakin yi tayi kamar bataji shigowarsa tazauna tafara shafa ma lallausan fatar jikinta mai, a hankali takebin kowane saƙo na jikinta tana murzeshi da mai, yayinda Sadam yana gefe yana ƙare mata kallo duk yanda ta sanya hannu idonsa nakai, kasa jurewa yayi ta isa zuwa wajanta hannu ya sanya ta tatsi mayin dake kan dressing mirror ya tsugunna akan ƙafafunsa murza man yayi atafin hannunsa yakai hannun zuwa jinyarta yafara shafa mata mayin amma kamar wanda yake murza fatar da gayya da wata manufa ta daban runtse idanuwanta tayi ta huɗesu akansa sannan ta dubeshi cikin wani yanayi daƙyar ta iya riƙe hannun haɗeda faɗin "yaya Sadam meye hakan ni nafa gama shafa man kaya kawai zan saka, janye hannunsa yayi batareda ya kalleta ba yacigaba da shafa man daga bisani ya janye towel ɗin yayi ƙasa runtse idanuwanta tayi bata buɗeba har yagama shafe kaff illahirin jikinta da man sannan ya miƙe ya dauketa cakk tsillo tafarayi tana faɗin yaya sadam meye haka? Yanzu fa nayi wanka, Sadam bai kulata ba har saida ya idda nufinsa, bayan nan sannan sukayi wanka wani man tasake shafawa ta sanya turare mai sanyin kamshi, kwalliya ba mai yawa ba zallan powder man baki da maskara tasaka ya sake fito da eyelashes dinta dake masu tsayine sai maskara ya sanyasu sukayi kauri, atampha tasaka rigada skirt wanda yafito da illahirin surar jikinta ba ƙaramin kyau kayan yayi mata ba ta ɗaura dan kwalinta ya zauna ɗass yayi kyau gwanin sha'awa,
Advertisement
Duk yanda ta wulga idanuwan Sadam nakan ta, ji yakeyi kamar ya haɗiyeta dan so da ƙauna,
Sai wajan 11:30am kafin sukayi breakfast, lokacin yaran har sun tashi ta wankesu ta shiryasu, tana shirin haɗa musu madara Sadam yace baisan zancenba mama zata bawa yaranshi, haka dole saida ya sanyata ta shayar dasu na tsawon lokaci kafinnan ya barta tabasu madara, kirjinta har zogi suke mata saboda ba halin ta zauna zaice ta shayar dasu koda kuwa ba kuka suke ba, tana gamawa dasu shima kans sai ha ɓullo da wani lamarin na daban wunin ranar Sadam ya sanya ta sake wanka yafi a irga kaman wani sabon aure haka yakejin kansa,
Wuni yayi curr babu yanda ya fita sai Sallah. Shi yama manta da Abida ko sau ɗaya bata faɗo masa arai ba, ya tarkata komai ya watsa gefe Sawwama da yaransa kawai suke gabansa,
Kwana biyun da sukayi tare ba ƙaramin farin ciki suka bawa junansu ba, a wannan lokacin soyayya da ƙauna kawai sukayita shayar da junansu toh ba anan gizo take saƙar ba, saida dare yayi sadam shaff ya manta da zancen wani raba kwana har saida Sawwama taga baida niyyar tafiya tayi masa tuni,
Ɗan karamin tsaki yaja cikin ransa yace "Wai har anyi kwana biyun? A'iya tunanina na ɗauka kwana ɗaya kaman jiyafa kika dawo, girgza kai Sawwana tayi tace "A'a ƙwana biyu kenan da dawowata yau yakamata ka koma, da sanyin jiki Sadam yace " lallai lokaci yana tafiya banyi auneba har lokaci yayi,
Yafaɗi haɗeda cigaba da zamansa an ɗauki lokaci taga baida niyyar tafiya ya sanya taƙara yimasa tuni miƙewa yayi rainsa ba daɗi, Sawwama wacce itama takejin ranta duk babu daɗi ta miƙe ta riƙo hannunsa kallonta yayi ganin yanyinta ya canja ya sanya ya sakar mata murmushi ko zata saki ranta, murmusawa itama tayi ya janyota jikinsa ya rumgume ɗago fuskarta yayi ya haɗe bakinsu wane ɗaya ya daɗe yana kissing nata sannan ya saketa har bakin ƙofa ta rakashi sannan ta kulle haɗeda yimasa fatan alkahiri ta juyo izuwa ciki,
Kashe duk wasu na'urori tayi tashiga ɗaki itada yaranta addu'a tayi musu ta ƙwantar dasu ta kwanta itama,
Kewar sadam ta isheta hakan yasa ta jawo yaranta ta rumgume ahaka bacci ya ɗauketa."
Sadam yana shiga gida ya tararda Abida ta cika tayi famm jiransa takeyi, yana shiga yayi arba da ita ya ɓata rai dama tun ranar bai ƙara sakewa da itaba, kai tsaye ɗakinsa ya nufa tabi bayansa tana faɗin "sai yau kaga daman dawowa? Ai ko zaka ka ajiye acikin gidannan zaka dawo kaduba yanda ka barta bare mutum, kuma matarka wacce nakeda hakki akansa wallhy Allah bazai barka ba mugu azzalimi, Sadam da ɓacin rai ya dubeta yace duk mai yayi zafi haka? da har kike bina da mugayen sunaye akwai wani abunda kike buƙatane agidannan wanda nafita ban tanadar miki ba?
Kona barki da yunwa?
Duk wani abu da zaki buƙata na ajiye miki shi, har menene haka tsagwaran rashin kunya zakizo ki nunamin?
Abida ta murguɗa baki tace toh ai ba abinci bane kawai matsalata ba tunda ba agidan yunwa ka ɗeboni ba,
Kuma bakakai nayi maka rashin kunya ba aiba girmata kayi ba ta ƙarasa maganar tana riƙe ƙugu da turo baki, dariya Sadam ya saka wanda saida yasa ta tsaya tana kallonsa, arayuwarsa ya daɗe baiga shashasha irin abida ba ko bai girmeta ba a haife amma darajar aure Allah yabashi girman"
Ya lurada cewa itaɗin sokuwa ce ta karshe,
Advertisement
Ɓata rai tayi tace kayimin laifi kuma kanamun dariya mahaukaciya ka ɗaukeni?
Dariya tana cinsa ya girgiza kai yace A'a, tace toh tunda ba hakaba kabani haƙuri zan haƙura, Sadam yace toh kiyi haƙuri, murmushi tayi ta zauna gefe kusadashi tace na haƙura amma da sharaɗi ɗaya,
Menene sharaɗin ina jinki, A'a saika yarda da sharaɗin kafin na faɗa, yace A'a tayaya zan yarda da sharaɗi batareda nasan wani iri bane faɗi ina jinki,
Sharaɗin shine nima zakamin ciki kamar yanda kamata ta haihu nima na haihu,
kallonta Sadam yakeyi rashin wayon Abida har yayi yawa sakarcine da ita gashi itakuma ba ƙaramar yarinya ba, nisawa yayi yace" toh naji amma sai kin bani haƙuri nima dan abunda kikayimin a ranar friday banji daɗinsa ba rains ya ɓaci daga dawowarmu kika ɓatamin rai wanda acan ba haka kikemun ba, canjawa Abida tayi takoma wata salaha tace "ai shiyasa nace maka muzauna acan karmu dawo zamanmu acan yafi daɗi kaima baka ɓatamun rai, iska sadam ya furzar yace ki fahimci wani abu inada iyali anan inada mahaifa ina buƙatarsu kusa dani ke baki buƙatar mahaifanki kusa dake?
Yatsina fuska tayi tace har indai zanzo ko sau ɗayana ashekara nagansu ai shikenan bbu komai,
Sadam yace "ni awajena akwai komai,
Nidai yanzu mubar wannan maganar kawai nima kamin ciki, toh yace haɗeda aikata abunda takeso kawai dan gudun fitinarta."
Washe gari kuwa itama ta tayarda rikici wai bazai fita wajan Sawwama ba itama dole tarama abunda tayi mata,
daƙyar ya zare yaje yaga Sawwama da yaransa dan bazai iya haƙuri ba idan yana nesa yayi juriyar rashin ganinsu yanzu yana kusa bazai iya ba."
Bikin najeeb yanata ƙaratowa hidima kawai sukeyi basa samun zama su dukansu Sawwama da abida bawani samun ganinsa sukeyi ba sai lokaci-lokaci,
Sawwama ta fahinceshi yayinda abida ta ɗaura hakan akan yana zuwa wajan sawwama ne shiyasa baya samun lokacinta,
Tunda aka fara bikin najeeb wata ƙawar amarya ta maƙalewa Sadam sai guje mata yakeyi amma kamar chewing gum tadawo masa wata bini zai-zai,
Tunda najeeb ya fahinci haka yayiwa amaryarsa magana cewa tayi mata magana dan Sadam matanshi biyu kuma yasan abokinsa mata biyu ma banda ya zama masa done da bazaiyi ba,
Shikuma Sadam dalilin dayasa wasu lokutan yake sauraronta saboda kasancewar sunanta hafsa, shikuma a duniya baya fata wata rana tazo da zai iya wulakanta mai sunan, sonda yake yiwa Sawwama bana wasa bane shiyasa duk wani abunda ya danganceta yana girmamashi, amma ya kuɗirta aransa biki kawai za'ayi agama, ana gamawa ko hanya bayason ya sake haɗawa da ita dan Abida Sawwama mai shiru-shiru da haƙurima take caja masa kai akanta bare ya ƙaro wata,
Amaryar najeeb da kanta tasamu kawarta tayi mata bayani, da mamakinta cewa tayi ko mata huɗu ke gareshi har indai zai saki ɗaya ya aureta toh zata aureshi bare mata biyu, ita taji tagani tana sonsa ahaka,
Najeeb yayi mamakin jin kalamanta dakansa ya sameta yace "hafsa ki fahimci wani abu koda kin aureshi bazaki taɓa samun soyayyarsa ba saboda mace ɗaya yakeso, ita kanta ta gidan takasa samun soyayyarsa saboda hankalinsa naga Sawwama, Dariya hafsa tayi tace ikon Allah tsawon lokacin aurensu takasa samo zuciyar mijinta ya sota lallai wannna sakaraAr mace ce bata iya takunta ba, kabarni kawai na aureshi a baya sona kowa ta iya allonta saita wanke, ganin tayi nisa ya sanya najeeb kawai ya rabu da Ita."
Tunda aka fara bikin sadam baije da matars ako guda ɗaya ba sai ranar wuni dafarko yaso yaje da kowacce ranarta daban sai hakan baiyiwuba,
Gidan Abida ne yafi kusada gidan bikin kawai sai yabi yafara ɗaukan sawwama sannan yawuce gidan Abida, yana isa ya kirata ya sanar da it aakan tafito, tafito taci wanka da kwalliya sai wani taku take tana zuwa taja ta tsaya cakk ita duk tunaninta da ita zai tafi sai taga Sawwama, ƙololon baƙin ciki ya tokareta kamar ta sa hannu akayi tayi ihu takeji,
Sadam yace "shigo mutafi mana ke kaɗai muke jira, kasa haɗiya baƙin cikinta tayi tana faɗin waye zai zauna abaya? Ni? Takoma baya saina shiga mutafi, batareda Sawwama tajira sadam yayi magana ba ta ɗebi ƴaƴanta ta buɗe ƙofa takoma baya, tissue ta sanya ta goge yanda Sawwama ta zauna sannan ta shiga, Sawwama ta gaisheta ko kallo Sawwama bata isheta ba bare yaran ganinsu kaɗai baƙin ciki take ƙara mata,
Sadam ya Shanye fushinsa ta hanyar furzarda huci yajuya yadubi sawwama ya sakar mata murmushi itama ta maida masa, yaja motar suka tafi,
Gidan Najeeb suka nufa dan anan za'ayi events na buɗar kai, suna isa Sadam ya fito ya buɗe ƙofar Sawwama ya karɓi hamdan sannan itama tafito ɗauke da hameeda, sunyi matukar kyau sosai Sawwama sai wani yalyali takeyi ba wata kwalliya tayiba amma tayi matuƙar kyau,
Saida yakaisu har cikin wajan yabata hamdan kafin ya juya dake anyi decoration wajan yayi kyau sai suka zauna amma kowa gefenta daban,
Kusada wasu ƴan mata Sawwama tazauna tana iya juyo hirarsu kaɗan-ƙadan wata daga cikinsu taji tana faɗin hafsa ga man ɗinki can ya iso fa kinga yanda yayi kyau? Yanda kasan shine ma angon da kansa, miƙewa hafsa tayi tana faɗin "ai Sadam ya haɗu bari naje na sameshi kona ɗanji sanyi araina zamana anan jiransa kawai nakeyi, ambatar sadam da tayi ya sanya gaban Sawwama faɗuwa rass, tanaso ta juya taga ko Sadam mijinta ake nufi amma fargabar abunda zata gano ya hanata,
Kasa jurewa tayi saida ta kalli wajanta wannna hafsa ta nufa, tabbas Sadam ɗinta ta nufa, Sadam mijinta dishi-dishi take gani Sadam ta hango yana saukewa hafsa sinƙi-sinƙin murmushi tun kafin ta ƙaraso, da rangwaɗa ta isa zuwa Sadam,
Tana isa tace "kayi wuyar gani man, tun datsu nake jiranka akwai wata muhimmiyar magana da nakeso muyi dakai,
Sadam yace gani nazo yanzu zamu iyayi ko sai angama events?
Hafsa no no muyi yanzu kafin amarya da ango su ƙaraso, amma nan yayi cikin mutane ko zamu ɗan keɓe? Why not yafaɗi haɗeda binta suka bar wajan, duk wannan abun akan idon Sawwama, nan danan tafara jin jiri shin me hakan yake nufi? Sadam aure zai ƙara? Dama yanada budurwa? Shine yake nuna mata cewa ta isheshi rayuwa,
Sunkuyarda kanta tayi kawai dan tanajin babu daɗi, hawaye yana bin fuskarta,
Abida duk batasan wainar da ake toyawa ba ta kifa kanta a waya sai danne-danne takeyi."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial41 Chapters
Era Of The Kobold
Era of the Kobold Returning July Third! Hi there! Thought I forgot about this series, didn't you? In all seriousness, I am sorry for not posting in such a long time. I've been really busy with other things, mainly my education. However, once July hits and I get the time needed to write, I'll be continuing EotK where we left off. It'll be the regular one chapter a week at least, though I'll try to post more frequently for that month. Hopefully you all have been doing well! I'll see you in July. Synopsis: All he wanted was to spend his life gaming. Samuel was an absolute nerd when it came to video games, RPGs especially. He'd play them all day, rarely leaving his house, or even his room for that matter. His peaceful days were sadly ended before he even finished college, however. Despite his expectations, he finds himself reincarnated in a new world as a Kobold. He must now live a hard life as a weak creature that tends to die young and is seen as a monster. How will he manage in this new life and what will he do with it? The rate of publishing will slow down, as I focus on my education.
8 191 - In Serial21 Chapters
Luck And Chronomancy
Time Magic is the best magic as everyone knows, although there are lots of unique Talents in the world. Most people only remember Haste because it is hard to get to higher Phases of Chronomancy. That is still enough to make the Talent iconic. A lucky enough Aleatory Talent can position you for greatness or leave you languishing in obscurity. The only true equality in the world is when that glowing message pops up at 8 years old. Even if it doesn't activate until you are an adult at 16 you still know. Sure you can find a new dungeon spawn and get another chance at a rare Talent, even this one, but you have to already be ready to delve into the *Far Wilds*, which is far easier with wealth or family power. This is the story of where my good fortune took me and the difference it made, even among a party of 7 others including an Arcanist. It is a journey of magic and monsters but also math, which some think is actually worse. Luckily I was born with Intelligence and Focus as my personal traits, and my parents were scholars. Of course Chronomancy can also be a frontline combat talent. Versitility well beyond other Elder Talents like Gravity, Abstraction, or Arcana. Might could have worked for me, too. I also met a runaway princess. All the best adventures have a princess. She hated being a noble and we didn't get married but it still counts. Besides she really filled out our front line. All that Leadership training came in handy. I still don't know where she's from. Who cares? How well Haste goes with giant hammers is what's important. I never learned much about anyone in the party, except the one I grew up with. I'm not a people person. I just wanted to optimize dungeon clearing time. *******Story Details******* No romance, politics, or traumatizing content, slice of life, or even dialogue. 1st person narration, like a guide/adventure log. 2000-7000 words a day, maybe 40-60% rpgish combat log with some reasoning on combat decisions, with the rest character Talent discussion and progression stuff. 8 person party with a decent variety in roles. Party members usually have 2 primary functions. Told from the support/control Chronomancer's perspective. Each party member will have 6 Basic/Background Traits, then 3 actual Talents with abilities. Capstone from their Educational Institution, Arbritrary as a gift from the temples, and Aleatory which is decided at birth, revealed at 8, and activated after adulthood at 16. Aleatory Traits ignore requirements and are random why is why they are so important. They'll gain new Talents from finding Dungeons to consume in the *Wilds*. Mature dungeons in cities can provide *Challenges* to raise the Phase of a Talent, up to 3 times from 1 to 4. Each character will get to roughly 8 non-Trait Talents. Attributes come exclusive from Talents, are required by Talents, and provide various effects as well. I designed about 220 Talents with abilities, 4 in each of 4 phases. "Traits" are just Attribute stuff. I'm not sure how many will be detailed in the story, more than 100 for sure. I used Talents because I want to be free of the legacy of tabletop. Half those rules are just because of the limitations inherent in a pre-computer ttrpg. This story mostly uses combat Talents, although like 1/3 of the 220 are for crafting and other society and economy stuff. If you really wanted to be a Thief you might take Intuition, Awarness, and Might for Basic Traits and Deftness, Manipulation, and Trickery for Family/Education. Then you'd pick Acrobatics, and Climbing for Educational Capstone and Arbitrary traits. You Aleatory Trait might be Shadow(Light/Dark) Magic, Umbramancy. A Bard might swap Dexterity for Charisma, Music for Acrobatics, and have gotten Illusion(Shadow/Sound(Air/Force)) for their Aleatory Trait.
8 193 - In Serial24 Chapters
Worlds: The Beginning!
A long time ago there existed only a single continent, the divine continent. And it was split into three great civilisations: the human civilisation, the tyrannical beast civilisation and the magical beast civilisation. These three great civilisations were ruled by emperors that were so powerful that they could kill anyone that they wished but each other with but just a single thought while being billions of kilometres away.But that was all in the past as now there is more than just one continent. Now there is no longer a civilisation that would dare call itself great. Now there is no human, tyrannical beast or magical beast alive that could kill anyone that they wished with just a single thought by being billions of kilometres away.But that could all change in the future.
8 185 - In Serial54 Chapters
The Break
What would you do if you knew humans were not the only Intelligent ones? What would you think if you knew humans had more potential and power than you thought? What would you aim for if you knew that all dimensions will merge and become one again? When you could have the power to not only protect yourself but to influence this changing world by the core, what would be your first goal? Laith Arslan never knew that he had to come across these questions. And it all started with one dream. A dream that changed his life completely.
8 144 - In Serial48 Chapters
Blood Lust (COMPLETED)
⚠️ WARNING ⚠️ THIS IS A REVERSE HAREM BOOK! IF YOU'RE NOT INTO AN MC WITH MULTIPLE PARTNERS, DO NOT READ! BOOK TWO OUT NOW!!!Highest Rankings:#1 in Erotic Romance #1 in Blood and Gore#1 in Bloodsucker#1 in Girl Problems#1 in Adult Situations#1 in Polyamory#1 in Adult Themes#1 in Reverse Harem#1 in Island#1 in Vampire Romance#1 in Undiscovered#1 in Vampire#1 in College#1 in Adult-Content#1 in ParanormalEighteen-year-old Audrey Ridley grew up a foster kid, shipped around from family to family, never really having a place to call home. Until she earns a scholarship for a prestigious university on an island in the pacific northwest. Now she's making friends, flourishing in a stable environment, but there's something up with the faculty members of Lachlan University. Particularly the campus security members.They gawk at her, eyes wide and unflinching, as if she were drink of water on a scorching day. They address her with a bow, going out of their way to speak to her. But that's nothing compared to the dean's behavior. His gaze follows her every movement, he calls her queen when he thinks she isn't listening. And he's always having to run off when they have a chance to be alone together. Only when a creature sinks his teeth into her neck does Audrey begin to unravel the bloody truth; both about the denizens of Lachlan Island and herself. COVER DESIGNED BY: @laylagriffin_
8 206 - In Serial65 Chapters
NCT 19th Member
The description is in the title :) If you have any suggestions on chapters make sure to let me know!
8 143

