《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 66

Advertisement

**

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by

zaynab bawa

#Follow me on

"

Marubuciyar

*BIBIYATA AKEYI*

* Y'AR FARI*

* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 66

Suna shiga ciki Sawwama ta sauke ajiyar zuciya mai karfi Halima t adubeta tace "wani abunne yafaru yaya Sawwama naga kamar kina tsorace Sawwama ta kalleta sannan tace "oh toh tun datsu motar da take binmu tun daga fitowarmu shagon lalle baki luraba? Girgzan kai tayi tace "A'a yaya Sawwama nikam ban lurada komai ba, nisaww Sawwama tayi tace yakamata kina lura saboda tun fitowarmu ake binmu, Halima tace in sha Allahu,

Suna ƙarasawa ciki wayar Sawwama tayi ƙara tana dubawa taga Sadam ta amsa tana fadin yanzu nakeda niyyar kiranka daga cikin wayar Sadam yace aiko baki kirani dama nayi niyyar zuwa yanzu ko ba'a gama ba mutafi haka, domin nasan yarana sun gama galabaita, ta murmusa cikin sanyin muryarta sannan "A'a sukanma sunyi bacci abunsu,

Sadam yace "Ok gani ƙarasowa toh na maidaku gida, Sawwama tace "au mukam har mun iso gida dan daff da magrib muka gama sai nayi tunanin kana sallah yasa ban nemeka ba, yanzu isowarmu gida dan ko mama batasan da shigowarmu ba, yace "ok yanzu kihuta zuwa jimawa zan zo shigo naga kwalliyar da aka yimin, toh Allah ya kaimu tace sannan ta kashe wayar, sanarwa mama da dawowarsu sukayi sannan suka shiga sukayi sallah, sai bayan isha'i sannan Sadam yakira wayar Sawwama ya sanar da its isowarsa, bata ɓata lokacinba yafito tayi masa iso zuwa ciki,

Hameeda da Hamdan dukan su sunyi bacci ta shimfiɗesu a man gado, kallonsu ya tsaya ya nayi na wani lokaci sannan ya juyo ya dubi sawwama, murmushi ta sakar masa a hakali yayi taku biyu ya isa izuwa gabanta, hannu ya sanya a ƙugunta a hankali ya jawota jikinsu ya hade waje daya fuskarsu ma haka numfashinsu yana dukan na junansu yayinda zuciyoyinsu suke bugawa da sauri-sauri, Daga kwayar idanuwanta sama tayi tana kallonsa, kallo mai cikeda shauƙi da soyayya, a hankali ya hura mata iska a idonta ta lumshesu sanban ta sake budewa ta ƙara zuba masa idanuwan sunkuyarda kansa yayi ya dai-dai ta lips dinsa dai-dai nata lumshe idanuwanta tayi tun kafin ya kaiga aikata abunda yake shirin yi, Lips ɗinsa ya sanya akn nata a hankali ya sumbaceta na tsawon lokaci sannan ya raba lips dinsa na nata ya haɗeta ya rumgume tayi luff ajikinsa tana shakar kamshin turarensa tsawon lokacin suka dauka ahaka, jin motsinda tayi cikin gida yasa tayi saurin raba jikinsa da nata ta zauna gefen gado yana binta da wani kallo mai cikeda ma'anoni ya nufeta shima ya zauna har izuwa lokacin kallonta yakeyi ta dubeshi cikin matsananciyar soyayyarsa dake dawainiya da ita barinma idan yana yimata irin wannan kallon tace "yaya Sadam kaga lallen da nayi maka? yayi kyau? ta tambaya tana kallonsa,

Kamo hannunta yayi yana ƙare masa kallo zanen baƙi da jaa yayi matuƙar kyau haka na ƙafar ma shima baƙi da jaa ya sumbaci hannunta sannan yace "kyau har ba'a magana bana tunanin nataɓa kallon wani lalle mai kyawu kamar haka lallai wannan mai lalle dani naje ɗaukoki sai nayi mata kyauta, dariya Sawwama tayi sannan tace tun datsu ake fadin kyawunsa amma danaji daga bakinka sai ya ƙaramin kyau, jawota yayi izuwa jikinsa a hankali ya sumbaci goshinta, tswon lokaci ahaka bbu wanda ya tanka ita ta katse shirun da faɗin baba yace zamu koma ranar latala idan Allah yakaimu, gobe zani kitso ranar litinin kuma za'a gyara gidan ankwana biyu babu ba'a cikinsa,

fara'ar Sadam bata iya ɓoyuwa ba yayi murna sosai jin cewa Baba bai saka lokaci mai tsayi ba dan shi dai ya ƙagu yaga matarsa kusa dashi da kuma yaransa,

Advertisement

Sadam ya labartawa Sawwama aikin daya samu a can amma yaƙi zama, da mamaki Sawwama ta dubeshi tace "yaya Sadam ko mai yasa?" wannan fa dama ce mai kyau bai kamata ace kayi wasa da ita haka ba,

hannu ya sanya ya lakaci hancinta ya sake rungumota jikinsa sannan yace "duk ɗaya kuke, baku tunani, tunanin damar dana samu nayi wasa da ita kawai kukeyi, baku tunanin halinda nake a can, na ɗauka ke zaki fahimci hakan tunda kinsan irin sonda nakeyi miki kin sani zamana ba'a kusa da keba gabaki daya atakure nake, wannan lokacin dana ɗauka ma nayi matuƙar ƙokari ban dauka zan iya zama tsawon wannan lokacin batare dake ba, yanzu ba daa bane inada yara inada iyalai bazai yiwu naɗauki mata ɗaya nazauna da ita acan ba bayan nabar wasu iyalan anan, basai na fada miki ba ke kanki kin sani har indai zaman za'ayi acan toh da Abida zan zauna domin mahaifinta ne ya nemi aikin tare da ita,

Ni bazan iya ba zamana anan tare daku yafimin zamana acan ko nawa zasu biyani ganinku tare dani yafiyemin komai,

Ƙara kwantar dakai Sawwama tayi a jikinsa a fili ta furta"koda na faɗa maka cewa kayi aiki acan bawai hakan yana nufin zan iya ƙara daukan tsawom lokaci batare dakai ba ko a wannan lokacinma idanna ce maka ban damu ba nayi karya amma yaya Sadam nasan mummy sam bazata so abunda kayi ba ita kuma mahaifiya ce ni inaso ka farantawa mahaifiyarka,,,,, shhhhh Sadam ya saka yatsa ya rufe mata baki yace "shikenan mubar maganar,

Canja wata hirar na daban sukayi suna suka jiyo yaro yana fadin wai ana sallama da halima, Halima! Halima kuma toh ko waye, abunda Sawwama tafaɗi kennan, Sadam ya dubeta yace "waye kuwa banda saurayi may be wani yaganta yaji yana sonta shine ya biyota, Sawwama tace "ina zuwa miƙewa tayi ta fice izuwa dakin mama dake dukansu suna zaune acan baba kuma bai rigada ya dawo ba,

Da sallam atashiga sannan tace wa mama "baku jiyo ba? Wani yarone ya shigo wai ana sallama ta Halima, mama tace Halima! Halima kuma? to ko waye? Mama tayi wani tunani sannan tadubi sawwama tace hafsatu kice batanan kawai a darennan bazan tura yarinya waje ba ga babanku bayanan, juyawa sawwama tayi ta sanarda yaron sannan ta shige wajan Sadam, Sadam bai tafi ba sai wajen goma na dare, sukayi sallama da cewar da safe zaizo yakaita kitso."

Washe gari da safe yazo kaita wajan kitso dan yace bazai yiwu tayi dare irinna jiya ba,

gabaki ɗaya 1hour suka ɓata wajan mai kitson sannan yawucw dasu kasuwa zasuyi shopping abubuwan amfanin gida, kai tsayw gidan suka wuce bayan sun gama suka ajiyw abubuwanda suka saya sannan yadawo dasu gida"

A ranar ma da dare saida akazo sallama da Halima mama ta cewa dan aiken yace "dare yayi idan yanason ganinta gobe yazo da rana,

Washe gari litinin gidan sawwama suka wuni sun gyara sunyi mopping an saka tutarukan wuta abubuwanda yakamata a wankesu duk wan wankesu,

Sadam ne ya saukesu sannan yawuce wajan najeeb domin shirya wani abun gameda bikinsa,

Daff dasu shiga ciki wata mota ta ƙaraso tayi parking kamar wanda dama jiran dawowarsu ake, Sawwama a tsaroce tacewa halima "kinga wannan ce motar ranar duk da kasancewar magrib tayi gari yayi duhu a ranar amma zan iya ganewa itace, kodai biyomu yayi? Halima tace "toh yaya Sawwama me yazo yi a ƙofar gidanmu kuma? Jan hannunta tayi suka shige ciki batarda tabata amsa ba,

Suna zama bada dadewa ba akai sallama da Halima mama tace oh Allah wannan mutumin ya dage gashi ni ko sanarda mahaifinku ma banyi ba,

Advertisement

Sawwama tace" yanzu muka ga wni yayi parking ƙofar gida kuma dama tun ranar ya biyomu daga shagon lalle inaga shine yaketa zuwa, mama tace"toh daga ya biyoku shagon lalle sai yasan sunanta? Sawwama tayi dariya tace "mama yanzu fa ba daa bane zai sani maman may be ma tambaya yayi ko wajen mutannen anguwa, taɓe baki mama tayi tace har yaushe kuke fitan da har mutanen anguwa zasu san sunanku? Mama yanzu fa mutune ake kiwo zakiga kamar mutane basu damu da rayuwarmu ba amma tsaff wasu idonsu na kanmu, nisawa mama tayi uta dai zuciyarta bata kwanta ba amma tacewa Halima taje karta dade,

Hijab Halima ta maida ta fita izuwa waje, waige-waige tafara yi tana neman mai kiran nata, yaron da suka fito tare dashine ya nuna mata yace"gashinan,

Kallonta takai gareshi matashi ne a kalla zai kai 37yrs mai yiwuwa yanada aure mai yiwuwa kuma baidashi, Alamunsa ya nuna nutsuwarsa da cikkekn kalamarsa, ga dukkan alamu ba mutumin banza bane,

cikin nutsuwa ta ƙarasa wajansa da sallama, ya amsa yana kallonta yanyinsa ya nuna kamar ba ita yayi tsammanin gani ba amma sai ya dake saboda karta fahimci hakan,

Bayan sun gaisa yadubeta yace "Gimbiya ganinki yayi wahala kwana nawa in aikawa ana fadin bakyannan dukda kasancewar naga shigarki ban kuma ga fitarki ba, sunna kanta ƙasa tayi sannan tace saboda babanmu baya nanne shiyasa bazai yiwu nafito ba, bai taba barina nafita ba yanzu hakama saboda dare baiyiba shiyasa Mama tace nazo naji.ko waye,

Murmushi yayi sannan yace lallai nazo a sa'a danga dukkan alamu Gimbiyar tawa nine wanda zan fara saye zuciyarta, sunna kanta ƙasa tayi kawai alamun tanajin kunya,

Gyaran murya yayi ya gyara tsayuwarsa sannan

ya dubeta yace "dafarko dai sunana malam Rabi'u, ni ba mazuanin garinnan bane aiki ya kawoni, kamar yanda kika gani ni ba yaro bane ba sannan bana kuma da aure ba wasa bane ya kawoni gareki, ganinki nayi kun fito daga wani shago yayinda nake ƙokarin komawa gida daga wajan aiki, ko lokacin na biyoku amma baku tsaya ba, hakan ya ƙara bani kwarin gwuwar binku domun tarbiyarku tayimin, tun alokacin naji kin kwantamin araina kuma aurenki zanyi, nayi ta aikowa bansamu ganinki ba zakiyi mamakin yanda akayi nasan sunanki toh tambaya nayi aka sanar dani, lokaci zaki bani mu fahimci juna sannan saina samu mahaifinki muyi magana dashi, idan kin amince amma zam baki lokaci kije kiyi tunani tukunna sannan zan dawo dan samun amsa naji yanda muka tsaya sannan da yanda zamu daura,

Ki ɗago idonki ki dubeni yanda zaki yi tunaninki da kyau dan bana tunanun kin kalli fuskata nasan ko gobe muka hadu bazaki iya ganeni ba, kasa ɗagowa

tayi ta dubeshi sai kawai tace "zan koma kar mama taga na daɗe,

Ok shikennan yanzu ki bani lambar wayarki in sha Allahu zan kiraki sai naji mai kika yanke idanma takama nazo nasamu baba ne kafin komai ya dai-dai ta sai nazo ma sameshi, lambar ta faɗo masa ya naɗe a wayarsa sannan ya mata sallama yatafi,

Bayan yatafi tashiga ta shaidawa mama yanda sukayi da wannan mutumin, mama tace" toh Allah ya zabarda mafi alkahiri, amma tunda naji yayi maganar auren sai hankali na kwanta tunda ya nuna mana cewa bada wasa yazo ba"

Bayan baba ya dawo mama ta shaida masa batun wannan mutumin da yazo wajan halima, Baba yace "idan yasake zuw ata aikoshi wajena muyi magana, dama nafaɗa miki har indai ta samu miji aurenta zanyi bbu amfanin zamannata har indai mun duba munga cewa mutumin kirki ne kuma tana sonshi zamu bashi ita Allah ya zaɓar mana mafi alkahiri mama ta amsa da amin,

Washe gari Sawwama ta shirya komaw agidanta mama da baba sunyi mata faɗa sosai, da dare yayi sadam yazo ɗaukanta haka tatafi cikeda kewar iyayenta da ƴan uwanta" shikuwa Sadam yau take sallah dan sai wani annashuwa yakeyi fara'arsa ta kasa ɓoyuwa,

saida ya biya yayi musu sayayya kananun abubuwa da zasu buƙacesu zuwa safiya sannan suka nufi gida,

Dake an rigada an kai komai da komai daga ita sai yaranta hakan yasa ta ɗauki hameeda ya ɗauki hamdan sukayi ciki ajiyesu yayi sannan yadawo ya kwashe sauran kayayyakin yakoma ciki,

Ajiye kayan yayi haɗeda fadin wash, kallonshi tayi tace "sannu ka gaji koh? gyada kansa yayi yace eh amma babu komai gabaki daya gajiyata yau zan sauketa, basarda zancen tayi tace ɗan taimakamin da Hamdan mu kwantar dasu ko zasuyi bacci,

Miƙewa yayi yace barsu kawai zuwa jimawa, yanzu kiyita mahaifinsu tukunna dan yunwa nakeji yafaɗi yana shafa cikinsa" ki shiga kitchen ki nema min abunda zanci, toh tace samnan ta miƙe tashiga kitchen" tana cikin aiki taji an rungumota ta baya lumshe idanuwanta tayi yayinda tsikar jikinta tabzuba yarr, wuyanda yabi yana shaƙar kamshin da jikinta yakeyi sumbatar wuyanta yafayi cikin wani irin yanayi saurin saurin kwace jikinta tayi tace"yaya Sadam bakaso nagama aikinanna koh? Kabarsu hamdan su kadai a falo, iska mai karfi ya furzar yace " toh gama da sauri ina jiranki,

jallof din taliya da kifi kawai tayi ta juye a plate da zafinsa tayi falo wasa yakeyk da yarnsa akan kujera yana ganinta ya sauko ƙasa yabarsu a sama, bspoon guda biyu tasaka sai ta dakko kwalin lemo acikin wanda suka saya yanzu ta zuba masa itakuma ta zubawa kanta zallan nadara tayi ta zauna suka fara cin abinci, taɗauki cup na madarar takai bakinta dubanta yayi yace"anyiwa yarana wayo munacin abinci sukuma basa cin nasu abincin, daukosu kibasu abincin, ban fara basu abinci ba tabashi amsa a takaice, No ba abincin da mukeci nake nufi ba abincinsu, mƙewa tayi yace"ina kuma zakije?

Madara zan haɗa musu, No dawo nan ba madarar zaki basu ba ina nufin shi shayar dasu, narai-narai tayi da idanuwanta sannan tace" yyaa Sadam bafa yunwa sukeji ba kuma ba kuka sukayi ba, Ke idan kinajin yunwa kuka kike? Zonan ki zauna ki shayar dasu, turo bakinta tayi ta zauna bata daukesu ba, yace "Sawwamaty aina kika koyi taurin kai? Hannu ta sanya ta dauki hameeda tace ba taurin kai bane fa kawai dai idan suna tsotso dayawa zafi yakemin, Yace "eyyerh sannu amma duk da haka ai baza'a barsu haka ba, ɗaga rigarta sama tayi ta sanyawa Hameeda nono abaki, Sadam yace "ɗan ƙara daga rigar sama bana kallonku, murmushi tayi sannan tace "oh dama dan ka ganni kasa nabasu mama?" girgiza kai yayi yace idan gani nakeson yi rigar zan cire gabaki daya, kawai dai inaso naga kina shayar dasune, ɗaukan cup tayi takai bakinta ya tsura mata, gira daya da ɗaga masa sannan ta tambayeshi mai yake kallo?" iska ya furzar a bakinsa sannan yace tunani nake shin da wanda kikesha da wanda kike bawa yarana wanne yafi kauri, laaa lallai yaya sadam dan Allah yaushe kadawo haka? Tafaɗi tana dariya,

Bude baki yayi sannan yace "ni dama na dade ahaka, kece dai inaga baki sani ba, amma yanzu yakamata na sanar dake,

Jijjiga kai tayi tace "yakamata kam, Oh kena kinsan yakamatan kenan koh? toh tashi mushiga daga ciki, ɓata fuska tayi tace "ni bahaka nake nufi ba, haɗe rai shima yayi yace "nikuma haka nake nufi,

Miƙewa tayi da hameeda tace "barina shimfiɗata tayi bacci dasauri tashige ciki."

✔️ote

Comment

Follow

Share plss

To be continued

Zaynab Alabura

💞

    people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click