《ƘADDARAR RAYUWA》K page 64

Advertisement

**

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by

zaynab bawa

#Follow me on

"

Marubuciyar

*BIBIYATA AKEYI*

* Y'AR FARI*

* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 64

Kallo mummy ke yiwa sadam mai cikeda zargi, sadam dake cire takalminsa a kofar palour ya karasa shiga ya zauna gefen mummy, harara mummy taci gaba da watsa masa, kawarda kansa gefe yayi kamar baiga irin kallon da mummy take masa ba, harararsa ta sake yi tace yanzu-yanzu zaka dawo shine ka wuni zubur? Daga isowarku ka sanya kai ya fice a cikin gidannan kace yanzu zaka dawo bakai ka dawo ba sai yanzu, ana tausayinka baka tausayin kanka, ka fife ka tafi can wajan wannan yarinya, ni mahaifiyarka ma baka daukin ganina amma ka tafi can wajan matarka ka zauna, murmushi sadam yayi yana fadin mummy dai bazata canja ba, a fili kuma yace mummy nifa ba wajanta naje ba, sai da magrib zanje na dubata in sha Allahu, yanzu wajan najeeb naje muka fita daga nan kuma mukayi wajan sauran abokananmu dake mun dade bamu haduba shiyasa na dade, dadi mummy taji cikin ranta tace au ai na dauka wajanta kaje tunda mu baka daukin ganinmu sai ganin matarka da yaranka, girgiza kai sadam kawai yayi, halin mummy bai canza ba izuwa yanzu yaci ace tana kaunar sawwama kodan jikanun data haifa mata, amma har yanzu dai tanan nan tana kishi da ida, baiga abu acikin ganin matarsa da yaransa ba bayan tsawon lokaci, yaransa kanka da baitaba sanyasu a ido ba sai awaya tayaya za'ace ma bazaizo ganinsu ba?

Mummy tafiye son kai dayawa itafa murna tafara yi alokacin data ganshi yayinda farin cikinta yakasa boyuwa, afili ta gwada daukin ganinsa hakan ba laifi bane sai idan shine ya gwfa daukin ganin nasa yaran yazama laifi Allah ya kyauta,

mummy jin bayanda take zargi sadam yaje ba sai hankalinta ya kwanta dan kuwa harta cika tayi famm tana jiran daowowarsa, kafin yadawo sai bambami take tana fadin ko abida da take mace bata nemi kallon mahaifanta ba zama tayi ta huta amma shi yafice bazai iya zama ya huta ba sai yaga matarsa,

Ajiyar zuciya ta sauke tace idan kabari hakuta na yau zuwa gobe ma ai zaka samesu basai kafita da magriba ba tunda kasan lokacin dawowar dadynku ne kuma yanata daukin ganinka sai abari zuwa gobe dan ba guduwa zasuyi ba, shiru kawai sadam yayi dan wasu lokutan fadan rashin gaskiyar mummy daure masa kai yakeyi miqewa yayi batareda yace ko komai ba yanufi fridge yadauki ruwa mai sanyi ya kafa kai saida yaji kansa yafara nuyin kafin yacire goran, cikin zuciyarsa yana fadin yadawo kuma kenan zai cigaba da fuskantar jaraba irinta mummy iya zamansa ya auna shi baiga wani laifin da sawwama tataba yimata, laifinta guda daya shine data kasance yar gidn takalawa,

Kasancewarta talaga shine abunda yaja mata tsanana wajan mummy, wannan kuma daliline maras ma'ana, wannan ba dalili bane da zaisa aqi dan adam ba domin bbu wanda yyiwa kansa arziki Allah shine mai azirtawa,

Abida tana ciki tana bacci saida ya dade da dawowa kafinnan tafito, zama tayi kusada mummy tana fadin kai badai gajiya ba,

Mummy tace aikin kyauta da kika kwanta kima huta gashinan shi ai ficewa yayi bai dade da dawowa ba,

Abida tace ai mummy kinsani kema wannan matsiyaciyar da ta tada masa hankali ya sanya muka dawo babu shiri ita zai fita gani, mummy tace nima haka nayi tunani amma ba ita yafita gani ba wajan abokanansa yaje, tabe baki abida tayi tace yanda yafada miki ba mummy ai ko can yaje bazai cemiki can yaje ba, hade rai sadam yayi yana hararar abida sam ita batada kawaici irinna sawwama, ita sawwama a kullum bata taba sanya kanta a abunda yashafi abida tana tsayawa iya matsayinta amma ita abida batada damuwa kullum daya wuce sawwama, dan qaramin tsaki yaja bbu wanda ya jiyoshi ya zauna a gefe can mummy ta dubesu tace ku taso na shirya muku abinci a dining dama jira nake abida tatashi sai muci gabaki daya, sadam ne yafara miqewa ya nufi dinning suma suka bishi abaya su duka suka nufi dining din,

Advertisement

Mummy ce tayi serving nasu duka,

sadam yafara cin abincin batareda ya tanka ba ya koshi amma haka yaketa durawa cikinsa abincin domin gudun magana daga wajan mummy dan yanzu saita zargi yaje wajan sawwama yaci binci ne,

kuma dadin dadawa ya dade sosai baici abincinta ba,

Farin ciki ne fall a fuskar mummy cikin fara'a take dubansu ita kanta tayi farin cikin ganinsu dukda kasancewar bataso dawowarsu a wannan lokaci ba amma taurin kan sadam babu yanda ta iya dashi,

Mummy tadubi sadam tace bansan me kadawo yi awannan kasar ba a yanzu aida ka karbi wannan upper kafara aiki nan gaba saika nemi hutu kazo idan munason ganinku basai mubiku can ba?

Sadam ba kowa ke samun irin opportunity din da kasamu ba amma ka watsar anya sadam wannan taurin kannaka zai haifar maka abu mai kyau kuwa? Yanzu za'a hanaka abu amma zaka nace saika aikata, sam da bahaka kake ba haduwarla da wannan yarinya yasa kadawo haka, duk wani cigaba a rayuwarka baka sonsa, irin wannan zama da ita bai kareka da komai ba,

Abida ne ta karbe zancen da fadin wallhy Allah mummy karkiga yanda dady yasha wahala kafin ya sama mana wannan damar da mutane dayawa suke nema amma basu samu ba, shi fir yaqi haka ya rufe idanuwansa ya sanya kafa ya shure ya tada hankalinsa shi zai dawo nan yabar matarsa da yayansa, bazai iya zama acan ba har sai dai in matarsa zata dawo mu zaune tare, abida ta rangwabar dakai tace kuma fisabilillahi mummy ta yaya za'ace mutafi da ita can? Bawani karatu fa tayi ba bare ace itama a sama mata aiki nikuma bazanma iya barin dadyna ya sama mata aiki acanba, abida tacigaba da fadin bbu irin kyautatawar da bana masa amma haka ya rufe idonsa ya nuna cewa abunda nakeso bashi yakeso ba kuma fa mummy da duk karshen shekara zamu ringa zuwa hutu,

Cikin takaici mummy tace wannan abu ai nayi baqin ciki abida ba kadanba ko su wanda suke zaune acan sai kace wanda ba rayuwa sukeyi ha ina wanda suka bar iyalansu gabaki daya suke zaune acan lokaci-lokaci suke dawowa,

Sadam ya dubi abida cikin bacin rai yace har indai kinason zaman lafiya dani ya kamata kisan yanda zaki zauna dani batareda kin soki abokiyar zamanki ba, ita bata damu da rayuwarki ba amma ke kullum cikin sukarta kike, kuma idan mummy tana min magna karki sake sanya bakinki dan ranki zai baci ya karashe maganar cikin bacin rai, abida zatayi magana mummy tace kingani yi shiru tunda bayaso idan ina masa magana kina saka baki ki daina, duk wani abunda mijinki bayaso kidainayi a kullum ina koya miki yanda zaki zauna da mijinki lafiya, turo baki abida tayi tace mummy da mukaje wancan kasar fa baya saurin bacin rai amma kiga yanzu ina kiran waccar kazar harya fara yimin masifa, mummy ni shiyasa banma so dawowa ba,

Mummy ta dafa abida tace yi hakuri ki barni dasu ni banaso kina samun matsala da mijinki,

Juyawa kansa mummy tayi taci gaba da bambamci Sadam baice komai ba saima zallan cin abincinsa da yake yi yagama ya tashi ya qara ce musu komai ba,

Dady bai dawo ba sai magrib ganinsu su sadam yayi farin ciki sosai, masallaci kawai sukaje suka dawo suka zauna anata hira,

Mummy kuwa qoqari take tayi saboda kar sadam yafice zuwa wajan sawwama, abunda bata saniba shine koda batayi qoqarin hanashi fita ba, ba zuwa ko'ina zaiyiba sai washe gari,

Advertisement

shi kawai a halin yanzu yana bukatar ya kebance yayi waya da sawwama,

Gabaki daya hankalinsa ya koma kan wayarsa,

Tun kafin yadawo ya rigada ya ayyana aransa cewa duk ranarda yadawo aranar zaiyi bacci tareda matarsa da yayansa toh tunda hakan bai samuba sai ya kudirta raba daren yau gabaki daya yana jin muryarta, idan yayi hakan yana tunanin ko wani abun zai ragu daga kewarta dayake ji."

Danna switch din wayar yayi tayi duhu yadan jaa kasa ua jingina sannan yaja siririn tsaki a hankali ya runtse idanuwansa,

Dady ya dubi sadam yace yakamata ku tafi gida ku huta yanzu dare yayi Allah yakaimu gobe weekend ne sai mu sha hirarmu dakyau, mummy tace gidansu ba agyare yake ba domin nasan yayi kura sosai samada shekara ba'a kwana cikinsa ba, danma kwanaki natura su hassana da hussaina su gyarashi, dady yace toh ai saisu kwana anan din zuwa goben in Allah yakaimu sai agyara musu addudduba shi dakyau, dan gida shekara bbu kowa aciki kai tsaye baza'a shiga akwana ba,

Miqewa sadam yayi yace saida safenku ni barina shiga na kwanta, mummy tayiwa abida ido akan tabishi dasuari ta miqe tace nima natafi mummy tace toh ahuta gajiya, yana shiga abida ta biyoshi abaya, kallonta yayi yace ke ma baccin zakiyi yanzu?Abida tace A'a bana wani jin bacci mummy ce tace na biyoka kai kawai ya gyada yashiga toilet yayi wanka yafito ya sameta tana danne-dannen waya,

Wayarshi ya sanya hannu ya dauka yafice zuwa corridor ya zauna yayi dialing numben sawwama ringin biyu ta daga kamar wacce dama jiran kirannasa takeyi,

Sallama tayi cikin zakin muryarta ya amsa hadeda lumshe idanuwansa saboda yanda muryarta ta isa izuwa kowane sassa na jikinsa lokaci daya wata nutsuwa da kasala ta sauka masa,

Ajiyar zuciya ya sauke hadeda fadin bakiyi bacci ba?

Sawwama acan gefenta ta gyara kwanciyarta sannan tace uhm!

Yace toh meyasa?

tayaya zan iya bacci? Bayan kewarka gabaki daya ta baibayeni, cikin zolaya sadam yace toh kona zone? Saina rage miki kewar tawa,

Zaro ido sawwama tayi tace yaya sadam rufamin asiri karka fito a wannan daren, afili sadam yace matsoraciya ni bawai daren bane bbu wani abun har indai zan samu ganinki kwata-kwata fa yanzu goma bata wuce ba,

Shiru sawwama tayi kamar mai tunanin wani abun can kuma sai tace toh kazo, da mamaki sadam yace inzo koh? Inzo kikace? Sawwama tace eh kaso amma da sharadi! Na yarda amma wani irin sharad'i ne wata yar qaramar dariya sawwama tayi tace sharadin shine idan kazo babu wani abunda zai faru tsakaninmu nida kai, bata rai yayi kamar kamar tana ganinsa yace wannan wane irin sharadine? Gaskiya ni ban yardaba, dariya sawwama tayi tace yarda na nawa kuma aika rigada ka amince tun farko, sadam yasha mur yace nafasa zuwan, dariya sawwama tayi tace dama abunda zai kawo ka kenan koh? Sadam yace no bahaka bane kawai dai ai kinmin wayo ne amma idan bahaka ba ta yaya zaki sani nafara yimiki alqawari kafin ki fadi bukata, kawai dama bakyaso nazone shikennan kuma nayi zamana, dariya sawwama takeyi ciki-ciki jin yanda ya kule sai wani magana yakeyi a kumbure, uhmm toh Allah yabaka hakuri ni bada nufi nayi ba sawwama tafadi cikin zolaya, sadam yace da sannu zaki shigo hannu na tunda abun zolaya ma zame miki, kamar wanda yake kallonta ta sanya hannu ta rufe bakinta tace zolaya? a'a wace ni da zan zolayeka, nisawa yayi sannan yace ke rayuwata ce! Matata! Uwar y'ay'ana, ke komai ce a gareni, duk wani mukami a rayuwa da namiji zai iya bawa mace a cikin zuciyarta to ni ke nabawa, ke ce sarauniya ta! Matsayinki yafi matsayin sarauniya, darajarki tafi darajar lu'u-lu'u a wajena kinga kuwa ke komai ce, ki zolayeni a duk lokacin da kikaso ko kika ji bukatar hakan domin hakan ya tabbatarmun da kina cikin nishad'i, ganinki da jinki cikin nishad'i a kullum shine muradina, shiru sawwama tayi tana sauraronsa yayinda zuciyarta take bugawa da karfi da karfi, cikin sanyayyar muryarta ta furta shin a wannan zamani za'a samu maza irinka kuwa yaya sadam? Kai din na dabanne komai naka na dabanne, murmushi yayi yace banace ba amma ke kam irinki inada yaqinin cewa baza'a samu ba,

Nisawa tayi sannan tace a duk lokacin danake tareda kai nakan jini wata daban a lokacin nakan tabbatar da cewa nima mutumce kamar kowa soyayyar da kake bani takansa na manta da komai naji kai kadai nake fuskanta arayuwata kaine abu mafi kyau, mutum mafi kyawun mu'amala a duniya gabaki daya kaine, ina farin ciki kasancewata matarka, murmushi sadam yayi yace duk da hakan amma ai kin hanani zuwa wajanki, turo baki tayi kamar yana ganinta tace ni ba hanaka nayi ba, abunda kika aikata dai-dai yake da hanawa sai dai kawai kin biyo ta wata hanya ce daban, sawwama tayi dariya tace yanzu da badan dare yayi ba da kazo ai, ina mai maraba dakai a kowanne lokaci,

A'a na hakura tunda dama ai bakiso nazo dinba nima zan jaa ajina tukunna, sawwama tace au ni dauka ai duk ajinnnaka ya sauka yanzu! No bai sauka ba dasaura tukunna yayi magana yana shan iska."

Sun dauki tsawon 2hours suna waya sai da hameeda tafarka tana neman mamanta kafinnan sukayi sallama ta dauki yarinyar dan ta shayar da ita."

Juyawarsa kenan sukayi ido biyu da abida ta cika tayi fam sai wani huci take sadam saida yaji gabansa yafad'i rass amma haka ya dake ya raba da gefe ya wuce a kufule abida tabi bayansa."

Dalilin dayasa bakwa samun post kullum saboda dayawa basuson nadawo rubutu ba, d'an lokacin da nake jaa lokacin wasu suke sanin nadawo, nafiso tun kafin nayi nisa a typing wanda dacan suke karantawa yanzu basu faraba ya isa garesu, yanzu dan Allah idan kina karanta book dinnan kikaga nayi posting ki turashi izuwa wasu groups dan masu karantashi susan andawo rubutunsa."

✔️ote

Comment

Follow

Share plss

To be continued

Zaynab Alabura

💞

    people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click