《ƘADDARAR RAYUWA》K page 63
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 63
Washe gari ma haka sawwama tatashi tun safe take aikin kiran wayar sadam amma yaqi shiga, gashi batada phone number na abida da tana dashi tabbas zata kira taji dalilin dayasa sadam ya kashe wayarsa, har indai taji ba wani abun bane yafaru toh hankalinta zai kwanta,
Sake-sake take tayi acikin ranta abubuwa kala-kala suke zuwar mata da wanda ya kamata da wanda bai kamata ba, sai takeji kamar taje gidan mummy ko zata samu lamarin sadam, amma sanin yanda suke da mummy ya sanya sam batason su hadu, aduk ranarda zata hadu da ita kokuma zasuje wajanta gabanta ya dinga faduwa kenan zuciyarta ta ringa dar-dar kenan, saurin kawarda tunanin zuwa gidan mummy tayi cikin ranta domin tasan koda taje bazata iya fadin dalilin zuwannata ba, idan harko ta iya fadi to sai tasha bakaken maganganu wajan mummy."
zaune suke dukansu cikin gida suna gyaran shinkafa da mama da halima sauran sun tafi makaranta halima kuma tagama makarantar dake tsakaninta da sawwama bbu wani nisa suna aiki suna taba tadi amma sam hankalin sawwama baya garesu kana ganinta zaka fahimci hakan domin kuwa hannunta na cikin shinkafar amma wasa kawai takeyi da ita, tunaninta yana wani waje can na daban, daya hannun kuma riqe yake da waya takasa koda saka ta caji sai faman kiran wayar sadam kawai takeyi dill-dill wayarta ta dauke alamun ba caji dan tun datsu take sanar da ita cajin ciki yazo karewa,
ajiyar zuciya ta sauke wanda yajawo hankalin mama gareta, kallonta mama yayi cikin kwana biyu duk ta canja da dan fadawa fuskarta tayi, hannu mama ta sanya ta dafa hannunta sawwama ta dago ta dubi mama,
Mama cikin kulawa tace lafiya dai hafsatu? Girgiza kai sawwama tayi tace ba komai mama kawai hankalina na wani wajanne,
Mama tana shirin magana bata kaiga furta komai ba suka jiwo karar zubewar abu hankalinsu suka maida wajan karar, hamdan ne ya juye garin tuwo a jikinsa gabaki daya yayi wani butu-butu kamar aljani, mama tace oh ni wannan yaro yanzu dan Allah kiduba yanda yayimin da gari! Toh ku dauke danku kona dakeshi, dasauri halima tatashi ta daukeshi mama tace wannan yaro idan yafara rarrafe ko tafiya kika kuskura kika bar wani abun amfani kusa tass zai baras miki dashi, rawar kaine dashi, ita dai yar uwarsa babu ruwanta shiru abunta amma shi kansa gilgilwa yakeyi, yana zaune yake jaaa yaje yayi ta'adi wannan yaro zaki shafa da ta'adinsa, sai dai Allah ya rufa asiri, mama taci gaba da fadin yayi kamar uwarsa amma bai dauki halinta ba uwarka sam batada kiriniya,
Halima ta turo baki tace mama toh duk me yakawo wannan maganar akan dan garin tuwon daya zubda, mama tace eh yoh kyace dan gari mana tunda ku y'ay'anku basa laifi,
tunda nawane kuwa ai yazama dole na tanka, murmushi kawai sawwama takeyi tana kallonsa,
Mama tacewa halima sai ki masa wanka kafin garin ya shige masa ido ya damemu da rikici, flask halima tadauko na ruwan zafi ta sirka ruwan ta wankeshi ta canja masa kaya suka dawo ta ajiye ta sanya hannu cikin gyaran shinkafar da sukeyi, mama tace kinga tashi ko gyaramin wajanda ya bata sannan ki dagamin shi anan karya sake wata barnar,
Advertisement
Mikewa halima tayi ta kwashe garinda ya zubda dake a sminti ne bbu kasa kuma ashare yake tass sake tankadewa kawai za'ayi sannan ta sanya tsintsiya ta share wajan, ta dauki zanin goyo ta saba hamdan a baya ta goyashi sannan ta nemi waje ta zauna sukaci gaba da aiki suna dan taba hira,
Yarone ya shigo da sallama mama ta amsa! Ya gaida su sannan yace wai sadam yana sallama a waje, mama tadubi sawwama tace kinji yaronnan kaman sadam yakira koh?
Sawwama tace eh nima haka naji mama tace toh dama yana hanya ne kokuwa? Sawwama tace mama bansaniba dan wayarsa bata shiga, mama tacewa yaron kace masa ana zuwa,
Mama tadubi halima tashi kije ki dubo ko shi dinne aiko da mamaki zuwa haka katsam dawowa daga wata kasa sai kace wanda yadawo daga anguwa, sawwama ita dai batace komai ba zuciyarta sai bugawa takeyi da sauri da sauri,
Halima ta dawo tace aiko mama shi dinne wallhy mama tace ikon Allah je maza ki shigo dashi, sawwama kasa motsawa daga wajanda take tayi, jin abun takeyi kamar wani almara,
Sallamar sadam ne ta daki dodon kunnuwan sawwama da sauri ta dago kanta yayinda idanuwanta sukayi arba da fuskar da da dade tana muradin gani batasan lokacin da wani murmushi mai sauti ya subuce akan labbanta ba,
Mama ce dake fitowa a dakinta ta sanyo hijabi amsa sallamarsa da fadin wa'alaikassalam , a dan nesa dasu ya durkusa har kasa ya gaida mama ta amsa da fara'a tanai masa sannu da hanya, sannan tadubi halima tace ki kaishi dakin hafsatu saikizo, mama tana shiga daki ya kai kallonsa izuwa sawwama wacce itama shi din take kallon takasa dauke idanuwanta fuskarta yalwace da annuri, fara'arta takasa boyuwa,
Murmushi ya sakar mata fuskarsa dauke da tsantsan soyayyarta,
halima ce ta ce yaya sadam muje ciki mikewa yayi fuskarsa nakan sawwama yabi halima suka shige ciki,
Sawwama takasa motsawa daga yanda take saida mama tayi mata magana sannan ta miqe ta nufi dakin hannunta dauke da hameedah, itakuma halima tafito bayanta goye da hamdan tashiga dakin mama tabata kudi tace tasiyo lemo da ruwa,
Da sallama sawwama tashiga dakin ya amsa idanuwansa akan kofa, amsa sallamar yayi yana mai cikeda fara'a karasawa kusa dashi tayi kan sallayar itama ya zauna da muryarta mai sayin gaske tace ina wuni yaya sadam?
Lpy sawwamaty ya amsa da sauri, turo baki tayi sannan tayi narai-narai da idanuwanta tace yaya sadam meyasa zakamin haka? Kasan halinda nashiga kuwa?! Tayi magana hawaye ya qarasa gangarowa akan fuskarta cikin zazzakar muryarta mai sanyin gaske tace na kiraka na kira wayarka bata tafiya gashi kuma kai baka kirani ba bana kusa dakai bare nasan halinda kake ciki zuciyata tashiga damuwa,
Ido sadam ya zuba mata a hankali ya sanya hannuwansa ya matso da ita kusada shi ya kamo fuskarta ya sanya harshensa ya dauke hawayen dake kan fuskarta runtse idanuwa sawwama tayi yayinda takejin wani irin yanayi ajikinta saida yagama dauke hawayen fuskarta gabaki daya sannan ya sauko da labbensa izuwa lips nata cikin nutsuwa yafara kissing nata sun dade ahaka saida ya tabbatar zuciyarta tasamu nutsuwa sannan ya saketa a cikin kasalalliyar murya ya rada mata a kunne kiyi hakuri sawwmaty banyi hakan dan na saka zuciyarki cikin wani yananyi ba, naso nayi suprising dinki ban yi zaton abun zai dauki har 3days ba, amma ki yafeni bazan kara ba, ki cire zuciyarki cikin kunci sadam dinki yadawo gareki, hannu ta sanya a hankali ya tsagayeyi ta rungumeshi dakyau ta kwantar da kanta a kirjinsa tanajin bugawar zuciyarsa a hankali take saukar da numfashi, su biyun duka ya hada ya rungume harda hameeda wacce sai kallonsa takeyi a waya tasaba kallonsa yau sai gashi a fili, sallamar halima ce ta katse musu yanayin da suke ciki da sauri sawwama taraba jikinta da nasa taja gefe shikuma, halima tashigo ta ajiye masa lemon dake hannunta da ruwa da cups sanya hannu yayi ya dauki hameeda halima ta kunto hamdan tabashi suka qara gaisawa sannan tafice tabarsu, sawwama ta dauki cup ta bude lemo ta zuba ta miqa masa tace yaya sadam ga lemo, sadam daya zubawa yarnsa idanu yana kallonsu ya dago ya kalleta cikin yanayin zolaye yace nikam nasha lemon daya kamaceni yafadi yana lashe lips dinsa kawarda kai sawwama tayi dan tasan abunda yake nufi ta ajiye lemon gefe ta zuba masa idanu."
Advertisement
Ya maida kallonsa izuwa yaransa yana murmushi har farcen hannunsu da kafafunsu saida yabi ya dudduba, kamannin fuska ne kawai suka dauko na mahaifiyarsu amma dai-dai da gashin kansu irin nasa ne, suma yaran kamar wanda suka san mahaifinsu ne ya dawo bayan tsawon lokaci sai wasa suke ajikinsa suna dariya hameeda da bata cika hayaniya ba kawai ta zuba masa idanu iya kaci tadan kamo hancinsa can ta sake ta kamo gashinsa,
Bayan yagama kare musu kallo ya ajiyesu gefe yajawo sawwama jikinsa, lips dinsa yasake maida wa akan nata yacigaba da kissinga nata hededa wasu abubuwa masu wuyar fassaruwa sawwama bata iya hanashi abunda yake shirin yiba saboda itama tana cikin irin halin da yake ciki na kewarta itama hakan take ciki domin itma tayi kewarsa sosai,
Sanyin da sukajine ya dawo dasu daga duniyar da suka lula da sauri sawwama ta miqe tsaye domin ajike ta jita ga wani sanyi dayake ratsata kallonta takai ga hamdan ya tuntsirarda lemon da ta zubawa sadam, da sauri sadam ya dagashi domin ya bata jikansa shima narai-narainda fuska sawwama tayi kamar wacce zatayi kuka tace yanzu fa! Yanzu fa halima ta canja mai kayan nan ko minti talatin baiyiba amma harya sake batawa, murmushi sadam yayi yace yana taba gagara kenan sawwama tace ba dan kadan ba yanzu ya zubdawa mama gari kar kaso kaga yanda yayi butu-butu dariya sadam yayi yace to ai haka akeso yanzu da bayida walwala sai ace baida lafiya Toh Alhamdulillah gara yayi na wani lokacine, zaro ido sawwama tayi taje gara yayi?? Gara yayi fa kace yaya sadam! Jijjiga kai sadam yayi alamun tabbatar da kalamansa yace eh! Uhmm kawai sawwama tace ya miqa mata shi yace canja masa kaya kada sanyi ya ratsa shi, karbansa tayi ta nufi akwatin yaran ta bude tana fadin akan canja masa kaya sai 3 yayinda hameeda bata bata tun wanda aka saka musu da farko ba, sadam yace dama yaushe zaki hada kiriniyar mace dana miji??
Sawwama ta canja masa kayan sannan ta mikawa sadam ta gyra wajan daya bata ta fitada sallayar ta wanke dai-dai wajan ta shanya ta kawo wata ta shinfid'a sannan suka zauna, hira sosai sadam da sawwama sukeyi har aka kira sallar azahar sadam yafita yaje yayi sallah, yadawo anan ne yayi mata magana akan ta shirya su tafi, noqewa sawwama tayi tace yaya sadam ba yauba kabari muji mai su mama zasuce! Kaga daka sanar dani dawowarka tunda wurine da kafin ka isoma zan koma naje nayi maka shirin dawowa, hade fuska sadam yayi yace toh bagashi nadawo ba mai kuma za'a jira? Kawai nadauki matata mutafi, cikin kwantarda murya tace yaya sadam kayi hakuri ka iya hakurin shekara harda watanni ma bare dan wani kankanin lokaci da zamu kara yanzu? Nima nayi kewarka kuma yanzu banki nabika mutafi ba amma mubi komai a hankali, yanayin yanda take magana ya sanya sadam yayi dariya yace toh shikenan mujira muji abunda zasuce Allah yasa jiran namu bazaiyi yawa ba, sawwama tace in sha Allahu bazaiyiba dadina dakai yaya sadam sauqin kai, komai na rayuwa da sauqi kake daukarsa, murmushi sadam yayi yaja hancinta yace har indai mutum zai zaune da ke mai sanyin hali dole ya zamana mai saukin kai, baki furta kalamai kawai sai kin tantance su baki magana batareda ki aunata a ma'auniba kina da hangen nesa baki yanke hukubci dan son ranki toh mai zai hana bazan zama miki mai saukin kaiba? Nazama miki raqumi da akala ko jani duk yanda kikeso in sha Allahu zan biki, murmushi sawwama tayi ta sumbaci gefen kumatunsa tace inasonka yaya sadam! Girgiza kai sadam yayi yace nima ina sonki amma ni ba'anan nakeso ba, dariya sawwama tayi tace abunda kasamu ya isheka a ranar yau kabari sai kasamu na gobe, iska ba furzar yace shikenan da sannu zaki shigo hannuna,
Murmushi tayi gefen kumatunta ya lotsa tace hmm! Yace fadi abunda yake bakinki tace no babu komai, yace gara dai da kikayi shirun dan duk wani abunda zaki fada zan boyeshi a ma'auni har izuwa ranarda zakiyi bayani,
Kawarda zancen sawwama tayi tace yakamat ka huta yaya sadam saboda gajiya, jijjiga kai sadam yayi yace sauke gajiya aida sauran lokaci, shiru sawwana tayi kamar bataji abunda yace ba,
Sai yamma kafin sadam yabar gidan cikeda kewar matarsa ya yaransa, itama sawwama yabarta da kewarsa."
kai tsaye sadam gidan mummy ya nufa dan saukarsa ma can ya fara sauka ya huta yayita kiran wayar sawwama bai samu ba yafito ya taho wajan sawwama, yacewa mummy yanzu zai dawo, dawowar da ba'ayita ba kenan sai yanzu da yamma liqis."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial12 Chapters
Fantasy Keychain Vol. 1
What if you bought a keychain, resembling a weapon from a fictional fantasy you like, becomes real. What would you do? After the death of his best-friend, Miki Ebisawa. Eijiro Suguha, who is a 3rd year high school student, tried to find an answer on why his best-friend was mysteriously killed the day after they went to hangout. Unfortunately, what he finds out instead is the sacred truth about his keychain and the secret society around him.
8 193 - In Serial40 Chapters
Myth of The World's Trees
And Simon answered their call with a single statement that nobody understood "Et super mos absit hoc hodie!" "Yah!" "WWWaaaaaaahhhhhhhh!" "AAAlllllaaaaallllaaaaallllaaaa!" "EeEEellllleeeeeelllllleeeeeeuuuuuuu!" I, too, yelled a battle cry at the top of my lungs. I had no idea what Simon had just spouted but from Camilla's giggling, I could guess that Simon thought that spouting nonsense was his way of getting out of the earlier predicament. "I forbid death upon this day," Camilla said. "What?" I answered a bit at a loss. "Ancient Latin," she replied smugly, "He said 'I forbid death upon this day'." I laughed aloud "Then he is gonna be really disappointed in everyone here," Camilla did not reply and instead took a deep breath. I did the same, zoning out everything in my surroundings. The environment became a world of electrical pulses traveling across several networks. I perceived the world through my lightning and sped my heartbeat to inhuman levels. I was present now, at this moment, at this point in time. I could feel the electrifying air saturating my lungs, the electrified ground vibrating at the rhythm of the approaching enemy. Then I took a step forward, everyone followed in tandem. Camilla the first, and then the others. Then I took a second step, and this time everyone followed simultaneously. Third step… Fourth step… Fifth step… Then light jogging… Speeding up… Running … Running faster…. Then suddenly, everyone disappeared into motes of light particles that re-constructed itself hundreds of feet above the horde, dozens of miles away from our initial position. We were literally 'diving' into battle.-------------------------------------------------------------------Despite a rough childhood in the slums, Omari had everything a guy could want - a loving girlfriend, an understanding sister, a wonderful teacher, and his dream job. Still, the scars from his childhood made Omari unable to live a dull life. He dreamed of something greater... something beyond the reaches of what humankind could achieve in the current era.Like always, Omari should have been careful what he wished for. In the year 2046, the World was thrown into chaos as the apocalypse came in the form of massive trees that shot up out of the ground one day.These trees towered over the tallest of buildings and had thicknesses that spanned kilometers at a time.They grew everywhere, in homes, businesses, and cities as they formed a complex network that overlayed the old world.The cause of the apocalypse was unknown, but Omari's workplace was believed to be the origin point of the unfortunate events.Fifteen years after the start of the Apocalypse... after all the pain and suffering... after losing everything he cared about, Omari sent his memories back in time to make sure that the future he lives in, never came to be.Will he be able to uncover the mystery of The Trees? Will he be able to protect all those he has lost? Will he succeed, or will his attempt be washed away by the currents of time? Will Omari be able to learn the truth about 'THE MYTH OF THE WORLD'S TREES'?
8 155 - In Serial18 Chapters
Eye of Amber
Kosian's life was turned upside down when he saw his brother being taken by men of the Faith, using words like 'cursed' and 'damned'. He did not care if his brother was the Ancient Gods incarnate -- he just wanted a friend with whom he could share his pain, his joy. And, after ten long years of planning, he is finally ready. With the help of a group of mysterious benefactors, Kosian saves his brother, fleeing their home and heading east, towards the port of Bez, accompanied by an unexpected but welcomed band of mercenaries. Meanwhile, Bel, a knight of the order Purtelis, hounds them, dead set on returning the Faith's stolen property. Both groups traverse the peaceful lands of Bollardia, each encountering roaming monsters, ancient evils and simple people, trying to survive. During his travels, Kosian is haunted by strange dreams and visions, all of which keep showing him the same image -- an eye of amber, etched with black runes. The sign of the Divided, masters of magic and saviours of the Seven Races.
8 140 - In Serial12 Chapters
A Royal Knight From Another World Got Reincarnated To Earth
Ragur, a Royal Knight from another world has passed away after defending his country against the demons. After waking up he found himself in a place where everything is white. There was a woman floating in the air who called herself a goddess. She promised Ragur that she'll reincarnate him to a place called Earth if he swears his loyalty to her. After the goddess reincarnated him to Earth, he woke up as a baby laying under a bridge. He stayed in the cold and starved there for hours till a girl came and took him to the orphanage she was raised in. When Ragur waked up again he found himself on a bed, with a girl laying next to the bed.
8 115 - In Serial14 Chapters
Hotel Transylvania
Male Mavis x Female ReaderBased on the movie Hotel Transylvania.(Y/n) = Your Name(H/l) = Hair Length(H/c) = Hair Color(E/c) = Eye Color(S/c) = Skin ColorI OWN NOTHING!!!
8 79 - In Serial10 Chapters
The Red Sun Never Sets
ABANDONED.The Cover Art does not belong to me. I found it on Google Images, but could not find the owner of the image. Credit goes to the person that drew it.I do not own any of those things above, except for the story itself.
8 183

