《ƘADDARAR RAYUWA》K Page 61
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Page 61
Da sauri tafarka daga baccin datake ganin rana tafito ya sanyata sakin salati domin ko sallar asubahi batayi ba a gaggauce tashiga toilet tafito daure da alwala tagabatar sallah sannan ta kishingida a jikin sallayar domin wani baccine a idanuwanta bata samu bacci dawuriba ba jiya da daddare tazauna tanata tunani kamar yanda tasaba tana tunanin daya zame mata jiki yazama aikin yinta a kullum, bayan baccin ya dauketa kuma saita yi wani mafarki, mafarkine mai dadin gaske wanda bata taba koda kwatanta irinsaba hakan ya sanyata makara sallar asubahi,
bata dade da kishingida ba wani baccin yasake daukarta irin mafarkin datsu taci gaba dayi gata gakuma yarima cikin hankalinsa suna zaune suna hira cikeda nishadi afuskokin kowannensu,
Suna zaune a wani waje mai yalwar furanni hadeda bishiyoyi, kana ganinsu zaka hango tsantsar farin cikin dasuke ciki a cikin mafarkin take karasawa kusa dasu, tazo daff dasu cikeda murnar ganin kanta tareda yarima a wannan yanayin, farin cikin dayake fuskartace ya gushe, annashuwan fuskarta ta canja izuwa tashin hankali sakamakon ganin fuskarta tana canjawa wani kamanni hankalintane yatashi ayayinda ta ga gabaki daya kamanninta ya canja izuwa kamannnin wata yarinya wacce bata taba ganin fuskartaba shikuma yarima ko ajikinsa kamarma baisan da canjawar fuskarba saima wani farin ciki daya karu akan fuskarsa a firgice nabila tafarka daga baccin data keyi mafarkin datayi datsu ya sanyata farin ciki amma na yanzu yabata tsoro, me mafarkin datayi yake nufi kenan? Fuskarta ta canjawa zuwa wata fuskar? Wacece wannan wacce tagani amafarkinta?
Wannan sune tambayoyin da batada amsarsu batada kuma wanda zai amsa mata, jiki a mace tatashi tashiga tayi wanka tukunna ta shirya tafara yan gyare-gyare,
Saida nabila tagama duk wani abunda zatayi na gyaran gida izuwa breakfast sannan tanufi dakin yarima dan ganin yanda yakwana, murda hannun kofan tayi tashiga da sallama duk da tasan cewa bazai amsataba, akwance ta hangoshi a katafaren gadonsa har yanzu bacci yake bai farkaba da sauri ta karasa gaban gadon tadan rankwafo tataba fuskarsa jikinsa bbu zafi ajiyar zuciya tasauke sannan a hankali tafara taba kafarsa tana fadin yarima! Yarima! motsawa yayi a hankali sannan yabude idonsa ya zubesu akanta gabantane yayi mummunan fadi sakamkon yanayin data ganshi irin yanayine mai kamada wanda taganshi ranar, kallo ne yakeyi mata kamar wanda yakeson gano wani abun tattare da ita, cikin faduwar gaba nabila tajuya dasauri niyyarta takoma dakinta tadauki waya takira umma tazo taga yanayin da yake ciki,
Caraf taci ya cafko hannunta a tsorace tajuya ta dubeshi batayi auneba taji sautin muryarsa ta daki dodom kunnuwanta,
Am sorry!
shine abunda yake kokarin ambata, dukda abunda yake fadi bai fito radauba domin harshensa kamar a harde yake amma nabila ta fahimta abunda yake shirin fada, sandarewa nabila tayi a tsaye takasa aikata komai cikin tsoro sai tsaro idanuwanta take koda sau daya bata tabaji ya ambaci wata kalma ba sai yau,
Advertisement
Saurin saketa yayi ya rike kansa,
Atake kansa yafara jujjuya masa kamar wanda ake hajijiya dashi haka yaji kawai ya sake wani irin kara a tsorace nabila tafita bbu mayafi tashi sashin mai martaba bata sameshi anan ba a firgice tayi hanyar fita sukayi kicibus da umma, umma wacce ganin nabila ahaka ya sanya itama ta rikice ta rikota tana tambaya nabila mai yasamu haaliifan? A firgice tace umma yarima yayi magana yanzu kuma ihu yakeyi umma tayi saurin sakin abunda yake hannunta tayi cikin sashinsu da gudu a haka taje ta tarasda yarima rikeda kansa yanata kuwwa,
Karasawa tayi tasaka kuka ta rikeshi gam ajikinta sai kokarin kwacewa yakeyi nabilace tayi aika akaje aka gayawa mai martaba yana faada yataso yazo yasamu abunda yake faruwa, mai martaba bai dade yana masa addu'a ba abun ya lafa ba kamar daba da sai yakusan kwana akansa ana abu daya,
Bayan yasamu baccine nabila take basu labarin abunda yafaru umma tana kuka tana fadin in sha Allahu komai yakusan zuwa karshe yarima kakusa samun lpy,
Mai martaba yace lamarin kam akwai cigaba domin ko yanzu a kankanin lokaci komai ya lafa saba'anin abaya da ake kwana ana abu daya,
Zamuci gaba da addu'a in sha Allhu komai zaizo karshe da yardar ubangiji,
Ranar umma anan takwana wajan yarima, shikuwa yarima bacci yawuni yakwana yanayi danko farkawa baiyiba."
Wazirinr gaban hajiya babba a zaune ya gurfana kamar mai shirin yimata sujjada,
Kana ganin hajiya babba kasan a kufule take ranta yana bace sosai,
Hajiya tadubi waziri cikin takaicin dake cinta arai tace waziri kanason 6atamin aikina, kanason cusamun bakin ciki, yaushe har kayi saken da har akakai wannan matakin?
Ashe idan bana saka idanuwa akan lamuran nan shikenan zaku barsu su tabar bare?
Ashe ni ban kai ku tsayamin akan abuba kenna kuyimin abubuwanda suka kamata ba?
Jiya nayi kwanan bakin ciki!
Naji bakin ciki da sako ya isoni wai haalifa yafara magana! Saida ta jaa numfashi mai cikeda huci da zafi tace nadade arayuwata banji bakin irin najiya ba,
Inaso kayimin bayani yaya aka samu akasi haka tafaru?
Waziri yayi kasa da kansa yana fadin Allah ya hyci zuciyarki ranki shi dade Allah yaja zamaninki yaja kwananki da girman kujerraki, bbu ke bhu faduwa har abada, bbu ke bbu kara shiga bakin ciki irinna wanna karon har abada, hajiya tace ba wannan nakeson jiba yaya akayi haka tafaru?
Lokacin sabunta aiki yayi ka sabunta ko baka sabunta ba?
Waziri yafara kame-kame yana fadin ayimin afuwa ranki shi dade tabbas lokacin sabunta aiki yayi amma bansan mai ya sha'afar daniba,
Hajiya babba tace ka sha'afa?
Me hakan yake nufi kenan? Aikin da ake yinsa shekara da shekaru dimun da'iman shine yanzu ya sha'afar dakai?
Advertisement
Waziri ya kwantarda kansa yana fadin Allah yahuci zuciyarki Ayimin rai, hakan bazata sake faruwaba gobe-gobe zan sauka a wajan aikinann,
Hajiya cikin fushi tace yau basai gobeba idan aka sake samun matsala irin haka zanyi maka horonmak bala'in tsanani ,
Waziri yayi kasa dakai yace makamancin haka bazata sake faruwaba ranki shi dade,
Hajiya babba tace da dai yafi, kuma ka taimaki kanka,
Hajiya tace dalilin dayasa banaso na hada maka aiki biyu lokaci daya kenan saboda ka maida hankali akansa kada asamu matsala, daya aikin da mukayi magana dakai ranar asamu wanda zaija ragamarsa amma ba kaiba dan banason sake samu akasi duk karancin ko yaya yake banaso,
Waziri yace yanda kikace hakan za'ayi,
Ran hajiya babba yabaci sosai da sosai batayi zaton wannan sakacin daga wajan waziri ba saboda yafi kowa maida hankali akan aiki,
Waziri yatashi yatafi aranar yayi shirin barin kasar dan sabunta aiki."
Hajiya suwaiba itama anataa wajan hankalinta ba karamin rashi yayiba da labarinnan ya isota, aranar ta nemi yaya hadiza tace mata duk yanda za'ayi ayi kuma duk yanda zata fita tafita taje ta nemi musu wanda zai share musu hawayensu dan wancan yayi sake har yabar yarima yafara magana, aikuwa hakan akayi aranar yaya hadiza tayita yawon nema musu wajanda zasuje a aranar tasamu amma sai dai ba'a gari bane kuma wajan da nisa, tana fadawa hajiya suwaiba washe gari suka kama hanya."
Cikin kwanaki kadan jikin yarima yasake rikicewa jikinsa yayi tsanani dayafi na baya sosai,
Murnar su Umma takoma ciki yayinda labarin rikicewar jikinsa ta isa izuwa ga hajiya babba sai alokacin hankalinta ya kwanta,
Itama hajiya suwaiba anata wajan zatonta nata aikinne yaci har ya dawo da yarima haka,
Waziri ne gurfane gaban hajiya babba kamar wanda yake shirin yimata sujjada, cikin kaskantar da kai dakuma girmamawa yace Allah yaja zamaninki Ranki shi dade, hannu kawai hajiya ta dagawa waziri nufinta ba haka takeson jiba,
Waziri ya fahimci yanda hajiya babba ta dosa cikin son ya birgeta yafara fadin Hajiya anje an sabunta aiki wannan karon aikine akayishi na hakikanin gaske matsalar da muka samu wancan karon baza'a sake samun makamanciyar hakanba,
Hajiya babba ta gyada kai cikin gamsuwa da zancen waziri domin kuwa labari ya iso gareta irin yanda jikin yarima ya koma,
Waziri ne ya katse mata tunaninta da fadin wani hanzari ba gudu ba hajiya wannan yarinya matar sa izuwa yanzu yakamata ace mun san yanda mukayi da ita, tunda har tatafi tadawo hakan yana nufin itama zai iya samun wani taimakon daga gareta toh amma idan muka kawarda dagabaki daya daga gareshi, zamu samu daya daga cikin iyalanmu tashiga a matsayin mata gareshi aikinmu zaifi tafiya yanda mukeso komai zai tafi a yanayin tsaronmu zai kasance babu wata fargaba a tattare damu duk wani abunda muke bukata zamu sameshi cikin sauki, nunfashi hajiya babba taja sannan tace"
Nabar komai a hannunka duk wani abunda yakamata ayi toh ayishi, cikin girmamawa waziri yafice daga wajan hajiya babba."
Umma zaune bakin gadon da yarima haliifaa yake kwance idanuwanta cike da hawaye tana kallonsa cikin ranta sake-sake takeyi tunanin bbu irin wanda baizo cikin ranta ba,
Daga hannuwanta biyu tayi sama tace Allah Allah abunda ta iya fadi kennan kuka yayi kokarin kwace mata saurin toshe bakinta tayi da hannunta a hankali taci gabada rera kukanta gwanin tausayi wannan al'amari na yarima izuwa yanzu yaci ace idanda sabo ta saba toh amma ta yaya?
Ta yaya uwa zata saba da ganin d'anda ta haifa acikinta cikin wahala? Wannan abune wanda bazai taba yiwuwa ba koda idanuwanta sun saba da ganinsa cikin wannan halin zuciyarta bazata iya sabo da ganinsa ahaka ba,
Akoda yaushe idan ta kalli yarima haliifaa cikin wannan hali rayuwarsa ta baya ke sake fad'o mata yarima haliifaa ya kasance saurayi mai cikeda gwarjini , birgewa, shiga rai uwa uba addini da sanin ya kamata, iya kacin wadannan halayensa tayi sabo dasu amma ba wannan halin da take kallonsa aciki ba yanzu,
Jin motsinda tayi ya sanyata saurin hadiye kukanta ta sanya hannuwanta ta share hawayen dake kan fuskarta, da sallama nabila tashigo dakin, umma ta amsa sannan tasaki wani murmushi mai cikeda zallan damuwa, nabila ma ta maida mata murmushin da qaraso tace umma kije ki huta saina zauna a wajansa, rankwafar da kai umma tayi cikin sigar tausayi tace kayya nabila babu wani hutun da zan iya cikin wannan hali ke kije ki kwanta koda baki samu bacci ba kidan huta jiya haka muka kwana ido biyu cikinmu babu wanda ya runtsa,
Sunkuyarda kai nabila tayi kwallar tausayin kansu ya cika mata idanuwa, dukansu sun dawo abun tausayi itada umman da yariiman gabaki daya wani lokacin ma harda shi kanshi mai martaba gashi girma ya kamashi ga wannan al'amari mai tsoratarwa da rikitarwa dake faruwa da magajinsa hawayenda suka cika idanuwata suka sauko akan kumatunta, hawaye sun kuyarda kanta kasa tayi saboda bataso umma taga halinda take ciki amma saida umma ta fahimci yanayinda tashiga
A fili umma tace kiyi hakuri nabila kiyi hakuri bazan gaji da tausarki da baki hakuri ba, hakika wannan itace *
*
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial23 Chapters
Malicious, Magical, Malfoy
People often complained about a lack of birthright. Being reborn as Draco Malfoy meant I had the opposite issue. So many new things to take into account. Politics, magic, family traditions, the wizarding world and this odd new power that insisted my new reality was a game. What's a Gamer SI to do.
8 218 - In Serial63 Chapters
Private Academy System
Ensen Fuentes was a teacher at a top-tier local private academy. However, a few months ago the board decided to transition the academy into a girls-only academy. Due to pressure from the families of the students, male faculty members were slowly let go. Because of Ensen's excellent reputation and progress with his students as a math teacher, he was kept but was ultimately forced to be let go after a few months. With nowhere to go and nothing to aim for, watch how a mysterious system changes his life and aids him to create a world-renown private academy!
8 117 - In Serial15 Chapters
A Meta-Human In Another World
Lilly Meadow, a genetically engineered Meta-Human from a dystopian future version of Earth along with two others and their android caretakers are transported to another world during a failed test in wormhole experiment. Lilly now has to adapt to a strange new world that is nothing like her own. Coming from a society where the concept of family and crimes among many other common concepts don't exist and all are conditioned and brainwashed to follow the commands from the government how will Lilly cope with the culture shock? Will Lilly be able to fight the brainwashing and conditioning? And how will the super genius change the world? I also update this on Scribble Hub. This is a rough draft, I will eventually rewrite this story once this is finished and am a better writer.
8 74 - In Serial8 Chapters
Paper Aeroplanes
In post-apocalyptic New Zealand, 2 clones communicate by paper aeroplane. 16-year-old Tui has never spoken to anyone outside their Block... until a paper aeroplane slips through the bars of their cell window. Can they fight the serum that numbs their emotions, and build a true connection with the girl on the other side of the barbed wire?
8 186 - In Serial40 Chapters
Vengeance of Carinae
When Ronja Larsen. Marine, Fighter Pilot and all around badass finds herself stuck on an alien world It's going to take more than a little luck to survive. Armed only with a flight suit, some wreckage and her wits she's left bewildered and angry in a foreign world in an alien biome with little to no hope of getting home. Will she be able to escape to take her vengeance? There's nothing to stop her. Well, nothing except a dangerous untamed world and a few thousand light years distance. But what's that to a marine? Hey potential readers! I hope you join me on an adventure in my writing and literary pursuits. This book will hopefully be an interesting read with extreme details on bizarre facts that I find interesting. I will throw in useless knowledge and scientific concepts and facts. Have you ever wondered why glass is transparent? Well I'm sure to throw it in somewhere, so I hope you find my story interesting. - Deflagration P.S If you ever find scientific innaccuracies please PM me. I truly want to know. Other mistakes I'm happy to respond to in comments. A Note on tags: Profanity: Not excessive but where i find appropriate. Gore: Well that depends how well I do my job doesn't it. If I can paint a vivid picture that has the potential to be gory, then my writing may be to an acceptable quality. Traumatising content: Again, this depends on my skill as a writer, I guess I hope you find it traumatising - no that’s not right. Well you know what I mean anyway. Hopefully I can paint a vivid picture in your mind that makes the book all the more special.
8 154 - In Serial10 Chapters
Still in my heart
One month after Eun Bi came back to Sekang high school. It's brand new life for her, she finally has a normal life. Just like a reset button, she has given a second chance. She decided to accept Han Yi Ahn's feeling and became his girlfriend. Gong Tae Kwang remains in her side and always support her. It seems like she has everything that she ever wanted. But why she still feels lonely? She starts to questioning her feelings whether she makes a right decisions or not, especially when a girl from Tae Kwang past comes back and starts to take him away from her.--------------------------Halooo.. I know it's been years since school 2015 end. But I miss taebi couple so much. And I really hate the ending so much so I decided to make another fanfics. Hope you enjoy it..Ps. Please forgive my terrible grammar
8 188

