《ƘADDARAR RAYUWA》K page 54
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
"
Assalamu alaikum Dafatan munyi sallah lpy Allah ya mai-maita mana Allah yasa munyi ibada karbabbiya, Amin."
Muna saida kaya, material, laces, atampha, shadda, takalma kayan kitchen da sauransu akan farashi mai sauki siyan daya ko sari,
Alarabee's hair cream is available pcs, cotton, half cotton, yana gyara gashi, cire dandruff, hana karyewar gashi, yana softening gashi, yana saka bakin gashi yana saka cika da tswon gashi🥰 masu bukatar kaya ko hair cream ku tuntubi wannan lambar 08161146563."
Page 54
Cikin sati biyun daya rage na tafiyarsu sadam sai karatowa yakeyi yayinda wata shakuwa mai karfi take kara shiga tsakaninsa da sawwama, wata shakuwace ta daban kamar yanda kulawarda yake bata ta zanto da daban, rititata yake kamar kwai sam bayason ta motsa koda nan da can idan yana kusa ko abu zata dauka shine yake mika mata idan kuma bayanan yakan cewa halima kada tabarta tayi aikin komai, itakuwa sawwama tana zaunawane kawai idan taga sadam yananan amma idan yafita takan mike ta motsa jikinta da wasu yan ayyuka koda bamasu yawa ba
Idan sadam yana tareda sawwama sam bayason rabuwa da ita akoda yaushe idan yatuna da zancen tafiyarsu sai yaji duk ransa yabaci walwalar dayake tareda ita sai ta gushe kunci ya mamaye cikin zuciyarsa, tun yanzu bai tafiba yafara kewarta dakuma tunanin rabuwa da ita, shiyasa lokuta da dama yakanji kamar yafasa tafiyar kodan ssaboda yanyin da sawwama take ciki yau lpy gobe ciwo haka kwanaki sukaci gaba da tafiya har yarage saura kwana daya tafiyarsu ita kanta sawwamar tashiga damuwa kawai tana dagewane ta daure donta karawa sadam karfin guiwa amma dukda haka saida damuwarta ta nuna ayanayin mu'alamarta dakuma kan fiskarta."
Ana washe gari tafiyarsu sadam ba'a gidan sawwama yakeba amma ya yankewa kansa anan zai kwana sai dai duk wani abunda zai faru ya faru, sawwama na kwance akan kirjinsa ta lumshe idanuwanta kamar mai bacci amma ba baccin takeba tayi shirune kawai tana tausayin kanta, irin kulawarda sadam yake bata da zarar yatafi bbu mai bata makamanciyar hakan,
Advertisement
Sadam yana wasa da yattsun hannunta wanda yasha jan lallae yayi kyau sosai ajiyar zuciya ya sauke bayan ya dauke idanuwansa daga kan hannunta yadawo dashi kan fuskarta, a hankali ya furta bacci?
Sawwama wacce ke kwance luff a kirjinsa ta girgiza masa kai,
Murmushi yayi yace toh kinyi shiru tunanin me kikeyi?
Cikin sanyin murya ta furta babu?
Bbu! Ya maimaita, kai ta gyada masa, iska sadam ya furzar ya tabbata sawwama na cikin damuwa sai dai kawai taki nuna masa dan batason ya tada hankalinsa,
A hankali yake shafa bayanta cikin sanyin murya yace wanann ATM din da nabar miki cikin drawer shine wanda salaryna yake shiga duk wani abunda kike bukata ki aika aciro miki kudi kisaya shikuma daya na saving wasu yan kudadene aciki koda wani abun zai taso lokacin ba'ayi salary ba sai ayi amfani dashi, sannan da zaran kinji ciwo ko yaya yake kifita kitafi asibiti,
sannan kin tabbata kin duba store dakyau?
Bbu wani abunda zaki bukaceshi kwana kusa?
Gyada kai kawai sawwama tayi saboda ya maimaita maganar yafi sau abunda yafi yafi 3days yanayi mata zancen ATM dinnan dakuma na abubuwan store kuma sam batason jin zancen saboda karyar mata da zuciya yakeyi, yanzu haka idanuwanta cike yake taff da hawaye kanta takara cusawa cikin jikinsa yayinda idanuwanta yakawo ruwa zuciyarta tayi mata nauyi wuyanta yana makakin zafi dan wani irin kuka takeji yana kokarin kwace mata,
Hannu tasanya ta kankameshi sosai kamar wacce zata shige cikin cikinsa tayi hakanne duk dan kada kukan daya tunkarota ya kwace mata, zuciyarsane tayi nauyi duk wani kwarin guiwarsa ya karye da sauri yake furzarda iska mai dumi daga bakinsa, wani dumi yaji yasauka a jikinsa hakan ya tabbatar masa da hawayene ne yake sauka daga fuskar sawwama zuwa jikinsa, hannu yasanya ya rikota da nufin dagota ya share hawayen amma ina gam-gam sawwama ta rikeshi ya jijjigata ko zata sake amma bata sakeba cikin matsanancin tausayinta yakoma ya kwanta flat ya mirginota gabaki dayanta yadawo kansa ya kwantar,
Yanata shafa bayanta ahaka suka dauki tsawon lokaci dukansu idanuwansu a lumshe sunajin yanda zuciyoyinsu suke bugawa cikeda soyayya hadeda tausayin junansu,
Advertisement
Tsawon lokaci kafin sawwama ta mike daga kwancen da dake hawaye duk ya bushe a fuskarta cikin dauriya tace yaya sadam dare fa yanayi yakamata yanzu katashi katafi!
Kai ya girgiza yace no! Yau anan zan kwana, dan tsaro ido tayi tace ka rufamin asiri yaya sadam gara katafi murmushi yayi yace babban rufin asirin da zanyi miki kenan nakwana anan sam banaso natafi na barki da kewata kokadan,
Mikewa sawwama tayi daga kan gadon da sauri shima sadam da sauri ya kamota ya maida ita yana kiyi a hankali tunda kinsan bake daya bace yanda kika mike dasauri haka zakije kiyiwa kanki da abunda yake cikinki illa, tura baki sawwama tayi gaba tace to ai ishirwa nakeji jan hancinta sadam yayi hadeda yin murmushi yace jirani na ebo miki yayi brushing lips dinsa akan bata sannan ya mike, cikin shagwaba sawwama takara turo bakinta
Numfashi sadam ya sauke a hankali idan sawwama tana shagwaba ba karamin burgeshi takeyiba sai yaji kamar ya hadiyeta ya maida ita cikin jikinsa gabaki daya,
A cup yakawo mata ruwa takarba tasha ya maida kofin sannan yadawo yazauna yajawota jikinsa, cikin sigar lallashi sawwama tace yaya sadam ni ganina daka tafi can tunda kwanantane kuma hakkintane yanzu idan ka zauna anan zai zamana kamar shiga hakki, kaga kuma bbu kyau shiga hakkin wani duk karancinsa, shafo girarta sadam yayi yace sawwamaty yau bazan iya tafiya na kwana acan ba saboda daga gobe zan kasance nayi nisa dake nisa mai yawa yayinda ita kuma nake kusa da ita a duk lokacinda ta nemeni zata sameni a duk lokacinda taso ganina zata ganni amma kefa?
Daga gobe bazaki sameni a lokacin da kika nemeniba haka zalika bazaki ganni alokacinda kikaso ganinaba, idan shiga hakkine ke naki hakkin da zamu dauka mutafi dashi akanmu na tsawon lokaci fa? Dan haka banaso kisake cewa naje can na kwana saboda bazan iya tafiya ba, sawwama tayi luff ajikinsa tana sauraren kalamasan yayinda wasu daga cikin kalmomin daya fadi suka tada mata hankali gabaki daya sai taji zuciyarta tacika ta kishinsa, taji zafin kalaman dukda tasan bada gayya yafadi hakanba saboda tanada yakinin bazai taba fadin abu dan taji zafin ba idanma yasan cewa zataji zafin kalamansa toh bazai fadesu ba,
Ranar haka sadam a gidan yakwana bacci barawone kawai ya sacesu washe gari sassafe suka fara shirin rakasa airport, 8:00am kuwa sungana duk wani shirin da zasuyi gidan dady suka nufa atare suka nufi airport da su dady abida dama ita tun can sun sameta agidan sai kumbure-kumbure takeyi amma sadam yayi kamar baimasan tanayi ba,
Dady yayi musu nasiha sosai har izuwa lokacin zasu tashi duk dauriya irinna sawwama saida tayi kuka kamar randa zai fita haka har suka tashi sannan suka juya gidansu dady suka wuce sai wajajen magrib kafinnan suka wuce gidansu ita kanta mummy jikinta yayi sanyi sosai kewar yaronta ya shigeta shiyasama bata samu lokacin nuna bakin halinta ba."
Sadam suna sauka bayan ya huta ya nemi mummy awaya bayan sun gaisa yakashe yanemi sawwama sun dade sosai suna hira yayita kwantar matada hankali sun dauki tsawon lokaci suna hira kafin daga bisani sukayi sallama."
Inaw kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial1363 Chapters
VRMMO: The Unrivaled
Lu Chen used to be a ranker of the most popular VRMMO game, Spirit of Grief. After a car accident turned his dreams into dust, his disability left him incapable of escaping the pit of mediocrity he was thrown into. Helpless and defeated, his story ended.Two years later, the Eternal Moon Corporation launched a new VRMMO called "Heavenblessed", and Lu Chen stumbled into another terrible accident that left him in a complicated situation far beyond his ability to handle. That won't stop him from rising to the top, however. Not again.Come witness the rise of the sword-wielding zombie and the relationships he makes during his journey to the apex! For riches and bi- ahem, for career and love!He wields a demonic sword from Hell, he dons armor shining with Heaven's light. His boots stride across the sky as his helmet devours the souls of his enemies. On his left side sits the Goddess of Death. On the other, the Angel of Beauty.From the land of ice and death, a generation of Asura Kings rises, their roars reverberating throughout the world.Tremble in fear, noobs!
8 8158 - In Serial1353 Chapters
Refining the Mountains and Rivers
A young man's life changes when he stumbles upon a mysterious item. Qin Yu had never been a lucky person. Weak of body, bullied by his peers, and with only his friend as his family, he struggles day-by-day to live. But everything changes when he stumbles upon a little blue lamp. An immortal and demonic cultivating adventure.
8 3346 - In Serial2455 Chapters
Mortal Cultivation Biography
A poor and ordinary boy from a village joins a minor sect in Jiang Hu and becomes an Unofficial Disciple by chance. How will Han Li, a commoner by birth, establish a foothold for himself in in his sect? With his mediocre aptitude, he must successfully traverse the treacherous path of cultivation and avoid the notice of those who may do him harm. This is a story of an ordinary mortal who, against all odds, clashes with devilish demons and ancient celestials in order to find his own path towards immortality.
8 1057 - In Serial1503 Chapters
Dragon Prince Yuan
Destiny stolen at birth, the prince of the once mighty Great Zhou Empire, Zhou Yuan, has been plagued all his life by a fatal poison, forced to suffer powerlessly until one day when fate draws him into a mysterious domain where he meets a beautiful girl in green, a bizarre dog-like creature and an unfathomable old man in black.Join Zhou Yuan as he is thrust into the whirlpool of destiny while he seeks the pinnacle of cultivation.
8 1060 - In Serial677 Chapters
Ranker's Return
In the early days of the virtual reality game, Arena, meleegod was the strongest ranked player! He deleted his character and suddenly left. In order to restore his bankrupt family, he returned to Arena!"Do you want to create a character?"
8 1719 - In Serial1525 Chapters
Monarch of Evernight
Qianye rose from hardship but was felled by betrayal. From then, one man, one gun; he tread the path between Evernight and Daybreak and became a legend. Even if Evernight was destined to be his fate, he still intends to become the ruler who dictates.
8 22867

