《ƘADDARAR RAYUWA》K page 49
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
"
Page 49
Kwanan su sadam biyu da tafiya mummy tafara tunanin raina mata hankali kawai sadam yayi bbu aiki kawai yadauki matarsa ne sunbar gari,
Kokuma suna gari suna wani waje daban,
Alokacin dayazo mata da zancen tarasa mai ya cushe a kwakwalwarta harta yarda da tatsunuyarsa nacewa aiki aka turashi domin kowa yaji zancen yasan akwai wata a kasa,
Mummy tayi bincike a wajan aikinsu ta tabbatar babu wani aikin da aka turashi hasalima hutu ya dauka,
Wani irin tsanar sawwama yakara sauka a cikin ranta danta datake kallo mai hankali da nustuwa yau dayi mata biyayya shine ya bijire umarninta akan sawwama yau har takaiga yayi mata karya ya rena mata hankali,
Duk yanda takaiga son samunsa a waya amma sam wyarsa taki shiga switchoff, mummy kullum da dacin wannan abunda sadam yayi mata take kwana tana tashi har,
Sadam a nasa wajan kamar yasan cewa mummy zatayi bincike ta gano gaskiya hakan yasa duk wata hanyar da zata saddashi da mutannen gida ya datseta zai dauki duk wani hukuncinta dazai biyo baya tunda yasamu farin ciki a tafiyarsa sam bazai damu da kalamanta da maganganunta ba,
Saida su sadam sukayi 2weeks a yankari sannan suka dawo gida, sunyi isowar dare hakan yasa bai sanarwa da kowa dawowarsa ba sai washe gari yashirya yatafi wajan abida,
Fuska a daure yasameta saboda itama jikinta yabata sadam ya raina musu hankaline kawai,
Gashi cikin 2weeks dayayi sau daya sukayi waya,
Sadam shi kansa yasan bai kyautawa abida ba hakan yasanya ya shiga da fuskar tausayi, ganin yanayinta saita bashi tausayi, yasan dole da hakkinta akansa kuma bai dace ace yayi 2weeks bai kira yaji lafiyarta ba,
Zama sadam yayi yaringa lallashinta da kalamai masu dadi wanda harya sanyata ta sauka daga fushinta, sadam bai samu fita a gidanba har rana domin abida ta narke masa gabaki daya ta hanashi motsawa nan da can, saida aka kira sallar azahar sannan yasamu yayi mata wayo yafita hakanma cewa tayi sai dai yayi sallah agida, bai yarda ba dai yayi tayi mata dadin baki dacewa yanzu zai dawo hakan yasa tabarshi yafice.
Advertisement
Gabansa yanata dukan uku-uku a yayinda yanufi gidansu dan baisan mai zaije ya taras wajan mummy ba,
Yasamu dawowarta daga office kenan tana zaune tana hutawa yashiga da sallama mummy ta amsa sallamar ciki-ciki yanda bazai jiyotaba ta kauda kanta gefe sadam ya iso gabanta ya tsugunna cikin dar-dar yace sannu da gida mummy ina wuni ya aiki? Ya jera masa gaisuwa cikin taraddadin mai zai biyo baya,
Mummy tayi banza dashi ta debeshi ta watsar sadam yakara maimaitawa amma yacce kasan babu mutum a wajan zaman wani lokaci sukayi babu wanda yasake cewa komai,
Sadam ganin fuskar mummy babu alamun koda wasane ya sanya duk gabobin jikinsa sukayi sanyi, domin mummy tasha murr sosai kamar ba mummynsa ba,
Yankewa kansa kawai yayi ya dauki laifinsa yafara bata hakuri domin yasan halin mahaufiyarsa zata gano gaskiya yasan yanzu haka tagani gaskiya,
Sun kuyarda kansa kasa yayi yace mummy dan Allah kiyi hakuri ki gafarceni nasan nayi miki laifi amma in sha Allahu bazan sake kwatanta hakaba,
Harara mummy ta watsa masa kusan 5minute kamar bazatace komaiba sai kuma tace sadam ni zaka nemawa hankali? Ni sa'arkace? Ashe har kayi wayon da zaka iya yimin karya? Akan wata shashashar matarka? Yaushema aka haifekane sadam nawa kake? Dahar zakayi tunanin yimin wayo batareda nagane ba,
Nawa kake sadam? Yaushe aka haifeka?
Sadam yayi kasa dakai yace mummy kiyi hakuri nasan nayi laifi amma Mummy bawai na raina miki hankali bane, mummy duk wanda zai raina miki hankaki a duniyar nan ni bazan taba jituwa dashiba balle har ace ni dakaina na raina miki hankali,
Mummy tace nanawa kuma sadam? Nanawa? Gashinann matarka ta zugaka ka yimin karya, ga gujeni, sadam yace wallhy mummy ba laifinta bane itama batasanda tafiyarba,
Salati mummy tayi ta sanrwa ubangiji tace sadam! Nashiga uku kana cikin hankalinka kuwa? oh kareta kakeyi? Gani uwar banza nayi mata karya koh? Saurin girgiza kai sadam yayi yace A'a ba haka nake nufiba mummy kiyi hakuri, in sha Allah haka bazata sake faruwaba,
Mummy tace shikenan ai tunda haka kace karka kuma sadam dan zaka hadu da fushina,
Sadam yace nagode in sha Allahu mummy bazan sakeba,
Allah yayarda mummy tafadi sadam yamike yayi mata sallama yatafi yana tunanin wannan sawa kai ijaba irinna mummy."
Advertisement
Sadam yakanyi kwana daya gidan wannan sannan yayi kwana daya gidan wancan ko sau daya bai taba hadasu waje dayaba,
Babu wacce tataba ganin wata acikinsu,
Sau daya yataba kaita ta gaida mummy basu samu tarban arzikiba kallon kirki basu isheta ba, har turmin zani tadauka a cikin na lefenta mai kyau da tsada da turare da man shafawa dasu sabulu takai mawa mummy su hassana da hussaina kuma yan kananun kaya ta deba musu, ko kallon arziki mummy batabi kayan dashiba, sawwama kuwa ko ajikinta bata dauki hakan a komaiba dan bai dameta ba, haka tatashi tayiwa mummy kaf aikin gidan komai da komai dake a weekend sukace, ba sannu babu madallah haka tagama aikin, harta da abinci ita tayi da mummy tashiga kitchen tabita ta karba sai tafice tabar mata kitchen din tayi tagama takai dining, tadawo ta zauna,
A sace mummy take kallonta ko zataga wata makusa a tattare da ita amma bata ganiba, gata karamar yarinya su hassana da hussainama zasu girmeta ko suzo sa'oi, aranta tana tunanin idan yartace bbu abunda zaisa tayi mata aure kamar haka,
Zuciyar mummy nason sauka akan taanar sawwama datakeyi saboda kyawawan halayanta datayi noticing amma mummy kyam haka tahana zuciyarta jin komai gameda ita, sai kara cusawa ranta takeyi cewa danta yaki bin umarninta akanta, ta mallake mata da aikuwa nan da nan taji wata sabuwar tsanarta tadawo cikin zuciyarta,
Koda zasu tafi mummy ta make adaki kin fitowa tayi suyi sallama sadam da kansa yashiga yace mata zasu tafi tace Allah raka taki gona, yafito yacewa sawwama su tafi amma fir haka taki tafiya wai saitayiwa mummy sallama, kofar dakin mummy yanuna mata taja yatsaya cikin ransa yana zullumin abunda zata taras, dankoda yakawota baiso barinta tawuniba alokacin yaso su tafi amma haka taki tafiya wai ita wuni zatayi haka yatafi yanata tunaninta, akai-akai yake dawowa gidan dubata, hakan kuwa ba karamin karawa mummmy haushin sawwama ba yayi aranta dan tasan dan ita yake wannan ziryan, shiyasa da zasu tafi taki fitowa,
A zaune bakin gado sawwama ta sameta tashiga da sallama mummy ta amsa ciki-ciki, har kasa ta tsugunna tacewa mummy, zamu tafi sai anjima, mummy kanta yana gefe tace mujima dakyau, sawwama ta mike tafita, mummy tabi bayanta da kallo,
Ita kanta acikin zuciyarta tasan sawwama tafi abida kirki, kyautatawar da sawwama tayi mata a yau kadai abida bata taba gwada makamancin hakaba."
Tafito tasamu sadam tace muje yaya sadam fuskarta yakebi da kallo ko zaiga wani yanayi amma sam baiga komaiba ajiyar zuciya yasauke yana tunanin ko mummy tafara saukowane toh? Dan yasan kyawawan halin sawwama dole idan ka zauna da ita kasota,"
Su hassana kuwa har mota suka rakata da murna kowannenssu a fuska ga dukkan alamu sun saba da ita adan zamansu na yau, suna cemata sai sunzo, itama da murmushi a fuskarta tace inajira sai kunzo."
Kwanansu sawwama biyu zuwa gidansu mummy tafara laulayi babu kama kafa gashi laulayin yazo mata da zafi,
Koda da yakaita asibiti aka auna 2month cikin dai-dai da lokacin aurensu, sadam bai bari kowa yaji labarin cikinba shine yake jinyarta akai-akai yake zuwa gidanta ranar dayake gidan idan yadawo a aiki baya motsawa ko ina,
Ganin idan baya gidan tana shan wahala yasanya ya dauko mata halima kanwarta dan sam bayaso tamotsa ko nan da can dan bakaramin soyayya yake nunawa cikin ba,"
Ana cikin wannan halin mummy tayi masa waya tanason ganinsa shida sawwama da abida duka suzo gobe, sadam baisan excuse din dazai bawa mummy amma sawwama kam sam batajin dadi yana ganin zaijene kawai batareda itaba."
Ih toh nace yauma dai banyi editing ba😀😀
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial22 Chapters
I maxed out my Stats, so why am I still a loser?
Ashner has no job, no girlfriend, and no good luck on his side. Until one drunken night, he finds a door to another world. And discovers monsters drop real gold. Not to mention a leveling system that's more detail orientated than he hoped for. With a tool that can bring him money beyond his wildest dreams, he decides to get as much as he can. Wealth, women, and status. But even with all that, why does his life always take the same unlucky turns?
8 104 - In Serial8 Chapters
Vanguard
Leon hid a grimace. He was no soldier, he chose this. At least in a way. He chose to risk his life for profit. He chose to fight in a war he had no real opinion of. Hell he even chose to join this assault. There was a bonus in it after all. The room shook.
8 226 - In Serial11 Chapters
THE JOURNEY
Hello my name is Brandon Simonds this is the story of how I made it back home or at least I thought so… It's my first story any comment is good ok.
8 158 - In Serial17 Chapters
Gates To Earth
It was like any other day on Earth, Until new land masses begun to appear at areas where there was once nothing. And then large Gates that look like doorways appeared on the new land masses as well in other isolated locations on Earth those Gates led to other worlds and possibly other Dimensions itself. No one knows how or why this had begun to happen the gates are not one way doorways on the other side is a whole new planet and possibly universe, Synopsis This is a work of fiction. Names, characters, places and incidents either are products of the author’s imagination or are used fictitiously. Any resemblance to actual events or locales or persons, living or dead, is entirely coincidental. It was like any other day on Earth, Until new land masses begun to appear at areas where there was once nothing. And then large Gates that look like doorways appeared on the new land masses as well in other isolated locations on Earth, those Gates led to other worlds and possibly other Dimensions itself. No one knows how or why this had begun to happen, the gates are not one way doorways on the other side is a whole new planet and possibly universe, What people once thought was a fantasy began to come to life, some of the creatures which came through the doorways use magic and others use technology that earth can only dream of. Each doorway has something new to be discovered, may it be a doorway to a dark age world or possibly a magical world with magic, Earth can only guess what's on the other side of every Gate. Each country has their own problems and the Gates just add to it, will Earth’s countries work together or fight for control over the Gates that lead to the new worlds. Join Rex Lopiz who has gained Necromancy and the power of Making all sorts of robotic creations, Rex must first start from nothing such these are new powers, he cannot make large undead armies or make advanced robots without starting from the basics. See how other people are dealing with the Gates, the main character is Rex Lopiz but there are times where you see what other people or creatures are doing in order to survive and live their daily lives and what they do. Not everyone is as lucky as Rex but they still try to survive even with Gates appearing. Follow how other people deal with situations as well as follow Rex through his journey. Authors Note This is a side project as well as my first time trying to write a book. I hope you enjoy it and feel free to give me pointers. Some things may be spelt wrong. I will usually try to fix them once I notice it, sorry and thanks again for giving my story a read. -Wikid81
8 67 - In Serial49 Chapters
Haunted Love | Colby Brock x reader✔
You meet Colby, Sam, Corey, Katrina and Brennen in a haunted/abandoned asylum, while exploring it alone. From there you become good friends and move in with them into their mansion. You do scary stuff and experience creepy incouners with spirits you wouldn't want to mess with. You go through these odd things together and fall in love. This is what you call haunted love. Falling inlove while being haunted.
8 162 - In Serial14 Chapters
Royal sonic ( sonic x reader)
Sonic x reader mediveal times
8 77

