《ƘADDARAR RAYUWA》K page 44
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 44
Mama tadubi baba cikin mamaki da al'ajabi jikinta duk yabi yayi sanyi basu gama al'ajabin kayan aure ba ga kuma na adda saratu ya biyo baya,
Nisawa tayi tace baban sawwama yaya kagani akan wannnan lanarin, baba wanda yarasa tacewa yace toh nidai a yanzu banda tacewa bansan gababa amma jikina yayi sanyi da wannan lamari kwarai da gaske,
Mama tace bbu komai bbu abunda yafi karfin ubangiji mu namu addu'a Allah ya sanya albarka a cikin lamarin amma kam wannan abubuwa sunyi yawa ina tsoron daga baya gori yazo yabiyi baya, baba shima aransa abunda yake gudu kenan hakan yasa ya mike yace barina shiga daga ciki zuwa gobe da safe zanje gida nasamu baba na sanar masa lokacin da sukeso ayi biki nan da sati biyu, mama tace Allah yakaimu, tatashi tabi bayan baba,
Sawwmaa na jiyosu daga dakinta ita kanta jikinta yayi sanyi matuka ko amafarki bata taba tunanin haka su sadam zasuyi kayan aure ba, ita kamma batayi zaton dukiyarsu harta kai haka bama,
Ranar baba da mama adarare suka kwana a gidan sakamakon kayan auren sawwama da suke tunanin jin labarinsa kadai ya isa ayi musu fashi a wannan rana bacci ragegge sukayi,
Adda saratu kuwa tun a daren tabi ta shaidawa dady yanda sukayi da iyayen yarinyar sannan tadaura da fadin a gaskiya sadam yayi sa'ar mata da dangi masu karamci hadeda gudun zuciya, domin nasamesu suna shawara akan dawoda kayan auren da aka kai musu wai yayi yawa sukuma albarkar aure sukeso, dady yaji dady matuka a ransa hankalinsa ya kwanta domin yasan tabbas duk abunda anty saratu ta yabeshi to tabbas abune mai kyau kuma baida makusa, dan ita kusancinta da abu bai hana ta kusheshi, kusancinta da mutum bai hana taki fadin gaskiya koda kuwa a gabansane, dady yace toh Allah yakaimu goben muji abunda suka yanke dan gara ayi abunnan kowa ya huta, adda saratu ta amsa da fadin amin."
Da safe bayan sun gama karin kumallo baba yawuce gidan mahaifinsa ya sanar dashi bukatar dangin sadam, malam sa'adu yadubi baba yace toh kai hamisu yaya naka shirin yake? Idan ka tanado abunda ka tanada sai na hado dana wajena sai asanya bikin idan kuma Abunda yake hannunka baida yawa sai muce suyi hakuri har izuwa lokacinda zamu shirya kar azo ayi abu a matse,
Baba yace toh da dai akwai wacce tace tadauki nauyin kujeru da gado toh mudai bamu nuna mana amincewarmu ba saboda gudun abunda zaije yazo ko kuma azo aga son zuciyarmu tunda mu muka haifi yarinyar mukeda hakkin yimata kayan dakin, mlm sa'adu yace toh Alhamdulillah abu yayi kyau matuka in sha Allahu bbu wani abunda zaije yazo, abarta tayi mai sonka shike taimakonka, bbu batun son zuciya a wannan lamari ai kai baka roketaba itace taga zata taimakeka to ka karba hannu bibbiyu kayi godiya,
Saika sanar dasu sati biyun yayi tunda dama abunda zai saka muja lokaci kenan na tabbata sauran kudin hannunmu zai ishemu muyi sauran abunda yarage,
Baba yaciro kudi a aljihunsa ya mikawa mlm sa'adu yana fadin baba ga wannan na kasan akwatin ne suka kawo,
Mlm sa'adu ya girgiza kai yace A'a A'a sam bazan karba ba aje ayi sauran sayayya dashi wanda yarage ka fulaste gidanka ayi wasu yan gyare-gyare tunda kasan baki zasu sauka,
Advertisement
Bbu yanda baba baiyiba akan yakarba amma fir haka yaki, baba yayi masa sallama yatafi, bayan yakoma gida ya sanarwa mama yanda sukayi da mahaifinsa sannan yadaura da fadin saiki shirya kishiga kasuwa abubuwan daya kamata si sassaya mata,
Mama tace toh shikenan angode zan cire abunda zamuyi amfani dashi sauran kamar yanda baba yafada ka gyara gida dashi domin baki, sannan aciki zan saya katifa koda guda biyune yan kananu da tabirmi, baba yace kiyi duk abunda yadace sauran zan san yanda za'ayi dashi,
Mama ta amshi kudin tashiga daki ta adanasu da zummar zata kira kanwarta sushiga kasuwa tare,
Bayan isha'i dady sukazo tareda adda saratu baba ya sanar musu ya amince a tsayarda biki nanda sati biyu, bakaramin murna sukayiba,
Dady bai sanarwa sadam ba sai washe gari ya sanar masa akan an sanya biki nanda 2weeks remain 12days dan haka duk wani shirinda zaiyi yafarashi yanzu, sadam kamar ya dauki dady ya tsomashi a aljanna haka yakejinsa sai faman sirfa masa godiya yakeyi finally shida sawwamarsa zasu kasance atare, jinsa yakeyi wani daban farin ciki sai ratsa gabbai da jijiyoyin jikinsa yakeyi,
Aranar wuni yayi yana kiran sawwama yana jinawa kadan zai kirata koda baida abun fada mata yaji muryarta kawai ya kashe, ba sawwama kadaiba duk wanda yake tareda sadam saida ya fuskanci farin cikin dayake ciki har gida yasamu najeeb ya sanar dashi najeeb yace ikon Allah, Allah buwayi gagara misali wai sadam a shekarunka kaine har zakayi mata biyu? Amma baka ganin kamar mata biyu sunyi maka yawa kaduba rike macefa ba abun wasa bane masu guda daya ma yaya suka kare??
Sadam ya hade rai gam-gam yace har indai kasan bazaka yimun addu'ar sanya alkhairi ba kayi shiru da bakinka kawai,
Murmusawa najeeb yayi yace wannan yazama dole, dolene nayi maka addu'ar alkhairi, Allah yabaka ikon rikesu dayin adalci atsakaninsu, bbu wani bata lokaci sadam yacewa najeeb ya shirya ya rakashi a buga kati, najeeb yace ayau za'a buga katin? Daga sanar maka sai buga kati? Toh kasanma yanda za'a daura aurenne? Kuma karfe nawa? Sadam yace duk zan tambaya,
Dariya najeeb yayi yace ban taba kallon mai zumudin aure irin naka ba, 😅😅😅,
Sadam yace bazaka gane bane ai kai duk yanda zanyi maka bayani bazaka fahimta ba, najeeb yace mai zai hana? Sai dai idan ba'a yimun bayani ba, sadam yace nikam tashi muje, aranar aka buga katin tsabar zumudi irinna sadam,
Bayan isha'i yaje har gida yakaiwa sawwama nata sannan yace aina zatayi walima sai yakama mata hall kafin ya bugo katin walimar wanda zata raba, murmusawa sawwama tayi domin zumudin sadam yanason wuce tunaninta, kamar bazata tankaba dan wata irin kunyarsa datakeji sai kuma tace ni bazanyi walima ba, da mamaki ya kalleta yace meyasa bazakiyi walima ba? Girgiza kanta tayi tace haka kawai, kaima ina fatan bazakiyi wani event ba?
Bakyasone? Ya tambayeta cikin kulawa, gyada masa kai tayi alamun eh, murmusawa yayi yace in sha Allahu bazan yiba tunda bakyso Allah ya sanyawa aurenmu albarka, ciki-ciki sawwama ta amsa da amin yanda bazai jiyota sosai ba,
Biki yanata matsowa yayinda mama ta sanya kai sosai wajan gyara diyarta sanin abunda yafaru da ita abaya, dafarko maganin infection kala-kala tafara hada mata kullum acikinsu take sannan daga baya aka koma na gyaran ciki da waje,
Advertisement
Mama tagama duk wata sayayyar da zatayiwa sawwama baba harya fara gyaran gida, afilin dake cikin gidan aka fara gina dakuna guda biyu idan angama mama zasu koma ciki sai agyara nasu domin saukar baki,
Biki yarage saura 1week takowani bangare anata shirye-shirye amma banda mummy wacce takejin zuciyarta kamar wuta, ko gaisuwa sadam bata amsawa, ganin haka shima yasanya yabata iska na kwana biyu, canma abida sai tijara takeyi akan batason auren da zaiyi, ko kulata sadam bayayi dan abunma mamaki yabashi ita sawwama lokacin daya tashi aurensa sam bata nuna masa tadamu ba dukda yanada tabbacin sonda takeyi masa abida bata dauki 20% cikin 100% ba, shiyasa ya debeta ya watsar dan ganinsa borin samun waje takeyi, shikuma a yanda yakeji yanzu babu wani abunda zai sanya yafasa auren sawwama idan bai aureta yanaga sai dai idan yamutu kafin lokacin aurensu,
Sam mama tahana sawwama fita koda kofar gidane dai-dai da wyaar hannunta kusan kullum akashe take sadam yakan kira ya kira harya gaji bai samuba, wani sa'in sai dare yake samunta hakanma idan taga mama tashiga dakinta ta kwantane sai takunna wayar tasakata a silent, kwana biyunnan sadam kamar akan kaya yake jinsa, koda yazo kofar gida yatura akirata mama saita tura masa haalima aikar daya kawo mata yabawa halima yakoma jiki duk amace, wani irin son ganin sawwama yakeyi ga wata azabebbiyar soyayyarta da take neman zautar dashi a kullum kamar kara masa sonta akeyi,
Halima ta shigo da kayan kai tsaye dakinsu tawuce dan mama tana ciki tana shafawa sawwama hadin datayi mata na Nikakken ridi da dakakken lalle da zuma da garin hulba sai ganyen nim da aka busar dashi a inuwa ya bushe aka dake garin, aka hadesu waje daya tana shafa mata safe da yanma idaya bushe saita murje matashi a jikin ta debo tafasesshen ruwan shamferan lalle ta rufeta dashi har sai tiririn yagama shiga ko'ina ajikinta sannan kuma sai tayi wanke da ruwan lallen bayan ya huce, na kwana uku kadai mama tayiwa sawwama wannan hadin amma jikinta yayi bala'in kyau da wani irin laushi da taushi sai sheki takeyi kamar madara wacce takashe kudi masu yawa wajan yin dilka dasu halawa bazata gwada mata kyallin fata ba,
Halima tashiga dakin da sallama hannunta rikeda wata bag haka trolley sai envalope adayan hannun, mama tadubeta tace meye wannan haka a hannunki kuma? Halima tace wai aikane shine yabani nakawo, mama tace zauna kibude ina kallo, halima tafara bude jakan dinkakkun kayane da gyalluka da takalma, sake baki mama tayi tace meye wannan nake gani me za'ayi dasu?
Halima tace toh yanzu sai dai ta kirashi ta tambayeshi danni baiyimin bayanin komai ba, mika mata envelope din tayi tace yace inbaki wannan sawwama ta sanya hannu ta karba kudine a ciki bandir na 500 yakama 50k kenan,
Mama tace ke yimaza kikirashi ni ban gane wannan zancen ba, lalubo wayar sawwama tayi aka kunna sannan tayi dialing mo dinsa yana shiga ring daya ya daga kamar wanda dama yake zaman jiran kiranta,
Sallama sawwama tayi ya saukar da ajiyar zuciya, cikin muryar kalar tausayi sadam yace sawwamaty mai nayi dana cancanci wannan hukunci mai tsauri haka? Koda muryarki anyimun katanga da jinta, uhum kawai sawwama tace shiyasa bata sanya a handsfree ba saboda tasan za'a rina, kawarda zancen tayi da fadin ina wuni? Lpy sawwamaty nayi missing dinki sosai uhum kawai takara fadi sanna tace naga ka aiko halima ban ganeba shine nakira na tambaya,
Lumshe idanuwa sadam yayi sanyin muryarta yana ratsashi yace kayan fitar bikine na bada aka dinka miki dan kayan dayake cikin akwati ina tunanin bbu dinkakku,
Kudin kuma nasan baza'a rasa abunda zakiyi ba sai kiyi amfani dashi,
Sawwama tace amma yaya sadam wannan kayan sunyi yawa harda kudinma ina zan kaisu haka?" Sadam yace basuyi yawa ba sawwamaty zan iya dukan duk wani abunda na mallaka na kashe miki shi muddin zai sanyaki farin ciki, shiru sawwama tayi tana jinsa aikuwa sai yafara janta da zance, dankwalo mama tayi mata alamun takashe wayar, dasauri sawwama tayi masa sallama tayi hanging call din batareda tajira amsarsa ba, mama tace mikomin wayar nan daga cewa ki tambaya saiki bige. Da tadi, sawwama batace komaiba mama takashe wayar ta rike a hannunta, sawama tayi musu bayanin yanda sukayi mama tace Allah ya kyauta daganan ta mike dan ebowa ruwan shamferan lallen dake kan wuta,
Biki na matsowa mafarkai suna damun sawwama sam har bataso ta kwanta dan da zarar da kwanta sai tayi mafarki wani lokacin tayi mai cikeda tausayi wani lokacin kuma mai cikeda tsoro."
Yau naga ikon Allah😅😅 yanda kasan kun hada baki wannan tana kira ta tambayi kaddarar rayuwa zuwa jimawa wannan zata kira😅 inajin ringing wayana nasan masu neman book ne masu cewa zaku tura kudi abaku Kaddarar rayuwa kaddarar rayuwa bana kudi bane kyautane🥰 fisabilillahi addu'ar ku kawai nake bukata nagode sosai da kulawa."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Yarima fayada akan naira dari biyu kacal🥰
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial7 Chapters
All Trades Book 1: Master of None
Alex is broke, has been broke, and safely assumed he would always be broke. That bleak outlook changes when a tech genius (and alleged asshole) embeds the code generating his globally implemented cryptocurrency into his new MMORPG! Now the only way to get any more of it is to play the game and make some gold! Unfortunately for Alex, a loan shark was his only shot at getting a VR rig. Can he turn a profit in time to save his knees? Do gnomes dream of electric sheep?? Can he possibly win Employee of the Month??? Find answers to these questions and more by following the high margin adventures of Jack Alltrades.
8 202 - In Serial11 Chapters
The M.S. Fortune
John comes out of stasis aboard Starship Fortuna and is instantly made Captain by the bestest Simulated Intelligence in the Universe and then they live happily ever after, solving problems. Yeah. That’s totally what happens. Where are you going John? Why don’t you like my synopsis? I think it’s great and totally not full of lies. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Written by Vitaly S Alexius (author of Romantically Apocalyptic) and Angry Spider (author of... various). Dark comedy! Fantastic Adventure! Space! Sexy robots! Please insert more descriptive keywords! Notice of interest:This book operates on a unique concept of "Reader Causality". Meaning - every review left on it incrementally impacts the story, adding in a new, minor twist to it. If you already left it a review - then you can impact the story by leaving comments beneath new chapters.
8 81 - In Serial18 Chapters
Coruscant Ela
A young chemist girl tackled the once-unbeatable Labyrinth Farwitch alone, in order to save her nearby village from being a casualty to the awakening of the Demon Lord. She surprisingly succeeded, but never returned, leaving behind a precious childhood friend and her young sister. Five years after, local librarian Key Falen is invited by the newly-summoned hero and his cohorts to conquer the Labyrinth in order to solve the mystery of the Demon Lord's defeat. The mystery behind his childhood friend grows larger the more Key learns about her...
8 185 - In Serial35 Chapters
Dragon, Knight
When one becomes a knight, they accept a certain standard befitting of one. Well, mostly. Volsten is a knight that isn't all that knightly. He's young, handsome, and quite gifted with a blade. His problems, however, aren't physical. He's rude, greedy, and a womaniser to his very core. Unfit for courtly life or the rigors of the king's army, he wanders the world in search of gold. That is, until he meets a mysterious dragon girl. This chance encounter changes the course of his life-for better, or worse.
8 136 - In Serial11 Chapters
Spiritual Point
Kyle has always been an unlucky boy. Ever since he was young, he has already experienced countless unlucky situations. Getting Crashed by a car, being a victim of landslides, and even creating a massive incident just by slipping on a banana peel. however, all of these jinx will suddenly show a massive change in his life with one simple incident. One which before he'll know it, will change the world forever. (This story is completely fiction. Anything that is remotely similar to real life is purely coincidental. With that said, please enjoy.)
8 90 - In Serial12 Chapters
Primordial Origins
All the power in the universe, amounts to shit when you've fucked up, and there's no way to undo what has already happened. Even if your the creator of the fucking universe and all its laws and whatnot, those below you must conform to the natural laws that bind them. Even when you want to say 'fuck you' to such laws and break them, you can't because that is how you made the universe and those below you must follow it or they cease to exist in it.I'm tired of having things taken from me because of my mistakes. I've only wanted to live with those I love, but somehow in the universe I created, it decides to fuck me over. I only hope that this time it goes better. Everything seems to be going swell at the moment, but I just can't shake off that feeling that I'm about to get fucked over by myself. I hope when I get the chance to start anew amongst others, everything goes well. _____________________________________________________________________________________________Hello, this is my first time attempting to write an original story on Royal Road. I hope you'll enjoy the story as much as I will while writing it. Sorry for any plot holes/ plot armor/ cliche shit because it happens. Anyway there will definitely be foul language and probably some mature scenes, sexual or not. No idea what the release timings will be. Probably whenever I finish a chapter or two and attempted to proofread them.
8 183

