《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 43
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 43
Hajiya suwaiba akoda yaushe kunneta yana sashin mai martaba akoda yaushe neman labari takeyi ko zataji wani abun yafito burinta shine taji wani irin hali yarima yake ciki, yanzu abu guda ɗaya data sanya aranta shine raba yarima da matarsa sannan tadawo izuwa kansa kamar yanda hajiya babba ta gwada mata,
Babban sashine wanda yafi kowanne girma a cikin masarautar,
sashin mai martana ne kawai ya ɗara wannan a girma fadawane zagaye da ko'ina gaba da bayan sashin,
Wajan ya ƙayatu iya ƙayatuwa, ya wadatu da shuke-shuken flowers nau'i-nau'i,
zirga-zirgan masu aiki kawai make gani kowannensu yana kaiwa da komowa,
wasu manya-manyan mutane ne suke fara shiga sashin da wata ƙofar wacce take ƙebantacciya ce wanda alamun hakan ya nuna akwai wani taron da zasuyi cikin sashin ne, a tamƙamemen palourn suka sami hajiya babba zaune ga dukkan alamu shigowarsu kawai take jira,
Bayan sun kwashi gaisuwa kamar da 10minute palour ɗin yayi shiru tsitt kowannensu yana jira yaji Abunda hajiya babba zatace,
Cikin izza, iko da mulki taƙama dakuma ƙasaita tafara magana da faɗin waziri lokacin sabunta aikinka yayi ina fata kana sane da hakan?
Durƙuso waziri yayi da kansa ya ɗago hannunsa alamun jinjina yace Allah ya taimaki gimbiya ƴar sarki matar sarki tabbas ina sane! Wannna aiki nane yazama dole na tuna shi da zarar lokaci yayi,
Jijjiga kai hajiya tayi tace duk abubuwanda ake buƙata atabbatar an tanadar dasu ka shirya tafiyarka a cikin wannan satin ta faɗi cikin bada umarni, waziri yace angama gimbiya,
Juyawa tayi wajan sauran mutanen da suke palourn tace akwai mai bayani a cikinku? gameda aikinsa!
Wani daga cikinsu yace hajiya babba aikinda kika sanyani ayi za'ayi najeni an tabbatarmin da yiwuwar hakan amma akwai abubuwanda ake buƙata, uhumm kamar me? Hajiya babba tatatmbaya, ɗan ƙara zakuɗawa yayi ya fitarda numfashi yace akwai shanaye da yace zaiyi aiki dasu yafaɗi kalolinsu dakuma yanda za'a samu toh kawosu zai ɗan ɗauki lokaci dayake sai can chadi baza'a samesu anan ƙasar ba,
Hajiya tace kayi lissafin komai da komai da za'a buƙata banason wani dogon bayani,
Duƙarda kansa ƙasa yayi yace Allah ya huci zuciyarki zan zauna na lissafa kai kawai hajiya ta jijjiga masa, shirune ya ratsa palour din hajiya babba tana jira taji wani yasake magana amma dukansu sunyi shiru,
tsaki taja tadubesu gabaki ɗaya kollon ƙasƙanci cikin ƙufula tace duk wannan taron naku amfaninku kaɗanne samada shekaru sai abu yayi gaba sai yayi baya sai yayi gaba yayi baya, a wannna taron naku cikin watanni yakamat kugama komai da komai amma abu ya ɗauka mana tsawon shekaru,
Anan daku muka shirya yanda za'ayi komai akan ƴar gidan waziri za'a aura mawa yarima yaya akayi y acanja wancan banzan mutumin yabada ƴarsa saboda wannan saken da kukayi a kullum aikinmu baya yake dawowa,
Waziri yace ranki shi dade Allah yaja zamani yabaki nisan kwana kinsan galadima amintacce ne sosai wajan mai martaba kamar yanda nafaɗa kafin kowa ya iskeshi shine yafara iskar mai martaba, hajiya babba tace shiiiiiiiiii nagaji dajin wannan zancen samada shekara guda zancen baya taɓa wuce wannan bakuda wata amsa data wuce wannan, waziri cikin ransa yace tambaya bata canjaba amsama bazata canjaba amma a fili yace komai zaizo karshe hajiya kwanannan,
Hajiya cikin dakewa tace ina fatan hakan, zaku iya tafiya kowa kuma yayi aikinsa yanda yakamata su duka duka amsa mata da toh ranki shi daɗe,
Waziri ne kaɗai bai fitaba sanda suka gama fita sannan yadubi hajiya yace ranki shi daɗe gimbiya ita kuma waccar matar yaya za'ayi da iita?
Advertisement
Wace mata kenan? Hajiya tatambaya badan bata gane wa yake nufiba, Hajiya suwaiba nake nufi, shiru hajiya tayi sai sannan tace ita wancan ban ɗauketa bakin komai ba ƙyaleta tayta haushinta, kabarta da tunanin cewa duk wani Abunda yake faruwa da yarima itace take aikatawa, waziri yace amma Hajiya babba itama da nata fannin fa ina gani kamar hauka-hauka da yaronnan yakeyi itace take haifarwa danmu sam babu hauka a cikin namu tsarin, hajiya tace wannan ita ya shafa ita keda matsala da wannan, amma sanin kanka ne abubuwan dake jikin yaronnan wannan yarinya yafi ƙarfin ta nakasashi,
Da itace tayi kuskuren fara aika masa da sihiri ina tabbabatr maka kanta zata komai dawo
ganima tasamu,
jijjiga kai waziri yayi yace hakane ni kaina yaronnan yana bani mamaki duk yanda kaso nakasashi all'amarin baya tafiya dai-dai wani lokacinma sai yafara yimaka gizo,
Jijjiga kai hajiya tayi tace shiyasa nakeso akawo komai karshe idan abun yaƙicin tura aikin zai dawo wajanka ne kaamr yacce akayi shekarun baya shima har yanzu bamu samu matsala dashiba samada shekaru,
Waziri yace hajiya dama hakan akayi shi yafi sauki dan yafi kowani aiki kyau, zamansa a cikin masarautarnan yana daɗa karyarmin da guiwa buɗeɗɗen ido gareshi,
Waziri yace amma hajiya babba ina ganin kamar kinyi gaggawar nunawa hajiya suwaiba cikinki, hajiya babba tace akwai abunda nake nufi dayin hakan danayi kai dai kawai ka zuba ido,
Waziri yace hakane hajiya na gaskatawa aikinki sosai komai zakiyi yana ƙunshe da dalilai da nasarori masu tarin yawa,
Jinjina kai hajiya babba tayi kawai najin daɗin yabonda akayi mata,
sun shari yakai 30minute itada waziri suna tattaunawa gameda nasarori da kuma matsalolinsu sannan da yanda zasu magance matsalar,
Bayan sun gama hajiya tatashi zata shiga daga ciki juyowa tayi tadubi waziri tace waziri wannan karon bana buƙatar akasi ɗiyarka zata auri yarima takowani irin hali, mun dade dayin shuka, shukarmu tafara fitarsa tsirrai yakamata a halin yanzu mufara girbewe bazai yiwu muyi tsawon shekaru muna shuka sai dai muyita kallon tsiro yafitoba bamu ankaraba mu nemeshi mu rasaba wannan karon zamu girbe kayanmu,
Waziri yace zancenki haka yake hajiya wannan karon dole mu girbe shukarmu,
Juyawa hajiya tayi tashiga ciki Saida yaga wucewarta kafinnan yatashi shima yafita."
--------------
Friends ɗin adda saratu da sauran ƴan uwan aka ranƙwafa zuwa kai lefe mota uku suka cika ciff,
Gidan mummy suka fara wucewa nuna mata lefe mumny tana zaune tana ɗan hutawa tadawo daga aiki taji sallamar su adda saratu da sauran ƴan uwa,
Mumy bata tsure da mamaki ba saida taga akwatuna takwas anshigo dasu da guda 3 wanda tabada aka tafi dasu sai kuma wasu guda 5 set ɗinsu daban,
Da mamaki mummy take kallonsu takasa cewa komai, adda saratu tace lokaci yana tafiya ba zama zamuyi ba kayan lefen sadam ne barina kira yaya sai ku kalla tare dashi, cikin tashin hankali mummy tace sadam? Wane sadam ɗin? Shaƙa adda saratu tayi tace akwai wani sadam ne bayan na gidannan ko baki sanshi bane??
Mummy bata tankaba adda saratu tawuce ɗakin dady tayi masa magana yafito suka gaisa da mutanen dasuke palourn ya zauna aka fara nuna kaya dady yadubu adda saratu yace adda saratu waɗannan kayan basuyi yawa ba? Kuɗinda nabaki nasan bazai taɓa isa ya siya waɗannan kayanba,
Adda saratu tace yaya sam baiyi yawa ba wallhy saboda kowace mace da irin goshinta sannan ni kuɗinda kabani ma ban taɓashi ba shine zan ɗaura a saman akwatin mummy ta kasa danne abunda yake cikin zuciyarta tace amma kunsan gidanda zaku kai wannan kayan kuwa? Yar talla cefa za'a haɗawa wannan kayan kuma ni bawai annemi amincewa ta bace akan auren dan sam ban amince ba wallhy, da yardata sadam bazai auri ƴar talla ba, ai inada iko akansa kuma dole nafaɗa yaji, wata uwar harara adda saratu ta watsa mata tace aike kin gama aikinki kuma bama buƙatar amincewarki a wannan lamari tun farko danasan wancan yarinyar ba sonta sadam yakeyiba wallhy da bazai aureta ba ke dai kawai Allah ya taimakeki lamarin baizo kunneba sai yanzu amma dana gwada miki yanda ake iko ke kika haifi ɗan amma haka zan hanashi auren wacce kikeso ɗin, ke har zakiyi maganar wata iko wani irin iko kenan ai kinyi sake tunda nakama ikon naki nayi ramm dashi, aure kuma babu fashi kamar anyi an gama in sha Allah, mummy tayi shiru takasa tankawa saboda tasan halin dangim dady bala'eeu ne bana wasa ba, tsaff zasu naɗa mata kafirin duka idan tayi musu wargi dama gashi ita ɗin wani lokacin kamar kaɗan suke jira su afko mata, tajuya zuwaga dady wanda yayi shiru yana jinsu yasan duk masifar bala'in mummy sai dai tayi haƙuri tarabuda adda saratu dan its kaff danginsu maza da mata yara da manya bbu wanda baya shakkarta idan tafaɗi magana da anso da anki zance ya zauna,
Advertisement
Adda saratu taci gaba da ɗago kaya tanayi tana zazzaga ruwan bala'i da masifa babu wanda ya kulata kayan sunyi yawa bazai yiwu agansu duka a wannan lokacin ba dan haka aka rufe kawai gudun kar dare yayi, kayane expensive masu tsada da kyau akwatin turarruka kanshi dabanne, adda saratu tayi ƙoƙari sosai wajan haɗa kayannan ko ma ɗiyarta za'a kawo akace tahaɗa iyakaci kenan,
Duban dady tayi tace toh mudai zamu tafi mukai kaya Allaj ya sanya mana alkhairi acikinsa mugunji mugum gani mugun nufi nugun ido mugun baki Allah yashiga tsakaninmu dasu yayi mana tsari,
Dady ya amsa da Amiin sannan taɗaura da faɗin idan naje sai nayi maganar sanya rana duk da maza keyi amma ba laifi idanna fara tunkararsu sausu sanya su sanar damu,
Dady yace kamar yayi wuri bazamu bari su gama shiri ba? Dayake kinsan ba ƙarfi garesu ba, adda saratu tace wannan ba matsala bace ka manta ni waccec ne yaya? dariya dady yayi yace aikuwa natuna ina tareda Hamshaƙiyar women care foundation tace yawwa gara daka tuna ina zuwa za'ayi zancen rana su bamu rana saboda idan baki da ido yayi yaww a abu sai ahankali gara ayi-ayi ahuta yaro yasamu kwanciyar hankali shima yasan yayi auren soyayya, dady yasan tana wannan maganar ne danta ƙular da mummy amma saiya biyeta yace aikuwa kingamawa ɗanki komai har indai aka sanya biki nanda kwanaki kaɗan dan yana cikin wani yanayi, adda saratu tace in sh Allah komau yazo ƙarshe yaya Allah dai ya yi mana jagora a lamarinmu ya rabamu da gurɓatattun mutane, su duka suka amsa da amiin,
Mummy tacika tayo himm kamar zata fashe haka takejin zuciyarta jitakeyi kamar ta sanya hannu akayi tayta runtum ihu ko zataji sanyi akan abunda ake shirin aikata mata,
Su adda saratu suka fice zuwa kaywa kaya, sun isa gidansu sawwama da taimakon ɗan jagora sun sami gidan cike da mata, matan yayyun baba da ƙannensa da ƴan uwansa mata wanda saida malam sa'adu yayi da gaske kafin sukaje sai ƙannen mama da ƴan uwanta" an shin shinfiɗa tabarmi a cikin gidan gidane na ƙasa ƙal-ƙal dashi ko'ina tass tass kana kallonsu zaka tabbatar da talakawane kurmus amma kuma zaka tabbatar da cikar tsabtar mutanen dasuke zaune a cikin gidan, ko'ina a ƙalƙale gwanin sha'awa,
Tarɓan arziki suka samu dangin sadam sunata yaba karamci da mutumci irinna dangin sawwama kamar dam ayanda bahaushe yafaɗi wai shimfiɗat fuska tafi shimfiɗar taburma aikuwa sunga shimfiɗar fuska,
Har mota aka rakasu da abubuwanda aka tanada musu suna tafiya matan yaya zakari suka kaɗa buje suna faɗin ayidai mugani indai tusa zata hura wuta, duk ƙaryar anan zata ƙare sun nanata sayarda yarinya za'ayi yafi sau goma suna gama faɗin haka suka kaɗawa ƙafarsu iska,
wasu daga cikin ƴan uwan mama suka fara shewa suna faɗin ahayye yauga ranar haihuwwar ƴaƴa mata man matarda ake yiwa gorin haihuwar ƴaƴa mata itace yau aka kawowa ƴa mace abunda kaff mazan dangin basu taɓa yiba ƴa mace aka kawowa kayanda ko alabari ba'a taɓajn irinsaba ƴa mace aka kawowa abunda ko gidan tv ba'a taɓa gani ba, ayiririr yirriririr yau haihuwar ɗiya mace tay rana, dangin baba kaff jikinsu yay sanyi kamar wacce ruwa ya cinyesu sunyi kuƙus kowanne da guntun kunyarsa sunajin wannna zancen sunsan tabbas dasu akeyi,
Sukam mamaki yaƙi barin zuciyarsu gani sukeyi kamar ɗan shugabna ƙasane kawai zai iya haɗa wannan kaya."
Sai kusan magrib sawwama tadawo daga ismaliyya hannunta dauke da jakar ta take sanya ƙur'ani ɗinta da sauran littafai, tasamu gidannasu saura dangin mahaifiyarta zallah sai wasu ƴan tsirarru daga cịkin ƴan uwan baba,
Tana shiga gida kuwa shewa ana faɗin yarinya tayi goshi tayi goshi,
.Kunya sawwama kamar ta nutse a cikin ƙasa,
Sai wajan 8:30pm baba yadawo ganinsa sai aka fara yimasa sam barka daganan aka fara watsewa baba dayaga kayannan saida ya yi hawaye ashe mama itama tayi nata tun aɗaki lokacin tana jiyosu,
Baba yadubi mama yace amma ummi kina ganin idan muka amshi kayannan bamuyi son zuciyaba kuwa??
Nisawa mama tayi tace nima hankaline yaƙi kwanciya da kayan wallhy sam, sallama sukaji ta mace baba yace bismillah shigo, adda saratu ce tashigo da sallama ta isa suka bata wajan zam ata zauna bayan sun gaisa baba cikin sakin yace sai dai kuma fuskar taɗan kwantamin baiwar Allah, murmushi adda saratu tayi tace dama baku sanniba nu kanwar mahaifin sadam ce datsu tare muka kawo kaya toh lokacin naga da mutane shiyasa banyi magana ba bazai kuma yiwu indawo da safe ba saboda yanayin aikina sai yamma kuma banida tabbacin samunka yanzu ne dai nake ganin lokacin daya dace baba yace toh aAllah dai yasa lafiya adda saratu tace lafiya lau sai ɗumbin alkhairai danake tafe dasu, mama tace toh Allah yaƙara jaddadar damu cikin alkhairansa su duka suka amsa da amiin, tace nafarko dai inaso na baku wanna sakon taciro kuɗi bunch ɗin ƴan 1k guda 200k kenan tace ga wannan kudin ƙasan akwatine nacire yanzu na kawoshi baba bai sanya hannu ya amsa ba yace kuyiwa girman Allah kudaina tulo mana abubuwa haka aure zamu baku mutumci mukeson ƙullawa atsakani ba kuɗi ba wannan kayanma da kuka kawo yanzu nake zancen za'a rage a maidasu sunyi yawa,
Adda saratu tace basuyi yawa ba iri muka gani a wajanku munaso toh babu laify dan mun kyautata muku kyautatawace kuma wanda ya ɗauki ɗiyarsa yabaka bakada wami abunda zaka biyashi dashi,
Kuyi hakuri ku karɓa bbu kyau maida hannun kyauta baya, shiru su baba sukayi dai basuce komai ba,
Adda saratu taci gaba da faɗin sannan suna roƙon arziki da alfarmar akan a sanya mana biki man da sati biyu,
Shiru baba yayi yace maganar gaskiya magana ta Allah itace biki bazai yiwu man da 2weeks ba, saboda yanayin shirye-shirye ance wai mai ƙwarmin ido dawuri yake fara kuka,
Adda saratu tace eh toh akwai wata ƙungiya danake da ita wanda muke taimakawa mata takowani irin hanya marassa sana'a mubasu sana'a wanda zasuyi aure zamuyi musu aure, wannan duk fannin taimakawa cigaban matane, toh alal haƙika na saka sunanta a waƴanda za ai musu kayan ɗaki har anbada order da komai da komai, karkuƙi wannan badaga ni bane wannna daga ƙungiyace,
Nasan zakuce A'a saboda na lura daku mutanene dasukasan ciwon kansu sosai toh abun ba haka yakeba shi kayan sure da iyayen yarinya sukeyi all'adane ba addini ba wannan duk hakkin mijine, ni bawai nafaɗawa kowa akan kayan ɗakinta daga wajanmu zai fito bane hatta da mijinta bai sani ba inaso kuma idan kun amince sai kuyi shiru da bakinku,
Ƴan ƙananun kaya haka zaku saya mata na amfanin gida amma funitures kam Allah yagani wannan nayi niyyarsu, zancen aure nanda sati biyu kuma zan barku kuyi shawari zan dawo zuwa gobe dan sanin matsyaarda muke ciki,
Godiya sukayi mata sosai tayi musu sallama tatafi aka tsaya akan gobe zata dawo jin matsayar zance."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
Werewolf huntress tribe
During the tutorial phase of her planet, Natasha Smith awaken with a race changing skill making her a werewolf, it also gave her an extra *tool* that she will need to use to grow her tribe and defeat her enemies.
8 226Jintetsu
The adventures of an Oni, who wishes to see just how big the world could be.
8 157Dungeon Irregular
A calamity among all boss monsters, the strongest living being, and a powerful weapon of an alien civilization is born. Well, at least that was the plan. Lucy was supposed to be the final boss of a heroic battle but... things don't always go as planned. This is the first wn I wrote. It is a hobby project I started to improve my vocab. Have mercy plz All credit for the cover goes to me, drew it myself in Photoshop :P
8 107Dimension Records (Ring of Reincarnation )
A Normal day in Tokyo a 31 year old politician get killed, by a gang choking him to death and gets reincarnated from a small world where not much about the universe is known, to a world that was first out of every world in cosmos.
8 81Demon Contractor Unknowingly Becomes Less Of A Jerk
Alright so I guess the basic summary would be. A demon with the ability to make contracts with the gods themselves, after working for his king for several years decides to hunt his original prey, the humans as the war between humans and demons has ended. He goes to the human land aiming to create pure chaos using his abilities but has to stop as he encounters some strange humans. He pauses his journey is joined by a beast man and a little mage to figure what is going on. (Alright dis is a newbies work and all so I just hope that this is good enough)
8 98Fandomshots O(≧∇≦)O
heyyy,uh these are random stories from different fandoms I'm in,just for fun!whoop whoop! I'm hyped for these new stories!some might be one shots some may get more parts,idk.some could be ships some might not be idk depends on how I feel.
8 58