《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 41
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Alhamdulillahi bayan tsawon lokaci yau Allah yayi dawowata in sha Allah zanci gaba da kawo muku Ƙaddarar rayuwa da yardar ubangiji."
Page 41
Jikin yarima kwana biyu yana ɗan tashi da dare ko kaɗan basu samun bacci danma wani lokacin mai martaba wajansa yake kwana,
Nabila sai idan rana tayi kafinnan take samun bacci, wahalarda takesha kwana biyunman ba abune mai misaltuwa ba,
Haka yauma suka kwana basuyi bacci ba, da rana ma haka tayta juyi akan gadon ta kasa bacci tunanine fall cikin ranta samada shekara guda suna abu ɗaya sai ciwon yayi kamar zai warke sai ya dawo sai yayi kamar zai warke sai yadawo, kwana biyunnan har wata rama tayi, zuciyarta ce take tambayarta shin haka rayuwarta zata ƙare cikin bauta batareda wani ci gaba ba? Haka zata zauna tayita bautar mutuminda bai masan tanayi ba?
Wanda a fili ƙiri-ƙiri yake nuna tsanarta, yanzu tafara gajiyawa sosai da irin halinda take ciki koda yaushe rayuwarta ahaka take, tunda ta auri yarima ko anguwa bata taɓa zuwa ba shekara guda, Sau biyu ta taɓa kallon mahaifiyarta, mahaifinta kuwa a shekarannan bata sanyashi a ido ba, nabila batasan lokacinda kukan tausayin kanta ya kwace mata ba, sanda tayi kuka har kanta yafara yimata ciwo sannan ta tsagaida ta ɗauki waya da danna,
Bugu biyu aka daga kiran mahaifiyarta ne cikin kulawa tayi sallama kasa amsawa nabila tayi cikeda tausayin kanta kuka ya kwace mata mai cike da tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro,
Shiru mahaifiyar nabila tayi na tsawon lokaci bata hanata kukanba sannan kuma bata tanka ba, shiru tayi ta tsaya tanaa sauraren kukan diyartata tana nazari akan kukanta tana sauraron yarenda yake cikin kukan da nabila takeyi wanda uwace kawai takeda wannan damar uwace kawai zata fahimci halinda diyarta take ciki daga sauraron muryarta kawai batareda labbanta sun furta halinda take ciki ba,
Nabila bata iya furta komaiba face kukanda yaci karfinta yafi karfin kalaman bakinta ta cikinsa kadai take samun damar isarda kuncin da zuciyarta take ciki da cikinsa kadai zata iya bayyana irin rayuwar takunkumin datake ciki, katse kiran tayi bayan zuciyarta takasa cigaba da sauraron halinda diyartata kecikiba,
Nabila batasan mahaifiyarta ta kashe wayarba domin hankalinta baya jikinta kukanta kawai takeyi domin fitarda dattin dake cikin zuciyarta ko zata samu sassauci a lamarin,
Tashiga tashin hankali sosai sakamakon jin kukan ɗiyarta mai cikeda kunci a ciki takasa tabuka komai zuciyarta tayi rauni yayinda hankalinta hankalinta gabaki daya yayi kan nabila saida ta dauki lokaci sannan tasake kiranta lokacin tanada tabbacin ta tsagaita da kukan nabila kuwa bayan ta idda kukanta iya son ranta tatatshi ta wanke fuskarta tadanji sanyi cikin ranta saboda fittarda kuncin datayi ta hanyar kuka, tana zaune wayarta tafara ruri tayi picking wayar cikin nutsuwa hadeda yin sallama mahaifiyarta tadan sauke ajiyar zuciya sakamakon muryar nabila dataji tadaina kukan,
Amsa sallamar tayi tace lafiya wani abunne yafaru kika kirani kina kuka? Nabila ta girgiza kai kamar wacce take gaban mahaifiyarta tace bbu komai umma mahaifiyarta tace bangane babu komaiba nabila akwai abunda zaki boyemin ne? Nifa mahaifiyarkice najiki kina kuka sannan kuma naji rauni cikin muryarki ina tunanin koda nunfashi kika fitar har indai yafito da wata manufa ina iya ganeshi bare kukanki,
Cikin kawarda zancen nabila tace kawai inason ganinkine kwana biyu watana hudu rabonda na sanyaki a ido shiyasa,
Ummanta tace toh ai hakuri zakiyi amma bai kamata kizauna kina kuka akan wannan dalilin ba, kinema abarki kizo idan babu hali zan samu rana nazo naganki naduba jikin mijinnaki,
Toh kawai nabila ta amsa saboda tasan ba zuwa mahaifiyartata zatayiba itama ba samun zuwa zatayiba barinma yanda yanzu jikin yarima ke tashi akai-akai,
Advertisement
Haka sukayi sallama badan mahaifiyarta tayarda da hakanne kadai damuwar ƴar tata ba."
--------
Ina cikin mawuyacin hali mai wuyar misaltawa ina cikin tashin hankali da matsin rayuwa Ina cikin gushewar tunani da sarkakiya a cikin rayuwa amma akoda yaushe na tuna cewa zakizo gareni zaki zama maganin cutarda take damuna nakan samu sanyi nakanji zuciyata ta warke daga zullumin datake ciki, na kanji sanyi a zuciyata da gabban jikina,
Dago kai tayi ta dubeshi cikin tausayawa idanuwanta yana zubda hawaye a kullum kalamanda wannan mutumi yake fadi kenan akoda yaushe a duk sa'in daya furta mata waɗannan kalaman tana cika da tausayinsa da tausayin halinda yake ciki sakamakon irin yanayi dayake ciki wanda yazama dole a tausaya masa yana cikin halin kunci da matsin rayuwa yana cikin kunci taraddadi da sarƙaƙiya na ryuwa ga dukkan alamu yana cikin rayuws mai cikeda ƙulli,
Wata muryace tadaban wacce ko kadan batayi makamanciya da wancan ba tafara yimata amo a kunne da fadin zakizo gareni zaki zama haske a cikin rayuwata zaki kawomin farin cikin dana rasa na tsawon shekaru,
Arazane sawwama tafarka daga baccinta sakamakon jin murya datayi wacce batayi makamanciya da wacce takeji a baccinta ba, addu'a tafaryi sosai sannan hankalinta yafara kwanciya numfashinta yafraa dai-dai ta batasan dalili ba kwannan take yawan mafarki da wannan mutumi yana neman tashigo rayuwarsa domin fitar dashi daga kuncin dayake ciki tashigo rayywarsa domin cireshi daga sarkakiyar rayuwar dayake ciki, takwana biyu tana wannan mafarkin wanda da zarar tafarka takan tsinci kanta cikin mutuwar jiki,
Yau kuma abunda ya tsoratata shine wata murya dataji ta daban wanda take fadin taza shigo rayuwarsa takawo haske da farin ciki a cikin rayuwarsa,
Batasan mai waɗannan mafarkai suke nufi ba amma haka kawai takeji a jikinta da ayar tambaya akan mafarkin, juyi tayi tadauki wayarta dake gefe taduba ko zataga missed call din sadam amma shiru bbu missed call dinsa, maida wayar tayi ta ajiye takara komawa ta kwanta."
Washe gari da safe ta shirya zuwa makaranta batareda ta fadawa kowa gameda mafarkin dat akeyiba,
Bayan sun tashi a school tafito domin zuwa gida tana tafiyarta cikin nutsuwa kamar yanda tasaba akoda yaushe a oppsite da gate din school dinsu yayi parking motanshi tsallaken titi,
Tun daga nesa ta hangeshi ya na tsaye jikin motan tanada tabbacin ita yake jira dan haka cikin nutsuwa tanufi wajansa daga nesa ya hangeta ya sauke ajiyar zuciya hadeda sake mata wani lallausan murmushi itama nata murmushin tasake masa mai narkarda zuciya, takarasa cikin sanyayyar muryarta tace yaya sadam ina wuni? Murmusawa yakarayi sannan yace lafiya sawwamaty ya karatu?
Alhamdulillah ta amsa atakaice sannan tayi shiru acikin ranta tana yaba yanda yakara cika yayi haske da kyau wato duk yanda namiji yayi aure yakan canja koda na lokaci kadanne,
Muryarsacr ta katse mata tunaninta da fadin shiga muje batayi masa musu ba ta shige motan shima ya shiga driver seat yafara driving a hankali sun dauki tsawon mintuna uku babu wanda yacewa kowa komai sanyayyen kamshin turarensane ya karade ko'ina a cikin motan kanta yana waje tana kallon titi amma hankalinta yana gareshi muryarsa tajiyo yana fadin saura kwana nawa kufara exam? Mako biyu tabashi amsa atakaice ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta finally mun kusa kasancewa atare, bansan wani irin farin ciki zan tsinci kaina a cikiba aranar da aka daura mana sure aka bani tabbacin kin zama matata, aka mallakamin ke zanyi farin cikin samun mace kamarki zanyi alfahari nasamawa ƴaƴana uwa tagari, murmushi kawai sawwama tayi batareda tace komaiba juyawa yayi ya kalleta sannan ya maida kansa akan tukin yanajin wani sanyi cikin ransa, wayarshice tadauki ruri a hankali yakai kallonsa gareta abida ce mai kira batareda ya taba wayarba ya juyarda kansa gefe yacigaba da driving cikin sanyayyar muryarta tace yaya sadam kiranka fa akeyi kadauka mana!
Advertisement
Batareda ya kalleta ba yace bana picking call idan ina driving, mamakin sawwama sosai yakeyi koda sau daya a rayuwarta bata taba gwada masa bacin ranta akan aurenda yayiba bata taɓa nuna masa rashin jin daɗinta idan bai kirata ba sam batada complain komai akayi bazata tankaba wannan yana daya daga cikin halayen dayake burgeshi yake sanyawa yana kara sonta,
Koda sau daya bata taɓa tambayarsa matarsa ko dalilin auren ba, bata taɓa furta kalma daya akan aurensa ba, bata taɓa nuna damuwarta ko akasin hakanba,
Tafiyarda zata daukesu baifi 20minute ba tadaukesu morethan 40minutes saboda yanda yake tukin cikin saiɓi kamar wacce aka sanyashi adole amma a zahirin gaskiya bayaso yarabu da sawwama ne ya sanyashi yin tuki ahakan,
Dai-dai ƙofar gidansu ya tsaya sannan yajuyo ya dubeta kanta yana kasa tana wasa da yatsun hannunta bata dagoba agogon hannunsa yaduba sannan ya maida kallonsa gareta yace zuwa magrib in sha Allah zan shigo yanzu akwai yanda zanje kuma krma akwai alamun yunwa a tattare dake ki tabbatar kina shiga kin samarwa kanki abinci, idan nadawo saiki duba idan akwai abunda yake baki wahala a karatunki saiki fitoda littafin nagani, toh sawwama tace sannan tayi masa godiya da sallama tafice, binta da kallo yayi sannan ya sauke ajiyar zuciya, yadade a wajan sannan yaja motarsa yabar harabar gidan,
Bayan magrib sadam ya sake wanka cikin shadda milk wacce take faman sheqi ya daura hula akan gashinsa yafeshe turare sai kamshi yakeyi ya daura agogonsa a hannunsa ya fito cikin sauri zai fice, saurin shan gabansa abida tayi itama taci wankanta cikin doguwar rigar abaya tayi kyau sosai cikin kissa da shagwaɓa take fadin habibi ina zaka fita da wannan kwalliyar?
Cikin sauri sadam yace wani wane zanje,
Diddire kafa tafarayi tana fadin gaskiya bazaka koina ba ni gaskiya kabarni nayta kallonka iska sadam ya furzar yace akwai alkawarin danayi zamu hadu da wanine amma in sha Allah bazan dade ba yanzu zan dawo, sadam yasakaya zancenne saboda baison taji wani iri kuma yasan zataji din har indai tasan wajan sawwama zaije, turo baki tayi tace koma waye gaskiya sai dai yayi hakuri amma banajin zan iya barinka kafita da wannan wannan kwalliyar zaiyi magana tayi saurin sanya bakinta tarufe nasa bakin sadam baiyi kokarin kwacewa ba yabarta tayi yanda takeso dashi daga karshe kafafuwansane suka kasa daukarsa ya zube akan kujerar nan danan tafidda sadam daga hayyacinsa ya manta da fitar dayace zaiyi bai dawo hayyacinsa ba sai bayan wani lokaci lokacin dare yayi yasan bai dace yaje wajan sawwama a irin wannan lokacin ba, kallonsa yakai akan abida dake kwance akan kirjinsa tana baccinta hankali kwance miƙewa yayi ya dauketa ya kaita daki ya kwantar zai zare jikinsa tayi saurin kankameshi komawa yayi suka kwanta tare, sai bayan baccin nata yayi karfi sosai sannan ya miƙe daga jikinta ya dauki phone dinsa yafice palour dialing number din sawwama yayi har zata fara ring yayi saurin hanging bai san daliliba amma sai yake ganin rashin dacewar hakan kiran sawwama a cikin wannan daren matsayinsa na mai aure
komawa yayi yazauna yana jin wani iri aransa bai saba yiwa sawwama alƙawari sannan kuma ya karya ba, yasan tazuba ido da ganinsa harta hakura, cheeeee yafaɗi a fili cikin rashin jin dadin abunda yayi,
Sawwama kuwa tajira-tajira harta gaji ganin dare yayi ya sanya ta cire rai, tazauna tayi tagumi tana jiran shigowar kiransa amma shiru, har dare ya tsala, hawayene yafara gangara akan kumatunta tabbas tasan sadam ya canja mata sam bata samun kulawa agareshi irinna baya, bataso ta sanya abun a rantane harya dameta, bataso taringa tunanin abun harta sanyawa ranta matarsa kesawa yana nisantarta tafara jin haushinta sam batason faruwar hakan,
Wata zuciyarta take fada mata dama dole zataga canji daga wajansa dan haka ta kwantar da hankalinta yana tareda cikekkiyar mace wacce ta kawo masa cikekken budurcinta batareda wani yasanta ba shine farkon saninta dole tasamu sauyi daga wajansa tunda yadade da sanin cewa wani yataɓa kusantarta, yasan cewa bazata zo masa acike kamar yacce wancan tazo masa ba,
Kukane ya kufce mata tanajin wani irin ɗaci acikin ranta bazata daina jin zafi da neman sakayyar ubangiji akan wannan mutumi ba har ranarda zata bar duniya, a cikin wannan hali bacci ya dauketa, bbu fashi mafarkin data sabayi yauna sanda tayishi nayau yafi na kullum daga mata hankali nayau yafi na kullum bata tausayi,
Amma yau bataji dayan muryar dataji jiya ba, bataji amon wancan murya ba,
Kiran sallar asuban fari tatashi sakamakon sururun mafarkin datakeyi ya hanata samun bacci mai dadi."
Sadam yanzu yamma tanayi yake ficewa a gidansa yawuce zuwa wani wajan daban koda kuwa baida wajan zuwa yakan fita saboda yasamu ya leka sawwama domin da zarrar yabari yashiga gida bayan magrib ko isha'i abida bata barinsa yasake fitowa takan riƙeshi da salonta tayi amfani da hakan ta hanashi fita ko'ina,
Sosai yadage wajan koyawa sawwama karatu akan abubuwanda suke bata wahala har suka fara exam cikin yardar ubangiji,
Ganin sun fara exam ya sanya yayiwa mahaifiyarsa maganar kaiwa kaya dan yanaso da zarar tagama exam baya bukatar karin sati guda idan kuma za'a karan bayaso yawuce sati guda ayi auren kawai,
Mahaifiyarshi tabashi rana akan yafada musu ranarda zasuzo,
Saura 2days sukai kaya sadam suna zaune a palour shida abida yayi matashi ya cinyoyinta wanda suke a waje domin dan karamin bumshort ne a ajikinta da kadan girmansa yafi na pant sai yar yololuwar riga wacce bazata wuce iya cibiyarta ba shara-shara ce komai ana kallo a jikinta,
Wayarshi dake gefe tadauki ruri yakai hannu zai dauka abida tayi saurin kaiwa nata hannun ta rigashi dauka sanda taduba taga mummy ke kira sannan ta amsa ta kara mai a kunne, cikin nutsuwarsa ya gaida mummy batareda ta amsaba tace kazo gida yanzu ina jiranka, tana fadin haka ta katse kallo yabi wayar dashi yana tunanin komenene kuma yafaru? Domin yanayin mummy ya nuna akwai wani abun akasa,
Miƙewa yayi yadubi abida yace ina zuwa mumy na nemana yanzu, ga mamakinsa daga kai tayi da murmushi batayi wannan tijararta ba domin idanya tashi fita ba mummy ba ko dady ke nemansa takanyi tijararta son ranta,
ransa cikeda zullumi yanufi gidansu yana zuwa yasamu mummy zaune a palour sai wani cika takeyi tana batsewa zaunawa yayi gefenta yace sannu da gida mumy ina wuni?
Cikin hasala mumy tace daban wuniba ga ganni? Nace da ban wuniba zaka ganni?
Cikin rashin fahimta sadam yace kiyi hakuri mummy amma wani abunne yafaru wallhy bansaniba idan na ɓata miki rai cikin rashin sanine da ajizanci na ɗan adam kiyi hakuri,
Mummy tace yoh iyi dole ai dolenka kafadi haka ba an shanyeka ba! Yanzu sadam fisabilillhi duk ƴan matan duniyarnan karasa wacce kakeso zata aura sai mai tallan awara? Ƴar tallance ta burgeka? Itace wacce kagani kakeson hada jini da ita? wacce tagama yawan bambaɗancinta a wajan tallah tafita dubiya kowa yaganta yaga surar jikinta, Yanzu kai abun kunyarda zaka kwasomin kenan?
Ƴar talla sadam Ƴar tallah? Hankalinka kalau kana cikin hayyacinka anya kuwa? Bansan yaushe har taɓararka da iso ga hakaba, bansaniba, tsabar shahanci da rashin sanin ciwon kai zaka auromin ƴar talla ta haifomin jikoki? Wallhy ko bayan raina sadam ban amince da wannan aurenba, badaniba tafaɗi tana kƴaɓe baki,
Duk sanyin Ac ɗin dake palour din bai hana zufa ketaowa sadam ba, a yanzu bayida wani babban buri daya sanya agaba kamar auran sawwama baida wani buri daya wuce yaganta matsayin matarsa, yanayi mata wani irinso wanda a halin yanzu baya tunanin zuciyarsa zata iya rabuwa da ita, rabuwarsu dai-dai yakeda tarwatsa duk wani farin ciki dayake tattare dashi, rabuwarsu dai-dai yake da ruguza duk wani plan dinsa na rayuwa anan gaba, zai dawo hopeless and useless idan akace zaici gaba da rayuwa batareda sawwama ba,
Wasu hawaye masu ɗumin gaske yaji suna saukowa akan kumatunsa zuciyarsa tafara ƙuna idanuwansa suna soyuwa gangar jikinsa tana rasa duk wata laka dayake tattare da ita, bai san mai yayiwa mahaifiyarsa ba a rayuwa takeyi masa wannan abun baisan mai ya aikata mata da muni hakaba datake ƙoƙarin rabashi da farin cikinsa ba,
Hassana da hussaina dasuke tsaya jikinsu yayi mugun sanyi jin kalaman mahaifiyar tasu wanda take fadosu batareda kowani irin tunani ba,
Miƙewa sadam yayi yabar gidan cikin ƙunar zuciya, awaya ya kira dady ya sanar dashi yanda sukayi da mummy dady yace karka damu sadam karka ɗaga hankalinka kamar yacce kayi mata biyayya kabi zaɓinta a karon farko yazame mata dole itama tabi naka zaɓin yazama mata dole tabarka ka auri wacce kakeso shi namiji anayi masa auren dolene? Amma kai tayi maka ka yarda ka amince ka zauna da zaɓinta lafiya itama yazaka dole ta yarda da zaɓinka sadam karya alƙawari baya ɗaya daga cikin halayena nasam kasanda hakan! So mahaifiyarka da yardarta ko amincewarta ko akasin haka zan aura maka wannan yarinya, in sha Allahu sannan ka sanar dasu kaiwa kaya yananan a jibi babu fashi a cikin lamarinm muba ƙananun mutane bane da zamuyi magana sannan kuma mu canja ba, bazai yiwuba yin hakan dai-dai take da zubda girmanmu, wanda zaiyi alƙawari yasaɓa batareda ƙwaƙƙwaran daliliba shi ake kira da ƙaramin mutum inaso ka riƙe wannan in sha Allah bbu abunda zai gagara,
Hankalin sadam yadan kwanta amma tuna zancen mahaifiyarsa data ambaci sai dai in bayan ranta ya sanya ƙirjinsa bugawa daram,
Yace amma dady tace fa sai dai in bayan ranta, shiru dady yayi jin kalmarda sadam yafaɗi sam baiso mummynsu taringa amfani da irin wannan kalma dan sam ba kalma mai kyau bace, idan tazo da ƙarar kwana sai kaga ta mutu kuma anyi auren har indai da rabo, cikin sanyin jiki dady yace zan sameta sadam in sha Allahu babu abunda yafi ƙarfin ubangiji ka sanya wannan aranka duk abunda kaga yafaru da sanin Allah sannan ni matsayina na mahaifinka zanyi ƙoƙari naga na shawo kan lamarin za'ayi komai cikin yardar ubangiji,
Sadam yace Allah yayarda sannan yayi ending call ɗin,
Ya kifa kansa a jikin sityarin motan ya lunshe ido yanajin kuna cikin zuciyarsa idanuwansa suna suya wanda ya gwammaji ya zauna yayita rera kuka ko hakan zaisa yaji sanyi amma kukanma yaƙi zuwa,
Daga ƙarshe rasa yanda zaiyi yaji dadi yayi hakan yasa ya kira sawwama a waya ya shaida mata yana zuwa yanzu."
Nasan dayawanku bakuji dadin tsayawa da typing da nayiba toh Alhamdulillahi yanzu nadawo kuma ina mai baku hakuri sakamakon faruwar hakan nagode da message da kiranku kwarai da gaske naji dadi maras misaltuwa adauk lokacin nasamu kira akan yaushe zanci gabada typing din ƙaddarar rayuwa nakan samu kaina cikin nishaɗi kuma haka yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sani na dawo da rubutashi bansan book ɗin yakarɓu har hakaba sai lokacin dana tsaya da rubutunsa toh gashi nadawo
Allah yabani ikon karasa muku cikin kwanciyar hankali, sannan kuma dan Allah adage da comment rashin comment yakan sakani naji ƙiwar yin typing amma da zarar nahau naga commenr sai naji wani nishaɗi saina tsinci kaina dason sake yin rubutu adai-dai wannan lokaci."
Allah yabani ikon yimuku rubutu kukuma Allah yabaku ikon yin comment."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial23 Chapters
Player Killer
In the world of New Dawn, the citizens seem to be suffering a divine punishment of some sort. The monsters that plague them are worse then devils, demons, or depraved criminals. The devils have their own twisted morality, demons are not intrinsically bad—they're just above humans in the food chain—and depraved criminals can at least be killed. The undying, capricious monsters kill anything and everything, devouring all in their sights like a swarm of locusts. What's more, the lords and kings who should be protecting them seem to be working with these monsters. When all seems lost, it falls to a young boy to save his people from these monsters… from the players. … In the players' eyes, he is a hidden boss—possibly even the final boss! In the developers' eyes… what the heck is this bug?!
8 253 - In Serial8 Chapters
Exchange Cultivator
Ye Hao cultivated with a single goal to achieve immortality, he cultivated diligently day and night, but to his horror, his results were just above average unable to accept the outcome. He left on a quest to find some opportunity, to achieve a breakthrough, unexpectedly he got a huge opportunity- Inheritance of 9 stage Tribulation Transcendent, he was over the moon, as he walked to accept the inheritance, someone killed him. ye hao last breath left the murin world. He knew he had died but really what was going on, he felt the sensation of soft pillow on his head, he quickly opened his eye, he saw a whole new world before him, he was initially happy he had survived, the feeling of dying, fading away was quite horrific but he lived. He had traveled through the Time-Space swapping body with the Below-Average rich boy, after recovering his sense he quickly checked his ding-dong, to his merry, it was there. If it was a woman's body, man it would have been awkward, so embarrassing, he would have committed suicide, rather than live shamefully, really. After calming down, he tried sensing his cultivation, there was no response, no feeling, "my cultivation... is..gone" "just like that.. it is gone" There were now two options, one start all over or to live a normal life, Feeling frustrated to cultivate all over, he gave up on cultivation all over. With a resolute heart, he decides to live a normal life. This world was different, so he thought he could take a different path in this life and live a life full of fun, no closed-door cultivation for decades only to suffer from piles. This world was quite the wonder, with its culture, technology, it was totally different from his previous world where weak and mortal were considered less than trash. He especially liked the Internet thing, god knows how addicted he became to insta reels, surfing for hours, and watching web-show, dramas. otherworldy fairies with no comparison would sing and dance for him free, life was truly awesome here. Among all the things he liked reading web-novel, he jokingly compared his experience with the main character where they send to the magical world, becoming extraordinary powerful, he frowned wasn't he the exact opposite? "..." "So am I like a waste product of this... boy" "he got Isekaied, WTF" he laughed, thinking all this. hadn't he left all this stuff behind, so why waste time thinking this, now he will enjoy his slow life. ------ Unknown to him, how heaven's were playing game with him, it was like feeding the sheep with luxury before butchering him. Would he be able to survive that?
8 139 - In Serial193 Chapters
Mortem Comedenti(Death Eater)
"How I wish I could save you from the anguish and pain you will receive. You will walk alone, afraid. You will gain power that you hate. That hate will turn towards yourself. Your convictions and principles will be challenged and thrown into the fires and woes of regret. Sorrow will replace your bones, anger will flow instead of blood, deceit will shape your eyes. Maybe, if your will is strong enough, Your soul will remain." Thanks Asviloka for the cover! :)
8 139 - In Serial6 Chapters
Super Sock Knitter
Knitting Fan Mei transmigrated into a world almost exactly like her own, except for one small detail. This new world had Superpowered Socks. Join Mei as she makes her way toward ultimate sock destruction. Inspired by Card Apprentice and Master of the Trading Star Card Game Instead of a world of cards, I just used socks, to me seems more interesting
8 188 - In Serial19 Chapters
Remarkable (Dance Moms Fic)
Abby Lee Miller's 14 soon to be 15 year old son, Shane, helps her lead her studio, the Abby Lee Dance Company to the Dancing National Title, can they do it? With moms causing drama, it's gonna be a bumpy ride to the title.
8 87 - In Serial33 Chapters
A Thousand Years
My name is Nina Ōtsutsuki. A thousand years ago I made a promise; one that I have never forgotten. Unfortunately, my friends seem to have some troublesome descendants, and their reincarnations are no better. [Madara x OC]
8 133

