《ƘADDARAR RAYUWA》K page 32
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 32
Da fara'a baba ya ƙarasa wajan yana faɗin A'a yaya zakari kaine agidan namu? Aida kayimun aike sai nazo basai kazo ba, da fara'a yaya zakari yace A'a zuwanne ai ya kama shi yasa kaganni niɗinne yakamata inzo ba kaiba, baba yace toh Allah yasa dai lafiya yaya? yaya zakari yace Ahh lafiyace ta kawoni wallhy haɗeda ɗumbin alkairi, baba yace toh alhamdulillahi madallah abu yayi kyau,
Gaisawa sukayi baba ya tambayi ya iyali yaya zakari yace sunanan lafiya to madallah haka akeso ai baba ya amsa,
miƙewa baba yayi yace barina shiga ciki na dauko tabarma yana faɗin haka ya sanya kansa ya shiga ciki a ƙanƙanin lokaci yadawo hannunsa riƙeda tabarma shimfiɗawa yayi yace yaya bismillah suka zauna,
Yaya zakari yace toh alkhairi ke tafe dani hamisu yarone ɗan wajena ismail ya hango abunda mu bamu hangoba kasan ana faɗin abunda babba ya hango yaro ko ya hau rimi bazai hango ba amma wannan karon zancem ba haka yake ba wannna karon yaron shine ya hangi abunda mu manyan bamu ganiba,
Cikin rashin fahimtar yanda maganar yaya zakari tadosa baba yace kamar me kenan ba yaya?
Shigowar halima zauren hannunta d'aukeda ruwa a cup na silver yasa sukayi shiru amsa sallamarta sukayi ta isa ta ajiye ruwan had'eda gaida yaya zakari amsawa yayi cikin fara'a,
Sai bayan tatafi sannan yaya zakari yace toh ismaila dai yazomun da wani zance, to shine na zauna dakyau nayi tunani sai naga zancensa yana kan hanya, yaro yayi kyan kai,
Shiru baba yayi yana saurarensa yaya zakari yaci gabada faɗin
Wato shi ismail yaga ƴar wajanka babbar me sunan mama kenan koh?
Baba yace sawwama kenan?
Yaya zakari yace eh ita ce inaga babbar dai yacemin ranar dayazo ya ganta ya yaba da hankalinta sosai sannan ya shaidamin cewa yana sonta zai aureta, gaban baba yafad'i dammm jin zancen ɗan uwannnasa yaya zakari yaci gaba da faɗin to shine nace barina sameka dan wannan abun farin ciki ne sosai zumunci mai ƙarfine zai ƙara ƙulluwa atsakani, dama nace masa toh baza'ayi abu kai tsayeba zan sameka kai mahaifin yarinya in faɗa maka sannan kuma kaje kayi shawara da mahaifiyar yarinya dakuma ita kanta yarinya kaji ta bakinsu idan babu idan wani tsayayye sai ayi magana tunda wuri ayi abu cikin kwanciyar hankali, tunda nasan koda ka samesu toh ai abu bazai gagara ba dan suma zasuyi murna amma adai samesu ɗin,
Advertisement
Baba kansa yana ƙasa daƙyar ya iya ɗagowa ya ɓoye damuwarsa yace toh shikenan yaya In sha Allahu can samesu muyi magana yanda mukayi zan sanar dakai Allah ya za6a mana abunda yafi alkhairi, yaya zakari ya amsa da amim miƙewa yayi yana faɗin toni barina wuce yanda kukayi sai ka sanar dani ɗin,
Baba yace har tafiya yaya baku gaisa da mutanen gidanba gashi kuma ko ruwa baka shaba, yaya zakari yace Alhamdulillahi nagode ina gama cin abinci na taho ka gaidamin da iyalin, baba yace toh zataji, miƙewa yayi ya rakashi har waje da ɗan nisa kafinnan yadawo,
Jiki a sanyaye baba ya shiga gida zama yayi gabaki ɗaya kamar wanda ruwa ya cinyeshi, mama ta kalli baba cikin kulawa tace baban sawwama wani abunne yafaru?
Girgiza kai baba yayi yace ummi bai faruba amna yana gab da faruwa saboda zancenda yaya zakari yazomin dashi yau yayi matuƙar girgizani narasa awani ma'auni can ajiye zancen,
Mama ta matso kusa dashi tace mai yazo maka dashi kuma?
Shiru baba yayi yakasa cewa komai yayi ƙasa da kansa, mama wacce iya tunaninta ya tsaya a abunda ta fahimta tace baban sawwama hhar indai akainane kada ka sanya ranka a damuwa nasan zancen bai wuce ace ka ƙara aure domin samun ɗa namiji da zai gajeka ya kula da kai ba, idanta nine kada kaji damuwa domin ba hanaka zanyi ba,
Girgiza kai baba yayi yace da wannan ne zaifi yimun sauki ummi domin inada damar da dance eh ko A'a wannan kaina kaɗai ya ashafa ba ƴaƴana ba zan iya ɗaukan ko wani irin lamari duk zafinsa akaina amma ba akan ƴaƴana ba,
Mama wacce kanta ya gama kullewa tace ban gane mai kake mufiba baban sawwama, baba yace wai ɗan wajansa isma'il yakeson auren sawwama, dafa ƙirji mama tayi tace auren sawwama kuma?
Baba yace haka dai yace kingani na farko bazan iya bashi auren sawwama ba saboda dalilai biyu, na biyu rashin bashi auren sawwama zai ta6a zamuncin mu,
Advertisement
Abu na farko da zaisa bazan bashi auren sawwama ba shine dalilin wannan abu daya faru da ita idan ɗansa ya aureta dole zai san da faruwar hakan zai dauki mamana da wata manufa ya ringa yimata mummunan kallo, ba fata akeyiba ba lallai ya iyaci gaba da zama da itaba, kuma bazai yiwu mugaya musu yanzuba saboda faruwar abu samada shekara uku ace bamu sanar da dangiba saida akazo neman aurenta zasu iya yiwa mamana wani mummunan fassara nikuma bazanso hakaba yayinda bazanso abunda zai taɓa zuciyar mamana ko yaya yake sannan daga karshe zasu iya cewa sun fasa auren yayinda sukaji wannan labarin kuma ba lallai dan suna ƴan uwanmu ace sun rufa mana siriinmu ba,-
Abu na biyu da zaisa bazan bashi aurentaba shine inason abunda mamana takeso mamana tanason wannan yaro sadam, dan kyautatawa ɗan ƴan uwana dasu kansu ƴan uwana bzan iya tauyewa ƴata hakkinta ba yazamana na barta ko oho sukuma na biya musu buqata ba na shiga rayuwarta na fifita farin cikinsu akan nata, bazan iyaba bazan iya yanda wasu iyaye sukeyi su fifita farin cikin ɗan ɗan uwansu akan na ƴaƴansu ba, shine yaganta yace yanaso kinga idanna bashi aurenta shi na cika masa buri na faranta masa na bashi abunda yakeso yayinda na baƙantawa ƴata na rabata da abunda takeso, kinga hakan babban shiga hakkine, wannan yaro sadam yayi ɗawainiya da sawwama yayi ƙoƙari ya naima mata ilimi na arabi dana boko sutura idanna samu inayi mata dai-dai gwargwado amma kafin nayi mata ɗaya yayi mata uku, yanason sawwama sosai kina kallon idan naki bashi aure nabawa ɗan ɗan uwana me sunanmu zai dawo?
Maciya amana mama tabashi amsa itama jikinta yayi sanyi baba yace bayan cin amana harda butulci, dan haka zuwa gobe idan yazo dakaina zan sameshi muyi magana dashi ya sanarwa iyayensa suzo ayi magana tunda aka fara haka gara ayi yawuce mana kawai duk wani tsai gumi da gutsuri tsome ya ƙare, ƴan uwana kuma nasan yanda zanyi dasu,
Sannan dan Allah wannan zance daga ni sai ke banason mamana tasan da wannan dance saboda nasan halinta dason faranta mana zata iya sacrificing na farin cikinta akanmu,
mama tace in sha Allahu babu wanda zaiji wannan zance, baba yace toh Allah yasa,
Baba ranar bacci ɓarawone kawai ya ɗaukeshi ya tsaya yanata tunanun yanda zai ɓullowa all'amarin."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial9 Chapters
H*llmark: But Murder and Aliens
After a bustling big city lawyer has a fateful encounter with a body-snatching alien, her new co-pilot steers her back to her home town. The rekindling of an old friendship with the struggling neighborhood painter leaves the foreign mind confused--and smitten. But all's not well in the city she left behind; a string of bodies takes a brilliant detective on something of a goose chase leading right to the lovesick pair. Can romance blossom in this classic tale of murder and aliens?
8 237 - In Serial12 Chapters
Trials of a Babysitter
Anna expected an easy babysitting gig, but when one of the kids disappeared she definitely did not expect him to be in another world. Still, she was supposed to keep an eye on him, so with his five-year-old sister in tow she made her way across dimensions to look for him. Hopefully she would find him before bedtime so she didn’t get her pay docked...
8 77 - In Serial6 Chapters
Prophecy of the Four Pillars
Dave Richardson was a normal guy from earth who was summoned to another world. However, before his adventure could really begin, he’s caught up in a teleportation spell that splits him into two beings. Richardson continued on the adventure to save the kingdom from a vile necromancer, never knowing anything went wrong. The other being, Dave, is sent to a realm of rot and death where he must struggle to find away out. [I write in my free time so my upload schedule will be erratic]
8 114 - In Serial24 Chapters
Missing World
Niu is a normal villager girl, perhaps apart from the fact that she lacks what most people have and possesses powers that most people don’t. Her daily life consists of going to school at the nearest town, where she studies along with her similarly gifted friends and tries to make everyone get along. But that relative peace does not last forever. One day, everything changes with a world-shaking event threatening town - that ends with Niu and her friends transported to an entirely foreign world, one that is spoken of in legends and fairytales. So begins the story of a girl as she attempts to gain control of her own destiny.
8 126 - In Serial28 Chapters
P A I N (FINISHED)
NOTE:THESE CHARACTERS DO NOT BELONG TO ME ( ocs that belong to me:rosean,julie,latte,edgar,and thats it)some stuff is from fnf incorrect quotes made by aesthetic_trash420(and from some vines i saw)
8 321 - In Serial7 Chapters
Who is She? {B.T.}
The years of the assassin girl leading up to the infamous ride on the Bullet train (2022). The white death, the prince, and the son all are characters from the movie bullet train. All characters from that movie belong to Sony.
8 165

