《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ PAGE 30
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 30
A gaugauce mama ta ke shiri, cikin Ƙaramin lokaci tagama shirinta, dubanta takai wajanda sawwama take zaune da ƙur'ani a hannunta tana karatu,
kinyi sadakan? Mama ta jeho mata tambaya, sawwama ta dago kanta da dubi mama sannan ta amsa da eh nayi mama, yawwa toh Allah yayi albarka ya sanyawa abunda kika karanta albarka shikuma Allah yabiyashi da alkhairin abunda ya aikata a garemu, ƙasa-ƙasa sawwama ta amsa da amin, babanku ma yace idan yafita zai saye koda dabino sai yayi sadaka na tabbata yanzu haka yayi,
Mayafi mama tadauko tafito tana fadin ki kula da ƙannenki ni zan wuce nasan yanzu baza'a rasa yan ayyukan da za'ayiba yanzu haka yan suna sun fara taruwa,
Adawo lafiya sawwama tayi mata ita kuma tajuya tatafi."
Mama bata dawo gidan ba sai wajen magrib su biyu suka shigo itada wani saurayi da bazai wuce sa'an sadam ba,
Buhun dake hannunsa ya ajiye ya dubeta yana fadin toh mama barina wuce, mama tace haba isma'il aika zauna babanku yadawo saiku gaisa idan kayi sallah saika tafi koh? Nasan yanzu haka yana hanya maza ƙaraso ciki,
Ƙarasowa ciki yayi ya zauna, halima ta kawo masa ruwan alwala,
Shigowa sawwama tayi da kayan sana'arta ga dukkan alamu tagamane tadawo ciki,
Da salla tashiga ta ajiye mama tace har kin gama kennan eh nagama mama sannu da dawowa sawama tayiwa mama, mama ta amsa da fadin yauwa,
Sawwama bata lurada wanda yake zauneba har zata shige daki mama tace sawwama bakiga yayanki bane baku gaisaba,
Juyowa sawwama tayi taɗan rusuna haɗeda faɗin ina wuni?
Lafiya ya amsa yana ƙare mata kallo, ita kuwa sawwma tana gama gaidashi ta sanya kai ta shige ɗaki, can tafito tayi alwala taqara komawa ɗaki saida taji dawowar babansu kafinnan tatashi zata fito, tsin kaya tayi baba suna gaisawa da wannan saurin cikin sakin fuska baba yake faɗin yaya su yaya zakarin jiya kuwa naso shiga masa nayi masa barka ansamu ƙaruwa Allah baiyiba to sai yau dama nake saka ran shigan, mama tace aikuwa yazama dole ma kashiga din gashi yanzu ma shiya aika aka rakoni da gero akawo maka, shine isma'il yadauko ya kawomun har gida, kuma sunata godiya, dan yace nafaɗa maka ma angode sosai Allah yabar zumunci, amin bbaa ya amsa sannan baba yace toh angode bari mu ci tuwo muyi sallan isha'i saimu fita tareda isma'il din muje saina yimasa barka daga nan sai nayi masa godiya, Jin zancensu yasa sawwama ta fahimci dan gidan yayan babanta ne dan ita ba shiga cikinsu takeyiba so dukansu bata sansu ba,
Advertisement
Ƙarasowa wajan tayi tana fadin sannu da dawowa baba! Yawwa sannu mamana, zama tayi gefe da mahaifinta yayinda idon ismail yake kanta har tazauna, suna cin abinci amma sawwama ɗagowa kaɗan zatayi su haɗa ido zaman wajen gabaki ɗaya yabi ya isheta tana gamawa dasauri tatashi tabar wajan,
Tana ji baba yayiwa mama sallama cewa daga sallar isha'i zasu wuce har ismail ɗinma yayi mata sallama suka wuce,
bayan sallan isha'i kamar yanda sawwama take tsammani saiga yaro yashigo wai sadam yazo,
Ɗauraye kafanta da hannunta tayi da ruwa ta shafa mai sannan ta sanya hijabinta tafita,
A can gefe ya ajiye motansa shi kuma ya ƙaraso ƙofar gidansu ya zauna ayanda suka saba zaunawa,
Da sallama ta ƙarasa wajan ya amsa haɗeda ɗagowa ya dubeta, zaunawa tayi gefe tana faɗin ina wuni yaya sadam, lafiya ƙalau sawwamaty yaya su mama da baba?
Lafiya sawwama ta amsa,
Suna cikin hira sadam ya miƙe yana faɗin ina zuwa wajan motarsa yanufa yaɗauko wata leda, miƙawa sawwama yayi yace kiringa amfani da wannan wayar saboda lokuta da dama inason jin muryarki babu hali idan kuma na iso ba kowani lokaci nake samun wanda zai kiraminke ba, nayi saving number d'ina a ciki zaki gani idan zaki buƙata,
Godiya sawwama tayi masa sosai dan taji daɗin wayar saboda itama wani lokacin takanso jin muryarsa amma babu hali, uhmmm yaya sadam dama baba yace in gaya maka waii,,, sai kuma tayi shiru, tattaro hankalinsa yayi gabaki ɗaya ya maida wajanta, yace mene? Ya tambaya yana son jin karshen labarin, yace wai yakamata yanzu aturo manya sushiga maganar,
Gaban sadam yayi wani dammm ya yanke ya fad'i jin yanda zancen yazo masa a bazata tabbas zaiyi murna zaiso ace yanzu manya sun shiga zancensa shida sawwama saboda zaman hakan yayi yawa yanzu lokaci yaja, shekara d'aya kenan harda months alokacinda yacewa baba saiya gama karatu kuma gashi yanzu yarigada ya gama karatun,
Amma kuma mene yanda zai fuskanci mahaifansa da maganar dakuma yanda zasu ɗauki zancen shine babban matsalarsa, bayajin dady akan yanda yakjin mummy, amma kuma duk wani abunda zai faru bayajin zuciyarsa zata iya jurar rabuwa da sawwama wacce ya koyarda zuciyarsa tsananin sonta,
Jin shiru yasanya sawwama ta ɗago tana dubansa,
Advertisement
Ganin yanda yanayinsa ya canja yasanya jikinta Yayi sanyi sosai amma bata bari yagane hakanba tace yaya sadam wani abunne yafaru? Naga yanayinka ya canja tunda na fada maka wannan zancen kashiga wani irin yanayi, ko bakayi murna bane?
Numfashi sadam ya sauke yace ba haka bane sawwama kinsan zanfi kowa farin ciki dajin wannan zancem amma bazan iya ɓoye miki ba nafada miki tun abaya zancen karatu yanda mummy keson zancen karatu, yanzune kika shiga ss3 koda anyi zance zatace abari sai kin gama school nasan zata faɗi haka shine abunda yake damuna,
Murmusawa sawwama tayi tace wannan aiba wani abu bane yaya sadam nasan cewa ko baba idan yaji haka bazai damuba,
Murmushi sadam yayi yace to ai shikenan amma zan fara yin magana agida idan yaso sai suyi magana koda za'abar bikin sai bayan kingama school, rufe ido sawwama tayi tana murmushi shima sadam ɗin murmushin yayi,
Bai daɗe sosai ba yayi mata sallama yatafi saboda hankalinsa gabaki ɗaya yatashi dayaji maganar sawwama tunaninsa gabaki ɗaya yatafi ayanda zai tunkari mahaifansa da maganar zaiyi aure sanin irin halin mummy."
bayan sawwama takoma ta nunawa mama wayarda sadam yakawo mata, mama tace toh Allah yayi albarka ya sanya alkhairi, sawwama ta amsa da amin,
Bayan tashiga ɗaki tafara dube-dube cikin wayar Number dinsa taga yayi saving da half💞 murmushi tayi sunan yayi mata ɗadi zataso ganin ita me yayi mata saving jikin nata No ɗin,
Har dare sawwama tana jiran kiran wayarsa amma bai kiraba saita danna zata kirashi sai tayi saurin katsewa tayi haka kusan karo na hudu kenan tanayi amma bata barin kiran ya shiga saita katse,
Haka ta zaune ta sanya wayar agaba tana jiran kiransa( ƴan matan hausawa😅 anyiwa matan hausawa wannan shaidar wai ko tanason kiran namiji tanason jin muryarsa takan barine saiya kira saboda idan takira ajinta zai zube😅Toh Allah ya kyauta, toh sawwama tazama ɗaya daga ciki kenan)
Tana zaune phone ɗin tafara ruri ta sauri ta tashi t zauna daukan wayar tayi haɗeda yin picking,
Sallama tayi sadam daga yanda sadam yake ya lumshe ido yayinda yaji zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi sakamakon sanyayyar muryarta da tashiga cikin kunnuwansa da ratsa izuwa gaɓoɓin jikinsa da zuciyarsa,
Jin shiru yasa tace yay sadam kana jina? Huuuu ya furzarda iska hadeda qara lumshe idonsa yace injinki sawwamaty, muryarki ce ta hanani ta6uka komai,
Shiru sawwama tayi sadam yace yaya kikayi shiru sawwamty? Kinyi missing ɗina dayawa ne?
Uhmm sawama ta amsa, toh mai yasa baki kirani ba? Ina wajan mummy ne sai yanzu na shigo, shiyasa ban kiraki ba, i thought da kikaji shiru zaki nemeni, nan ma dai sawwaman shiru tayi.
Dare suka raba suna hira sannan sukayi sallama."
in sha Allah daga yanzu zanyi qoqari na ringa yin typing kullum-kullum koda kuwa ba dayawa ba ko short page ne yafi ace banyiba, dannima na matsu labarin yayi nisa, ban ta6a rubutu mai wahalar typing ba wallhy irin ƘADDARAR RAYUWA, zasuga na canja sunan daga QADDARAR RAYUWA yakoma ƘADDARAR RAYUWA hakan yafarune sakamakon anyi book mai irin wancan sunan, naso canja sunan gabaki ɗaya amma hakan bazaiyiwuba saboda nakai kusan page 30 toh masu searching book din yanzu yadawo ƘADDARAR RAYUWA ba QADDARAR RAYUWA,
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial1269 Chapters
Sword Among Us
When he returned to the World of Martial Arts, the game was filled with blood and battles! Chen Kaixin had chased after the footsteps of the one emperor, two empresses, three princes, seven dukes, and thirteen aces for three years, but during the eve of the Sword Among Us tournament in Mount Hua, he was ambushed by evil bastards, and was killed so much that his level dropped to that of a newbie. He completely lost the chance to join the ranks of the powerful players in the game! In great disappointment, Kaixin quit the game and got drunk so that he could forget his sadness, but during that stormy night, Chen Kaixin found that he had actually dreamed for a total of three years, because when he woke up again, he woke up to three years ago, when he was still a student.
8 167 - In Serial150 Chapters
Weaponsmith : [A crafting litRPG]
[I accidentally got engaged to the evil owl-goddess who is obsessed with the number-three and now I have to make weapons for our new adventuring guild] In an era in which ancient gods live in the world’s cities together with their mortal followers, forming tight-knit guilds and powerful temples, the disfigured ash-caster and blacksmith Hineni has lived his entire life as a reclusive outcast. Hidden away behind layers of clothing and just as many walls and doors, he only ever leaves the house in the dead of night, so that neither the gods or anyone else can ever see him. However, on one of these night-tide outings, he finds that has gained the unwanted attention of what is seemingly a perfectly normal owl and through his unwitting efforts at simply filling his nights with acts of personal meaning, he ends up promising himself to a creature that is perhaps even less versed in human ways than he himself is; a mysterious, odd owl-goddess that nobody seems to have ever heard of, Obscura. Hineni, having had no greater purpose in life until now, finds himself willing to accept this turn of events and dedicates himself to creating a brand new adventuring guild, under the watchful eyes of the ancient entity Obscura, who has only one, clear, proclaimed goal - - To hunt the BIG FROG! BIG FROG! BIG! [litRPG] [Soft romance] [Crafting] [Base/Guild-building] [Pact with a diety] [Slice of life] (Updates every Wednesday / Saturday)
8 822 - In Serial34 Chapters
Convergence of Fates
After being rescued by an Assurian scientist, Fenicia Kranicar wakes up panicked, afraid and very angry. Her plans to escape must be put on hold when she learns that dangerous mercenaries are about to attack the space station she is on. The half Assurian-Saryan female will soon discover things about herself that she would never have guessed. Will the knowledge of her new powers and where they came from be enough to save her? Warning : COF contains violence, trespassing, bad language, multiple references to various matters of fandom, questionable interrogation tactics, kidnapping, arguable murder, justifiable murder, filthy murder, assault and battery, abuse of authority, destruction of private property, disorderly conduct, dismemberment, and an uncomfortably sexy mother. Cover commissioned by Jackiefelixart
8 203 - In Serial18 Chapters
Re:Stoat
This story is utterly brutal, sick, twisted, and vile. Rape, Murder, Gore, Nature. Elephants rape and murder rhinos... I want to make this story twisted from the start. The world is a viscous and cruel place. My story is going to push limits. Abandon all hope, ye who enter here.
8 101 - In Serial15 Chapters
Speedrun
Quick lesson on time dialation, the closer you are to a heavy object, the slower time goes for you, if the mass is large enough, one could freeze in time. Now, send a few person you trust to a remote planet where life is just starting to take off, you yourself staying besides say, a supermassive black hole, aka Joe, wait for a few hours, what do you get? Simple, a bunch of very advanced civilisations, probably a few with mal intent, which is way ahead of you in terms of technology. What do you do now?
8 94 - In Serial57 Chapters
ᴛʜᴇ ʟᴀꜱᴛ ᴛɪᴍᴇ » ʜꜱ (ꜱᴇQᴜᴇʟ ᴛᴏ 24 ʜᴏᴜʀꜱ)
[COMPLETED] //Продолжение 24 Hours// Если вы не читали 1 часть, я настоятельно рекомендую прочитать сначала ее// Прошло четыре года после игры. Карисса борется с последствиями. С новой личностью она работает в детском саду, но даже это не может полностью отвлечь ее от воспоминаний, которые по-прежнему влияют на ее жизнь. Но это только начало.Внезапно Карисса начинает сталкиваться с людьми из прошлого, что в итоге подталкивает ее к переломному моменту. Слишком скоро она поймет, что больше никому не может доверять, в том числе и себе.© 2019
8 182

