《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 26
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 26
Tun ranarda wannan abun yafaru kullum kwanan duniya yarima saiya tashi cikin dare yayita wannan kuwwa da ihun, mai martaba yana iya qoqarinsa wajan yimasa addu'oi to Alhamdulillahi dai abun yaragu, yanzu ba sosai yake tashiba sai sa'i-sa'i,
Dake kullum mai martaba yakan yi masa addu'a cikin ruwa addu'ar tazama itace ruwan shansa akowani lokaci,
Lokacinda labarin komawar yarima sashin mai martaba ya riski hajiya suwaiba sanda tayi y'ar qaramar hauka,
Sumbatu ta ringayi da fad'e-fad'e tasan yanzu batada wani contact da yarima,
Duk yanda zatakaiga son cutar dashi hakan bazai yiwuba saboda amintattun mutane ne atare a sashin mai martaba wanda zasu iya bada rayuwarsu akansa, batada wani hope yanzu,
Hajiya suwaiba tarasa mai yake mata dad'i da ta yanke shawarar bazata qara tuntu6ar yaya hadiza ba amma yanzu batada wata mafita daya wuce wajanta,
A waya ta kirata ta shaida mata cewa tana son ganinta, yaya hadiza tana kallon kiranta tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi, hajiya suwaiba bata ta6a nemanta har sai idan tana neman wani abun a wajanta, cikin rawar jiki yaya hadiza ta shirya zuwa wajan qanwartata saboda a wannan aikenda takeyi mata ba qaramin samu takeyiba,
Bayan tazo hajiya suwaiba ta shaida mata duk wani halinda ake ciki,
Aikuwa yaya hadiza batayi qasa a guiwa ba ta amshi kud'i ta tafi tsubbace-tsubbacensu, taje wajan mutane sunfi biyar kowanne idan taje shaida masa takeyi akan yayi aiki batareda an basu wani abu su aikataba saboda basuda contact da wanda sukeson aikatawa lamarin,
Abubuwa dadama yaya hadiza ke amso musu, takan kawo suyi amfani dashi
Sannan kuma da kwanaki kadan suke bayarwa suke tusa aikinsu, suyi su qara basa daukan lokaci sai sunyi shirkansu son ransu,
Awannan lokaci yanda suka dage kan wannan abun badan Allah yasa mai martaba yana tsaye akan yarima ba da yarima bazai qara wani lokaci araye ba,
Addu'a mai martaba yakeyi ba dare ba rana dama kuma addu'a sabonsa ce ba ciwoma bare kuma da ciwo,
Kullum da safe umma ke zuwa tana dubashi takan d'an dauki lokaci wajansa kafin tadawo, idan taje sai dai ya zuba mata idanuwa kawai yayita kallonta babu baki bai iya furta koda kalma d'ayane, sai dai ido,
Rana dai-dai ne idan umma tadawo daga wajan yarima bata zubda kwalla, wani sa'in tun awajansa take zubda kwallar tausayinsa,
Itama umma bata zaunaba addu'a takeyi sosai tad'age da addu'a fiyeda na kowani lokaci,
Mai martaba yanzu zancen auren yarimane kawai agabansa ya tsaya yana son nema masa mace mai nagarta wacce zata kula dashi acikin yanayinda yake batareda ta cutar dashi ba koda na misqala zarratin."
Advertisement
—————-
Mummy data koma gida jikinta yayi sanyi sosai maganar gaskiya kuma magana d'aya itace bazata ta6a barin sadam yayi aureba batareda yayi zurfi akaratu ba, ita kanta abidan nawa take? Bare sadam shi da yake namiji,
Mummy tagama zancenta ita kadai ta shanye acikinta bata bari dady yajiba bare sadam,
Tasan halin dady yanzu abune mai mugun sauqi yace yanajin kunyan yayanta zai yarda ayi auren,
Cire komai tayi cikin ranta saboda tasan baza'a ta6a yiwa sadam aure batareda amincewarta ba tafara tunanin irin kyautarda zata yiwa sadam na cin jarabawarsa da yayi."
Sadam yakaiwa sawwama result dinsa tagani sosai tayi murna da result dinsa har mamakin yanda ta nuna farin ciki yakeyi,
Tsura mata idanuwa yayi yanda fuskarta ta yalwata da fara'a sai tayi masa kyau sosai,
Daura idonta tayi akan fuskarsa idanuwansu ya hade waje d'aya kunyace ta kama sawwama ta sunkuida kanta qasa tana murmushi,
Numfashi ya furzar mai d'umi soyayyar sawwama takansa wani lokaci yaji qirjinsa yayi masa nauyi,
Shi kadai sai yayita ajiyar zuciya d'abi'unta da halayyarta ke dad'a sanyawa soyayyarta tana daduwa cikin zuciyarsa sannan soyayyarta tayita fusgarsa aduk lokacinda yake tare da ita,
Lokuta da dama Batareda sanin saba yake tsura mata idanuwa yakan tsinci kansa da kallonta sannan kuma saiya kasa dauke idanuwansa daga kanta,
Komai nata cikin nutuwa take yinsa, hankalinta yafi qarfin shekarunta, ajiyar zuciya ya qara saukewa yana jin yanda zuciyarsa tayi nauyi tacika da soyayyarta,
Dubanta yayi cikin so da qaunarta yace sawwamaty na kawo miki result kin gani kin yaba amma baki bani tukuiciba,
Kinsan idan nine kika kawomin abun farin ciki haka bazan iya barinki batareda nabaki tukuiciba,
Shiru sawwama tayi batasan mai zata bashiba tasan batada wani abunda zata bashi komai yana dashi arayuwa,
Sunkuida kanta qasa tayi jikin sanyin jiki tace to mai kake so?
Kagani banda abunda zan baka komai kana dashi,
Murmushi yayi yace kene kuwa kike da abunda zaki bani,
Menene shi? Ta tambaya cikin sauri sannan tadaura da cewa Kafadmin har indai baifi karfinaba bai kuma sabawa shari'a ba nayi alqawarin bakashi babu abunda kafi karfinshi aguna,
Murmushi yayi yana jin muryarta mai sanyi tana ratsa kunnensa da gabobin jikinsa izuwa kowani bargo dake cikin jikinsa,
Lumshe ido yayi yace baifi karfinkiba sawwamaty bai kuma sabawa shari'a ba,
Tukuicinki shine ki furtamin kina sona,
Cikin jin kunya sawwma ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta tana y'ar dariya,
Murmushi yayi hadeda lumshe idanuwa yasake budesu akanta, ajiyar zuciya yasauke a hankali hadeda furzarda iska mai zafi, ya tabbata yana yiwa sawwama so mai tsanani shiyasa yake ganin komai nata kalan burgewane dashi komai tayi abun yakan zama ya burgeshi hadeda kuma wani salon daukar hankali babban abun shine nutsuwarda take tattare dashi,
Advertisement
Ehem am all ears 👂 ina sauraronki,
Jikin jin kunya sawwma tace ai basaina fadaba kasan inayi,
Uhm-uhm naki wannan wayon adai fadan naji da kunnena,
Sanya kanta cikin hijabi tayi akanhanki yanda zai jiyota da muryarta mai dadin gaske tace" ina sonka yaya sadam, cak sanda numfashin ya tsaya na wani lokaci jikinsa kamar wanda aka zare masa kuzarinsa kawai yazama wani statue saboda yanda kalmar da dukeshi sosai ta shige ta samu mafaka cikin zuciyarsa ta maqale garin shiga cikin zuciyar harta zare masa kuzarinsa na wani lokaci,
Jin shirun yayi yawa ya sanya sawwama tafito da kanta ta kalleshi,
Ganin yanda ya zuba mata idanuwansa masu ruwan kyau ya sanyata turo bakinta cikin shagwaba tana fadin yaya sadam kaifa kasanyani fada kuma ka tsaya kana kallona,
Runtse idonsa yayi hadeda fadin ya Allah bude idon yayi akanta yace ai nakasa aikata komaine gabaki d'aya kalmar tatafi mun daduk wani kuzarina,
Rufe fuska sawwama tayi tana dariya, murmushi yayi yace matana badai kunyaba, kunyarki kadai takan dad'amin soyayarki cikin zuciyata,
Qara sunna kai sawwama tayi cikin zuciyarta tana jin dadin yanda sadam yake yabon duk wasu halayyarta duk da kasancewar wani lokacin sai taga kamar kawai yana fadane amma duk da hakan tanajin dadi acikin ranta aduk sanda ya yayabi halayenta,
Sadam yadade wajan sawwama dan har 9 tawuce kafinnan yatashi zaiyi mata sallama har sunyi sallama ya dubi sawwama yana fadin sawwamaty bazaki qara fad'aba kinga ba sau daya kika fada, kuma kamata yayi ace duk wani course nasa fadan dabanne,
Murmushi tayi tace toh ina sonka dasuari tayi cikin gida tana gama fadin hakan,
Y'ar dariya sadam yayi kawai yanda tayi tafiyar dasauri kamar wacce tayi laifi shine yabashi dariya,
Ajiyar zuciya ya sauke yawuce yayi gida dan kada ya karya dokan dady dayake bi masa baya abun kuma bazaiyi ddi ba."
Sadam ya dage da koyawa sawwama karatu sosai yadage akan ganin tasamu wadataccen ilimi wanda ita kanta zatayi alfahari dashi, dan ilimi shine mutum ko aikin mai ilimi da maras shi ba d'aya bane,
Yanason macenda tasan addini hakan yasa zai dage wajan ganin sawwama tayi karatun addini fiyeda tunani,
Wannan shine son gaskiya sadam yana son mace mai addini hakan yasa yafara qoqarin maida sawwama tazama daya daga cikinsu bawai yarabu da ita dan batada dashiba ya nemi mai shi wannan ba soyayyayr gaskiya bace,
Har in dai kanason abu da gaske wanda kake dashi yakamata ka gyara yazamana yadawo irin yanda kakeso bawai dan wanda kakeso bai dashi ba nemi wani maishiba,
Wannan shine ake kira soyayyar gaskiya mugudu tare mu tsira tare kamar yanda yakeson tsira wajan ubangiji haka yakesonmawa sawwama shiyasa yadage sosai kuma Alhamdulillah ko ayanzu sawwama tasan abubuwa dayawa bayan wanda ake koya mata a school harda wanda shi kansa sadam yake daura mata kuma ya lura tanada sanya kai sosai wajan neman ilimi kuma Allah yana shige mata gaba al'amuran suna zuwa mata da sauqi."
——————
Lokacin satinsu sadam uku da gama exam alokacin yake sanya ran zaiyiwa sawwama maganar komawa makarantar boko,
Mummy kuwa tana ta shirya suprise dinda yakeson yiwa sadam amma sai dady ya rigada dan ya shaida mata ya biya musu umra su uku itada sadam da shi,
Mummy tayi murna sosai nan ta sanarwa sadam shima yayi murna sosai,
Mummy ita tabar tata kyautar sai bayan sun dawo dayake tafiyar tasu bazata wuce nan da 1week ba."
—————
Cikin amintattun mai martaba ya duba ya qara sabar wanda ya yarda dasu aciki kiransu yayi ya shaida musu cewa acikinsu yanason wani yabawa yarima auren yarsa, amma baiyi musu doleba yace tunda sun san lafiyar yarima so idan wani aciki yaga zai iya sai ya bada,
Yarda dasu da yayi ya sanya ya za6esu cikin wanda zai nemowa yarima auren d'iyarsu, kuma koda yarima yanada lafiya idan bawai shi da kansa yaga macenda yakesoba toh acikin yayansu zai nemawa yarima aure, yabasu lokaci suyi shawara saboda baison auren yawuce sati d'aya zuwa yamma yace su fada masa idan da wanda ya amince."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Toh Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial30 Chapters
On Parts and Precedence
A mysterious damsel appears before King Arthur’s court with a strange sword, and promises it to whoever can draw it from its scabbard. King Arthur fails to unsheathe the weapon, as do all his knights present at his court. However, an ex-convict named Balin succeeds in unsheathing the wicked blade Tyrfing. What dangers loom before him and his newly acquired weapon? What misfortune awaits him on his adventures? Find out in On Parts and Precedence. New chapters weekly.
8 185 - In Serial127 Chapters
ARC
Book 2: New World Order is now being released, chapters will be uploaded as they're written. Noah wakes up after another failed date in a new city only to find the world in chaos. A fleet of alien spacecraft hover over every major settlement on Earth, their intentions unknown. It doesn't remain that way for long. The planet is rapidly terraformed to become unrecognisable, also granting Users the ability to awaken supernatural powers. Noah is one such User. What to expect: • Slow burn • LitRPG without the status screens • Weak to strong • Struggle and betrayal • Realism
8 237 - In Serial45 Chapters
The Portable Dungeon
Drake, a game developer, after finally finishing creating his new game called "Dungeons and Mayhem", gets sucked into a parallel world where swords and magic rule the continent, as well as where various monsters and dangerous creatures roam about. The only forgiving thing is that he was transported with a benefit where he doesn't know left to right, and that is the power to view and manipulate the status! Of a dungeon of course.
8 184 - In Serial40 Chapters
The Princess of Victory
The Crown Princess of Forewood Kingdom, Victoria, was said to be perfect in all the things that she did. Which was an exaggerated rumor, of course. She was hardworking, but she was also mischievous, always looking for a chance to escape her guards and sneaked out to work through unconventional means. When the rebels-turned-kingdom Lirsk breached the peace treaty between them, war broke out. But Lirsk Kingdom was by no means fair, and countless underhanded matters was done in the military compound, pointing to a cause: there was a traitor amongst them. With the ever-wary, wrongly-accused young Major Dev, they tried to uncover the unknown: who was the traitor that caused hundreds of deaths? [Book 1 of the Guardians of Forewood series]
8 97 - In Serial43 Chapters
Sirens in Seattle
When pre-med student Mia gets pulled over on her way to school, she doesn't think that the rude Officer Phoenix Adams is anything more than a factor of a bad day. She definitely didn't think she'd see him again.She definitely never thought they would fall in love.Cover done by the amazing @couchpotato2022 !
8 106 - In Serial43 Chapters
Tears of Dusk
The War had left the world destroyed and barren. Mankind was on its knees, weak and doomed to extinction. The only comfort was the knowledge that they had won and that their enemy had been destroyed… or so they thought. Thirty-five years ago, the Obcys had invaded Ziemia. They were monsters from another world and brought with them pain, desolation and the Taint. As Isyd and his companions led the last expedition to destroy the remnants of the Obcys forces, they activated a trap that killed the entire party… and sent Isyd back to the past! Now years before the War even started, Isyd swears to change the future he had once lived. Only, the War had profoundly changed Isyd… Tainted him…
8 184