《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 25
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Ina alfahari dake antyna, ina matuqar alfahari dake Allah ya sanyaminke a aljannah ya biya miki buqatunki na alkhairi, Allah yasaka miki da mafificin alkhairi, *ANTY RASHIDA*(mrs mustapha)."
Alkhairin Allah yakai miki aduk yanda kike XEECUL🥰 wannan shafi sadaukarwane agareki."
Page 25
Wuni zubur haliifaa yayi yana bacci bai farkaba, miqewa umma tayi akaro na biyar tashiga d'akinsa domin dubashi,
Ajiyar zuciya tasauke ganin yanda yake baccinsa cikin nutsuwa,
Ahankali ta fito ta rufo da qofar saboda kada qaranta ya tasheshi,
Zaunawa tayi tana fadin yau dai yarima haliifa bacci yaketayi gabaki d'aya wunin wannan ranar,
Ummi dake zaune agafe tace" jikin haliifa kam yanzu abun sai godiya kullum lafiya yake samu Allah yaqara masa lafiya,
Amin umma ta amsa zancen y'ar uwartata cikin jin dadi."
————-
Har dare ya farayi hajiya suwaiba tana jiran taji labari akan jinyar yarima amma shiru babu wanda yakawo mata wani labari gameda hakan,
Aikawa tayi aka kira mata jakadiya, bayan tashigo ta tsugunna ta kwashi gaisuwa tayi shiru tana jiran jin dalilin kiran,
Hajiya suwaiba tadauki lokaci kafin tace bakiji wani abun gameda shahsinsu haliifaa ba??
Cikin ladabi jakadiya tace har yanzu babu wani abunda naji,
Jijjiga kai hajiya suwaiba tayi tace shikenan zaki iya tafiya, amma kina jin wani labari ki tabbatar kinzo kin sanar mun,
Toh ta amsa sannan ta fita,
Tsaki hajiya suwaiba tayi tana tunanin anya kuwa wannan abun yaya hadiza zaiyi aiki?
Itafa daga yanzu ta rigada ta yankewa kanta shawara babu wani jira da zata qara yi zata aikata abunda take kallo shine mata mafita,
Zata bawa salim dama yayi aikinsa kokuma ita tayi aikinta."
———————
Bayan isha'i umma ta dubi ummi tana fadin kinga har yanzu yarima bai farkaba gashi kuma baici komai ba yau through out, ummi ce tace" toh ko za'a tasheshine abashi abincin saboda cikin dare kada ya farka,
Miqewa umma tayi tace toh barina gwada tashinsa kinsan shi dole saiya yi niyya kafin yake kar6an abincin Allah yasa yayarda,
Qarasawa tayi cikin d'akin agavan bed din ta tsaya ta sanya hannu ta ta6a shi temperature d'insa normal, d'an bubbugashi tayi amma shiru bai miqeba taqara bubbugashi still baiyi motsiba, hannunta takai dai-dai saitin hancinsa ajiyar zuciya ta sauke jin yanda numfashinsa yake fita a hankali, rufo masa qofar tayi ta dawo saboda taga yanda yake jin dadin baccin,
Tsakar dare umma tana kwance a d'akinta taji wani irin qawa had'eda kuwwa,
Advertisement
Arazane ta miqe tana fadin inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un wanna wace irin qarace haka?
Yarimane ya fad'o mata arai da sauri ta sakko da kafafunta daga kan gadon, hijab tadaura akan doguwar rigarta tayi waje,
Duk illahirin mutannenda suke sashinta kowa ya fito, tareda ummi suka qaraso wajan cikin tashin hankali tayi hanyar dakin yarima,
Sauran masu aiki da suka tsattsaya a qofar kowa yana taraddadin shiga suka buda mata itada ummi suka shige d'akin kai tsaye,
Da gudu da qarasa ganin yanda yake wata irin qawa yana sassandarewa,
Hannunsa ta kama ta riqe tana fadin inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un haliifa maiya sameka?
Kuka tasaka saboda tanada raunin zuciya ta kamkameshi ajikinta tana kuka sai qoqarin kwacewa yakeyi dayake yanada karfi tashi daya ya kwace yaci gaba da kawa mai amsa kuwwa,
Qarasawa ummi tayi itama tahau gadon tafara yimasa addu'a tana tofa masa kusan 3minute suna ahaka saika ruma tashigo,
Kuka tasake tana fadin na shiga uku,
Kanta babu dankwali bbu takalmi aqafarta tafice a sashin bata tsaya ko inaba sai sashin mai martaba duk yanda tsakanin wajen takeda nisa amma a qaramun lokaci ta isa,
Tana isa masu gadin sashin suka fara tsareta kota kansu batayiba har sanda takai izuwa falonsa qofar d'akinsa ta tsaya tana kuma tana bubbugawa, mai martaba dake kan sallaya yaci bubbugawar qofa, bai kulaba har sanda ta idda ya sallame tukunna,
Ba'a daina bugun haukanda akeyiba shima bai kulaba sai da ya idda,
Tashi yayi yana fadin subhanallah waye haka?
Cikin kuka ruma take fadin yaya yarima! Yaya yarima!
Dasauri ya qaraso ya bude qofar cikin faduwar gaba yace mai kuma yasamu yariman?
Nima ban saniba tafad'a cikin kuka,
Jirani ina zuwa yafadi cikin qanqanin lokaci ya shirya ya fito,
A lokacin aka kawo motoci suka shirya suka fita,
Koda ya isa kai tsaye ya shiga d'akin da yarima yake,
Yayiwa su umma umarni dasu fice adakin su barsu su kadai,
Umma na kuka tafita ummi ma tafita ya zamana saura shida yarima kadai,
Wasu yan dabaru yayiwa yarima yadade cikin d'akin dan har saida aka kira sallan asubahu kafinnan yafito lokacin qawanda yarima haliifa yakeyi ya lafa,
Ficewa mai martaba yayi zuwa masallaci daga nan kuma sai ya koma shahinsa dan hutawa,
Sai bayan anyi sallah umma takoma d'akin idonta yayi jaa saboda yanda taci kuka,
Qarasawa gabon gadon tayi ta tsura masa idanuwan ba bacci yakeyiba amma hankalinsa ba ajikinsa yakeba,
Zaunawa tayi ta kamo hannunsa da yayi sanyi qlau hawaye yana bin kan kumatunta,
Advertisement
Allah yabaka lafiya yarone Allah cire maka wannan lalaura tafad'a kuka yana shirin cin karfinta,
Babu yanda ta iya dole tasha kukanta ta gaji saida hantsi kafin tabar d'akinsa,
Jiki babu karfi tayi wanka amma bata iya sanya komai abakintaba,
10:00am mai martaba ya aiko yana son ganinta,
Bata 6ata kokaci ba 10:30am tayi mata a sashin mai martaba,
Tana zaune a palour bai dauki lokaciba yfito,
Gaidashi umma tayi cikin ladabi ya amsa yana tambayarta mai jiki,
Amsawa tayi da fadin Alhamdullah,
Cikin tausayawa mai martaba yake kallon umma, acikin surukansa kaff babu wanda yakaita hankali da nutsuwa irin soyayyarda yake yiwa dansa yasanya yakejin itama batada bambamci da dannasa,
Shine dalilin daya hanata fita daga gidan bayan mutuwar dannasa,
Kuma data tashi ta raini jikinka ta bashi tarbiya mai kyau wanda ko ina yashiga ana yaba halinsa. Da irin tarbiyarda yasamu duk yanda ya shiga mahaifiyarda ta haifeshima tana shna addu'a ba shiba kad'ai,
Nisawa yayi cikin tausayawa yace" hafsatu! D'agowa umma tayi cikin ladabi ta dubeshi sannan ta dukar da kanta tace" na'am abba,
Nisawa mai martaba yayi sannan yace wani abu na hanga ganeda ciwon yarima na yanke shawararda abunda ya kamata,
Nasan ba lallai shawararda na yanke tayi miki dad'iba,
Amma hakan shine mafi A'ala,
Yarima zai dawo sashina da zama gabaki d'aya,
Sannan kuma abuna biyu shine, zanma yarima aure domin yasamu mai kula dashi da kyau,
Idan da mace kusa dashi wasu abubuwan dasuzo dasauki, sannan ko bayan aurenda zanyi masa zai zauna anan 6arin daya layin shida matarsa,
Ta dalilin wannan auren sai kiga Allah ya dubu niyyarmu yabashi lafiya,
Umma cikin zuciyarta bataji wani abu gameda dawowar yarima wajan mai martaba ba, saboda tasan shi zaifi kula dashi zai samu wanda zasu kula dashi fiyeda kowa, kuma zaman awajansa zaifi zama masa sirri, akoda yaushe kuma zai samu damar yimasa magani, ta tabbata idan asaahin mai martaba yake babu mai shiga wajan yarima dai-dai da matansa kuwa,
Dan mai martaba ba fita yakeyi sosaiba zaman fada bawani yinsa yakeyiba sabida da jikin tsufa,
Nisawa umma tayi bayan tagama tunaninta cikin ladabi tace duk yanda kayi dai-dai ne abba Allah yabashi lafiya,
Amin mai martaba ya amsa sannan yace Allah yayi miki albarka zuwa dare zanzo da kaina in tafi dashi,
Sallama umma tayi masa tatafi,
Bayan umma takoma ta shaidawa ummi yanda sukayi da mai martaba sannan tace wallhy ni ba wannan bane damuwata tunda nasan can wajansa zaifi samun kulawa, damuwata itace aurenda yace zaiyi masa, dududu nawa yariman yake?
Bazai wuce 24yrs ba sannan kuma gashi bansan wace irin mace za'a aura masaba shin wacce zata kula dashibr kokuma wacce bazata kula dashiba shine babban damuwata,
Nisawa ummi tayi sannan tace nikam banga aibu a hakanba saboda yanzu duk cikinmu babu wacce zata kula dashi kamar matar aurensa, kinga auren shine yafi,
Nima bawa naga aibun hakan bane cewa umma kawai dai ina duba yanayinda yake cikine,
Hakane kam mudai namu addu'ane zallah Allah yabashi lafiya shine babban damuwarmu, amma nasan mai martaba kafin ya aikata abu yakan tsaya yayi shawara sosai akai."
——————-
Hajiya sabuwa kuwa da asubahi zancen ciwon yarima ya risketa taji dadi sosai,
Amma shaida mata da akayi mai martaba yaje acikin daren ya lafa ba qaramin tashin hankali ta shigaba,
Abunda bata saniba shine addu'a bata bar komaiba."
———
Umma na zaune da yamma abokin abban yarima yazo dubasu kamar yanda yasaba baya daukan lokaci baizo dubasu ba duk dukiyarda suke dashi ba hakan yake hanawa shima ya narkar musu da tashi dukiyarba,
Har qasa biyu ya fitada yarima saboda nema masa lafiya ba'a daceba,
Koda abban yarima ya rasu duk dukiyarda mahaifin yabar musu dakuma wacce take cikin gidan sarautar bai hanashi daukan wasu daka cikin dawainiyar yarima da mahaifiyarshiba,
Bayan sun gaisa umma ta shaida nasa yanda sukayi da mai martaba saboda kamar mahaifi haka tadauke ma yarima, yaji dadi sosai, cikin ransa yake ayyanawa da'ace yanada yarinya budurwa da batayi aureba toda ma yarima zai bawa amma kuma yarasab mata biyune duk sunyi aure sai uku maza,
Abun arziki yakawo musu sannan yayi musu sallama yatafi,
Da dare yayi maimartaba da kansa yazo yadauki yarima ya tafi dashi kamar yanda yace."
Idan kunason na ringa qoqartawa inayu muku typing gaskiya comment yayi yawa danni rashin comment na daya daga cikin abunda yake hanani typing."
————
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Toh Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial354 Chapters
The Numbers That Brought Our Fates Together
Elena Lee, the daughter of the pharmaceutical tycoon, has been tormented by nightmares since she was six years old. In those dreams, she meets a strange man. It looks like he is trying to save her or... to kill her. But what will the girl do when the man from her dreams suddenly appears before her eyes in reality? *** *** *** Flames devoured the remnants of a fallen plane. The pilot's voice was no longer audible. Slowly falling white snow reinforced the feeling of complete hopelessness. "Lena, run!" "But…" "I said, RUN!" Taking his words as an order, Elena's legs, not listening to the desires of her heart, carried her away from this place as quickly as possible. Out of breath, but finding the strength to run farther through this dark forest, she heard nothing but the knock in her chest. Suddenly, the ground disappeared under her feet, and the body lost its balance. "Oh, and who is this hiding in here? Did the little mouse decide to play with the big cat? Oh dear, as I said, you can not hide from me. Neither in this life nor the next one." Elena's heart sank in horror. She has just lost the last chance to survive.
8 437 - In Serial19 Chapters
The Gods' Chosen Few
This is a story about six summoned humans from modern earth to a world of magic, monsters, and gods'. There are five large cities in four kingdoms. There's the Fire kingdom to the south. Almost completly a desert known for their cheifs, fire mages, and their mostly beastkin kingdom blessed and watched over by the fire god Pyritis. Then there's the Air kingdom full of trees the size of mountains to the east known for their magnificent carpenter's, archer's, wind mages, and mostly elves living there watched over by the air goddess Zephra. After that there's the Water kingdom against the ocaen to the west known for their massterwork alchemy, massive navy, and water and ice mages mostly populated with humans cared for by the water goddess Aquatis. Finally the earth kingdom in the massive mountains to the north known for their expert blacksmithing, earth mages, and being mainly filled with dwarves protected by the earth god Teran. There are temples of healing throughout all the four kingdoms that worships the goddess of light and life Rayanna. There is also a sixth goddess who isn't mentioned any longer due to the zealots killing innocents in her name in the name of Nyx goddess of death and darkness. There is one massive city built on the corner of all four kingdoms where many people live and the kingdoms' kings' and queens' come to meet and conduct political business as well as meet and realx as friends. It also serves on major purpose. It is used to summon heroes from another world. The kings' and queens' have been notified by the head preists of their respective gods that it's time to summon heroes to help quell the rising army of zealots. Hi there ladies and gentlemen. This is my first time writing and uploading a story on Royal Road. I'm looking for constructive criticism and helpful input. I'm looking forward to a long and amazing journey from here on out.
8 161 - In Serial33 Chapters
The Four Guilds Of Gravenhall
The massive castle of Gravenhall rises above the town of Providence like a huge grey monolith, seemingly bigger than every other building in the town combined. It is a beacon of learning and opportunity for hundreds of miles in every direction, drawing hopeful students to its hallowed halls like moths to a flame. Terri Tillerson is one such student, a peasant by birth with no hope of escape from a life of subsistence other than the risk and adventure offered by a career at Gravenhall. But the massive keep hides a deadly secret that will take Terri and her three companions on a journey through intrigue, danger, and even death in a world far more complex and sinister than they ever imagined…
8 170 - In Serial14 Chapters
Quest for Madness
This world is one of many that has been enriched by magic. Unlike the other worlds, this one's magic can force the user into the long windy road of madness. The main character must make hard choices to leave the only place she has ever known, one that negates and protects from dangers of the rest of the world, all to bring her older brother back. She must decide how much to rely on the magic to safely complete her objective. Balancing on a knife's edge or become a grotesque form of herself that ravages all those around her.
8 189 - In Serial8 Chapters
Who's That Cool Rider?. | Grease 2 fanfiction
Lara DelFuego little sister of Anthony "Doody" Delfuego is a Pink Lady at Rydell Highschool.Her best friends are Stephanie Zinone and Paulette Rebchuck.
8 97 - In Serial13 Chapters
Hammer Of The Gods
(THIS WAS PREVIOUSLY ON MY LAST PROFILE- I STILL HAVE COMPLETE OWNERSHIP! DO NOT SAY ANYTHING ABOUT ME STEALING THE BOOK!) BOOK FOUR OF THE SOULMATES SERIESSam, Dean, and (Y/n) are held hostage by a group of gods who want to use them as bargaining chips to stop the apocalypse.(I do not own Supernatural or (Y/n), the only thing I own is the not-really-romantic subplot.)Warning: This is an entire episode of Supernatural: Season 5 Episode 19, so buckle up for the matching scenes and incredibly long chapters.Book One: Tall TalesBook Two: Mystery SpotBook Three: Changing ChannelsBook Four: Hammer of the GodsBook Five: Bring 'Em Back Alive & Unfinished Business(THIS WAS PREVIOUSLY ON MY LAST PROFILE- I STILL HAVE COMPLETE OWNERSHIP! DO NOT SAY ANYTHING ABOUT ME STEALING THE BOOK!)
8 114

