《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 21
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
Page 21
Washe gari sassafe sadam ya shirya yafice dayake yanada lactures da safe,
Bayan sun gama lactures sun fita yazamana akwai interval tsakaninsa da next lactures dan malamai dayawa sunyi covering,
Wasu yan qalilai ne daga cikinsu basuyiba,
zaune suke shida najeeb kamar yanda suka saba dama akullum atare zaka samesu idan suna tare basa kula wasu abokanai haka,
Ko najeeb sau dayawa sai sadam yatafi gida yake neman friends dinsa,
Najeeb wanda tun ranar yake jiran sadam yabashi labarin feedback din yarinyar sadam bai bayarba yagaji da jira dan haka yadubi sadam yana fadin kaifa ko sadam har indai mutum zai tsaya kayi ra'ayin kanka kafada masa abu inaga zai jima ba'a fada masaba,
Kallonsa sadam yayi cikin rashin fahimta yace mai kuma nayi?
Harara najeeb ya watsa masa hadeda fadin kaikam ai kullum bakasan abunda kayiba,
Ka manta tun shekaran jiya kacemin zata baka amsa baka shaidamin yya kukayi da itaba,
Nisawa sadam yayi yace intakaice maka kennan ko yaya?
Koma yaya kayi najeeb yabashi amsa,
Toh naji ta amince har munyi magana da babanta,
😳😳😳zaro ido najeeb yayi yace sadam hankalinka daya kuwa?
Kallon banza sadam yayi masa yace A'a nahada da naka yazama biyu,
Mtsww najeeb yaja tsaki sannan yafara fadin haba sadam kayi gaggawa wallhy babantafa kace,
Ehem sadam yayi sounding yana kallonsa,
Rage murya najeeb yayi yace sadam inaso ka fahimceni bai kamata kasamu mahaifintaba,
Kallonsa sadam yakeyi kawaia yarasa abun cewa,
Najeeb ne yaci gabada fad'in sadam kasan halin mummy itace abunji ba baban yarinyarba idanma matsala zatazo daga wajan mummy ne nasani kagani babanta baida matsala amincewar mummy shine mai wuyan da zarar ta amince komai zaizo dasauki,
Amma yanzu daka samu mahaifinta da farko mai kake tunanin zai faru idan mummy taki amincewa?
Wani irin kallo kake tunanin mahaifan yarinyar zasuyi maka?
Kallon mayaudari zasuyi maka wanda ka yaudara musu yarinya,
Zasuyi maka kallon maras gaskiya,
Huuuuuu!!!! Sadam ya furzarda iska sanya hannusa biyu yayi ya rufe fuskarsa,
Shi wai yaya akeso yayine
Shi kokadan baiga aibuba akan samun mahaifinta dayayiba,
Jikinsa yana bashi ko yaya sawwama zata kasance matarsa,
Advertisement
Huuuuuu yaqara fitarwa wata iskar mai zafi,
Dafashi najeeb yayi yace bawai nafada maka dan ka sanya kanka cikin damuwa bane sadam bafada makane saboda abunda nake ganowa nan gaaba,
Murmushi sadam ya kwakulo wanda bai kai cikin zuciyaba yace banajin hakan najeeb,
In sha Allah mummy zata amince,
Allah yayarda najeeb ya amsa.
Sadam ne yaci gabada fadin
Kuma yazama kamar dolene saina samu babanta,
Idan ban sameshiba bazai yiwu nayi tarayya da diyarsaba,
Jijjiga kai najeeb yayi yace shikennan Allah ya sanya alkhairi,
Amin najeeb ya amsa,
Kallon najeeb sadam yayi yace amma maiyasa najeeb nida kai duka mummy mukeji azancen aurennan?
Murmushi najeeb yayi yace saboda munsan halinta mana, kai nifa banajin mummy zata barka kayi aure daga gama degree kawai,
Saboda taci buri akanka,
Mtseww sadam yaja dan guntun zaki sannan yace buri koh?
Ehem! Buri inji najeeb
Hmm Allah ya kyauta sadam yace sannan yadaura da fadin kasan jiyama sanda nayiwa mummy karya har nace takira ta tambayeka,
Dariya najeeb yayi yace kuma da takira fa?
Shima sadam din dariya yayi sannan yace haba ai nasan dai zaka kareni, shiyasama nyi,
Dariya najeeb yayi yace kaifa yanzu naga alama zamu daina yarda da kowace maganarka,
Hararan najeeb yayi yana fadin wato ga makaryaci koh?
Iyi! Najeeb yabashi amsa hadeda miqewa yabar wajan yasan yanzu sai sadam yacika famm."
Yau sadam baibi wajan sawwama ba tunda dama jiya bawai yace mata zaizo bane,
Dalilin dayasa yau din baijeba saboda yaga yanda jiya mummy tadauki lamarin da zafi dayayi dare amma bawai don bayason ganintaba,
Haka ya kwana da tunaninta,
Itama sawwama nata wajan da tunaninsa ta kwana."
Daga ranar sadam ya shaidawa mummy zai ringa tsayuwa karatu zainayin dare,
Mummy taso tadamu amma jin karatu zai ringa tsayawa saiya daure zuciyarta dan ita dai har in dai za'ayi karatunnan to komai zaizo matada sauki."
Najeeb kullum kwanan duniya saiyaje wajan sawwama,
Yanzu ya daina zuwa lokacin da take aiki yakan bari sai bayan isha'i sai yaje lokacin yasan tagama komai,
Ita sawwama anata wajan itama tafijin dadin hakan,
Dan takan samu tadan canja kaya koda kwaskwarinma nema tayi."
Yauma kamar kullum suna zaune suna dan shan hirarsu wanda suke yinta jifa-jifa,
Advertisement
Sadam har cikin ransa yanaso sawwama tayi karatu tun ranar yakeson tambayarta a matakinda ta tsaya a karatu bai samu damaba,
Bayaso yayi wani abunda zataga kamar yana son shiga rayuwarta,
Yau kam ya daure zuciyarsa ya dubeta yana fadin sawwama nikam na tambayeki mana?
Allah yasa nasani sawwama tafada a kunyace,
Kinma sani sadam yafadi sannan ya jefo mata tambaya da fadin shin wai ajinki nawane lokacinda kika tsayada karatu?
Yanda yayi zaton zata dauki abun ba haka tadaukaba domin murmushi yagani a kwance akan fuskarta,
Cikin halin rashin damuwa tace"
Uhmm aji uku,
Zaro😳 ido yayi yace uku?
Primary ko secondary?
Dariyace takama sawwama sanda tadan dara sannan tace primary kuma?
Nisawa yayi sannan yace to ai amsarda kika bayarne,
Girgiza kai tayi tace ina nufin jss3,
Gyada kansa yayi kawai,
Yanason yayiwa sawwama maganar karatu amma yanaga yanzu kamar yayi wuri dayawa,
Yanaso yabari sabonsu yadanfi hakane saiya samu damarda zaiyi mata magana, ya tabbata alokacin bazataqiba,
Islamiya fa?
Ya jefo mata tambaya!
Shiru tayi tana tunani domin rabonta da islamiya ta manta,
Bazata iya tuna lokacinba,
Shirunda yaga tayine yasanyashi tunani kodai batayi islamiya bane gabaki daya,
Rabona da islamiya na manta yaji tabashi amsa atakaice,
Jijjiga kai kawai yayi bai iya cewa komai ba abun yanata tsumashi,
Tayaya iyaye zasubar diyarsu haka babu islamiya,
Yasan wasu daga cikin makarantar islamiya babu tsada wasun kudinta gabaki daya baifi naira dariba,
Kaishi yasan har makarantar 20naira akwai wacce ake biya duk sati,
Ya lula tunani yama manta da agabanta yake,
Lafiya kuwa?
Muryarta ta katse masa tunani,
Dawo da hankalinsa gareta yayi ya sake mata murmushi sannan yace lafiya qlau me kika gani?
Naga kayi shiru tabashi amsa,
Babu komai yafadi,
Kai ta daga na gamsuwa da maganarsa,
Bai jimaba ya miqe da zummar zai tafi har yayi mata sallama sai kuma ya juya ya dubeta yace uhmm naceba wani satin zan fara exam ina buqatar addu'a'
Jijjiga kai tayi tace in sha Allah zanyi maka,
Allah ya taimaka yabada sa'a, ya sanya jarabawar tayi kyau fiyeda na kowani lokaci,
Amin ya amsa hadeda murmushi yaji dadin addu'ar ta sosai har cikin ransa,
Ahaka yayi mata sallama yatafi."
————
Sa'i-sa'i sadam yakan yiwa sawwama tambaya abunda yashafi addini,
Wani lokacin haka zaiyi mata da wayo yanda bazata ganeba,
Abunda ya lura shine sawwama tana buqatar ilimin addini sosai fiyeda komai,
Dan ya lura dan abunda tasani bai taka kara ya karyaba,
Abubuwa dayawa kawai tana yinsune batareda sanin hukuncinsu a addiniba,
Wannan abun ya tsayawa sadam arai sosai dan wani lokacin shi kadai idan ya zauna abunda yake tunani kenan kawai,
Gaskiya ayanda yake dan gwada sawwama wajan ilimin islama baiyi tsammanin samun hakaba,
Saboda atunaninsa duk rashin dukiya irinta mutum duk talaucinsa ba'a rasa yayansa da ilimi islama koda basu samu damar yin boko ba,
Yanzu haka exam dinsane kawai ya tsaya masa arai amma daba hakaba daya dade da nemowa wannan lamarin mafita,
Amma yanzu madai yana gama exam zai san abunyi."
————-
Sawwama kuwa yanzu anata wajan bata fashin yin sallah akan lokaci dan kawai tayiwa sadam addu'a yaci exam dinsa,
Akoda yaushe komai takeyi ana kiran sallah zata tashi tayi sai tayi masa addu'a,
Sa6anin da abaya wanda wani lokacin saita gama duk wani abunda takeyi kafin tadawo gida tahada sallar magrib da isha'i."
Lokacin saura 3days Sadam yafara exam sawwama da kanta tacewa sadam yarage zuwa saboda yasamu lokacin karatu dan tanaso yaci jarabawarsa fiyeda nakowani lokaci,
Haka sadam badan yasoba yafara tsallake kwanaki kamar yanda ta buqata,
Karatu kuwa sadam yanayinsa dagaske saboda abun yahadu masa biyu, ga mummy kullum addu'arta sadam yaci exam yayi karatu, har raba dare takeyi tana sallah tanayi masa addu'a wani lokacinma haka zata tashi tsakar dare taje dakinsa yana tsaka da bacci tatasheshi wai yayi karatu,
Shikuwa sadam tana juya baya yake komawa ya kwanta,
Yakance idan ba mutuwa akeso yayiba abarshi yayi baccin dare,
Wuni yakeyi yana karatu saboda a school yake wuni bayan yadawo gida kafin yayi bacci ma saiya ta6a karatu yake kwanciya amma wai ahakanma sai an tasheshi cikin dare kawai yayi karatu, inji fadinsa aiko karatun shiga aljanna iyakaci,
Ga sawwama itama nata wajan tanaso yayi karatu yaci sakamako mai kyau."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial6 Chapters
LandFall's legacy
An 18 years old ojou san considered as the youngest martial art genius and master of other fields , found herself transported by an unknown item into an another world.Find out about her decisions as she embrasses her new life .
8 124 - In Serial289 Chapters
The Adventurer's Academy
Rin Asahiro, a twenty-year-old sex worker, decides to turn her life around and become an adventurer. Only, she has a vague idea of what the actual occupation of being an adventurer entails. In an effort to lead a life she could be proud of, Rin will learn exactly what encompasses the dichotomy of adventuring: Glory and devastation, all while she tries to maneuver around obstacles in a strange world. ---------- A slow-burn high fantasy story about a young peasant trying to make it as an adventurer.
8 334 - In Serial11 Chapters
Asthetic (Audrey Jensen)
Hi I'm Sheylee Eckhart and I'm an asthetic Lesbian who is in love with the towns bad ass Audrey jensen.
8 104 - In Serial11 Chapters
Great Master of All
Hmm, Basically no Idea for a sypnosis but well. Will he be the great master of all or what might happen? Uhh, warning is there for whatever it is better warned than nothing kek
8 184 - In Serial6 Chapters
COTE Reacción a Vida Pacífica
Fanfic of reaction, but it will not be about the one we all know, but of reaction to Vida PacificaThis is my first reaction fic, I hope you like itIt will be a reaction to my other story, how the COTE characters would react to a world where Kiyotaka has a Peaceful Life, I invite you to read my other fic first to avoid spoilers!!
8 179 - In Serial23 Chapters
Story Of My Life
This book is all about a real story of my personal life and every up and down, with changes only of places and names of people. Mature scenery is to be expected
8 174

