《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 20

Advertisement

**

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by

zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)

#Follow me on

Wannan shafin sadaukarwane gareki Qawar arziki *Badi'atu abdulsamad* (beesamad)amincin Allah yakai miki aduk yanda kike, ILYSM🥰

Sanda sadam yatsaya a masallacin da suke sallah yayi sallahn isha'i sannan yawuce gida,

Da sallama yashiga ciki ya samu mummy zaune afalo ga dukkan alamu hankalinta yana wajansa, dawowarsa kawai take jira,

Amsa sallamar sukayi ya qarasa gefen dady ya zauna,

Gaisheda dady yayi, dady ya amsa cikin fara'a yana fadin sadam an dawo?

Ya karatun?

Karatu Alhamdulillah sadam ya amsa,

Kallon mummy sadam yayi sai wnai cika takeyi da dukkan alamu da shaqa dayawa, dariyane taso kamashi amma ya matse yana fadin mummy sannu da gida,

Shiru tayi kamar bata jishiba tashi qara mai-mai tawa yayi amma nanma bata amsaba, miqewa sadam yayi ya isa kujerarda take zaune ya zauna,

Sannu da gida mummy yaqara fadi akaro na uku,

Kamar wanda aka dama jira take yaqara magana cikim zafi tafara fadin, wato sadam ka rainani koh?

Yanzu karfe nawa?

Duba agogo kagani karfe takwas sai yanzu kake dawowa gida?

Sadam bai samu damar bada amsaba dady ya amshe maganar da fadin haba sajida wai mai kikeson kidawo ne?

Eyemm yaro yana qoqarinsa dai-dai gwargwado eyem amma ke bakya gani, iya qoqari yana yinsa balle sadam shiba rawar kai gareshiba kinaso ki takura masa takurin yayi yawa harya kaiga yafarayin abunda bamaso ba fata nakeyiba,

Shi yaro namiji zakayi tayi masa kulle kamar macene?

Balle yanzu shekarunsa nawa?

Shiba qaramin yaro bane,

Ko yanzu akayi masa aure zama zaiyi ya riqe matarsa gam, iyeh

Amma kin maidashi qaramin yaro,

Jin zancen aure da sadam yayi ya sanya yafara murmushi,

Amma me? Mummy ce takatse dady da fadin sadam dinne zai iya riqe mata?

Kwarai kuwa dady yabata amsa,

Aikuwa dai ko zai iya sadam baisan shekarun aureba nanda shekaru gaba,

Idan yayi aure karatunsa fa?

Nima aii bawai nace miki yayi auren bane misali nake miki saboda ki rage wanna takurin, amfaninsa kadanne,

Advertisement

Shiru mummy tayi batace komaiba sadam kuwa gabasa sanda ya fadi jin yanda mummy tadauki zancen da zafi, akwai qura yafadi aransa,

Dadyne ya kalli sadam yace daga yanzu idan kanason zuwa wani waje kajeka bazan qara kullekaba ai kai ba mace bace,

Banaso dai ya kasance goma tayi baka dawoba aduk yanda kake tara da rabi 9:30pm tayi maka a gida,

Lasisi! Sadam ya furta cikin zuciyarsa afili kuwa yacewa dady ya gode,

Mummy kuwa baqin ciki ya hanata cewa komai,

Itafa nata tunanin dalilin dayasa take hanashi fita daga school sai school bawai tsantsan kulle bane A'a son yayi karatu da kuma qin kada ya je yafara soyayya dan ita taci buri akan karatun sadam bata sanya masa shekarar aureba shiyasa take wannan taka tsan-tsan gashi kuma dady yazo ya 6ata mata duk wani budget dinta,

Satan kallon mummy sadam yayi yaga yanda take wani cika tana hura hanci,

Qara matsawa sadam yayi kusada ita ya kamo hannunta juyawa tayi ta kalleshi sannan ta juyarda kanta gefe,

Langa6arda kansa yayi yana fadin eyya mummy am karatufa natsayayi, sadam ya samu kansa da fillo qarya,

Karatu! Mummy ta mai-maita,

Eh mummy karatu natsayi,

Mummy tadan fara saukowa tadan kalleshi alamun tanason yarda da zancensa tace" to maiyas baka dawo gida kayi karatun agida ba?

Uhm-uhm mummy wani karatun sai cikin abokanai aii mummy zaki iya kiran najeeb ba ki tambayeshi, sadam yafadi cikin son ta gamsu da maganarsa,

Girgiza kai mummy tayi na gamsuwa da zancensa tace" basaina kirashiba ai nasan dama karatunne kadai zai tsaidaka,

Murmushi sadam yayi na ganin mummy tafadawa zancensa,

Kallonsa mummy tayi tace bawai na kyaleka bane dan wani abuba sai dan darajar karatunda ka tsaya kayi,

Kuma kaine da shegen taurin kai sadam babu yanda banyiba akan kakoma hostel kaki to ina amfanin yin daren?

Jijjiga hannunta kawai yayi hadeda fadin mummyy,,,, yafadi hadeda dan jann sunan, nidai kawai kimun addu'a in sha Allah sai result dina yabaki mamaki,

Advertisement

Mummy in sha Allah zanyi qoqarinda ban ta6a yiba,

Washe baki mummy tayi tana fadin kaga kuwa idan kamin haka ka gamamin komai,

Kaga sadam dalilin dayasa nakeson kayi karatu ka zama nutsattse dalilin kaine babba acikinsu abunda kayi shi qannenka zasubi suyi,

Wata rana kaima kazama mai sanyasu a hanya kabasu shawarar yin abu mai kyau,

Murmushi sadam yayi yace in sha Allah mummy zanyi,

Badai karatuba?

Zan cika miki burinki,

Shafo kansa mummy tayi tace Allah yayi maka albarka, ni ai har indai zakayi karatu sadam duk wani abunda kakeso arayuwa zanyi maka shi,

Murmushi sadam yayi yana ayyana abubuwa acikin ransa, afili kuwa ya furta kinyi alqawari?

Nayi alqawari mummy tabashi amsa kai tsaye batareda tunanin komaiba,

Shikenan mummy tunda kinyi alqawarin cikamin burina idan nayi karatu nima zan cika miki burinki da yardar Allah,

Murmushi mummy tayi najin dadi,

Sadam zuciyarsa abunda take tunani masa daban, yayinda itama mummy yanda zuciyarta tatafi daban,

Dady dayake sauraronsu ya girgiza kai kawai,

Shi har cikn ransa yanason yaransa suyi karatu amma na mummy abun har yayi yawa,

Shafo fuskar sadam mummy tayi hadeda fadin tashi kaje kayi wanka ka huta saika fito muyi diner,

Gyada kai yayi hadeda miqewa ya shiga daki, ya zauna akan katifansa shi kadai yana tunanin qaryarda ya gillawa mummy yanzu,

Shi har mamakin kansa yakeyi abaya kwata-kwata bai iya qaryaba gaskiya zai fada ko wani hali kuwa za'a shiga,

Amma gashi yanzu soyayya ta canjashi,

Yanajin kansa cikin nishad'i bayason wani abunda zaizo ya gusar masa waannan yanayi mai dadi dayake ciki,

Yana zaune bai tashiba yaji sallamar hassana, jaddada masa tayi akan mummy tana jiransa yazo ayi diner,

Shi harya manta ma shadaf soyayya ta cike masa ciki bayajin yunwa badan yaci abunciba,

Agaugauce yashiga wanka yafito ya sanya kaya yafita,

Lokaci-lokaci mummy kan sakin murmushi ganin haka yasa mummy ta tsareshi da tambaya,

Kasace mata komai yayi dan haka dole zaiyi controlling kansa idan yana tareda mummy saboda kada ta ganoshi,

Tambayoyinta ba masu amsa bane,

Yana gamawa kuwa yashige cikin daki yahau aikin tunanin sawwama,

Yana buqatar jin muryarta amma kuma baisan yaya zaiyiba saboda ita ba waya garetaba,

Haka dai ya daddaure ya kwanta."

——————

Ita ma sawwama anata wajan haka ya kasance wani irin farin ciki ta tsinci kanta aciki,

Haka tashiga gida da wannan fara'ar,

Jira kawoi takeyi baba yadawo ta shaida masa zuwan sadam,

Bayan baba yadawo tayi masa sannu da dawowa ta tsugunna gabansa takasa magana,

Baba yana ganin haka yasan da magana abakinta,

Mamana yakira sunanta na'am ta amsa hadeda dagowa ta dubeshi,

Dawonan ki fadamin da magana abakinki,

Matsowa tayi kusadashi fuskarta cike da annuri,

Murmushi baba yayi yana fadin maiya farune mamana?

Naga annuri cike a fuskarki,

Wasa sawwama tafarayi da yatsunta kanta yana qasa,

Cikin jin kunya tace baba dama yazone,

Murmushi baba yayi yace" toh Allah mun gode maka,

Mama ma taji sanyi aranta sosai,

Baba yaci gaba da fadin irin wannan mijin akeso wanda bazai gujeka dan wani abun yafaru da kaiba,

Allah ya za6ar mana mafi alkhairi,

Amin su duka suka amsa,

Sannan baba yadaura da fadin sawwama inaso kisani bawai dan ya yarda dake ahaka kekuma kisake jiki ba,

Ina nufin ki kama mutumcinki ki rufawa kanki asiri, dan wannan abun yafaru bashi yake nuna bakida sauran kima ba,

Nasiha baba yayita mata sosai har taji jikinta yayi sanyi, sannan daga karshe ya sanya mata albarka yana qara jaddada mata riqe mutumcinta,

Sawwama ranar tayi kwanan farin ciki

Sa'i-sa'i kalamansa suke dawo mata, aduk sanda tatuna takanji wani irin sanyi ya ratsa duk wani gabban jikinta,

Ita kanta ta tabbata tasamu saurayi mai sonta tsakani da Allah, tasamu mijinda kowace mace zatayi alfahari da samun irinsa."

Yau dai banyi editing ba zai iya yiwuwa aka mistakes kala-kala sai akaranta da hakuri🥰

✔️ote

Comment

Share

Follow plss @zeeyybawa

To be continued

Zaynab Alabura."

people are reading<ƘADDARAR RAYUWA>
    Close message
    Advertisement
    You may like
    You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
    5800Coins for Signup,580 Coins daily.
    Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
    2 Then Click【Add To Home Screen】
    1Click