《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 19
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 19
Haka sadam yatafi gida jiki duk amace,
Yarasa mai yake masa dad'i tunda yake arayuwarsa bai ta6ajin tausayin wani mahaluki kamar yanda yakejin tausayin sawwama a yanzu ba,
Tabbas dole sawwama taringa gwada rashin yarda qiri-qiri dole sawwama taringa nuna tsoronsa a fili, dole taqi aminta dashi alokacinda yazo matada batun taimako dakuma lokacinda yazo matada batun soyayya,
Wutarda ta qoneka bazakaso tasake qonarka ba,
Abaya yayi kuskure na daukan fushi da yayi da sawwama akan abunda takeda gaskiya akai,
Tabbas yanzu yaqara yarda idan ba kaine amtsayin mutum ba kokuma yafada maka abunda yake faruba dashi ba, kada ka ta6a daukan fushi da yanayin mu'amalarsa dakai,
Zancen baba yakasa fita aransa zancenne yake dawo masa yanajin wani irin zafi da quna cikin ransa, shekarun baya da suke wuce an ta6a yiwa sawwama fyade!
Shekarun baya da suka wuce hakan yana nufin sawwama tana qaramar yarinya kenan,
Inbanda wasu mutanen da rashin imani da tausayina menene har zakaji ajikin qaramar yarinya,
Ko yanzu sawwama bawani gama cika tayiba balle shekarun baya, yaqraa tabbatarwa rashin imani na mutane yayi yawa,
Yarassa ta yanda zai fassara wanna abun,
Haka ya kwana zuciyarsa cike da dumbin tausayin sawwama hadeda zugi da radad'i
Yanajin zafi aransa kamar ma qanwarsa aka aikatawa hakan,
Haka a school ya wuni jiki babu kwari, najeeb yaso sanin mai yake damusan shima sadam da farko yaso gaya masa amma sai yaga rashin dacewar hakan saboda shima kansa wannan abun yanzu yadawo sirrinsa ba sirrinta ita kadaiba idan yafadawa najeeb koba yanzuba zaiyita kallonta da wannan abunne,
Shikuma bazai ta6oso ayiwa matarsa wani kallo ba,
Haka ya shanye abun cikin ransa,
Duk da yaso yabi wajanta yau amma bai samu damaba,
Saboda yanda abun yake damunsa cikin jiki zuwa zuciyarsa,
Sawwama batayi mamakin rashin ganinsaba saboda dama tasa ranta da faruwar hakan,
Koda babanta yadawo ya tambayeta ko yadawo ta shaida masa bai dawoba,
Advertisement
Jijjiga kai baba yayi sannan yace nasan za'ayi haka shikenan ai Allah ya za6a miki mafi alkhairi kici gaba da addu'a,
Amin sawwama ta amsa,
bayan sun shiga d'aki itada qannenta da shirya musu wajan kwanciya kamar yanda ta saba itama ta kwanta amma me har qannenta sukayi bacci idanuwanta babu alamun bacci,
Saida dare ya tsala sannan sawwama tasamu damar yin kuka, awannan dare sawwama tayi kuka kamar ranta zai fita ta jawa wannan mutumi daya aikata mata Allah ya isa yafi cikin kwando."
Duk wata addu'arda tazo bakinta yi masa takeyi ta tabbata bazata ta6a yafe masaba, kuma ta tabbata komai daren dadewa sai Allah yayi mata sakayya akan wannan mummunan aikin da yayi mata."
Mama anata wajanma hakane har sanda baba yayi bacci ya farka ya ganta a zaune tambayarta yayi kafiya batayi bacciba,
Cikin damuwa tace baban sawwama tunanina wannan yaro gashi kafad'a masa komai kuma bai dawoba ina tsoro abunda zai biyo baya ba lallai ya iya riqe bakinsaba zaije yayita fadawa mutane har azo abu ya bazu bamusan wani irin kallo mutane zasuyi manaba.
In sha Allah haka bazata faruba baba yafara kwnatar matada hankali, nayi magana dashi na roqi wanna alfarmar yarufa mana sirrinmu,
Kayya baban sawwama ba kowa keda wannan alqawarinba saboda mutane yanzu sun 6aci kowa jira yake yaji taka yaya yayataka,
Da wannan dan wannan baba yafadi sannan yadaura da cewa nasan da haka amma yanada kyau mu kyautata masa zato in sha Allah haka bazata faruba,
Allah yayarda mama tace baba ya amsa da amin sai alokacin mama tadanji sanyi tasamu ta kwanta."
Bayan magrib kawai sai ga sadam yazo sawwama tana zaune hancinta yafara jiyo mata kamshin turarensa,
Bata d'agoba saboda tasan zuciyarta ke yaudararta tarigada ta cire rai da sake ganinsa, tasan bazai ta6a dawowaba,
Gabanta ya tsananta faduwa tashiga wani yanayi aduk lokacinda sadam zaizo saida tsinci kanta cikin wannan yanayin,
Aikinda takeyi takasa cigaba, jikinta yadauki rawa, jiki babu kwari tajuya ta kalli gefe, aikuwa ga mamakinta idanuwanta suka sauka akansa yazo daff da ita baqaramin mamaki sawwama tayiba mamakinta har ya gaza 6oyuwa sanda ya nuna akan fuskarta,
Advertisement
Qarasowa sadam yayi yana sakin mata qayataccen murmushi wanda ya qarawa fuskarsa annuri,
Zama yayi gefe dan kusada ita kadan sawwama takasa dauke kanta daga ganinsa,
Mamaki qarara akan fuskarta, wani murmushin sadam yaqara jefanta dashi sannan yace"
Mamakin me kikeyi? Daburburcewa tayi cikin rawar jiki tace
Mamaki kuma? Tafada tanason kauda zancen, gyada kai yayi yace" eh mamaki! saboda fuskarki tanuna hakan,
Jijjiga kai tayi yana kawai tayi tarasa mai yasa yake saurin gano halinda take ciki,
Bakiyi zaton sake ganina bane?
Taji ya jefo mata tambaya,
Gyada kai tayi hadeda fadin abunda yabani mamakin kennan nadauka katafi kenan bazan sake ganinkaba,
Girgiza kai yayi yace Akan wani dalili zan bar zan tafi bazan sake dawowaba?
Saboda!!!! Sawwama tafara magana sai kuma takasa qarasawa ta sunkuida kanta qasa,
Murmushi sadam yayi cikin tausayawa yace" zan dawo sawwama ai sonda nake miki ba qarya bane, akanme zan rabuda abunda nakeso dan wata qaddara ta fada miki?
Ashema soyayyata bata cikaba kenan.
Ashe ba son gaskiya nake mikiba,
sawwama ina sonkine tsakani da Allah soyayyarda nakeyi miki babu algus acikinta,
Dan wannan abun ya faru dake bazai rage dai-dai kwayar zarra cikin sonda nake mikiba,
Inaso kisani bazan ta6a rabuwa dakeba da yardar Allah zamu kasance atare,
Dagowa sawwama tayi ta dubeshi cikin rawar murya tace to idan kai ka yarda iyayenka fa?
Murmushi sadam yayi yace akanme zasu sani?
Ni zan aureki ba kowaba,
Wannan sirrin ni kadai ya shafa, babu ruwan kowa cikin wannan lamarin sawwama,
Wannan sirri nane ni dake zan rufa miki sirrinki
Kamar yanda zan rufe nawa sirrin kai koma fiyeda yanda zna rufe nawa sirrin, mahaifana da kowa bazan bari susan wannan zancenba saboda sirrinki sirrina ne, sirrinki yarufu awajena bazan bude ba har wani yaji,
Sunkuida kanta tayi qasa kwalla yanabin kan kumatunta ta tabbata sadam masoyin asaline,
Zaiyi wuya tasamu wanda yakeyi mata so irin wannan,
Sadam ne yaci gabada fadin sawwma nasan qaddara zatayi iya fadawa kan kowa bbu wanda yafi qarfinta,
Bazan iya gudun dan adam akan wata qaddara data fada masaba saboda nima banfi karfintaba akowani irin lokaci Allah zai iya jarabtata,
Nidai abunda nake buqata daga gareki kisoni sonda babu algus acikinsa,
Kisoni tskani da Allah
Kada kisoni dan wani abu kodan na nuna miki cewa inasonki cikin kowani rin hali kema kiji zaki sakamin da maidaomin da soyayya ba,
Inaso ya kasance kin soni saboda Allah yakasance kin soni saboda kasancewata ni bakowaba bakuma dan wani daliliba,
Idan so ya kafu dan wani dalili ba fataba mai zai faru ranarda akace babu wannan dalili?
Bayan gushewar dalilin da aka gina soyayya akansa shin soyayayr zataci gaba da yaduwa ko zata mutu,
Abu dayane zaka yishi wanda har abada bazakaga karshensa ba shine yin abu dan Allah,
Nidai ina sonki dan Allah sawwama, aduniya da kika gani babu wanda yake tsarawa kansa rayuwa komai kikaga yafaru daga Allah ne,
Babu wanda yake za6awa kansa rayuwa dan damuna za6in rayuwa akanmu da dayawa baki gansu a halinda suke cikiba,
Dago ido sawwama tayi tana dubansa kalamansa cike suke da hikima da sanin ya kamata,
Kalamansa sun shigi sawwama sosai, komai zaiyi yana aiki da hankalinsa wajan aikatashi hatta kalamansa suna kan mizani,
Cikin yanayin jin dadi sawwama tace nagode da muna qaunarka a gareni,
Allah yabani ikon mayar maka qaunarda kakemin,
Amin sadam ya amsa cikin jin dadi hakan ya nuna ta aminta dashi kennan."
Tad'i suka dan ta6a jefi-jefi saboda rashin sabo da juna,
Dare yadan farayi kafin sadam ya anqara miqewa yayi zumbur yana fadin natsaya hira dare yayi barina wuce, sawwama ji tayi kamar ta hanashi tafiya amma kunya ta hanata, agaugauce yayi mata sallama yatafi hankalinsa yayi gida baisan mai zai gayawa mummy ba yasan sai tayita fada, shikuma baison fadanta kokadan."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial128 Chapters
Is that a Wisp?
In this universe, wisps are the absolute weakest forms of life. Although intelligent, they are basically not suited for cultivation due to their very limited life spans.Krune just so happens to be one of them. Worst of all, wisps are frequently used as cultivation resources. Since they are beings of energy, they are suitable for cultivation due to their high concentration of it. In a fated night, while wisp hunters were pursuing him, Krune will meet a little lady who will change his life. Here, on the distant planet of Makui, a legend is born. This story is also available on webnovel.
8 159 - In Serial34 Chapters
Runic System
A world that runs with the power of runes. Cultivation to immortality is possible. Legends are possible. A world of martial arts, where survival of the fittest is supreme. EPUB AND PDF FOR THE FIRST VOLUME CAN NOW BE FOUND FOR FREE IN THE LINKS BELOW. shorturl.at/etGIX EPUB shorturl.at/ciFTW PDF (image resolution is worse due to the smaller file size.) Release schedule. (MAY VARY) SUNDAY - chapter 3300~ words average Monday (rare) Wednesday (rare)
8 103 - In Serial25 Chapters
Accused: The KC Warlock Weekly, Book One
My name is Levi. I’m a journalist, I’m autistic, I’m bad at magic, and I swear I didn’t kill her.Research for the paper usually falls into a few basic patterns. Someone in the city says there’s a troll under Buck O'Neil Bridge, or they’ll call just so a friendly ear will listen to them complain about a pixie infestation.That sort of content carries me through slow news weeks. It’s rare that I uncover a murder.Being framed for murder, though? That’s a first.With the Wizard’s Council hunting me for a crime I didn’t commit, I’ve got no choice but to solve the murder and clear my name. If I don’t unravel this case, nobody will, and I’ll go down for it so hard I might never see the light of day again.
8 114 - In Serial8 Chapters
Space Explorers (Dropped)
What do you do if you have nothing to do because the world is fully automated? What do you do if humanity has reached all they could except for exploring the universe because alien creatures are blocking us from exploring outside of our solar system? Enter the story of Space Explorers and find out the answers to these questions and more.
8 135 - In Serial8 Chapters
Project from December 2019
Starting chapters are heavily invested in psychology and philosophy. A story about John Keene exploring a different world. This project is similar to 'Ex Legacy' and 'Aidan Alastair'; they follow similar plots. Ex Legacy has more of a completed feel so far - it's debatable, but you are free to read both of them: Aidan Alastair: https://www.royalroad.com/fiction/31409/aidan-alastair-volume-1 Ex Legacy: https://www.royalroad.com/fiction/48422/ex-legacy
8 182 - In Serial11 Chapters
'Til Death Do Us Part [Bleach Fan Fiction: sequel to Be My Fraccion?]
In this sequel to the hit Fan Fiction; 'Be My Fraccion?' Brooke is a sixteen year old girl who was transformed by Aizen into an Arrancar, and now lives in Hueco Mundo, serving as Grimmjow Jeagerjaques Fraccion. Her life becomes complicated, however, when Grimmjow, Aizen, Ulquiorra, and Gin all begin a deadly battle for her affections. Join Brooke in her heart-wrenching journey to discover who she really loves, and who really loves her. Warning: violence and steamy hot scenes with Espada and ex-shinigami. Rated T.
8 62

