《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 18
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 18
Wannan dare sawwama bata samu ta runtsa ba, kamar yanda taga rana haka taganshi har tsoron wayewar gari takai batayi bacci ba, gashi wani irin sauri da daren yayi mata, adaren sawwama taja Allah ya isa ma wanda ya aikata mata wanna abun yafi cikin kwando, baqin ciki da tashin hankali daya sanyata aciki kadai ya isa Allah ya saka mata, ta dalilinsane take cikin wannan fargaba da zullumi da tashin hankali, sake sakenda taringayi kenan har sanda taji kiran sallah,
Gani tayi Anyi saurin kiran sallah, daren yayi mata gajarta garin ya waye mata da wuri anata wajan, koda mama tazo tashinta ta sameta idonta biyu,
Mama batayi tunanin sawwama batayi bacci bane anata tunanin kiran sallah ne ya tasheta, da fargaba tatashi dan gani takeyi rabuwarsu ne yazo taje tayi alwala baba yajasu sallah, Addu'a kam kala-kala sawwama tayisu wasuma bata ta6a yiba amma yau sanda tayi."
Haka da gari ya waye ma gani takeyi komai sauri yakeyi mata,
Ba taso yamma tayi saboda ba taso sadam yazo har wannan magana tashiga tsakaninsu da mahaifinta ta tabbata daga wannan lokaci bazata sake sanyashi a kwayar idanuwanta ba,
Haka tawuni jiki duk a sanyaye mama da kanta ta fahimci hakan ta kirata tanata yimata nasiha akan tadauki qaddara ko wace irice,
Kuma koda ace wannan yatafi idan yaji abunda tafaru da ita Allah zai sake kawo mata wani,
Haka tayita lalla6ata."
Sai bayan anyi magrib kafinann sadam yazo, ayanda ya saba zama ya isa ya zauna,
Sawwama tana kallonsa jikinta yadauki rawa takasa gaisheshi tana addu'ar Allah yasa kar yazo sai kuma gashi yazo,
Gabantane yahau faduwa ta sunkuida kanta qasa har cikin ranta bataso zuwansaba,
Dakyar ta iya furta sannu da zuwa,
Amsawa yayi da fadin yawwa,
Daga nan dukansu sukayi shiru,
Har yanzu baki yanke shawaraba kenan?
Ya jefo mata tambaya,
Nisawa tayi cikin nutsuwa tafara magana da fadin yanzu yanke shawara yana wajan ka,
Kamar yaya awajena?
Ya tambaya amma kinsa nikam aii na sanar dake abunda yake zuciyata sannan kuma nabarki ki yanke hukunci,
Girgiza kai tayi sannan tace yanzu hukuncinka ne yarage ni nawa zakaji daga baya,
Cikin rashin fahimta yace kmar yaya? babana ne yakeson ganinka zaiyi magana dakai, ta katse zancen batareda tabashi amsa tambayarsa ba,
Toh sadam ya amsa
Ko d'ar sadam baiji ajikinsaba cewar mahaifinta yana nemnasa, yasan koda mahaifinta bai nemeshiba shi zai nemeshi, tunda yasan shi bada wasa yazoba,
Advertisement
D'agowa tayi taga yanayinsa amma sai taga babu ko alamar damuwa atattare dashi,
Alokacin ta qara tabbatarwa cewa da gaske yakeyi danta tabbata daba da gaske yakeyiba da tana ambatar mahaifinta yanayinsa zai canja,
Kallonta yayi yace baban yana inane?
Yana cikin gida tabashi amsa,
Ki sanar masada zuwana sadam ya umurci sawwama,
Jiki a sanyaye sawwama ta tashi tanufi gida tana tafiya tana kalloshi kamar wanda ya kasance kallonta na karshe dashi kenan,
Ta shiga cikin gida tasamu baba yana zaune abarandar qofar d'aki qarasawa tayi ta durkusa tana fadin sannu da dawowa baba,
Amsawa yayi yana fadin sannu sawwama,
Duqarda kanta qasa tayi tace" baba ya iso,
To madallah yana qofar gidane?
Girgiza kai tayi tace A'a yana wajan canne,
Maza je kice masa ya qaraso zuwa qofar gida,
Miqewa sawwama tayi cikin nustuwa tafice baiji zuwantaba ya nutsa cikin tunani saida tayi sallama da siririyar muryarta,
D'agowa yayi ya amsa cikin nutsuwa,
Qasa tayi da kanta tafara wasada yatsun hannunta a hankali ta furta wai inji baba ka qarasa zuwa qofar gida,
Miqewa yayi yace muje cikin nutsuwa tafara tafiya yana binta abaya,
Yarinyace qarama amma komai nata anutse take yinsa har yanda take taka qafafunta cikin nutsuwa komai nata atsare yake,
Nutsuwarta tana d'aya daga cikin abunda yake fisgarsa yakejin kullum tana qara shiga ransa,
Sanda suka kai qofar gidan sannan tatsaya tace barina shiga nayi masa magana,
Kai ya gyada tashiga ciki ta sanarawa baba qarasowarsa,
Baba bai dauki lokaciba yafice,
Atsaye yasameshi sadam yana kallonsa ya tsugunna qasa cikin girmamawa yana gaidashi,
Amsawa baba yayi cikin sakin fuska,
Yana fadin madallah mamana ta sanar dani abunda yake tafe da kai, to shine nace mata inaso mudan zanta ni da kai sai naji ta bakinka,
Waqa bakin mai ita tafi dadi, yanzu saika yimun bayani inaji duk da tayimun bayani amma zanfison ji daga bakinka,
Cikin jin kunya sadam ya sanarwa baba abunda yake tafe dashi,
Baba yace toh yanzu aina kake sannan kuma inason sanin sunan mahaifinka dakuma yanda kuke zama,
Ko d'ar babu sadam ya sanar dashi abubuwanda ya kamata ya sani gamedashi,,
Jijjiga kai baba yayi yace toh banqi takaba sadam amma baka ganin cewa kai din ba sa'an aurenta bane? Ina nufin kwarya tabi kwarya tanemi dan uwanta talaka marar galihu irinta baka ganin hakan zaifi, duba da yanda ya kasance cewa kai qaramin yarone, idan kai kagani kanaso kana ganin wajan mahaifanka baza'a samu matsala ba?
Girgiza kai sadam yayi yace baba nikam tunda ni na ganta ina sonta ai babu komai, dama kuma yanzu ina karatune baifi saura shekara daya da rabi nagama ba,
Advertisement
Idan nagama nasan lokacin bazan samu matsala daga wajansu ba amma yanzu koda naje musu da zancen ban rigada nagama makaranta ba bazasu amincewaba,
Jijjjiga kai baba yayi yace naji dad'i daka fito ka fadmin gaskiyarka,
Hakanne yasa nima yanzu zan fito nafad'a maka iya gaskiyata,
Abunda nakeso kasani shine ita Qaddara abace marar tabbas zata iya zuwa maka mai kyau kokuma marar kyau,
Qaddara bata wuce kan kowaba sannan kuma ita rayuwa daka gani kowa da irin tasa Qaddarar,
Qaddarar rayuwa mafi yawanci kowa saiya fuskanceta wasu ta kasance musu mai kyau wasu asakin haka,
Babban abun shine muyi imani akanta mai kyau ko marar kyau,
Mu sanya aranmu cewa ubangijine yake daurowa bawansa kaddarar,
Jarabawace ya jarrabeka,
Tabbas akwai qaddara mai muni data faruda mamana,
D'agowa sadam yayi yana dubansa gabaki d'aya jikinsa yayi sanyi ya qagu yaji mai akeson fada masa,
Nisawa baba yayi sannan yaci gabada cewa ba ita ta za6awa kanta hakanba, bakuma ita tadaura kanta hakanba ubangijine ya sanya wannan Qaddara ta fad'o cikin rayuwarta,
Sadam Shekarun baya da suka wuce babban al'amari yafaru da sawwama nisawa baba yayi sannan ya saukarda numfashi sannan ya furzarda iska mai zafi ga dukkan alamu abunda yakeson fadi yayi masa nauyi,
Cikin sanyin jiki sadam yake dubansa gabaki daya yanzu yashiga wani yanayi, zuciyarsace ta hau bugawa fargabarsa d'aya kada baba ya furta masa bazai iya bashi auren sawwama ba,
Baba ne yaci gabada magana, anta6a yiwa sawwama fyade shekarun baya da suka wuce,
Runtse ido sadam yayi jin yanda maganar ta dukesi,
Bai bude idonsaba yaji baba yaci gaba da fad'in,
Sawwama bata cuci kowaba kuma bata zalinci kowaba amma ita anyi mata zalinci mafi muni,
An 6ata mata rayuwarta,
Hawayene suka taru tabb a idon sadam cikin jin zafin abunda yafaru da sawwama yace baba kuma ba'a dauki mataki ba?
Babu matakin da aka dauka. Saboda koda zamu dauki mataki bamusan wayeba, koda munsan waye bamuda halin yin shari'a dashi,
Baba yadubeshi yace" sawwama tnada tarbiya tanada hankali sosai,
Tanajin zafin abunda yafaru da ita fiyeda kowa aduniyarnan, sawwama tanada kyawawan halaye d'abi'unta masu kyaune, bawai danna kasance mahaifin sawwama ba A'a duk wanda yake tareda ita zai fad'i kyakkyawan halinta."
Nafada maka wannan abunne saboda har indai neman aurenne dagaske tabbas ya kamata kasani, sirrinane nida iyalaina,
Kaje ka yankewa kanka hukunci,
Ka yanke duk wani abunda zuciyarka ta ayyana maka bazan hanaka ba zan fahimceka,
Saboda ba kowa bane zai iya daukan wannan al'amariba,
Idan ka yanke shawarar ci gabada nemanta Alhamdulillah sai muyi muku addu'a idan kuma ka yanke shawarar rabuwa da ita dan Allah ina roqonka daka dauke kafa daga wajanta dan Allah kayimun wannan alfarmar banason ganinta cikin wani hali,
Ganinka zai iya sanyata cikin wani hali,
Sannan ina neman alfarma d'aya har indai ya kasance zaka rabu da ita ina roqonka daka rufamun sirrina,
Duk duniya idan kacire ita da mahaifiyarta dani babu wanda yasan wannan zancen sai kai dana fadawa,
Inba ace yakamata kasaniba bakina bazai iya furtawa kowa wannan zacenba,
Dan Allah ka rufamin sirrina wanda ya rufa asirin wani Allah zai rufa masa nasa,
Har indai kabud'e duniya tasani kowa da irin kallonda zaiyi mata, wani bazai dauki hakan matsayin Qaddara ba, kowa da irin fahimtarda zaiyiwa lamarin,
Sadam bai iya cewa komaiba har baba yayi masa sallama yakoma ciki,
Sadam ya dade awajan dakyar ya iya d'aga kafarsa yabar wajan."
Baba bayan ya shiga gida yakira sawwama zuwa d'akinsu,
Itada mama yabasu labarin duk abunda yafaru sannan yadaura da fadin mamana inaso ki sanyawa ranki samu da rashi na Allah ne banaso kishiga damuwa ga duk wani irin hukunci dazai yanke inaso kidauka rubutaccen al'amarine duk abunda Allah ya rubuta saiya faru,
Kina zaune mijinki zai riskeki, idan kuma Allah ya rubuta cewa mijinkine babu makawa kota wani irin hali saiya zama mijinki,
A gaskiya na yaba d hankalin yaron sosai yanada nutsuwa irin mijinda nakeyi miki fata kenan akoda yaushe,
Amma idan hakan bai yiwuba inaso ki sanyawa ranki salama. Allah shi yafimu sanin abunda yafi dacewa damu,
Jijjiga kai sawwama tayi kalaman mahaifinta yasa taji sanyi cikin ranta,
Godiya tayiwa babansu sannan ta miqe tatafi,
Bayan ya fita mama tadubi baba tace duk wanda ya aikatawa sawwama wannan aiki Allah bazai barshiba.
Sai Allah yayi mana sakayya mai muni shi ya cuci rayuwarta shine yasamu cikin wannan zullumi da taraddadi,
Shine ya jefe rayuwarmu cikin tunanin zai yiwu ko bazai yiwuba. Amma babu komai Allah yana ganinsa kuma zaiyi mana sakayya,
Nisawa baba yayi sannan yace wannan haka yake, koma wayeneshi bai kyautatawa rayuwarmuba bai duba irin halinda muke cikiba ya qara jefamu cikin wani halin amma babu komai da sanin Allah."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial71 Chapters
The One Luna
Luna and his best friend Boni only wanted to play an upcoming MMORPG.But what happens when a System is introduced to Earth. Zombies spawn out of nowhere, beasts start to mutate, new races from a failed world appear out of nowhere.A new world where those who adapt the fastest will be rewarded. FIGHT. STRUGGLE. EVOLVE! Before you can even try to find out why these strange events have happened, you have to be strong enough to even survive in the first place and figure out what rules govern this new world!
8 208 - In Serial13 Chapters
Celestial Void
After a year of being unable to play the newest virtual reality space game, Cam is finally able to log in. He is behind everyone else, but his friend, Will invites him along on a mission for his guild to help him get started. Soon he will push his limits of how fast he can progress to help his friends. He will have to to navigate his way through the enormous, open universe filled with all sorts of space ships, combat, politics and crafting. The universe called Celestial Void.
8 102 - In Serial80 Chapters
The Human Conduit
On a mission to try and uncover clues about the mysterious fire on a space frigate, Milo Greene will discover his connection to one of the universe's deepest secrets and find himself caught in a tug-of-war that goes beyond nation versus nation or solar system versus solar system. Science fiction with some fictional science. No Lit-RPG elements. Some war, politics, sexuality, unapologetic supernatural elements, mystery, adventure, and weirdness.
8 108 - In Serial8 Chapters
Code Scarlet
Activate Code Scarlet! After crashing on a zombie-infested world, raised by the forgotten machines of the past; Flow spends her days scavenging the ruins of the colony in order to construct the ship that would take her far away from the rotting ruins. After an encounter with an unknown and hostile alien race known as fiends, Flow stumbles into a strange vault buried below the colony. Then, accidentally, she awakens an ancient android with no knowledge of herself, fueled only by the desire to destroy the fiends. So begins the intergalactic journey to find the Aigis and continue the androids mission, to complete Code Scarlet. ------------ A tail inspired by sci-fi fantasy settings like Star Wars and Destiny, with elements of Xenosaga and Mecha anime. It's a genre I'm definitely new in compared to my other works but am looking forward to exploring what this world would have to offer. Updates will be slow and inconsistent.
8 76 - In Serial18 Chapters
Machine Gun Kelly - General Admission Lyrics
lyrics to every song on General Admission, enjoy
8 238 - In Serial12 Chapters
Number Of Virtues
In the universe of Aether Rivers, since more than one hundred thousand years, gates of transcendence are closed. From one hundred thousand years plans are made, since all who remember, fear the return of the “one that brings change.” From that long, one's far dead hope for finding a way to avoid the worst scenario. Taihon is one of three greatest worlds in this dimension. Here young man called Mark with a soul that just taken form will be reincarnated. This is place and era where plans and struggle of one hundred generations will be brought to a closure. The Sword wants vengeance, Pathfinder a way to survive, Clock that was once called “sage” wants to know if he made the correct decision. Four want to find hope. Three want more time. Two want to fulfill they fate. One wants to die.Born in this new world with his soul that taken the form of a Chain Mark will begin adventure of gigantic proportions...
8 134

