《ƘADDARAR RAYUWA》Q Page 17
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 17
Duk wani laka dayake jikin sawwama yadauke tarasa mai yakeyi mata dad'i,
Eh tabbas sai yanzu tagane mai yake d'awainiya da ita sonsa takeyi,
Idan kuma tace bata sonsa wannan qaryane ta fahimci hakan yanzu komai yake dawo mata filla-filla,
Lallai zuciyarta ta yaudareta dason abunda yafi qarfinta, Anya kuwa zata yaudari kanta dafara soyayya da wannan mutumin?
Ko daga yanayinsa kasan baidace da mace kamartaba,
Mai zaisa yazo matada wannan zancen?
Anya kuwa ba yaudararta zaiyiba?
Kaima koma ba yaudararki zaiyiba kisani cewa koda son gaske yake miki aranarda yasan abunda yafaru dake abaya, daga ranar bazaki sake sanyashi a idanuwankiba, zuciyarta take sanarda ita,
Kuka ta sanya mai karfi tashiga yinsa babu qakkautawa lallai zuciya ta zalinceta data fada irin wanna soyayyar mai zafin gaske,
Sawwama tadad'e awaje har saida halima tafito kfinnan tayi saurin shashshare hawayen fuskarta tafara tattara kayan, deban wasu kayan halima ta tayatayi itama sawwama ta debi wasu, suka shiga ciki da kayan,
sadam nasa wajan kwanan zullumi yayi saboda baisan wani irin kallo sawwama zata yiwa maganarsaba,
Ko washe garida sukaje school najeeb ya tambayeshi yaya sukayi yafada masa yanda sukayi,
Dafa kafad'arsa najeeb yayi yace kada ka damu mutumina nasan bazata qi kar6an soyayarkaba,
Nasani inada yaqini akan hakan abokina baida makusa dahar mace zata ganshi takushe, babu wacce zata ganka bata mato makaba,
Kayya najeeb walhy halin yarinyar nan daban yake ina tsoron amsarda zata biyo baya ni nasan halinta abune mai mugun sauki taqi amsar soyayyata,
Zaro ido 😳 najeeb yayi yace dakuwa ta tafka babban kuskure zata yiwa rayuwarta asararda bazata ta6a maida gurbiba,
Hmm kawai sadam yace bai qara tankawaba,
Najeeb ya ringa kwanatar masada hankali saboda yaga yanda abokinnasa yashiga d'imuwa,
A kullum najeeb baida aiki idan sun zauna sai bawa sadam baki yana qara karfafa masa guiwa."
Sawwama fadin irin damuwarda tashiga ma bata lokacine ba qannenta ba hatta iyayenta sanda suka fahimci hakan kowa tambayarta yakeyi dalilin damuwarta amma amsarta guda d'ayane shine babu komai,
Mama tadamu sosai haka ta sanyata agaba tana tambayarta shiru sawwama tayi hakan ya nunawa mama cewa akwai matsala kenan,
Data takura mata saita sanya kuka hakan yasa kawai tarabu da ita amma zataci gabada binciken abunda yake damunta,
Sawwama cikin ranta tasan tanason sadam amma kuwa bazata yaudari kantaba saboda tasan rabuwa zaiyi da ita,
Advertisement
Bazataso sawa kanta son samun abunda yafi karfintaba, dan haka ita tagama yanke shawarada zata bashi yanzu jiran zuwansa kawai takeyi."
————————-
Shikuwa sadam anasa wajan haka ya daure yadauki kwana uku curr batareda ya qara zuwa wajantaba acewarsa yabata lokaci tayi tuanani ta yanke shawara,
Ranarda kwana uku tacika sadam haka yatashi da faduwar gaba da wani irin zullumi saboda rashin sanin amsar da zata fito a bakinta,
Najeeb ya fahimci hakan shi abunma dariya yabashi wai sadam ne haka yake son wata kuma har yadauki abun da muhimmanci haka?
Bazaice sadam bai ta6a soyayyaba saboda koda suna secondary school ma yayi amma shi sam bai d'auketa da muhimmanci ba,
Shidai kawai a sunan yanayine, tunda daga bayama yan matan gajiya sukeyi da halin ko inkula da yake nuna musu su samawa kansu mafita, amma wai yau sadam ne yake cikin soyayya mai zafi irin wannan."
Idan najeeb yaga yazauna yayi shiru sai yayita jansa da tad'i haka dan yanaso ya d'an mantar dashi damuwarsa koda kadanne ma."
Sadam suna gama lactures kai tsaye wajan sawwama yawuce saboda bazai iya wucewa gida batareda yaji amsa daga wajantaba,
Kai tsaye yawuce wajanta da sallama ya isa yazauna gefe yanda yake zaunawa,
Amsawa tayi jiki duk asanyaye tajuyo ta fuskanceshi,
Nisawa yayi sannan yace sawwama nazo jin amsata kamar yanda mukayi dake kwana uku yau kwana uku yacika,
D'ago kai sawwama tayi ta kalleshi nan da nan gabanda yahau faduwa tabbas idan tace batason wannan bawan Allah tayi qarya, qaryarma mai munin gaske,
Amma yaya zatayi? Ki aminta dashi zuciyarta tafara amsa mata, saboda idan baki aminta dashiba bazaki samu kamarsa,
Idan kikaqi amsar soyayayrsa zaki qare cikin danasami da nadamar yin hakan,
Girgiza kai tafarayi batason yarda da maganar zuciyarta bataso zuciyarta ta yaudareta,
Cikin sanyin jiki tafara magana,
Ban amince da soyayyarkaba saboda koda yatsun hannunmau ba daya bane kamar yanda muke ni da kai, akwwai tazara mai nisan gaske tsakanina da kai, kamar yanda hausawa suke cewa kwarya tabi kwarya idan tabi akushi fashewa zatayi,
Bazan bari zuciya ta yaudareniba, koba haka bama hasali akwai dalilin dazaisa bazan yarda da soyayarka ba,
Wanda daga baya zata iya kasancewa lokacinda kasani kaji bazaka iya ci gaba da soyayyarba,
Wanda hakan ni zaifi cuta anan gaba,
Dan Allah kayi hakuri Allah yahada kowa da rabonsa, nagode da nuna qaunarka agareni bazan ta6a mantawa dakaiba,
Advertisement
Da ido kawai sadam ya tsareta maimakon ya nuna 6acin ransa kawai sai yayi murmushi yace ai lokacin da zan tafi na barki sanda nace miki kafin ki yanke shawara kifara saurarar zuciyarki tukunna,
Sawwama har yanzu baki kawomin dalili guda d'aya dazanji inason rabuwa dakeba,
Dalilanki bamasu qarfi bane da suka isa su raba soyayyarmu ba,
Ko magana daya da kika fada babu wacce kika fadeta daga qasan zuciyanki,
Idan yanzu kika yanke alaqarmu yaya zakiyi da dumbin soyaayyata da take cikin zuciyarki?
Da sauri sawwama ta dago tana kallonsa daga mata kai yayi alamun cewa abunda taji shi yake nufi, mayarda kanta qasa tayi gabanta yana tsananta faduwa,
Da cewa kika bakyasona kokuma banga soyayyata ko kwaya a kwayar idonkiba zan iya rabuwa dake, amma bawai wad'annan magana marassa tusheba,
Jikin sawwama yamutu luqui kamar wanda akayi mata shegen duka, tayaya har ya gane tana sonsa?
Tayaya yagane zuciyarta akoda yaushe bata shawara takeyi akan ta amshi soayyarsa?
Tsorone ya kamata kodai aljanine? Toh idanba aljaninba waye zaisan duk wadannan abubuwanda yake kunshe cikin ran mutum?
Tsorone ya kamata takasa motsa koda da yatsar tane,
Miqewa yayi yace bazan gajida baki lokaciba har sai lokacinda kika saurari abunda zuciyarki take gaya miki,
Gobe zan dawo inji abunda kika yanke nabarki lafiya,
Tana kallonsa harya tafi tana kallon tafiyarsa kawai tafashe da kuka,
Ahaka halima tafito ta sameta tanata riskar uban kuka,
Akid'ime halima ta tsugunna tana tambayarta dalilin kukan amma taqi bata amsa daga bayama saita share hawayen tace mata babu komai,
Komawa gida halima tayi ta shaidawa mahaifiyarsu ayanda tasamu sawwama,
Kikoma ki tayata ku tattaro kayan kuzo zanyi magana da ita,
Komawa halima tayi ta tayata suka tattare kayan suka nufo gida, sawwama bata nunawa mahaifiyarta komaiba itama mama batace mata komaiba sanda tabari tayi sallah har sun zauna zamnan cin abinci alokacin babansu yadawo,
Bayan sun gama har sunyi isha'i mama tadubi baba tace masa ga sawwama nan katambayeta ko zata fada maka abunda yake damunta,
Kullum cikin damuwa take nayi rarrashin duniya tafadmin abunda yake damunta taqi yanzu haka qanwarta tafita ta sameta tana kuka kafin tashigo gida ta share hawayenta tanuna cewa babu wani abunda yake damunta,
Gara tun wuri ka titsiyeta tafada maka sai ayiwa tufkar hanci,
Sawwama tanajin abunda mamansu tafad'i sai jikinta yayi sanyi ta sunkuida kanta qasa tasan dole yanzu tafada musu gaskiya sannan kuma batasan yanda zasu dauki zancenba,
Mamana baba ya kira sunanta dagowa sawwama tayi ta dubeshi hadeda amsawa tace na'am, dawo nan ki zauna ya nuna mata kusa dashi,
Cikin nutsuwa ta miqe ta isa kusa dashi yanda ya nuna mata ta zauna,
Mamana yaqara kiran sunanta,
Wannan karon bata amsaba saima qara sunkuida kanta da tayi,
Inaso kidubi girman Allah mamana ki fadamin mai yake damunki, banason kimun qarya duk da nasan ba halinki bane, tsantsar gaskiya nake buqata,
Mai yake damunki?
Menene dalilin damuwarki da kukanki?
Idan ba kinaso muma mu shiga tashin hankali bane ki fada mana musan yanda zamu 6ullowa wannan al'amarin,
Jijjiga kai sawwama tayi hawaye yafara kwaranya a idonta cikin sanyin jiki tafara yimusu bayanin abunda yake faruwa,
Nisawa baba yayi bayan yagama jin bayanin sawwama yace mamana toke yanzu kina sonsa ne?
Shiru sawwama tayi takasa bashi amsa,
Mamane ta mai-mai ta tana fadin bakiji tambayarda babanki yayi miki bane?"
A'a kibita a hankali baba yadakatarda mama,
Ai basai tafad'a ba wannan shirunda tayi ya nunamin alamun cewa tana sonsa,
D'agowa sawwama tayi tace" baba tsoro nakeji,
Tsoron me kuma sawwama? Baba ya tambaya,
Sunkuida kanta tayi takasa cewa komai baba ya fahimci abunda take nufi hakan yasa cikin lallashi yace"
ai ba duka aka taru aka zama d'ayaba mamana,
Bakowane yakeda mugun nufi akan mutaneba,
Akoda yaushe muringa kyautatawa mutane zato,
Mama ne tace hakane baban sawwama amma kuma ni abunda nakeji shine kada abarshi yafara zuwa daga baya kuma idan an fada masa abunda ya faru da ita yazo yaji bazai iyaci gaba da nemantaba, azo abar yarinya cikin damuwa,
Sawwama najin haka gabanta ya yanke yafad'i itama abunda yake bata tsoro kennan bakowani mutum bane zai iya zama da macenda wannan qaddarar ta afka mata ba,
Kowani namiji bane zai iya daukar wannan qaddarar akan macenda yakesoba,
Halima ne tadubi mama tace mama menene yafaru da sawwaman?
Babu mama tabata amsa a takaice,
Nisawa baba yayi yace sai an gwada ake gane na kwarai ummi,
Mamana gobe idan har yazo ki shaida masa inason magana dashi,
Tun kafin abu yayi nisa sai asan matsaya,
Anan suka tsaya dazance akan idan yazo gobe baba
zai sameshi."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial9 Chapters
Beyond the Veil
When Lynn's best friend gets abducted, she doesn't think twice about following after her. She enters a world with vampires, fey, angels, and every other creature to ever inspire mankind's most fantastical stories. During her search, she discovers the world is being threatened by a sorceress hell bent on getting her revenge. Will Lynn be able to stop The Queen Beyond the Veil from destroying the world? Mobile version can be found on https://www.wattpad.com/story/251183008-beyond-the-veil
8 122 - In Serial20 Chapters
DRAGON HUNTERS
Many centuries ago in a world of Magic, there existed a group of figures known as the 9 Dragons, who led a large cult called the Dragon-Tails, whose only purpose was to cause chaos all throughout the land, stopping at nothing just to have their own way. But, there rose up a large resistance force led by Two Warriors, and with their might, they subdued the Dragons, and brought about an era of peace once more. Years later however, the Dragons had slowly risen up once again with their devious schemes, and standing against them were the descendants of the Warriors, known as Hunters. Tune in as the Hunters pour out every ounce of their power to suppress the Dragons before they can achieve their ultimate goal: to revive the 9 Elders.
8 155 - In Serial75 Chapters
Water and Ice | Shoto Todoroki
⌜ Y/n is finally on her way to the school she's wanted to attend since she was a child. Surrounded by powerful classmates at UA, she's immediately thrown into the whirlwind of making friends, enemies, and training to become a hero. However, it's a little hard to focus when a red and white haired boy is constantly occupying your thoughts. 」__________➳ credit for bnha world components to kohei horikoshi➳ credit to original artists for pics at the top of chapters➳ loosely based on bnha timeline➳ some events and almost all interactions are stuff i come up with➳ slow burn even tho it looks rly fast at first lol__________➳ all rights reserved➳ not mature➳ rly cringe➳ completed➳ unedited
8 59 - In Serial34 Chapters
Goblin Cave
[Goblin Cave] is a perfectly average Dungeon that becomes unsatisfied with its work.
8 71 - In Serial90 Chapters
February of 1996
Irena Becksky decided to attend a Valentine's Day party that was taking place in the Gryffindor common room. She didn't expect the outcome that February of 1996 would bring into her life. Fred Weasley X Female OCRankings: #1 Fred 11/11/21#1 George Weasley 12/05/21#1 Fred fanfiction 12/13/21#1 Weasley Twins 7/05/22#2 Pregnant 01/31/22#3 Fanfiction 02/10/22#3 Weasley 07/30/21#4 Fred Weasley 07/30/21
8 87 - In Serial22 Chapters
Curse of Muzan
Family burned at the stake, Izuku Midoriya runs away from the sight of the assailants he had lived with to find somewhere to hide. His crime in their eyes, his half demon blood lineage with his family paying the punishment of hiding him. Now trained in the art of the Demon Slayer Corps, Izuku fights the endless hoards of demons to one day face off against the man responsible for so much misery in the world. His father, Muzan Kibutsuji.MHA is rightfully owned by Kohei Horikoshi and Demon Slayer is owned by Kyoharu Gotouge. All art is rightfully owned by their respected owners. Please support the official release.
8 51

