《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 16
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on wa
Page 16
Jijjiga kai najeeb yayi yace ko kaso ko kaqi sadam soyayyace ke d'awainiya dakai,
Soyayyarma mai zafi kuma mai wuyar sha'ani,
Cikin rashin yarda da maganganun najeeb ya miqe yace" sai gobe zan wuce,
Najeeb ne yaci gabada magana yana fadin duk rashin son gaskiyarka sadam sai dai kaqi yarda da gangan amma bawai dan bakasan gaskiyaba yarinyarnan sonta kakeyi,
Nafad'a maka na nanata sonta kakeyi,
Kai kanka idan kazauna zakayi tunani,
Nidai kasan bazanki fada maka gaskiya dan son rankaba
Kuma bazan fada maka karya dan son rainaba,
Sadam bai kula maganar najeeb ba saboda zuciyarsa bazata iya daukaba yakasa gaskanta abunda kunnuwansa suke fada masa. da sauri-sauri yafice har yana shirin gudu ya fice,
Yana fita dai-dai mashin d'insa ya tsaya yana maida numfashi kamar wanda aka biyoshi yasha dakyar,
Yadade ajikin mashin dinsa kwalkwalwarsa bata iya tunano masa komai,
Dakyar yaja mashin dinsa ya koma gida, bai buqaci ganin kowa ba daya koma shi kad'ai ya zauna a d'aki yanata zullumi,
So? Shi kuma?
Inna lillahi wani irin so kenan?
Kai ina ba sonta yakeyiba tausayinta kawai yakeji,
Tayaya za'a ace shine yafad'a a soyayya, soyayyarma na mai saida awara,
Inna lillahi, kawai yaketa nanatawa,
Yarasa yanda zaiyi hankalinsa duk yafice ajikinsa,
To shi yaya akayi yakasa gane cewa sonta yakeyi sai najeeb ne yagano?
Ya tabbata da ace da gasken sonta yakeyi da shi zai fara ganewa ba najeeb ba,
Aranar yacewa sawwama zai koma amma irin halinda yake ciki bai sanya yakomaba,
Da wani ido kenna zai kalleta?
Shin itama ta fahimci yana sonta kenan? Tunda har najeeb ya fahimta,
Aranar sawwama ta zuba ido taganshi amma shiru cikin ranta take tunanin koba lafiyaba, kokuma zancenda jiya tafad'a masa wani ya 6ata masa raine,
Ita kadai tayita tariyo zancenda sukayi dashi jiya, kuma amma ai harya tafi babu alamun 6acin rai a tattare dashi,
Haka taita saka da warwara tarasa gane dalilin daya hanashi zuwa,
Shikuwa sadam anasa wajan ya saka ya warwara ya rasa gane inda maganar najeeb ta dosa nikuwa araina nace ai sadam ka dade da gane yanda maganar najeeb ta dosa sai dai kawai kanata yaudarar kankane."
Cikin dare kuwa najeeb bawani baccin kirki yayiba wasu irin sururun mafarkai daya ringa yi marassa kai, gashi yafarka a bacci yakai sau bakwai kuma duka da tunaninta yake farkawa,
Advertisement
Wasu mafarkinma idan ance masa yafadesu bazai iyaba,
Gabaki daya sadam yabi ya rikice,
Haka suna breakfast ya manta yakira kanwarsa da sunan sawwama,
Taimakonsa d'aya mummy bata wajen ya tabbata dasai yasha tambayoyi,
D'aki yakoma yana fadin wasa gaske maganar najeeb tanason dawowa gaskiya,
Wata zuciyarce tayi saurin gargad'araa dacewa tayaya za'ayi wannan zancen yadawo gaskiya?
Huuuuuuu ya furzarda iska abakinsa,
Agaugauce ya yi wanka ya shirya zuwa school,
Yasamu mummy tarigashi fita dan haka shima yafice."
Ya isa school ya sanya najeeb agaba ya titsiyeshi akan cewa saiya fada masa dalilin dayasa yace son yariyarnan yakeyi gashi tun jiya ya hanashi sukuni,
Dariya najeeb yayi yace" malam badai ni na hanaka sukuniba, yarinya dai ta hanaka sukuni zakazo ka sauke akaina,
Zama sadam yayi cikin rashin sanin abunyi yace" najeeb toh yaya zanyi?
Yanzu ka yarda kana sonta kennan?
Gyada kai sadam yayi yace har indai abunda nakeji shine so nayarda ina sonta, son ma mai tsananin zafi,
Jijjiga kai najeeb yayi na gamsuwa da maganar abokinnasa,
Tasan kana sonta? Najeeb ya jeho masa tambaya,
Girgiza kai sadam yayi yace A'a najeeb nima kaina ban saniba ita tayaya za'ayi tasani?
Murmushi najeeb yayi yace sadam kenan bakasan mataba sau dayawa kafin mu kanmu mu fahimci muna sonsu sun rigamu fahimtar muna sonsu,
Kawai dai bazasu gwada maka sun saniba sannan bazasu furta makaba zasu jirane har lokacinda zaka gane kokuma ka gajida riqewa ka furta,
Yanzu dai ba wannan ba koma tasani ai baka furta mataba dan haka bazata nuna maka tasaniba, mubarshi a bata saniba d'in,
Wani abu nakeji sadam, najeeb yafad'i cikin taraddadi, wani abune sadam ya tambaya cikin faduwar gaba,
Mummy nakeji sadam, baka ganin idan tasani za'a samu matsala? Ni inaga kayi gaggawa sadam saboda duk yanda kake sonta yanzu mummy bazata bariba har sai ka gama school,
Shiru sadam yayi sai can yace" akwai matsala mana sosaima sadam amma ai sai dai yarinyar qaramace kwata-kwata yanzune take 15yrs shekaru sha biyar, sannan najeeb aiba ni nayiwa kaina gaggawaba, bansan lokacinda nafara sontaba, idan nace maka ga dalilin kuma daya jani y sanya nafara sonta ban saniba, sone yayimun gaggawa banine nayi gaggawa, akwai wani boyeyyen al'amari da ubangiji ya 6oye tattare da wannan abun,
Numfashi najeeb ya sauke sannan yace dasauki tunda qaramace idan yaso idan kagama karatunka lokacin saika tun kari mummy da maganarta,
Advertisement
Kai kawai sadam ya gyada amma yasan ba matsalarba kenan,
Sai ankai ruwa rana da mummy kafinnan ta yarda tabarshi ya auri sawwama saboda rashin karatu ga kuma talauchi,
Bayajin talaucima kamar rashin karatu, mummy taqi jinin rashin karatu,
Shi har indai akan sawwama ne zai dage harsai mummy ta amince da auransa, zai zama jajirtacce akan soyayyarta komai zai taso zai jure ya jajirce wajan ganin ya nemawa kansa mfita,
Tunda harya fahimci ga abinda yakeso to lallai zai jajircewa abunda yakeso wajan ganin ya sameshi,
Mummy rashin karatu ne bataso yayi alqawari zai sanyata tayi karatu bayan aurensu,
Zatayi karatu har sai itada kanta taji tagaji zata bari,
Zai zamarda ita irin macenda mummy take burin ganin y'ay'anta sun zama,
Zai zamarda ita surukarda mummy zatayi alfahari da samunta,
Najeeb ne ya katse masa tunaninsa yana fad'in me kake tunani haka?
Bbu sadam yabashi amsa,
Yanzu yya kake gani? Nasanar da ita kokuma nabari lokaci yaja? Lokacin tadan qara shekaru? Sadam ya tambayi najeeb,
Girgiza masa kai najeeb yayi yace" karka fara wannan saken sadam, gara tun wuri idanma tashin zatayi tatashi da soyayyarka,
Kada ya kasance alokacinda take girma kai katsaye kana gadinta ta girma, katsaya kallon ruwa shima kwado yazo yayi maka qafa,
Subhanallah me kake fada najeeb?
Gaskiya! Najeeb yabashi amsa,
Kada ka tsaya wani jinkiri duk wanna jinkirin bashida amfani sadam nida tawa shawarar kenan,
Jijjiga kai sadam yayi na gamsuwa da maganar abokinnasa yace shikenan najeeb nagode,
Daga kafadarsa najeeb yayi sannan yace babu komai,
Abu daya nakeso kasani sadam tunda har kasa aranka tsakani da Allah kake sonta kuma aurenta kakeyi dole ka jajirce sadam kazama mai hakuri shi neman aure baya zuwa cikin sauqi,
Shi neman aure daka ganshi dole yana zuwa da qalu bale kala-kala,
Gyada kai sadam yayi sannan yace in sha Allah najeeb,
Duk wannan zancenda akeyi har yanzu bansan wacece ita bafa, aina takene matar abokinnawa? Najeeb yafada cikin zolaya,
Murmushi sadam yayi yace kada ka damu zaka santa,
Kabari abun yayi karfI har wajanta zan kaika,
Toh Allah yabada sa'a najeeb yace sadam ya amsa da amin."
Ranar ya yanke shawara gaya mata dan haka duk da cewa yagama lactures da wuri saiya jira yayi magrib a school sannan yadauki hanyar wajanta,
Cikin zuciyarsa sai zullumi yakeyi saboda baisan yaya zata dauki zancenba amma yana addu'a tayiwa zancen kyakkyawan tunani, ta dubeshi da kyakkyawar manufa,
Sa'i-sa'i yakan saki dan siririn tsaki taraddadin yanda zata dauki zancen kawai yakeyi,
Ya isa wajan ya dade atsaye yana kallonta bai qarasaba, har hankalinta yakai kansa,
Ganinsa atsaye can nesa yasanta sakin ajiyar zuciya,
Yadauki lokacin kafin yaqaraso,
Da sallama ya isa yazauna dan nesa da ita, amsa sallamar tayi hadeda gaisheshi,
Amsawa yayi yadubeta yace sawwama kingama abunda kikeyine?
Girgiza kai tayi tace bangamaba saura wannan na kan wutan kawai,
Nisawa yyi yace gama ina jiranki,
Bata musa masaba sanda ta tsame ta sauke man saita juya ta dubeshi,
Tace nagama,
Yawwa magnarda zamuyi dake tanada muhimmanci sawwama sannan inaso kiyi mata kyakkyawar fahimta, nikaina bansan mai yake damuna ba bansan kuma yaya akayi haka tafaru ba,
D'agowa sawwama tayi ta dubeshi taqagu yafad'a mata wace maganace wannan,
Muryarsa taji yaci gabada fadin babu niyyar cutarwa kokadan a cikin zuciyata, akullum inaso ki sanya aranki duk wanda ya cuci wani Allah bazai barshi ba,
Idan na cuceki nan duniya ko lahira na tabbata sai Allah yayi miki sakayya, a kullum anaso ka kyautatawa mutumin kake tare dashi zato,
Shiru yayi na wasu lokaci,
Can ta tsinkayi muryarsa yana fadin sawwama tun lokacin baya abu yana faruwa ban kumasan mai yake faruwaba banmasan dalilin faruwar hakanba,
Yanda nake jinki acikin raina yawuce akira hakan amatsayin sabo,
Sawwama sonki nakeyi! Arazane sawwama ta d'ago ta dubeshi nan take gabanta yahau faduwa amma me tsantsar gaskiya tagane akwance akan fuskarsa,
Maganarda yakeyi daga qasan zuciyarsa take fitowa babu algus acikinta,
Qasa tayi da kanta gabanta yana cigaba da faduwa, ni banson yaushe nafaraba sawwama banyi niyyar gaya mikiba saboda rashin sanin yanda zaki dauki maganar,
Sannan kuma maganar gaskiya sawwama son tsakani da Allah nake yi miki kuma aurenki zanyi, nafadi abunda yake raina nasa dole zakiso yin tunani akan maganata zan iya baki daga yanzu zuwa nanda kwana d'aya zuwa uku kiyi tunani idanma da shawara duka kiyi, kafin ki yanke hukunci,
Zanso ki sauraro zuciyarki alokacinda zaki yanke hukunci, abunda tafad'a miki kiyi amfani dashi saboda shine za6inta,
Miqewa yayi bai jira cewartaba yace nabarki lafiya kiyi tunani mai kyau,
Allah ya shige mana gaba."
Yana fadin haka bai qara juyowaba yasai kai yawuce, yabar sawwama azaune awajan matsayin mutum-mutumi."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial28 Chapters
The Nexus Point Chronicles
My name's Samson, and I'm a Soldier For The Terran Coalition. Before War became my future, before it became all of our futures, earth was a peaceful place... Well not really but we did our best with what we were given. And then the elven Gods of another universe decided they wanted to play a game, they wanted power, they wanted the Nexus point of all creation.... they wanted EARTH. And so they brought death, They brought pain, and suffering and loss unlike any other as humanity died in the millions. But they brought magic and the system and the catalyst for the Gods of earth to reawaken, fight and defend that which is theirs. Now we're playing their game, fighting the war that they started, staining our hands with the blood of the innocents and the Guilty alike. But make no mistake, in this war of cosmic stakes, we will be the victors! We will be the one that seats on the throne of multi-univeresal supremacy. Because we have miracles, guts and the all too annoying trait of not staying the fuck down! and there are none in all of the universes more vindictive, more destructive than humans. This is our story, this is our tale! this is our saga! Our futures, for our children! Remember it! This novel is also hosted on scribblehub. Please support me on my Patreon. Updates are sporadic but at least three times a week, so please show your support. Thanks 😊 The cover does not belong to me and was taken off the internet 😅. Discord server below https://discord.gg/tWSG5XN Participant in the Royal Road Writhaton Challenge
8 286 - In Serial15 Chapters
My Hero Academia: Hero's Horizon
A young man after being killed gets a second chance at life and not only that but in a world he loves and knows will help prove to himself that he deserves this second chance. Follow him through UA High as he makes friends, allies and enemies alike. (Also posted on Fanfiction.net, Archive of our own, Wattpad.com and quotev.com)
8 179 - In Serial22 Chapters
Mother of Monsters
Rage, humiliation, disgrace, and a darkness that pulls at her insides. Abandoned by the other Gods and forced into eternal imprisonment. Evdokia, Mother of Monsters, Mistress of the Dark, and Lady of Shadows who has been trapped for thousands of years, finally escapes. To avoid drawing the other Gods' attention, she descends to Hellas disguised as a mortal girl. There she finds that the world has changed. The heroes that once fought to protect and save, now slay her children in an attempt to gain recognition and fame. The Gods hold on the hearts of the people has weakened and now Evdokia has a chance, a chance at revenge, or a chance at happiness, it´s up to her. Authors Note: This is my first attempt at writing. Please read and tell me how you like it. I would love feedback, good or bad. I love the Forgotten Conqueror series and I'm begging Za1d3 to continue writing. If he chose to do so, it would make me and many other people very happy. :) UPDATE: Wow! I can't believe it's been 3 years since I wrote this. I have grown a lot as a writer, and I think this story has potential, so I will edit and continue it. Thank you for all your love and support
8 198 - In Serial30 Chapters
How do I break My Limits?
Starting a new high school I tried to lay low, I tried to stay out of trouble. Thats when I met him,The Old man, why is he so mysterious. Who knows? but why is he a pain in the ass? He smokes,he drinks to much and goes on about how he once ruled the world, something about him is off? I get a feeling that under this Old mans persona lies a ferocious Tiger... Please help me...
8 83 - In Serial39 Chapters
La Loi du Mystère [French]
L'équipage de l'Imbattable est loin de se douter que le naufragé repêché en pleine tempête est l'un des derniers utilisateurs de la magie, un art interdit par le Mysterium et ses inquisiteurs. Mais quand il revient à lui, le naufragé a perdu la mémoire. Qui est-il et comment s'est-il retrouvé là? C'est ce qu'il va devoir découvrir par lui-même.
8 186 - In Serial22 Chapters
McShot's Crazy House: Many Stories in One Setting, It's an Anthology!
*This is my first time attempting to author on Royal Road and as such I cannot find a true series to write. Due to this, I will occasionally produce one shots or add on to existing one shots on this page. As such, do not believe too much of what I marked in the genre boxes. I will try and update as much as once a week but I procrastinate things like crazy so start out by hoping for by-weekly updates first.Welcome to McShot's Crazy House! I am Mr. McShot, the lord of this incredible house you are now residing in. In each door resides a different world with a different story. Of course, looking inside for too long may hurt your eyes so I will limit the amount of exposure. Plus there is food and magic aplenty. May there be something to your liking.
8 192

