《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 15
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 15
A hankali ta d'auke idanuwanta daga kansa gabanta yana tsananta faduwa, yayinda taji qirjinta yayi mata nauyi,
Shikam sadam bai dauke idanuwansa daga kantaba bai kuma qarasa wajanba,
Ahaka najeeb yaqaraso ya siya abunda zai siya jikinta duk yabi yayi sanyi tazuba ta miqa masa,
Kudin ya miqa mata ta girgiza kai alamun bazata kar6a6a
Da mamaki najeeb ya kalleta yana fad'in kudinkefa nake miqa miki zatonsa ko bata gane mai yake nufi ba, qara girgiza kanta tayi cikin sanyin murya tace eh nasani kabarshi kawai,
Babu yanda najeeb baiyi ta kar6aba amma fir taqi haka yataho yana mamakinta,
Yaqarasa wajan machine din yana fadawa sadam,
Sai alokacin sadam ya kauda idanuwansa daga gareta yadubi najeeb ya ta6e baki baice komaiba yahau kan machine d'insa,
Bin bayansa najeeb yayi shima yahau bai qara juyawa wajantaba ya tada mashin dinsa suka bar wajan,
Wasu hawaye masu d'umine suka zubo daga idanuwan sawwama,
Hannu ta sanya ta share hawayen fuskarta taci gabada aikinta,
Ko babu komai tadanji sanyi cikin ranta saboda ta tabbata yafara saukowane har yazo wajan dukda cewa bai qarasoba,
Koma dai yayane yau abunda takeji yadan ragu,
Share hawayen taqarayi daya qara zubowa,
Ita kad'ai tana aiki tasamu kanta da sakin murmushi,
Shikuwa sadam nasa wajan fess yakejin ransa sanyata a idanuwan dayayi kad'ai ta d'ebe masa kewarta dake addabarsa, barinma tsakanin jiya dayau, sosai ya kalli kewarsa akwance akan fuskarta,
Kamar yanda suka zo yana tuqi ahankali haka suka taho ahankali zuciyarsa gabaki daya tana cikeda annashuwa,
Sa'i-sa'i yake sakin murmushi,
Ta6oshi najeeb yayi yana fad'in lafiya kuwa?
Sadam baice masa komaiba saima qara maida masa murmushin yayi,
Ganin haka yasa najeeb yin shiru har suka isa babu wanda ya tankawa wani,
Ana shirin yin magrib sadam yakoma gida, agida yayi sallah,
Yana zaune hotonta ne kawai yake fado masa arai saiya lumshe ido yayi murmushi,
Duk da bawani magana ne ya hadasuba amma yau kam sadam yayi kwanan farin ciki,
Zafinda yakeji cikin ransa duk babu."
Itama sawwama nata wajan abubuwan da sauki yau kam,
Ko babu komai ta sanyashi a ido tasan yana cikin qoshin lafiya,
Sannan alamu yanuna yafara sauka,
Akowani irin lokaci zai iya saukowa gabaki d'aya."
Kafin weekend ya qare kullum sai sunzo amma shi daga gefe yake tsayawa sai najeeba ya qarasa,
Idan ya harde hannu akirji sai yahau aikin kallonta har sai najeeb yasiyo yadawo sannan sutafi, kuma har lokacin taqi kar6an kudinsu, ganin haka yasa najeeb idan bata kar6aba Sai kawai ya ajiye mata yatafi."
Advertisement
Ranar monday tareda najeeb suka koma school,
A school sadam yayi magrib,
Yakamo hanya, yau kam sadam da niyyarsa tazuwa wajanta koda sallama ce tashiga tsakaninsu,
Wajanta ya nufa lokacin yasameta tana tattare kayanta tagama sana'arta yaqare dawuri,
Nesa da ita ya ajiye mashin dinsa ya tattaki ya qaraso wajanda take,
Sallama yayi da sauri ta juyo jin muryarsa,
Bakinta yana rawa ta amsa sallamarda yayi mata, adan daburce ta daura da fadin ina wuni?
Lafiya ya amsa yabude baki zaiyi magana kafin ya qarasa yaji siririyar muryarta ta daki dodon kunnuwansa da fadin ya qare, ita azatonta awarar yazo siya,
Toh kawai ya amsa atakaice baibar wajanda yakeba bai kuma juyawaba yana tsaye,
Itama shiru tayi takasa aikata komai."
Tsugunnawa yayi a gabanta nan gabanta yahau dukan uku-uku
Cikin sanyin murya yace" nayi miki tambaya na nemi alfarma wajanki amma ban samu koda guda d'aya cikin abunda na buqataba,
Dafarko na dauki fushi sosai akan abunda yafaru, daga baya nazo nayi realinzing kowani mutum da irin yadda yake tafiyarda rayuwarsa,
Kowani dan adam akwai abubuwan acikin rayuwarsa,
Duk wanda kaga ya aikata wani abun na tabbata akwai dalilin aikatawa,
Bazan tilastakiba bazan takuraki akan saikin fadamin dalilinki ba,
Amma inaso kisani wallhy banida niyyar cutar dake, banida mugun nufi akanki,
Wanima bazan iya cutarwaba balle ke da haka kawai nake ganin kimarki da girmanki a idona,
Nasan akwai abubuwa arayuwa wanda suka zama sirrin mune, kokadan bazamuso wani yasaniba, balle daya kasance har yau bakisan koni wayeba, nasan wannan abune mai wuya kisake jiki da mutuminda bakisanshiba, awancan lokacin yakamata na fahimci hakan,
Amma nagaza fahimtar hakan,
Dole zanci wani iri har indai da gaske nake na damu dake iringa kallonki ahaka baki zuwa makaranta,
Bance sana'arki ko neman na kanki yazama aibuba nasan kowa da matsayinda ubangiji ya ajiyeshi,
Lokuta da dama zuciyata takan nusar dani akan narabuda ke nadaina shiga duk wani harkokinki saboda bakyason hakan amma na gaza,
Zuciyata atsarkake take akanki,
Bansan daliliba bansan mai ubangiji yake nufiba Allah yagani shine yahada jinina dake, magana bawani shiga tsakanina dake takeyiba amma Allah yasanyaki cikin mutane masu mahimmanci arayuwata kuma bazan iya cewa ga daliliba,
Kamar qanwata haka nake jinki bazanso aikata mugun abu akankiba,
Dan Allah kiyi hakuri kidaina nuna wannan tsoron nawa kokuma rashin yarda afili hakan zaisa nayi nesa dake koda banso hakanba,
Saboda duk yanda naso in kyautata miki idan naga hakan zai cutar dake dole zanja jikina,
Advertisement
Shiru sawwama tayi tana sauraron kalamansa zuciyarta take tayi mata zullumi shin da gaske yakeyi tana daya daga cikin mutane masu muhimmanci arayuwarsa? Har cikin zuciyarsa yayi wannan maganar kokuma dai kawai ya fadetane?
Amma kuma alamu yanuna mata daga qasan zuciyarsa maganar take fitowa,
Hawaye taji yafara gangara akan fuskarta,
Ganin hawaye akan fuskarta ya sanyashi runtse idanuwa yana fad'in subhanallahi wani zafi yaji acikin zuciyarsa ganin hawayenta dai-dai yakeda tarwatsa duk wani farin cikinsa, cikin sanyin jiki yace dan Allah kibar wannan kukan idan nine nayi alqawari bazan qara takura mikiba,
Girgiza kai tayi tace ni baka takuramin ba, hasalima ban dauka zam sami muhimmanci arayuwar wani irin hakaba,
Kamar yanda kafada kowani bawa da tasa qaddarar kowani dan adam da jarabawarda ubangiji yake aiko kasa,
Ni tawa Qaddarar kenna,
Zuwana makaranta bazai zama maslaha a halinda muke cikiba,
Baka takuramin kuma baka ta6a takuramin ba,
Nidai kawai banaso karinga sanya kanka cikin al'amurana dayawa, rayuwa tana da sirri, kowani dan adam yanada sirri, bai dace ace nafada maka sirinaba,
Nisawa yayi sannan yace idan bakyso nabari bazan ringa qoqarin sanya kainaba,
Amma dole in damu da halinda kike ciki,
Jijjiga kai tayi sannan tace nagode da kulawa Allah ya biyaka da mafificin alkhairi,
Amin ya amsa sannan yace har yanzu bansan sunanki,
Qasa tayi da kanta tace hafsatu sawwama,
Ma sha Allah kawai ya furta,
Ni zan tafi zan iya dawowa gobe? Ya tambaya,
Dasauri sawwama tad'aga masa kai,
Murmusawa yayi sannan yace nagode sawwama, kanta yana qasa kawai tayi murmushi,
Sallama yayi mata yatafi yayinda ran kowannensu yake cike fall da farin ciki,
Awannan ranar dukda cewa cikinsu babu wanda yasan mai yakeji gameda d'an uwansa amma dai sun san sunyi kwanan farin ciki,
Sadam koda yazo school tunanin maganganu sawwama najiya kawai yakeyi, da nutsuwa sosai atattare da yarinyar maganganunta akwai hankali aciki,
Idanta furta kalma idan kaduba zaka samesu a mazauni yanda yakamata a ajiyesu,
Najeeb ne ya qaraso lokacin sadam yayi nisa cikin tunani har yazauna baisanda isowarsaba,
Saida ya ta6ashi sannan yadawo daga tunanin yajuya ya dubeshi,
Kai najeeb ya d'aga masa yace lafiya?
Babu komai sadam yabashi amsa atakaice,
Ehem dama nasan amsar kenna babu komai babu komai,
Kullum dai zancen kennan,
Wai sadam har yanzu bamu kai matsayinda yakamata ka fadamin sirrinka bane?
Nayi shiru koda zata fadamin amma shiru kaki fada kuma nasan abun yana damunka,
Barin kashi aciki baya maganin yunwa,
Daka furtamin wata qila na iya sama maka mafita,
Kasanni sadam kasan halina bana boye maka al'amurana idan ina neman shawara kai nake fara tinkara,
Yanda na daukeka sadam ba haka ka daukeniba amtsayin dan uwa na ajiyeka wanda zan iya sharing damuwata dashi amma kai ba hakaba,
Iska sadam ya furzar sannan yace me kakeso nace maka najeeb,
Kace komai inajinka, najeeb yafad'a,
Najeeb ni kaina bansan mai yake damunaba,
Wata yarinyace
Zaro ido😳 najeeb yayi yace yarinya?
Eh lallai yace sai kuma yahau dariya,
Bata rai sadam yayi nan da nan zuciyarsa tahaura sama,
Banson rashin mutumci najeeb ina ga irinta nan kace nafad'a maka damuwtaa nafara fadi kahau yimun dariyar iskanci,
Mtseww yaja tsaki,
Dakewa najeeb yayi yace" kayi hakuri nabari,
Bata rai yayi yace shikenan ai yawuce,
Cin serious najeeb yayi yace dan Allah kayi hakuri Allah nabari,
Sanda yadan dauki lokaci kafin yaci gabada fad'in,
Wata yarinyace najeeb wallhy tausayinta nakeji tana cikin wani irin hali da zaran na ganta cikin damuwa kokuma wani abun bacci kauracewa idanuwana yakeyi
Banida aiki sai tunaninta da halinda take ciki,
Kowacce magana tafad'i takan tsaya min arai,
Nadade banji mutuminda tunaninsa ya zamanmin jikiba irinta,
Najeeb koda abun 6acin rai tayimun 6acin ran yakan shafi kowa da kowa,
Nakanji zafin kowa abu kadan akaimim zan farajin haushin mutum,
Ta dalilin son ganinta yasa nake skipping lactures,
Ranar sanda nayiwa mummy qaryan test akanta,
Nan yaringa yiwa najeeb expressing abubuwanda yakeji akanta, sannan yadaura da fadin najeeb bansan mai yake damunaba,
Bansan dalilin duk wannan damuwarba,
Jijjiga kai najeeb yayi yace wato duk wannan tarin dalilin daka lissafomin bakasan menene dalilin hakanba?
Gyada kai sadam yayi,
Miqewa najeeb yayi yana kallon zancen sadam ma rainin hankaline,
Aishi ba qaramin yaronda har zai kasa gane mai yake damunsa bane,
Kallonsa sadam yayi yana fadin ina kuma zakaje na tambayeka maimakon ka bani amsa shine zaka fice,
6ata rai najeeb yayi yace Allah sadam abunnaka harda tsantsan rainin hankali yanzu kacemun bakasan abunda yake damunkaba?
Gyada kai sadam yayi yace wallhy babu rainin hankali awannan lamarin najeeb dagaske nakeyi,
Tsantsar gaskiya najeeb ya hango a idon sadam hakan yasa ya koma ya zauna,
Yadubi sadam yace" sadam son yarinyarnan kakeyi,
Zaro ido sadam yayi atsorace yace so kuma?
Kai ina A'a."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial7 Chapters
Cosmocrat
"Everything at some point will meet the end. Death, death was a living creature tormented by his past. Death was once a mortal."Arthur, in pursuit of power, to uncover the truth behind his dreams and visions. Map: Link to imgur or it's displayed on chapter 3 Note:*This is my first time writing a novel; feel free to give me tips to improve as I go along. Cover Art: Harvest Moon by dblasphemy- Nima Tamizi
8 84 - In Serial23 Chapters
Omega System
Important Notice!: I’ve started writing a new novel, so please go check it out! It’s called The Power of Systems. Go check it out guys! One minute, everything was normal, the next minute, Earth became like a fantasy novel. Unique powers called skills awakened in the residents of Earth. The day the world changed was called Omega. A few years after, people decided to found schools that taught children about these skills and how to control them, along with how to deal with monsters and physical training. It was all for the sake of a safer future. These schools were named Academies. Join Damon Zellar as he experiences life in The Royal Academy in England, while constantly seeking strength. One particular day, he stumbled across a unique system so impressive, that it could shake the power balance of the world, but no one knew about this mysterious power. What is the origin of the system, and why was he granted such a treasure? An unknown organization is also after his life, causing Damon to discover even more about his past. Will dark secrets await, or a truth so unbelievable that Damon himself wouldn’t even believe it? What will be Damon’s destined fate? To die or to live? *** Authors Note: He receives the system after a few chapters, just if you wanted to know!
8 61 - In Serial6 Chapters
I am the system
Looks like I got banished to mortal world with no cultivation, Run over by a car! I will get my revenge against you Subaru… ehh what’s health insurance… huhh what’s a ‘system’… In Soviet Russian the MC doesn’t have a system, the MC is the system.
8 83 - In Serial7 Chapters
The Old Steward Journey in Cultivation World
Old man Wu has been living for more than 60 years old. In all his life he never been able to do something big, yet an encounter with a supreme individual change all that.
8 68 - In Serial22 Chapters
I'm just a mortal
I am a human, forced into a virtual world, where my morals and hard life clashes, but I will not drop my beliefs
8 170 - In Serial61 Chapters
The human hunter avp
Mark Johnson, 23 years old, is a navy seal in the US army, master MMA fighter and expert in hand to hand combat, he is the model soldier for new candidates. His life is perfect, he never fails his missions, being completely successful.All of this changes when he awakens in a cage, on the home world of the Yautja. He is to be sold as a slave, but his fierce determination shall render him a great hunter.
8 53

