《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 9
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 9
Sawwama tana gamawa tashige gida, dama idan tagama abunda takeyi bata tsayawa yin komai takan tattara duk wani abunda tasan zatayi amfani dashine tawuce gida,
Koda tashiga bayan ta idda sallar isha'i d'inta bata tsaya hiraba kamar yanda sukeyi acikin gida itada mahaifantaba,
Saboda tagaji liqis kuma idanuwanta lumahewa sukeyi tanajin bacci,
Hakan yasa tayiwa mahaifanta sallama tashige d'aki,
Bayan tashiga ta kwanta ga mamakinta sai bacci yakasa daukanta dukkuwa da jin baccinda takeyi,
amma gabaki daya baccin ya kauracewa idanuwanta,
Sai kuma zuciyarta tashiga saqo mata bayanai kala-kala, tunane-tunane kala-kala tashigayi, wanda ba wasu ma'ana garesuba,
Juyi tashigayi ta juya nan ta juy can ko bacci zai dauketa amma shiru,
Rass gabanta yafad'i tunowa datayi da mutumin d'azu daya bar mata kudi awajanta, koh mai yake nufi da barin mata kud'i dayayi yatafi ohow??
Shin koda wani mugun nufi yazo wajanta siyan awara dahar zai bar mata canji haka??
Ko amma kuma aii a fuska baiyi kamada mutumin banza ba zuciyarta tafad'i,
Wata zuciyarce tace mata shin dama wasu lokutan mutanen banza sunada kamanni ne??
Ajiyar zuciya tasauke amma cikin ranta sam batajin tsoronsa bata kuma tunanin akwai wani mugun nufi atattare dashi, saboda yanada cikar kamala da nutsuwa atattare dashi,
Nisawa tayi afili ta furta koma dai yayane idan yasake dawowa zan maida masa da kudinsa,
Idan kuma bai sake dawowa ba zatasan yanda zatayi ta rabuda canjinsa,
Cikin zuciyarta kuma tana fatan sake dawowarsa saboda tanason sake kallonsa haka kawai,
Kuma ita kanta batasan dalilin hakanba,
Haka tayita juyinta da tunaninta bata San lokacin da bacci ya ebeta ba."
Da safiya kamar kullum ayyukan da takeyi wanda suka zama kamar farilla ta gabatardasu,
Sannan tashiga aykin sana'arta,
Itadai bata san mai yake damuntaba amma gabaki d'aya wani iri take jinta,
Advertisement
Koda tazauna tayi tunani abu d'aya ne yake fad'o mata aranta shine wannan mutumin,
D'aukan duka damuwarta tayi ta watsar saboda tasan abu d'ayane sai sanyata tunaninsa shine kudinsa dayake wajanta,
Tadaura niyyar kuma saita maida masa kudinsa, koda kuwa ba yanzu bane."
———————
Shikuwa sadam anasa wajan tun sassafe ko karyawa baiyiba yafice izuwa makaranta,
Haka kuwa koda dayaje school yayi niyyyar idan zai dawo yabi ya siya,
Amma bai samu damaba,
Saboda bai dawo daga lactures sai daff magrib, saida ya tsaya a school yayi sallah sannan yakama hanyar gida,
Haka koda yadawo dare yayi sannan tsakanin gidansu da wajan akwai nisa hakan yasa yawuce gida kai tsaye,
Koda yashiga gida yasamu mummy atsaye tana jiransa a palour duk hankalinta yatashi saboda bai saba kaiwa hakan awajeba,
Da sallama yashiga palourn su dukansu suka amsa,
Momy wacce take tsaye dama kamar jiran shigowarsa kawai takeyi tafara magana da fad'in sadam ina kaje kazauna har iwar haka baka dawoba?
Qarasowa ciki yayi sannan yace momy lactures sai daff magriba muka fito shiyasa na tsaya nayi magrib acan,
Jin haka mai makon tayi shiru sai tahau maganganu,
Ai shiyasa tun farko nafadawa dadynku babu anfanin zamanka agida,
A hostel zakafi karatu hankali kwance yanzu ina alfanu ace sai yanzu zaka dawo gida,
Iyeh hankalinka yabi ya rabu kashi-kashi, mu kanmu idan baka dawo da wuri ba hankalinmu ba akwance yakeba,
Dady dayake gefe ya amshe zancen da fad'in,
Yaro yadawo baki barshi yahutaba kin haushi da fada tun safe yafita yadawo ko hutuwa baiyiba,
Plss kibarshi yashiga ya huta,
Kada kai mummy tayi sannan tace ai shikenan tunda kai bakason laifinsa bahali afad'i aibunsa,
Murmushi dady yayi sannan yace ba son kaiba amma d'ana baida wani aibu ajikinsa,
Baida aibu a halayyarsa,
Baida aibu a d'abi'unsa,
Haka zalika baida aibu a zaman takewarsa,
Advertisement
Kinga laifina dan naqi afadi aibun wanda baida aibu?
Itama mummy murmushinne ya su6uce mata sannan tace shikenan tunda haka kace,
Nima na yarda juyawa tayi wajan sadam sannan tace" son shiga d'aki ka huta,
Jijjiga kai yayi sannan ya kamo hannunta ya sumbata,
Shafa kansa tayi da daya hannun sannan tace Allah yayi maka albarka, amin ya amsa,
sannan yajuya zuwaga dady yace sannu da gida dady,
Sannu sadam ya makarantar?
Lafiya qlau sadam ya amsa,
Ma sha Allah dady yafadi sannan yadaura da fadin kashiga ciki kahuta sannan kafito a muyi sallar isha'i sannan saimuyi diner,
Toh sadam yace sannan yawuce ciki.
Mummy ta qarasa wajan dady ta zaune da dubeshi cikin nishad'i tace"
D' sadam yanada hankali sosai, a kullum na kalleshi ina farin ciki kasancewarsa d'ana sam yaronanan baida rawar kai koka d'an,
Halinsa dana yaran yanzu daban yake,
Hannu dady ya sanya a kafad'arta sannan yace' abunda nake fada miki kenan aii,
Yaronnan yanada hankali sosai banaso kiringa yawan qorafi akansa saiya kasance yana ganin kamar ya gaza yimana biyayya ta wani abunne,
Hakane mummy ta amsa sannan tadaura da fadin wasu lokutan bawai ina qorafi akan halinsa bane,
A'a ina yine akan inaso yaqara himma yaqara dagewa,
Da wannan dan wannan dady yafadi sannan yace amma duk da hakan yakamata ana rage wasu abubuwan,
Toh in sha Allah zan rage mummy tafad'i
Daddy yace toh Allah yayarda.
Sadam kuwa anasa wajan yana shiga daki yazube takardunsa, ya nemi waje ya zaune,
Sanda ydan huta kafin yatashi yashiga wanka daga nan ya hada da alwala yafito suka tafi masallaci shida dady,
Kafin su dawo mummy tagama shirya musu abuncin akan dining koda suka dawo kai tsaye wajan cin abunci suka wuce bayan sun gama sun dade suna hira saida dare yayi kafinnan kowa yashiga d'aki."
————————
Sawwama anata wajan kuwa tanata zuba idon ganinsa amma harta gama tatashi baizoba,
Ahaka suka dauki wajan sati guda kullum sadam yakanyi dare a school so bai samu yabi yasiya,
Ita kam sawwama tama cire rai da sake ganinsa,
Atunaninta dama hanyace kawai takawoshi tunda dama bata ta6a kallonsa yazoba sai ranar,
Kuma tun daga ranar an debi lokaci bai sake dawowa ba."
Sadam da najeeb ke zauna cikin school lokacin yamma tayi liqis kusan 5:00pm miqewa sadam yayi yana fadin najeeb barina wuce naga magrib ta kawo kai,
Sallama yayiwa najeeb yahau machine dinsa yawuce yana hanya saiya samu kansa da juya kan machine dinsa juyawa yayi yaduki hanyar wajan sana'ar sawwama,
Ya'isa amma yadad'e da isa wajan ya tsaya yana kallonta tanata harkokinta,
Cikin takunsa na nutsuwa ya qarasa wajan yyi sallama
Sawwama kanta yana sunkuye ita harda cire ran sake ganinsa, kawai sai taji sallama d'agowa tayi dasauri idanuwanta ya sauqa akan fuskarsa."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial156 Chapters
My Passive Skills Are Invincible!
It was an era taken over by a single online game, the Second World.
8 198 - In Serial104 Chapters
The 8th Day
One day life is good. The next day it isn't! The boundaries between... well, whatever they're between.. have shattered! Monsters burst out from cracks in the universe, and reality suddenly begins to function similar to a game -- but not a game that anyone knows all the rules about! Magic is suddenly real, but so are monsters and death! Lots of death!And the worst part of it all? I think we did it to ourselves! We invented video games, and personally I think that great Finger-in-the-Sky picked up a console somewhere and started playing them. Since He liked what he saw, he must've declared, """"On the 8th Day, let there be Game!"But what do I know about it all, really. After all, I'm just """"The Witness"""" forced to observe it all.__________________________________________________________________________Author's Note: There's a lot of tales where characters get stuck in a Virtual Reality. """"Sword Art Online"""", """"Log Horizon"""", """"The Legendary Moonlight Sculptor"""". This is a story told with the premise inverted -- instead of a person from reality going into a virtual world, what would happen if the virtual world instead came to reality?I want this tale to speak about the aspects of the game, as it has affected the current reality, but the focus of the story should never be on the """"reality-turned-game"""" itself, but on the characters and their oh-so-human struggles, personalities, and attempt to adjust and live within the bounds of their new existence. Hopefully this won't just be a story of """"reality turned into a game"""", but instead will be something more meaningful such as a story of the strengths, perseverance, and humanity of man-kind as they try to adapt and face the unknown.*** And, most importantly, I hope everyone enjoys reading it as much as I've enjoyed writing it. ***WARNING: RATED MATURE M[18+] FOR GORE, SEX, VIOLENCE. The apocalypse isn't a pretty place to try to survive in, and neither is every scene in a story trying to describe it.
8 79 - In Serial25 Chapters
The Wonderful Wizard of Oz
The Wonderful Wizard of Oz, is an American children's novel written by author L. Frank Baum and illustrated by W. W. Denslow, originally published by the George M. Hill Company in Chicago on May 17, 1900. It has since been reprinted on numerous occasions, most often under the title The Wizard of Oz, which is the title of the popular 1902 Broadway musical as well as the iconic 1939 musical film adaptation. The story chronicles the adventures of a young farm girl named Dorothy in the magical Land of Oz, after she and her pet dog Toto are swept away from their Kansas home by a cyclone. The novel is one of the best-known stories in American literature and has been widely translated. Its groundbreaking success and the success of the Broadway musical adapted from the novel led Baum to write thirteen additional Oz books that serve as official sequels to the first story.
8 110 - In Serial7 Chapters
Pooping pants
A girl discovers something she loves
8 153 - In Serial45 Chapters
Insane
All it took to meet one of the world's craziest, most dangerous serial killers was being in the wrong place at the wrong time. This was all it took to send Alice into the world of a criminal. *FINISHED*
8 417 - In Serial16 Chapters
to be together | chase davenport/reader
"I wanted to think we were destined in some way - to end up happy, to grow old, just to be together."Thanks to everyone who stuck with this.
8 167

