《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 8
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 8
Cincin rundon jama'ane na gaske sannan kuma ba qananun mutane bane,
Gabaki d'aya suna tsaye jiran fitowar Haliifa kawai sukeyi, burin kowanne daga cikinsu haliifa yafito su ganshi ya samu lafiya,
Kowannensu ya maida hankalinsa wajanda mutane suke fitowa,
Gadonda haliifaa yake kwance aka fara turowa aka fito dashi daga cikin jirgin,
Sai umma agefen sa tana biye dasu, ummi da ruma suma duka suna biye dasu abaya,
Farin cikin da yake tattare da wad'annna mutane da sukazo taryansu ganin a irin halinda aka dawoda haliifa dukansu sai murnarsu ta koma ciki,
Dogara dake gefe suna kallon fitowarsu sukayi saurin qarasawa Wajan jikin gadon suka zazzagaye tako'ina suka rufeshi ruff yanda babu mai iya kallo abunda suka zagaye,
ahaka sukayiwa gadon jagora har izuwa bakin motar za'a shigardashi,
Wasu daga cikin mutanen airport din suka tsatssaya suna binsu da kallo saboda ga dukkan alamu wani babban mutum ne ya iso, kuma bamai cikekken lafiyaba,
Wasu sun tausayawa masa yayinda wasu suke alhinin komai yasameshi,
Wasu daga cikinsu sun san waneneshi saboda koda ganin wad'annan mutanen sun san yareema haliifaa kuma sunsan kwanakin baya ya haduda ciwo,
Wanda suka sanshi daga cikinsu sun tausayawa masa saboda sanin wanene haliifa dasukayi,
Halinsa mai kyaune baida mummunan hali, bai kumada girman kai ko wani jijji dakai,
Mutum ne mai sauqin kai
Shikuwa bai shiga harkan wani,
Zaiyi duk wani iya qoqarinsa na ganin cewa bai shiga hakkin waniba,
Amma yau shine cikin wani hali aciwonda ankasa gano kansa gabaki daya,
Rufe wajan sukayi gabaki daya har aka gama shigarda shi mota,
Sannan su umma kowa yashiga mota aka rurrufe,
Dogarawa kuwa suma nasu motocin suka shiga,
Duk da kasancewar kowani mota daya akwai dogari agaban motan dakuma drivern motan,
Daganan motoci suka d'aga sai cikin fada,
Advertisement
Acanma tako'ina ana jiran isowarsune suna shiga umma tabada umarni kai tsaye awuce shashinta,
Can suka wuce daga nan aka shigarda haliifa izuwa bangarenda yake tun kafin tafiyarsu,
Suma su umma suka shige domun hutawa."
Cikin d'an qanqanin lokaci labari ya karade cikin masarauta kaff akan dawowarsu haliifaa,
————
Macece mai cikakkiyar izza, isa dakuma d'agun kai yanayinta kadai ya isa ya nuna jiji dakai dake tattare da ita,
Akishingud'e take jikin wani d'an tuntu idanunta yana lunshe,
Shigowa d'akin jakadiya tayi da dan saurinta ga dukkan alamu maganace abakinta, tsugunnawa jakadiya tayi agabanta tana fadin takawarki lafiya ranki shi dade, Allah yaja kwana yaja zamani, uwargida wajan sarki, Allah yajikansa, mahaifiyar magajin gari,
bude ido wannan matar tayi ta dubeta sannan ta maida idonta ta lumshe ga dukkan alamu taji dad'in wannan kirari da akayi mata, amma bata nuna hakanba,
Jakadiya taci gabada fad'in"
Ranki shi dade' yarima halii,,, saurin d'aga mata hannu wannan matar tayi lokaci daya alamun 6acin rai ya bayyana a fuskarta,
ganin haka yasa jikin jakadiya yadauki rawa atsorace tafara fad'in agafarceni ranki shi dade.
Hannu kawai ta qara d'aga mata alamun ya isa haka,
tsawon lokaci batace komaiba itama jakadiya tana tsoron taqara magana tayi laify,
Tsawon lokaci jakadiya na zaune awajan
Kai kace ta manta cewa da mutumi kusa da ita amma sarai tana sane batajin maganane alokacin kawai saboda dan 6ata mata rai da jakadiya tayi,
Kuma dama koda ba'a 6ata mata ranba takanyi fiyeda hakama,
Jakadiya kuwa tayi shiru tana sauraron wannan mata jira takeyi abata izinin magana amma shiru,
An d'auki tsawon lokaci kafin tasake bude idonta ta maida taqare lumshesu,
Jakadiya harta cire ran da za'ai mata magana kawai sai can tajita tayi magana cikin izza, isa, sarauta, dakuma mulki kamar wacce take tsron buda bakinta tace" maike tafe dake?
Jadakidaya jin an tambayeta yasata saurin fadin ranki shi dade,
Advertisement
Haliifa sun dawo yanzu,
Saurin bude idanuwa wannan matar tayi tana kallon jakadiya,
Neman qarin bayani takeyi jakadiya tagane hakan yasa taci gabada fad'in,
Tunda naji alamun shigowarsu cikin masarauta naje na tsaya a hanyarda zata sadani da sashin mahaifiyarsa,
Mtseww wannan mata taja wani dan siririn tsaki saboda bayani takeso kai tsaye bawai atsaya jan lokaci ba,
Ganin takosa yasa jakadiya saurin dukar dakai tace"
Allah ya huci zuciyarki ranki shi dade amma yanda aka tafi dashi haka aka dawo dashi,
Jijjiga kai tayi alamun taji dad'in zancen sannan tayi mata alamun akan tatafi,
Tashi jakadiya tayi tatafi tabar wannan matar cikin farin ciki."
—————
Mai martaba yana zaune acikin d'akinsa,
Babbane sosai domin tsufa takamashi,
Ta bayyana ajikinsa, Qur'ani ne abude agabansa da dukkan alamu bai dade da gma karantashiba,
Yana zaune akan sallaya carbine ahannunsa yana lazumi,
Sallama akayi daga qofar d'akin ya amsa sannan yabada umarnin shigowa,
Shigowa tayi tazauna agefensa, itama dai tsufar ta kamata ga dukkan alamu matarsace,
Sanda ya idda abunda yakeyi sannan ya rufe qur'anin gabansa ya juyo ya dubeta,
Sannu da hutawa tafad'i,
Amsawa yayi sannan tadaura da fad'in,
Ranka shi dade yarima haliifa sun iso tun d'azu labari ya iskeni shine nace bari naje induba jikinnasa,
Nisawa mai martaba yayi sannan yace"
Jiki kam sai Godiyar ubangiji,
Yana fad'in haka ya miqe tareda alqur'aninsa zai maidashi mazauninsa,
Wajan littafai ya nufa kala-kala na addini ya ajiye qur'anin amazauninsa daban,
Miqewa itama matar tayi had'eda fad'in
Bari na shiga wajan yarima na dubashi,
Da kai ya amsa mata,
Hanyar fita ta nufa saboda taga alamun kamar bayason hayaniya,
Fita tayi ta wuce shashin umma,
Itada muqarrabanta,
Acikin falon umma sukayi masauqi,
Sannan jakadan da suke shshin suka shiga sanarwa umma da zuwannasu,
Fitowa umma tayi cikin ladabi ta zube gaban wannan matar tana kwasan gaisuwa,
Amsawa matar tayi ta tambayeta hanya da jikin yarima,
Amsa mata umma tayi da fad'in jiki Alhamdulillah,
Yanzuma haka yana bacci ne,
Jijjiga kai tayi sannan tace babu damuwa dama nazone kawoi nayi muku gaisuwa,
Allah ya qara masa lafiya tafad'i,
Amin umma ta amsa,
Sannan suna tashi suka tafi."
——-
Kusan duk wanda yake cikin masarautannan labarin isowar yarima haliifa ya iskeshi amma kuma wannan mata ita d'ayace ta taka sashinsu dan duba jikinsa,
Sai mai martaba wanda kullum dare sai ya tafi can tsawon lokaci yake eba yanayi masa adduo'i
Hakan yasa tunda suka dawo jikin sai yafi nacanma sauqi saboda bai sake attempting dukan wani ba,
Wannan kennan,
Mai martaba mutum ne shi mai addinin gaske,
Allah yabashi ilimi sosai babban malamine,
Idanda wani abunda yakeso fiyeda komai a duniya shine haliifa,
Saboda ko cikin matansa yafison kakar haliifa, Allah yayi mata rasuwa,
Haka cikin yaransa kaff yafison mahafin haliifa,
Shima Allah yayi masa rasuwa,
Haliifa kawai yake kallo yaji sanyi, saboda kallonsa yakan tuno masa da matarsa dakuma dansa, sonda yake yiwa matarsa da d'ansa saiya tattaro yadawo kan jikansa,
Kuma haliifa dik cikin jakannunsa yafi bashi kulawa, yafi yarda da hankalinsa da nutsuwarsa addni da iliminsa,
Halayensa na kirki yasa yaqara shiga ran mai martaba,
Kwatsam sai wannan rashin lafiya tazo tasamu haliifa,
Baqaramin tashin hankali mai martaba yashigaba,
Yanzu haka matan mai martaba biyu,
Yaransa kuma duka yanzu matane biyu maza amma duka mazan sun rasu, ahatsarin mota,
Mahaifin haliifa yabar d'a daya kacal haliifa,
Yayinda dayan kuma yabar yara biyu duka maza,
Wannan kennan,
Mai martaba ya dagewa haliifa sosai da addu'a har takaiga yanzu ko alamu ajikin haliifa bazaka gani cewa baida hankaliba,
Sai dai kawai baya magana baya kula kowa,
Idan zaka shekara kana masa magana baisan mai kake fad'iba,
Shi dai gashi nanne kamar mutum mutumi."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial215 Chapters
The Abandoned Hunter
“Dark Overlord! All hail the Dark Overlord!!!”
8 616 - In Serial7 Chapters
Bloody Haze
It's all fun and games at the start for Smithy and Justin, they're counting the cash after kicking the doors off, not so much when they start kicking back.This novella is a gritty story, following the journey of two young men into the drug business with everything that entails. Strong language, violence and drug references throughout.
8 165 - In Serial13 Chapters
Vapid Recourse
In the past ten centuries humanity has been able to extend its lifespan, cure all diseases, and spread to the far reaches of the Galaxy. What happens, when we take the next step? What if the step after is taken for us? What if we have to pin it all on a farm boy, one that is not charged by the sun? A thousand years was not enough time to prepare for this. Answers to Ancient questions will be given. At the same time, in the galaxy nearest to the Milky Way, a Princess who as just come of age, must escape here fathers thumb to follow her destiny. Her destiny lies in the unification of these two galaxies. Can she find the mythical tigers before the ValRachna destroy everything. In the midst of it all a wayward Mithrin, outcast for is repeated failure, will try again to complete his task. Can he succeed in guiding his new Recipients on the path to reawaken the Ancients and crown the next Masters.
8 91 - In Serial18 Chapters
Desperate Times - A 49ers GameLit Trilogy
Like first person shooters?If you could feel every bullet, knife, explosion; every injury, every death, would you still play your favourite games?On their last life, the 49ers have no choice.After a war which nearly ended the world, a single virtual reality game replaced war.Trapped, fighting for their very survival, the 49ers will do what it takes to PTFO.If you like Call of Duty, Battlefield, or PUBG, you’ll love this series.
8 175 - In Serial9 Chapters
Chaos: Another World Betrayal
It feels like an eternity since I was trapped within this dungeon... My arms have been crushed, my spine is broken, and my friend is dead. I was summoned to this other world along with my classmates in order to save it, but being betrayed by one of my classmates, I fell deep into one of the dungeons. My friend sacrificed himself to keep me alive. And it also seems that the people of this kingdom have been lying... ‘Demons are evil!’ Don’t make me laugh! They’re the ones who saved me! I swear I’ll get back out of here and destroy everything. Not one person will survive my wrath. Wait for me motherf*ckers, because your worst f*cking nightmare’s still alive!
8 60 - In Serial43 Chapters
My meme collection
Look, I'm bored okay.This is my meme collectionNot my memes bye luwlThank you Pinterest
8 176