《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 7
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 7
Wata matashiyar mata ce mai cikeda kamala azaune a palour wacce bazata wuce 45yrs ba duk cikar zatinta da kamalarta, da sauqeqqen yanayi da yanuna ajikinta amma hakan bazai hana kana kallon wannan matar ka hangi damuwarda take tattare da ita qarara ba
alamunta yananun hankalinta atashe yake kokuma tana tattare da wata cikekkiyar damuwa,
Tayi nisa cikin tunani sosai tadaura hannuwanta ta tallafo fuskarta tayi tagumi, sosai ta nitsa cikin kogin tunani
Har suka qarasa shigowa palourn batasan sun shigoba saida wata yar budurwa ta qarasa kusada ita ta ta6ata tana fad'in umma lafiya kuwa?
Tunda muka shigo hankalinki baya jikinki gabaki daya,
Wani abunne yafaru??
Babu komai ruma! Tafad'i atakaice,
Zata qara magana wacce suka shigo tareda ita ta katseta da fad'in A'a ruma kada kija zancen,
Kefa kanki kinsan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi,
Zaunawa kusada ita ruma tayi tana fad'in nasani ummi,
Sannan ta sanya kanta akan kafad'ar matanda take zaune tace" umma dan Allah kiyi hakuri kisawa ranki sanyi,
Kowani dan Adam da kika ganshi da tasa qaddarar mukuma tamu qaddarar kennan tanan Allah ya jarabcemu,
Nasan dole mu kasance cikin damuwa amma umma damuwar idan tayi yawa sai tazo ta haifar mikida wani ciwon ayi d'a kwance uwa kwance,
Umma kiyi addu'a kawai Allah zai fiddamu,
Nisawa wanda aka kirada umma tayi sannan tace ruma abun yana damuna,
Kullum ciwon halifaa gaba yakeyi baya raguwa,
Yanzu tsawon watanmu shida anan qasar magani anayi kamar ba'ayi, yanzu kiduba abunda yafaru shekaran jiya ban ta6a tunanin faruwar hakan ba, saboda bai ta6a aikata Wani abun makamancin hakaba,
Kinga kuwa abu gaba yakeyi,
Hawaye yana gangarowa akan fuskarta tace Allah mun tuba Allah ka yafemana,
Allah kajikan wannan bawa naka kabashi lafiya,
Advertisement
Tana kuka taci gabada fad'in
Wato shi halifa tasa QADDARAR RAYUWAR kenan?
Shekaru biyu baya babu wanda yata6a tunanin faruwar hakan,
Sanya tissue tayi tashare hawayenta
Sannan taci gabada fadin yaro mai cikeda nagarta kuzari dakuma jarumta yanzu shine ya dawo haka,
Taqarashe magana hawaye yana qara bin kan kumatunta,
Qarasowa waccar matan danaji ankirada ummi tayi tana fad'in yahyah kiyi hakuri ki daina kuka in Allah yayarda Haliifaa zai samu lafiya,
Mudai muci gabada addu'a Allah yana gani zaiyi mana maganin komai,
Jijjiga kai umma tayi na gamsuwa da maganar yar uwar tata tace,
Hakane sadiya amma ace samada shekara biyu kennan ana abu daya bbu canj?
Yanzu asibitoci wani irine bamu zagaba?
Hannu ummi tasanya ta shafa kafadun umma sannan tace" hakane yaya amma ai kinsan shi magani dacene,
Idan Allah yasa sai kiga andace,
Hakane umma ta amsa sannan tace shikenna Allah yabashi lafiya,
Amin su duka suka amsa,
Kushiga kushirya muwuce asibitin,
Toh suka amsa sannan duka suka miqe zuwa ciki,
Cikin qanqanin lokaci suka gama shirin suka fito,
Umma kam dama ashirye take dan haka suna fitowa suka fita zuwa wajan mota,
Driver wanda yasanda fitar dama yana jira suna fitowa ya bude musu qofa shiga sukayi kai tsaye yawuce dasu asibitin,
Bayan sun shiga asibitin kai tsaye suka wuce ward din
Wani daki suka mufa mai kyau sosai ga dukkan alamu bakowani marar lafiya ake kwantarwa awanan d'akinba,
Da sallama suka shiga dukda kasancewar sunsan bawai zasu sami amsa bane,
Azaune yake akan gadonsa na marassa lafiya idonsa yana kan qofa,
Suna shiga yafara binsu ta kallo d'aya bayan d'aya kamar maison gano wani abun tattare dashi,
Umma dasauri tanufeshi tana fadin yarona nayi kewarka sosa,,,, bata qarasaba taji an qireta juyawa tayi domin ganin wacce tariqeta sai taga ummi,
Girgizaka mata kai ummi tayi sannan tace yaya kada ki qarasa kusa dashi kizauna daga nesa,
Advertisement
Kokin manta abunda yafaru shekaran jiya?
Jaa da baya umma tayi ta tsaya tana tunano abunda yafaru shekaran jiya,
Shaqeta halifaa yayi dakyar aka kwaceta,
Hawayene ya zubo mata ganin danta kusada ita amma babu halin taqarasa kusadashi,
Zama tayi akujeranda take facing dinsa, kallonsa takeyi cikin tausayawa,
Hannunsa tabi da kallo chain ne ad'aure a hannun wanda suke saqale ajikin gadon basuda tsayi yanda bazaiyi nisan zangoba,
Saboda tsayinsu iyakaci walwalarsa jikin gadonne,
Hawaye yana zuba a idonta tafara fadin sannu haliifaa sannu,
Allah zai baka lafiya in sha Allah
Binta da kallo kawai yakeyi amma baisan mai take fadaba,
Saboda babu hankali ajikinsa, da dukkan alamu kansa yana ta6e, yana famadq rashin hankali,
Amma yanayinsa bai nuna hakanba, kayan patients ne ajikinsa bbu alamun qazanta ko wani abun haka,
Amma kuma dai kasan bai cikin hankalinsa,
Umma tana kallon sa batasan lokacinda hawaye yake zuba a fuskarta ba,
Ruma ne taqaraso tana fadin umma wannan hawayen kidaina zubdashi,
Nasan koda yaya haliifaa yana cikin hankalinsa baya son ganin hawayenki, yanzuma nasan saida baida halin fadi amma hakan bazaiyi masa dadiba,
Ummi ne tace yaya wannan jarabawace kuma kaddarace dan Allah kiringa daure zuciyarki.
Tsowon shekaru biyu ace ana abu daya amma kin kasa kwantarda hankalinki,
Babu abunda Allah bai bamu ba bbu ta yanda ya ragemu ,
Idan kika duba tako ina Allah yayi mana budi mulki da dukiya, ilimi dakowani fanni, duk wani abunda mukeso arayuwarnan zamu sameshi har indai dukiya zata iya badashi, har in kuma ilimi zai badashi toh munada shi kokuma zamu sameshi,
Amma kuma saiya dauke mana abu daya acikin zuri'armu wanda yayi hakanne ya jarabcemu ya nuna mana dukiya ko ilimi da muke dashi bazai siya mana komaiba,
Dukiyarmu takasa samawa yaronmu lafiya abunda zamuyi shine kawai mu komaga ubangijinmu mu roqeshi shine zai fiddamu daga cikin quncinda muke ciki,
Sannan kuka bashi zai bashi lafiyaba,
Yaya dan Allah kizama mai dauriya,
Toh umma tace kawai,
Suna zaune wajan kusan 2hour saiga doctor yashigo shida wani dan matashi wand bazai wuce 35years ba,
Qarasa shigowa sukayi shida likitan
doctor ya qaraso suka gaisa da umma,
Shikuma wannan mutumin ya tsaya wajan ummi sukayi magana sanda suka dan dauki lokaci har doctor yagama abunda zaiyi yafita,
Sannan yaqarasa wajan umma da takardu ahannunsa.
Gaida umma yayi cikin ladabi sannan yace hajiya duk wani shirye-shirye daya kamata anyishi yanzu haka wad'annan takardunne zuwa jibi in sha Allah zamu koma komai ya kammala.
Miqawa umma takardun yayi tasanya hannu ta kar6a,
Nuna mata yanda zata sanya hannu yayi ya kar6a ta sanya tamiqa masa ya kar6a yafice,
Awajan suka wuni zubur sai magarib suka koma gida,
Akwana biyu suka gama duk wani shirye-shirye na komawa kasarsu,
Washe gai jirginsu zai tashi zuwa gida,
Ummi da ruma ne sukayita shiga kasuwa wajan sayayyar abubuwanda zasu buqata,
Ita kuma umma tana gida ko asibiti"
Washe gari da safe jirginsu yatashi bayan anyiwa haliifaa allurar bacci na iya tsawon awanninda zainkaisu gida,
Ahakanma sanda suka taho da nurse mai duba lafiyarsa,
Tunda suka tashi har jirginsu ya sauka bai tashiba."
Bayan sun sauka motoci nagani masu yawan gaske sunzo taryansu,
Kowanne kagani acikin jama'arda suka zo taryansu fuskarsa cikeda fara'a da dukkan alamu jama'ar suna daukin ganinsu."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial42 Chapters
Do You Like Skydiving?
It’s 2050 something and at the verge of a new era, the first well known superhero is rising to the peak of his career. His presence is impossible to be ignored. Criminals in a city he believes to be cursed never feel safe. Countless lives are saved. “Cleansing crime,” he calls it. Boasting whacky superpowers and a chilling costume, he can be found flipping across the skies, sometimes laughing so cheerfully that it’s contagious. Psycho the Superhero is his name, and even the toughest of criminals with their big boy pants cower in terror after hearing a certain catchphrase… “Do you like skydiving?“ Upload schedule: Every Wednesday + Friday.
8 275 - In Serial197 Chapters
Cosmosis
Book 3, Through the Cracks, is ongoing. New chapters Monday and Friday at 8:30 PM EST. Join the Discord for discussion and extra goodies! Caleb hasn't had a good day ever since he was abducted into outer space. The food sucks. Nobody understands a word he says. The aliens won't even let him leave his cell. He's driven to fight his captors and escape their clutches. Confronted with hostile aliens, intent on holding him prisoner, Caleb chooses to dive headfirst among forces he can't understand. He'll either learn the eddies of the alien worlds he's stranded in, or else he'll never make it back home. If his hallucination of one of the other abductees can be trusted, maybe they can make it through the trials before them. At least there's no homework?
8 537 - In Serial13 Chapters
My Thoughts Exactly
Ryu, a teenage boy with no respect for social norms, is starting his education as a magician; however, starting alongside him is his sister Ruri, a devil (in his opinion) who loves nothing more than to tease him and make his life miserable. A shameless boy, a sister who keeps him on edge and a city of students full of hormones. What could go wrong? Oh, and the world is at war.
8 184 - In Serial14 Chapters
The Night Sorceresses
Magic is illegal in Ethermoor. Willow Nightshade is a young sorceress living in the village of Fernhollow. After her parents are brutally murdered at the hands of the police for practicing sorcery, she vows revenge on the evil King Banderon for the kingdom's unjust laws against the magical people. Betrayal lurks around every corner, and Willow must be careful whom she trusts. And something else that may not be human at all is killing the magical people of Ethermoor. Can Willow restore peace and magic to the kingdom? full novel can be purchased on Amazon.
8 206 - In Serial6 Chapters
The End!?
A hero who has tried to end all misery by himself and abandoned everything for this end. A story of a future where world changes, earth changes, 'Yug' era changes as 'change is the law of universe' When earth face devastating changes and world changes a new world arises human civilization gets transformed after an anhilation. Story of uncovering all the truths!!
8 185 - In Serial15 Chapters
قومارباز Jikook
jikook
8 122