《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 6
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 6
K'arasawa najeeb yayi zuwa bakin titin wajanda sawwama take suyar awaranta,
Yayinda shikuma sadam yatsaya can gefe tsallaken titi yana jiran dawowarsa,
Dake najeeb yadan samu layi hakan yasa bai samu yasiyo da wuriba,
Sanda ta sallami yaran da suka rigashi zuwa sannan tajuya zuwa gareshi,
Mai za'a baka?
Tatambayeshi kasancewar akwai wasu abubuwan kusada ita bayan awaranda take suya,
Awara yafadi hadeda miqa mata dari biyu 200 kar6a tayi tana fadin na nawa za'a baka?
Zubamin na duka yafadi toh tace sannan ta zuba a baqar leda mai zafi hadeda daura masa yaji afarar leda ta miqa masa,
Qarba yayi tayi masa godiya ya juya yakoma,
Bayan ya isa wajanda suka tsaya shida sadam
Bata rai sadam yayi yana fadin ka barni sai jira nakeyi idan babu da kadawo ai sai kaje wani wajan kasiya
lallaine sai nan kadai zaka siya?
Yaqarasa fadin haka yana hawa kan mashin din ya tayar,
Shima najeeb hawa kan mashin din yayi sannan yace"
Ai nasaba yawancin awajanta nake siyan awara ta'iya sosai,
Sadam bai qara cewa komaiba yaja mashin din suka tafi,
Gidansu najeeb suka wuce kai tsaye suka shiga dakinsa,
Bude awaran najeeb yayi ya sanya agaba yafaraci yana fadin bismillah sadam nikam nafara,
Kallonsa sadam yayi sannan yace kasan dai bazanci abu aleda bakoh?
Miqewa najeeb yayi yana fadin har yanzu baka bar wannan halinnakaba,
Yanata surutai ya qarasa cikin gida yadauko plate,
Juyewa yayi ajikin plate din sannan yamiqa masa,
Banci" sadam yafadi atakaice, kaifa iskancinka yawa gareshi najeeb yafadi,
Yaya zaka sanyani nadauko plate najuye kace bazakaciba,
Yatsina fuska najeeb yayi sannan yace kasan ban cika cin abun kan hanyaba,
Bata rai najeeb yayi hadeda fadin ko mutuwa zakayi idan kaci sai kaci kuwa,
Kasan karamin aikina yanzu ind'ura maka gara ka kar6a da kanka yafi maka,
Mtseww sadam yaja tsaki yasan halin najeeb zaiyi fiyeda haka,
Shikuma bawai yanason wasan banza bane,
Jan plate din yayi gabansa yafaraci fuska ayatsine,
Aikuwa sai gashi mutuminka yasake yafaraci sosai
Dan tunaninsa bai kawo abun yanada dadi hakaba
Sanda yaci seven sannan yaturawa najeeb sauran ahakanma bawai ya isheshi bane kawai baiso ya zaqe dayawane tunda tun farko yanuna bazai ciba,
Advertisement
tsaki najeeb yana yana fadin ashe dai rashin cin na munafurcine
Sadam bai kula shiba saima kishin gida dayayi kawai ya kwanta,
Jan plate din najeeb yayi yaqarasaci sannan ya fitar dashi cikin gida,
Sanda sadam ya huta sannan yacewa nejeeb zai wuce,
Sallama sukayi yawuce gida.
Washe gari kuwa dai-dai wannan lokacin najeeb yabi gidansu sadam suka fice yauma sanda suka tsaya suka siya awara,
Yau sadam bai jira najeeb yayi masa tayiba yasanya hannu yafaraci,
Najeeb sanda yayi dariya sannan yace mutumina a leda fa yake ban juyeshi a plate ba,
Ko kulashi sadam baiyiba yaci gabada cin abinsa."
Bayan sun gama suka dan jima sannan yatashi yawuce gida,
Saboda bai ta6a iya wuce magrib agida duk rintsi koda ace yakai yamma zai nemi hanyar gida,
Saboda babansuma yamma liqis yake dawowa,
Idan sun shiga gida kuwa sallah kadai ke fiddasu waje, sai washe gari,
———————-
Haka yazamana kullum najeeb da sadam sai sunbi sun siya awara,
Wata rana subi gidansu sadam suci wata rana kuma gidansu najeeb
Ya danganta a gidanda suka fito,
Kullum suke zuwa siya babu dauke kafa
Har tsawon sati daya,
Saboda yanzu sadam yasaba daci sosai shine yake biyawa yadauki najeeb subi su saya,
Ko sau daya sadam bai ta6a qarasawa wajan awaran sai dai najeeb yabi yasiya musu shikuma yana gefe yana jira,
Suna zaman gida alokacin suna jiran result a week dinda suka shiga week dinne ake sanya ran ganin result,
Cikin lokacin result dinsu yafito sosai result din sadam yayi kyau,
Yayi qoqari domin yasamu sakamako
Dady da momy sunyi murna sosai na ganin qoqarinda dannasu yayi hakan yasa momy ta siyo masa waya mai kyawun gaske gift na result nashi,
Dady kuma already ya siya masa mashin amma dukda hakan saida yasiya masa wasu yan abubuwan buqata,
A cikin satin suka koma school, yayinda najeeb yakoma hostel
Shikuma sadam dama yafada wannan karon bazaiyi zaman hostel ba, agida zai zauna sai dai yana zuwa yana dawowa,
Anasa wajan hakan yafi masa sauqi
Koda suka koma school kwana biyu basa zuwa siyan awara,
Saboda najeeb yana kamaranta shima sadam din sauda yawa a school yake wuni sai yamma liqis kafinnan yadawo gida,
Haka har yakai kusan 1week baiciba daurewa kawai sadam yakeyi domin kwanakinnan yasaba sosai dacin awaran sun saba kullum sai sun saya,
Advertisement
Hakan yasa yana dawowa daga school ahanya yaga wata mai suyawa cikin murna ya tsaya ya siya,
Bayan yashiga gida ya huta agaugauce yafaraci,
Amma ga mamakinsa dakyar ya iyacin guda daya daya dauko, danko yaji wani irin ko dadi baiyi masa ba,
Ga tsami ga wani irin hamami-hamami, har warin hayaki yakeyi,
Bazai iya qara ciba dan haka saiya tattaro duka ya dauko yafito cikin gida ya miqawa qannensa yakoma d'aki."
Daya shiga daki sanda yayi brushi saboda bakinsa gabaki daya yaji yayi masa wani iri,
Bayan sunyi sallar isha'i suka gifo cin abinci,
Bayan sun idda momy take tambayansa,
Sadam ina kasamu awara?
Naga kabawa qannenka
Ahanya na siya ya bata amsa,
Juyawa tayi ta dubeshi tana fadin yanzu sadam har kana iyacin abuncin wad'annan qazaman yara akan hanya wanda jahilci yayi musu yawa,
Kallon mahaifiyarsa yayi sannan yace momy menene kuma hadim jahilci da abinci?
Kinsan halina aii idan naga sunada qazanta kinsan bawai zanci bane,
Gara dai karaba kanka kam tafadi,
Miqewa yayi yace saida safe zan shiga daki bai jira cewartaba yawuce d'aki abunsa."
——————
Kwana biyu bai qara tsayawa yasiya awara awani waje ba sannan kuma baije can wajanda suka saba siya ya siya ba bai kuma sake saye awani wajan ba."
Bayan sun fito daga lactures suna zaune shida najeeb dasauran abokanansa,
Duban najeeb yayi sannan yace najeeb kasan kwanaki nasiya abunnan amma kwata-kwata baiyumin dadiba har amai yayi shirin sanyani,
Shiyasa wani lokacin koda naji inasonci idannayi tunanin na ranar saina hakura,
Sanda yaqare maganarsa sannan najeeb yace aikuwa kaga ban ta6a samun irin hakaba,
Bankuma san ya akayi yanzu abuntan yadawo hakaba,
Jinginuwa sadam yayi sannan yace malam bafa awajanta nasiyaba
Wajannata yayimun nisa inje daga school sannan in wuce gida,
Ahanyane kawai ina wucewa nasiya,
Aikuwa dai dukna sauran shirmene cewar najeeb,
Kagani idanba wajanta nasiyaba banajin dadin abun,
Kuma kaga aii ita tanada tsafta, idan kanaso cire ganin nisan zakayi sai kabi kana siya,
Tsaki sadam yaja mtseww abu yadawo sai kace abun jaraba duk kai kaja daka matsa sainaci ranar,
Harararaa najeeb yayi sannan yace" da Allah malam bawani nan,
Dama tun can ranka naso halinkane bansaniba ko yaya?
Miqewa sadam yayi yace ni yanzu sallah zan tafi idan zaka iya tashi saika bini idan kuma bazakayiba ka zaune,
Wucewa yayi abunsa najeeb yabiyoshi abaya
Saida sukayi lactures har 6:00pm sannan sadam yakamo hanyar gida,
Tunaninsane yarabu biyu yanason bin yasiya amma baisan ko zaki sametaba saboda lokaci yadanja shirin kiran magrib akeyi,
Haka dai ya yanke shawarar bin layin idan batanan saiya wuce,
Ya dade tsaye awajan tana tunanin tayaya zai fara dakyar ya nisa sannan ya d'aga kafafuwansa yafara tafiya zuwa wajanta,
Bbu kowa awajan dan Haka yaqarasa dasauri yasiya ya tafi kafin wasu suzo,
Sallama yayi tad'ago ta kalleshi anutse hadeda amsa masa,
Miqa mata kudi yayi sannan yafadi na yanda yakeso,
Kar6an kudin tayi sannan tazuba ta miqa masa,
Yanda take abunta anutse ya burgeshi sosai danshi yanason yaga mutum cikin nutsuwa gata kuma da tsafta,
Sanya hannu yayi ya kar6a sannan tamiqa masa canji,
Kibarshi kawai yafada yana qoqarin juyawa,
Girgiza kai tayi sannan tace A'a katafi da kudinka nagode,
Da mamaki ya kalleta amma sai taqara miqa masa kudin,
Bai sanya hannu ya kar6aba ya tsareta da ido,
Sunkuyarda kanta tayi ganin yanda ya tsareta da ido amma har yanzu bata sauke hannunta ba tana miqa masa kudin,
Girgizaka kai kawai yayi yajuya yatafi baice komaiba,
Dago kanta tayi tabi bayansa da kallo har ya hau kan mashin dinsa yatafi,
Ajiyar zuciya tasauke sannan ta sanya kudin cikin wajanda take ajiyar kudinta,
Shikuwa a mashin yana tuqi amma yana tunanin yarinyarda yabawa kyautar kudi taqi kar6a,
Alamun talauchi ya bayyana ajikinta qarara amma kuma wai yabata kudi taqi kar6a mai hakan yake nufi kennan?'
Bataso mana zuciyarsa tabashi amsa,
Abun yatsaya masa arai sosai haka yatafi gida da tunanin komai yasa taqi karba, ko bata yarda dashi bane oho,
Koda ya isa gida bayan ya gabatarda sallar magrib yazauna yaci awaransa tass,
Ajiyar zuciya yasauke bayan yagama cinyewa,
Yayi hamdala tabbas akwai banbanci sosai yanayin nata dana wancan daya siya,
Abunda yafi burgeshi daga gareta nutsuwarta,
Tabbas yarinyar tanada nutsuwa domin komai takeyi ya lura tana yinsa cikin taka tsan-tsan,
Ajiyar zuciya yaqara sauqewa akaro na biyu,
Saannna yatashi yafita zuwa cikin gidansu."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial23 Chapters
Core Worlds
A mysterious alien ship approaches earth. Its mission to Initialize and Seed the planet. But what does that mean. Invasion? Just visiting? Alien virus? 10 years later: The Alien invasion? Nope. Schools became Co-ed/Co-ET. Elves? good cheerleaders. Friendly port of call? Orks and Dwarves love Microbrew. Animals turning into large killing machines? We hunted it. No tag limits. Good barbeque too. The Alien virus? Oh. That. They gave us nannite Cores attached to our spine. No biggie. It made us stronger and faster though. Only if you are 18. Seriously. Follow Brian Hunter as he navigates through life as a young man, Discover new worlds, and maybe get an Elf girlfriend.
8 93 - In Serial10 Chapters
Hound of Ériu
Gaia, a land of adventure, where heroes emerge and create legends of their own. The land where Gods roam and myths live. Lewis finds himself in this land after his untimely death. This is Lewis' legend. This story will be written in my free time so there is no set release times or schedule. I will be using curse words and other such words so if you want a nice and polite story, this isn't it. If you have any suggestions towards the story either leave it in the comments or send me a message.
8 69 - In Serial24 Chapters
EDIT
"People live. People die. Monsters can't do either. I'm a monster, you can call me Joshua, it's nice to meet you." [participant in the Royal Road Writathon challenge] Waking up after ten years to a modern world revolutionized by the internet, Joshua needs to learn how to navigate society again. Best place for someone who looks like him to do that? Let's see if Highschool is still a thing. Old friends, enemies, Joshua really needs to reconnect. Ten years is a bit long after all, maybe they have let down their guard. There must be just so much killing to do! And maybe, just maybe, someone will have figured out how to kill me by now. One can hope. Hello! This is my first public work, so rip me to pieces. That's right, critique please.
8 183 - In Serial12 Chapters
A Helpful Resource
This is a book that will tell you basic grammar rules. I have books that will give you tips on verbs, adjectives, pronouns, punctuation, and transition words as well. I will definitely write a book to help with every genre! Happy writing.
8 128 - In Serial56 Chapters
Serendipity | YKH
(n.) finding something good without looking for it. Park Jin Hee experience struggles in her life. She keeps on finding for a reason to stay but once she gave up she found something that changed her life.
8 172 - In Serial21 Chapters
I have reach boundless infinity as a good for nothing. Now I want to restart in another world being the ultimate genius.
Just a random story guys. Just another of my OP stories but this time with cultivation.
8 314

