《ƘADDARAR RAYUWA》Q Page 5
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 5
Bayan yara sun shiga sun kwanta mama da baba sun shiga d'aki, zama tayi bakin yar yololuwar katifansu tadubi baba tace"
Amman baban sawwama baka ganin mubar yarinyarnan taci gabada sana'arta tunda aqofar gida take?
Saimu kula sosai mu ringa sanya idanuwa akan yanayin zamanta awajan sannna mu gargadeta akan kada tabar qofar gida, duk wani abunda zatayi saiya zamana tana zaune aqofar gida, komai zatayi kuwa kada tawuce qofar gida tana yinsa awajan,
Sawwama tanada zurfin tunani na tabbata ta zauna aqofar gidanne saboda tasan tanada tsaro anan sannan kuma kusada gida, kuma kaima abubuwan sunayi maka yawa ga dawainiyar karatun yara gata gida,
Wani lokacin idan an korosu daga makaranta sukan ebi lokaci azaune agida,
Tunda tafara baba bai tanka mataba yayi shiru kawai yana sauraronta,
Saida tayi shiru alamun tagama yaja yakwanta, dubansa tayi yanyinsa ya canja,
Duk sai taji bbu dadi gani takeyi maganartane ta sanyashi cikin wani yanayi,
Nisawa tayi sannan tace baban sawwma kayi hakuri bawai na furta hakan bane dannuna cewa ka gazaba,
Shidai harta gama baice komaiba yadaiyi shiru yana sauraronta,
Ganin haka yasa itama mama ta kwanta batarefa taqara cewa komaiba, bata dade da kwanciyaba bacci yadauketa,
Shikuwa baba ba bacci yayiba tunanine fall cike a ransa hadeda zullumi,
Ya dade cikin wannan halin kafin daga bisani ya fawwalawa Allah komai ya kwanta."
Washe gari da asuban fari kamar kullum baba yatashi jin kiran assalatu kafin shiga sallah,
Mama yatasa,
Sannan yafita domin kama ruwa yayi alwala,
Itama mama fita tayi tashigo d'akin su sawwma tatashesu,
kamar kullum bayan mama tatashesu tafita sawwama taqara bin kan qannenta daya bayan daya tatashesu,
Waje suka fita alwala sukayi babansu yajasu sallah bayan sun idda sauran yaran suka koma cikin d'aki
sawwma kuma da halima suka jira awajan har gari yadan fara wayewa sannan suka hauyin ayyukan cikin gida,
Sanda suka gama komai sannan mama tafito hannunta daukeda wani dan kwano kallon gidan tayi gidan yayi qalqal ya sharu yayi kyau,
Miqawa sawwama kwanon hannunta tayi sannan tace ga wannan,
Cikin ladabi sawwama ta sanya hannu ta kar6a gari tagani acikin kwanon,
D'agowa tayi ta kalli mahaifiyarta tana neman karin bayani ganin haka yasanya mama tace"
Garin dawane aciki kisanya ruwan zafi yanzu akan wuta sai ki jefa mana dan wake dashi zamuyi karin kumallo,
Toh sawwma ta amsa dama tadade da sanya ruwan zafi saboda batada tabbacin abunda zata girka,
Advertisement
Kanwa da kuka sawwma ta sanya ya kwa6a dankwaken cikin qanqanin lokaci ta gama jefa musu dan waken,
Sannan mama ta aiki halima tasiyo manja da barkono aka soya manja sannan aka dak barkonon,
amarmarce suka ci dan waken saboda sukan d'au tsawon lokaci batareda sun sami cikakkiyar karyawaba."
Bayan sun idda karyawan sawwama taqara tattara kwanukan ta wankesu ta kifesu abaranda,
Sai da hantsi sannan baba yafito zai fita,
Sawwama ya kwalawa kira data fito ya ciro kudi a aljihunsa yaraba kashi biyu yamiqa mata daya sannan ya maida daya aljihu,
Kallonsa sawwama tayi saboda tana buqatar qarin bayani,
Batakai ga tambayarsa abunda zatayi da kudinba yace" kudin sana'arki na jiya na raba kashi biyu zan fitada rabi abunda ya sawwaqa saina sara na zagaya muga abunda Allah zaiyi,
Miqa masa sauran tayi tace baba kahada duka kayi sarin dashi sabodani bbu abunda zanyi dashi,
Katseta yayi da fadin A'a ai ban kaiga qarasa bayaninba,
Sauran kisiyo waken suya kiyi sana'arki dashi,
Tunda dai nan kusane qofar gida kizauan anan qannenki idan sun dawo daga makaranta saisu zauna awajan suna tayaki,
Nazauna nayi tunani mamana sannan nayi addu'a Allah yasa sana'arki tazame mana allhairi,
Amin ta amsa barina dauko barona nafita,
Allah yayi miki albarka
Da amin taqara amsawa,
Sallama yayiwa mama yafice"
Ita kuwa sawwama tatashi tafara shirin yin sana'arta,
Sana'a takar6i sawwama cikin qanqanin lokaci abu ya kankama,
Ganin haka yasanya mama tafara yimta wasu abubuwna kamarsu kantu, aya da gyada ana ajiyewa agefenta,
Sannan kuma idan halima tadawo daga school agefenta saita fitoda kashin taliya itama tana siyarwa,
Awannan lokacin gidansu sawwama yadan samu budi sun samu sauqin al'amura sosai saboda basa rasa abuncin safe rana da dare,
Koda ace basu daura abuncinba, abunda suka dafa a sana'arsu sukanci suyi handala awad'annan lokuta baba yasamu sauqin al'amura,
Abunda yafita ya nemo qara jari akeyi dashi sukuma wanda su sawwama suka kawo sai asamu abunda za'a daura."
Sannan awari dan kadan daga ciki sanya a asusu wani lokacin hamsin wani lokacin qasama da haka.
Saboda ko buqatar kudi zata taso batareda an shiryawa hakanba."
Alokacinda sawwama tacika shekaru sha biyar cif-cif alokacin girma yafara bayyana awajanta,
Alokacin tafara al'ada koda tafara yazo matada yan matsaloli amma sai baba yatafi wajan wani makwabcin bababnsa wanzami yabashi wani icceh
Aka dafa aka jika mata sannan tadan samu sassauci,
Har izuwa lokacin sawwama tana kan sana'arta, yayinda bata zuwa makaranta ta boko kota islamiyya itada iyayenta sunfi maida hankali akan sana'arta ba karatuntaba."
Advertisement
____________________________________
Tattara kayansa yakeyi cikin qaguwa dasauri,
Amma koda saurinda yakeyi wajan hada kayan bazai hana. yanayinsa na nutsuwa yanuna ba,
abokinsa dake gefensane ya dubeshi, wanda shi akwance yake baimada niyyar tashi balle yayi qoqarin hada kayansa,
Cikin jin haushi yake magana yana fadin sadam sai kace wanda kake kan qaya?? Wai korarka akeyine?
Haba-haba ai zaka jira ko zuwa gobene kafin ka wuce zuwa gida,
Wanda aka kirada sadam baice uffan ba har yagama shirya kayansa tsaf sannan yajuyo yadubi abokinnnasa
Sai alokacin ya bude baki yayi magana yana fadin
Eh aii akan qayar nake kasandai bazan zaunaba nagana exam bbu abunda zan zauna nayi amakaranta,
Hasalima ni bawai inason zaman hostel bane kasani,
Tunda narigada na gama exam kagani bbu abunda zan jira gida zan wuce,
Gyada kai abokinnasa yayi hadeda fadin ok toh shikenan aii
Idanna dawo zan shigo,
Gyada kai sadam yayi sannan yace toh saika dawo,
School back dinsa yadauka ya maqala abayansa sannan yasanya hannu ya jawo trolly dinsa yayiwa abokinsa sallama yafice,
Yana fita ya tsari mashin har zuwa cikin gari har qofar gida mashin ya saukeshi ya sallami mai mashin
Yaja trolly dinsa zuwa cikin gida
Gidanda yanufa baida girma sosai amma yanada kyau dai-dai gwargwado kana kallonsa gidane na masu dai-dai kar6i wanda sukefa rufim asiri dai-dai gwargwado,
Tura qaramar qofarda take jikin gate yayi zuwa cikin gidan,
Da sallama yashiga wata yar matashiyqr maga yasamu zaune a falo wacce bazatafi shekaru arba'in ba zuwa da uku,
Murmushi tasaki na ganin dannata sannan
Tace"
Sadam ashe kana hanya,
Eh yafad'i sannan yaqaro ciki,
tsugunnawa yayi yana gaidata ta amsa hadeda riqo hannunaa tana fadin sannu yaya jarabawar??
Momy jarabawa Alhmdulillah yafad'i yana murmushi, itama murmusawan tayi sannan tace toh Allah ya taimaka da amin ya amsa sannan ta umarcshi daya tashi ya shiga daga ciki ya huta,
D'akinsa ya qarasa yazauna ya huta sannan yafito wajan mahaifiyarsa,
Koda yafito tadin school da exam kawai sukeyi,
Sai yamma liqis mahaifinsa yadawo lokacin sadam yana zaune ad'aki
Saida suka fita sallar magrib sannan yahaduda babansa,
Anan suka gaisa,
Bayan magrib suka hadu dukansu a palour akan dining dancin abunci,
Saida suka gama sannan sadam yadubi babansa cikin nutsuwa yace dady gaskiya ni idan aka dawo hutu bazan zauna a hostel ba,
Sai dai asiyamin mashin naringa zuwa ina dawowa zaman hostel dinnan babu dadi,
Dafa kafadarsa mahaifinsa yayi sannan yace' naga alama daga gareka saboda gashi dukka rame, hutun sati nawane? Dady ya tambayeshi,
Sati Biyu sadam yabashi amsa atakaice, dadyne yacw toh hutun babu yawama sanann yaci gaba da fadin in sha Allah cikin week dinnan zan siya maka mashin,
Momy wanda tunda suka fara maganar bata sanya musu bakiba sai alokacin ta amshe da fadin A'a dadyn sadam adai barshi yazauna a makaranta idan yana can zaifi karatu yanda ya kamata,
Girgiza kai dady yayi sannan yace banqi takiba amma shima abi tasa saboda shi yake karatun shi yakejin abunda yakeji,
Tunda bayason zaman makarantar gara ace yazauna agidan,
Shiru momy tayi bawai dan ranta yasoba,
Haka suka gama cin abuncin kowa yatashi yakama gabansa."
——————
Waye Sadam??
Sadam d'ane ga Alhaji usman balli Wanda yanzu haka yakai matsayin director, mahaifiyarsa kuma hajiya sajida principle ce awata government school, yaransu shida sadam shine na farko sai qaninsa maibi masa salim, wanda ynzu haka yana makarantar kwana secoundry school, sai qannensa yan biyu hasssana da hussaina masu biwa sirlim sai hanif sai autarsu hanifa,
Alhaji usman da hajiya sajida basuda buri daya wuce yaransu suyi karatu mai zurfi har indai akan karatune toh kome sukeso zasu siya musu,
Sadam shine dan Fari yanada hankali sosai
Komai nasa anutse yake yinsa dai-dai da maganarda zata fito abakinsa zaka jita anutse take sannan kuma akan hankali,
Baida irin rawar kai kokuma rashinji irinna samarin zamani dukda kasancewarsa mahaifansa sunada dan abun hannunsu wannan bai dameshiba,
Hasalima shi rayuwarsa yakeyi kamar kowanne dan adam,
Yanayinsa d'abi'unsa duk masu kyaune."
Sai mahaifiyarsa ita kuma tasanyawa kanta kyamar talaka dakuma wanda baiyi karatuva, dan acewarta mutuminda baida ilimi jahilci yaci qarfinsa baida marava da dabba."
Wwannan Kenan,
Bayan kwana uku dayin wannan maganar da mahaifinsu ya 6aro masa sabuwar mashin dall a aleda jincheng rover,
Sosai sadam yayi murna da kyautar mahaifinsa,
Aranar najeeba yazo masa,
Ad'aki yasameshi bayn yashiga sun gaisa da momy yawuce dakin sadam,
Akwance yasameshi yaqarsa yazauna gefen katifarsa yana fadin kai mutumina kullum kana gida baka dan fita ka zaka ko nan dacenne??
Murmusawa sadam yayi yace kasan ban cika son yawoba,
Amma garada kazo yau jirani nashirya saimu fita,
Miqewa sadam yyi yashiga wanka yafito yashirya tsaff,
Yace muje koh?
Miqewa najeeb yayi suka yiwa momy sallama suka fita.
Alokacin sadam yake nunawa najeeb mashin din da babansa yasiyo masa,
Sosai najeeb yayi murna ko babu komai sun sami na fita yawo,
Yanzun hakama akan mashin din suka fita,
Sun zazzagaya wajaje dayawa,
Sannan daga bisani suka tsaye gefen titi najeeb yaga mai suyar awara zai siya."
To be continued
Zaynab Alabura
✔️ote
Comment
Share
Follow @zeeyybawa #wattpad
Advertisement
- In Serial35 Chapters
On the Edge of Eureka
Currently on hiatus because college is hard. I promise it's not abandoned! Eleutheria, the crown gem of the Solar System, has stood tall for nearly two dozen centuries. Forged in a plague-stricken, war-torn wasteland and tested by fire for hundreds of bloody years, Eleutheria has learned how to survive calamities that would have decimated lesser nations. Its power waxes and wanes, but the empire itself is as steadfast as the Moon; it's an inscrutable, indestructible force of nature no human being could ever hope to stop. But under its glimmering exterior lies a tangled web of secrets and lies, a deadly and decadent court, and corruption that runs from the kings to the kingpins. As its leader loses her grip and opposing forces grow ever stronger, the threat of civil war looms closer and closer to home. The whole country is a chemical reaction waiting to happen, and all it needs is a catalyst. Acidalia Cipher is that catalyst. Cover designed on Canva, images are Creative Commons stock photos from Pexels and Unsplash.
8 188 - In Serial15 Chapters
Tom
A boy Tom get's reincarnated in an alternate reality.
8 60 - In Serial11 Chapters
Oceaniq
One century ago the world was changed. In forty terrible days and forty terrible nights the oceans rose to swallow the land. Now only the sea and the island nations remain.Naoto Aequitas knows that he is... different. A scaleless mer, he was raised by his father on the outskirts of an underwater nereid city. He knows the ins and outs of his corner of the ocean and has never met another nereid like him.Charles Denali grew up around boats. Part of the second generation of humans born after the Second Flood, life in one of the smaller island nations isn't easy - especially when your luck is as fickle as Charles's.When they both end up stranded on a mysterious island that's home to a hungry amphibious creature, they must work together to defeat it and find a way home. But being stranded on a deserted island with a monster is the least confusing thing about their new partnership.
8 198 - In Serial24 Chapters
Hero of Naught
The future is here. A century after the human-A.I. wars, the two races have settles together in a country of peace. From their mutual cooperation, science has exploded once again into a revolution. At the forefront is the newest and most advanced game to ever exist, Everlife. Plat was a senior in the academy when he first began his adventures into the game world. After years of suffering from his betters, he now had a chance to shine in a world where everyone was equal. Unless, his troubles follows him into the world. And Everlife isn't just what it was advertised to be. Will Plat survive in both the real world and the game world as he struggles against his oppressors? Or will he fall into corruption and take back what is owed him?
8 85 - In Serial30 Chapters
KA THINLUNG HMUTU SEASON 1 (Complete)
he story hi 2021 a Facebook Gayrobawm a ka ziah min tawn leh ka suangtuahna in kawp a ka ziah chhuah ani e..
8 90 - In Serial61 Chapters
Déjà vu (Epistolary) ✔️
An EpistolaryStarted: June 2022Finished: June 2022
8 114

