《ƘADDARAR RAYUWA》Page 4
Advertisement
QADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Zaynab bawa
Follow on
Page 4
Da asuba babansu da kansa yatashesu suyi sallah,
harda qananun yaran kowa sanda yatashi babansu yajasu sallah suka gabatar, addu'oi yaketa yimusu kala-kala akan Allah yakawo musu dauki cikin lamarinsu dakuma kariya cikin rayuwarsu, byan sun idarda salla sauran kuma suka koma d'aki itakuma tafito tafara share-share na gida da wanke-wanke da sauran ayyuka kafin mahaifiyarta tafito tagama komai halima tana tayata suka hade cikin gidansu tass,
Dama daii sukam ba daga nanba sunada talauci kam gashi gidannasu na talakawane kurmus amma sunada tsabtar gaske komai masu ataltale yake,
Duk rashin kyawu na gidan amma idan suka shareshi suka taltaleshi saiya baka sha'awa."
Mamansu tafito lokacin suna surfa gero wanda zasuyi kunun karyawa,
Sannu tayi musu suka gaidata sanna sukaci gabada aiki, kicin tawuce sun shareshi tass-tass sun daura ruwan zafi akan wuta,
Suna gama surfawa suka bushe suka wanke,
Barshi sukayi yadan bushe sannan suka dakeshi cikin qanqanin lokaci suka gama,
Aka dama kunu mamansu tabasu naira ashirun suka siyo sugar,
Dalam-dalam haka sugan tayiwa kunun amma ahakan sukasha domin rabonsu da samun karyawa mai kyau kamar hakama an d'an dauki lokaci,
Sai dai idan babansu yasamu ciniki mai kyau sannan ya siya musu koko da qosai na karyawa."
Da wuri mama tagama shirinta tsaff na fita anguwa da hindatu kawai tafita tabar sauran agida sanda taja kunnen sawwama akan takulada qannenta,
Sannan ta jaddada mata akan kada tabarsu da yunwa dukda tasan cewa bazata barsunba amma taqara tunasarda ita, akan ta dafa musu shinkafa,
Tana fita kuwa kamar jira sawwma takeyi tashiga dakinda babansu yake ajiye baronsa yadauko baqar leda,
Shinkafa ta gwada tiya biyu tafice, domin aiwatarda nufinta da takwana dashi cikin ranta,
Shago tatafi can ta aunar sannan ta auno mudun waken suya da duk wani abunda zata buqata tadawo gida,
Gyara waken tayi takai markad'e ta tace tadaura, wasu dan lokuta kadan tahad'e awaranta, tazauan ta soya, miyar jajjage tayi ta zuba akai ta juye a bokiti tafita,
Advertisement
Aqofar gida tazauna dake gidansu bakin titine hanyar wucewar jama'ane, kuma akwai shaguna agefen titin,
Lokaci kadan tadauka tafara ciniki, lokacinda baifi awa biyuna gefen gidansu akwai almajirai, haka sukayita siya mai goma mai biyar tana zaune anan harta siyar aqofar gida bata motsa ko'inaba,
Batayi zaton qarewarsa dawurina amma ganin yaqare yasanya,
Bata zaunaba takoma kasuwa ta auni wanda yafi nada yawa,
Abinci tafara daurawa qannenta domin gargadin mahaifiyarta tadace kada tabarsu da yunwa,
Dake tanada zafin nama wajan aiki, lokaci qalilan tadauka tagamawa qannenta abinci, sannan tafara aikin awara, har yamma taci mata bata gamaba,
Tunani tafaryi tasan har indai tayi tazuba cikin bokiti irinna datsu ba lallai tayi ciniki ba saboda yamma tayi, wata dabarace tafado mata dan haka tahad'a murhu aqofar gida tafara suya,
Abundai alhmdllh sai dai ace sam barka tafara ciniki dake wajen akwai karancin masu abun siyarwa, kuma akwai yawan shagunaan sana'a, har magrib ta risketa awajan tana suya tana cinikinta.
Dake baba shima yafita dawuri bai san mai yake faruwaba,
Yafice zuwa gidansu daga nan yabiwa mama yagaida nata mahaifan, sannan suka kamo hanya,
Ana kiran magriba mama da baba suka doso layinsu daga nesa suka hangi sawwama zaune bakin murhu da yara akanta suna jira azuba musu,
Ganinta haka mamaki ya kamasu babu wanda ya'iya magana acikinsu suka shige ciki,
Ita kama batama luradasuba kanta yayi zafi wajan saida awara,
Sanda taga anfito a sallah sannan tatura yaro yakira mata halima zata dawo yin sallah,
Halima tafito ta kar6eta, ita kuma tatashi tanugi gida da sallama tashiga gida kanta tsaye batareda wani tunaninba,
Aqofar d'aki ta samesu alamun sun idda sallah, gabantane yafadi ganinsu sun dawo dan batayi zatoba, ad'arare ta qarasa kusa dasu tana fad'in mama, baba sannunku da dawowa,
Sannu baba ya amsa, mama kuwa batama kulataba dauke kanta tayi daga kallonta, sawwama tana kallon yanayin mama jikinta yayi sanyi sosai, babane ya katseta da fadin je kiyi sallah kidawo zamuyi magana,
Miqewa tayi har tana tuntu6e ta dauki buta tashiga bayi tayi tsarki tafito tayi alwala ta gabatar da sallah,
Advertisement
Koda tadawo agefe tazauna cikin nutsuwa tace" baba gani"
Kallonta yayi cikin nutsuwa yace" mamana me nake gani?
Mamana tallan kika koma yi?
Mamana bakiga illar wannan tallar bane?"
Mamana talla tayiwa rayuwarki illa amma baki fahimci hakanba, mamana kinason qara jefa kanki cikin wani halinne?
Ko shawarata kona mahaifiyarki baki nemana lokacinda zaki fara wannan abun,
Mamana idan abunda nake kawo muku yagazane zan qara qoqari,
Nasan hakuri kawai kukeyi da duk wani abunda nake kawo muku,
Zan qara qoqari inakawo muku fiyeda na baya,
Mama wacce tunda baba yafara magana batayi maganaba sai yanzu tace"
Aiso take ta nuna cewa iyayenta sun gaza sun kasa daukar d'awainiyarta bari tafita itada kanta ta nema,
Mama taqarasa maganar cikin zafin raii,
Girgiza kai sawwama tahauyi hawaye na zuba a idanuwanta,
Cikin muryar kuka ta zakud'a kusada mahaifanta tafara fad'in,
Baba dan Allah kuyi hakuri wallhy ba nufinaba kenan,
Baba kokadan ban raina abunda kake kawo manaba,
Baba a kullum tausayinkane cikin raina jiya ban iya runtsawaba saboda tunanin halinda jiya kadawo aciki,
Baba banyi haka dan 6acin rankaba nayi hakane dan taimakonka,
Juyawa tayi wajan mama tace mama dan Allah ku yafemin,
tana fadin haka taqara sanya kuka bata ta6a tunanin cewa mahaifanta zasu dauki zancen hakaba da bata faraba, dan babu abunda taqi jini irin 6acin ransu,
Kukanda takene yasanya duka jikinsu yayi sanyi koda bata fadiba sun san halinta sun san halin d'iyarsu sunsan sawwama bazata ta6a yin haka danta nuna cewa mahaifanta sun qaza ba, tayi hakanne kawai danta taimaka musu, amma dole su nuna 6acin ransu saboda ta fahimci halinda takeson jefa kanta aciki,
Da halinda tafad'a abaya, sannan su sanya mata tsoron wanda zai faru nan gaba,
Jikinsu yayi sanyi sosai suka gaza magana
Ido kawai suka tsira mata tana kukanta babanta yarasa mai zai furta shidai yana tsoron yaqara barinta talla akaro na biyu,
Dakyar ya'iya daurewa yafara fadin naji na fahimceki mamana, ina gudun qara faruwar abunda yafaru abayane, saboda kowani mahaifi zaiso kare d'iyarsa kada wani abun yasameta, ni nagaza akaro na farko banso nakara bari wani abun yasameki, tunda kinga ni nakasa kareki kiyi haquri ki taimakeni wannan karon na kare rayuwarki,
Zuciyata bazata iya juran wani abun yaqara samunkiba."
Girgiza kai kawai sawwama takeyi,
saida tadan tsagaita kukan sannan tafara fadin mama baba kuyi hakuri dan Allah ku yafeni bazan sakeba,
Tausayintane yaqara kamasu,
Har cikin zuciyar mama take tausayin diyarta kuma tana sonta sosai akullum takalli d'iyarta ta tuna abunda yafaru da'ita takanji tausayinta da soyayyar diyarta cikin ranta,
Shikenan yawuce Allah yayi miki albarka, amin ta amsa da dishasshiyar muryarta."
Suna zaune awajan sukaji kiran sallar isha'i hakan yayi dai-dai da shigowar halima,
Ta miqawa sawwama kudin cinikin da tayi tawuce domin yin alwala,
Daukan kudin sawwma tayi tamiqawa mahaifinta batareda tace komaiba tamiqe tana mai qara basu hakuri tashiga d'aki ta gabatarda sallar isha'i sannan tazauna tunani,
Abunda yafaru abaya yake tariyo mata tabbas tasan cewa dole hankalin mahaifanta yatashi sosai duk da cewa har yanzu bawani shekaru garetaba amma zuwa yanzu tafara gane illar da rayuwarta take ciki,
Abunda yafaru abaya ne yake tariyo mata lallai ta tabbata wannan mutumi ko wanene shi babu d'igon imani cikin zuciyarsa, idan akayi la'akari da shekarunta a wancan lokacin,
Nisawa tayi afili ta furta kalmar Allah ya'isa wanda tun lokacin data fahimci illar yayi mata take furtawa,
Akullum yafad'o mata sai tayi masa Allah ya'isa,
Kuma tanada yaqinin ako'ina yake wata rana Allah zai amsa addu'arta yayi mata sakayya akan abunda yayi mata,
Ta tabbata idan Allah yatashi kamashi sakayyarda zaiyi masa sai yafi wanda yayi mata munin gaske,
Hawaye taji yana zuba akan kumatunta ta share afili taqara furta ya Allah kamar yanda ya sanyani da mahaifana kuka,
Ya Allah ka sakamun,
Jingunuwa tayi da bango haka har bacci yadauketa azaune,
Sai da kannenta suka shigo sannan suka tasheta tagyara kwanciyarta takwanta saboda gajiya nan da nan bacci yaqara dauketa."
Asuba tagari
Lockdown🔐
To be continued
Zaynab Alabura
✔️ote
Comment
Share
Follow
💞💕
Advertisement
- In Serial14 Chapters
Lyca: Rise of Asura
In a time where power is only granted to noble and rich. Betrayed by his kin left to die in an abandoned town. Vengeance was the only thing that kept him alive it was all he could think of to keep himself going. Power he needed power to complete his revenge. Those trampled on him to reach the top shall beneath his feet. To have his revenge he basked in the darkness and found a power that is only mention in eras long pass. He would awaken this power and unleash its wrath upon them...... They destroyed his home, his village. That's what his father always told him "One day my boy you will be the leader of our small village." until that fateful day the village was attacked by a group of mercenaries. His father had told him to take his sister and run. That was all he could do for he was weak. He vowed to never let anyone he loved ever died again. After all losing your parents at the age 10 is a most dreadful pain..... Legend, you can say a prophecy speaks of a child born of this world. With the birth of this child comes the birth of a power once thought lost. A power only mentioned in legends. None of this age has seen such power, a power to liberate and form the earth to his desire. With the birth of the child also comes an evil. Darkness in one of its most purest forms to conquer the world. The fate of this world lies sole in the hands of this child. You don't believe in prophecies you, when that day comes you will remember my words for this child fails the prophecy also says it will bring about about the birth of a god.....
8 169 - In Serial128 Chapters
Absolute Divinity (JJBA)
When you're given the chance to bring prosperity to the entire world, would you deny it because of the horrible person you are now taking over? "It takes a fool to underestimate true justice. The Heavens have Spoken, for I am the bringer of peace for this world!" A look in a somewhat less-malicious SI!Dio's tale of deception, family and some bizarre stuff.
8 68 - In Serial18 Chapters
LUCID DREAMS︱FEZCO
─── 𝙇𝙐𝘾𝙄𝘿 𝘿𝙍𝙀𝘼𝙈𝙎❝ 𝘺𝘰𝘶'𝘳𝘦 𝘵𝘩𝘦 𝘰𝘯𝘭𝘺 𝘨𝘪𝘳𝘭 𝘪𝘯 𝘮𝘺 𝘥𝘳𝘦𝘢𝘮𝘴, 𝘣𝘢𝘣𝘦. ❞☆*.☽ Eva's life consisted of sex, drugs, and alcohol. That was until she moved and met a certain drug dealer. ─── ・ 。゚☆: *.☽ .* :☆゚. ───
8 137 - In Serial64 Chapters
History's Strongest Disciple Fanfiction
I love the Manga and Anime so much that I wanted to put a bit of myself inside it, It might come as a stupid power fiction, but I did my best to make it at least a bit amusing and a bit more believable. The plot will go sidelines with the occurrences from the original story and do my best to not side track the story, but I have to warn that at some point the story goes highwire. This is the Story of Yashin, whom transfers schools at the same point as Miu, ending in the same school as Kenichi and ending falling in love with a certain someone. There's not much going on, but I think the start is rather good.
8 74 - In Serial20 Chapters
MY YOU || TAEKOOK
Jeon Jungkook, who is a doctor by profession, also happens to be a single parent of a baby boy.He was getting used to live only for his son until.......One day, Jungkook had to take the little munchkin with him to his workplace and the very same day, their new department head joined the hospital.
8 161 - In Serial15 Chapters
kleinsen vs treebros
I dislike treebros because it makes no sense. blah, blah, blah, AU's, I KNOW! it's just my opinion.kleinsen is canon, could happen, and is adorable.I don't want to offend anyone and I respect everyone's opinions. butConnor 👏is👏Dead👏dEAL wiTH it![edited 7/15]
8 116

